Showing 15001 words to 18000 words out of 78655 words
Chapter 6 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
min
sannan kiyafe min."
cikin rashin fahimta ta ce
"Me kake fad'a ne kam mene ne? kayi min yan da zan gane wani irin hukunci a ka yanke maka
haka me ka aikata haka akayi maka irin wannan mummunar hukuncin haka!."
"Fyad'e na aikata, hukuncin fyad'e a ka yi min ke ma kiyi min naki kuma dan Allah idan kika yi
min ki yafe min."
wani irin waro ido Maman Zeey tayi tare da d'an ja da baya.
a hankali Kamal ya matso yashiga yi mata bayani cikin sanaki, yadda abun ya faru da zuwa
gidan su Naseeba yanzu da suke akan niman aurenta da yake har zuwa yau dayakai kansa
kotu a ka yanke masa hukunci.
hawaye tashiga sharewa kana ta matso taruko hannun Mukhtar ta ce
"Nayefe maka Allah ya yafe maka, duk da ina da tabbaci da yakinin yafiyar ubangiji a gare ka,
tun da har kabi ta hanyar da zai yafe makan, Allah ya dad'a tsare ku da sharrin shaid'an me
ingiza mutum izuwa ga halaka."
wani irin dad'i ne ya mamaye zuciyoyin su ganin yan da ta fahimce su cikin sauki...
kwanan Mukhtar biyu a asibitin a ka sallame shi,babu wan da yasan dalilin da yasa a ka
kwantar da shi a asibiti ko 'yar uwarsa na jini wato Zeey har yau bata san dalilin kwanciyar nasa
ba, ko ta tambayi dalilin sai dai ace mata hatsari yayi duk da kuwa shatin bulala da take gani a
jikin sa sai dai bata kawo komai a ranta ba, a ranar kwanan sa na biyun a ka sallame sa.
A cikin satin manya suka shiga maganar auren shi da Naseeba, hamaifin Naseeba ya aminci da
batun auren sakamakon kiran Naseeba da ya yi ya tambayeta tana sonsa bata da zab'in daya
wuce Eh dan hakan ne kad'ai take ganin mafita cikin rayuwar ta da take wa kallon ragegge.
aka kuma sa aure wata biyu masu zuwa, har kuma yau babu wan da yasan da batun fyad'en da
Mukhtar ya yi wa Naseeba in ban da Kamal da SEEDRAH sai kuma Maman Zeey kasan cewar
mahaifin Mukhtar d'in baya raye 'yan uwan mahaifin su ne suka wuce gaba kan maganar auren,
sai dai har yau Naseeba taki ta bawa Mukhtar da ma ko da sau d'aya ne su had'u. ko da sunzo
kofar gidan su sai dai SEEDRAH ta fito, dan yanzu tafara rage jin haushin su tun da Kamal ya
bata labarin hukuncin da Mukhtar d'in yakai kansa a ka yanke masa....
yanzu shirye-shiryen biki SEEDRAH ta ke dan ita ke gudanar da tsare-tsaren bikin dan idan ta
Naseeba ne ma kada a yi komai, ita dai a d'aura aure a kaita shine take ganin rufin asirin
rayuwar ta.
bayan watanni biyu aka d'aura auren Naseeba da angonta Mukhtar, ta tare a cikin gidan su
Mukhtar d'in a d'aya shashin dake bayan na Maman Zeey.
a ranar da yamma kowa ya watse yarage Naseeba da SEDDRAH sai kawarsu Nabila
kasancewar gidanta babu nisa dana Naseeba'n. har wajen sallar isha suna tare da Naseeba a
shashinta.
Nabila tayi ta zolayar Nasiba cikin zolayar da tun d'azu take ta mata ta ce
"Yau yarinya zaki gane shayi ruwa ne idan kika shiga hannun wannan bawan Allah'n, ba haka
kukayi ta min dariya ba lokacin nawa,to ni yanzu anshani na warke har na saba yanzu babu
wani ragowar zafi sai dad'i."
bugu SEEDRAH ta kai mata tana fad'in
"Allah ya shirye ki Nabila yanzu dai kin zama 'yar iska."
dariya ta yi ta ce
"Babu wani iskance ai gaskiya ce saura kema ki shigo hannu, ke kam nasan sai makota sun
kawo miki d'auki sabo da tsabar tsoro irin naki."
"Allah ya sawake to ni anfad'a miki ma zanyi aure yanzu ne tun yayu na basuyi ba, kin san ai
gidan mu bi da bi ne,sai Halimatu da Suhailat sun tashi kafin nan na kara girma babu katon
gardin dazaici zalina."
SEEDRAH ta fad'a tana dariya.
Naseeba kuwa shiru tayi bata ce ko kala ba yayin da zuciyarta ke kuna, Nabila bata san komai
game da fyad'en da akayi mata ba tana yi mata kallon wata cikakkiyar budurwace, k'walla ne
suka ciko idon ta.
Nabila kuwa cigaba da fad'in
"Ko shekaru talatin zaki kai kafin kiyi aure ni na tabba a irin tsoron ki sai kin tara makota
SEEDARH, yarin ya kiyi shiri yau fa zaki yabawa aya zakin ta, gobe da safe ina zuwa nakuma
sake yi miki wani gashin dan nasan wanda zaiyi miki a darennan bazai wadatar ba sai an
taimaka miki da safe." ta karasa maganar tana duban Naseeba da tuni idanunta suka ciko da kwalla.
lura da yanayin da ta shiga yasa SEEDRAH girgiza mata kai ta dubi Nabila ta ce
"To tashi ki tafi gidan ki an fad'a miki kowa raguwa ce irin ki zuba ido kiyi kallo zakisha mamaki
aure kuma ba yanzu ba."
"Sai yaushe? ni da nake saran a karshen watannan a ramawa kura aniyarta, yadda mukasha
wuya a auren su haka kuma zasu rama mana."
cewar Kamal da yanzu shigowar su ya sinci cancen a sama yakuma cab'e. Mukhtar nabiye da
shi suka shigo ciki.
SEEDRAH ta hararesa tare da murgud'a masa baki, dama taga take-taken sa tun ba yauba taki
basa fuska ne.
shiko 'yar karamar dariya yayi yadubi Nabila yana fad'in
"Ko ya kikace kawar mu?."
dariya Nabila tayi ta ce "Wlh kuwa ina goyon baya d'ari bisa d'ari."
mikewa SEEDRAH tayi ta d'au gyalen ta da jakarta tana fad'in
"Sai kuyi kuma ai kanku a ke ji."
ta nufi kofa.
Kamal yabi bayan ta. Nabila ma ta mike tana dariya tayi musu sai da safe tayi waje.
a can waje ta iskesu suna ta dirama dariya tayi dan tasan halin SEEDRAH sarai bata kula
samari tun suna makaranta ma irin samarin da ake nacikin aji ita bata sauraran su bare ma har
ta tsaya zance da su, shi yasa da yawan samari suke ce mata wai tana da girman kai ko dun
taga tana da kyau ne, kuma sam abun ba haka yake ba sai in kazauna da ita zaka fahimci halin
ta sassanya kamar ruwan randa, ita dai haka rayuwarta yake da kin kula samari, a cewar ta wai
bata kai na tsayuwa da saurayi ba sai idan yayun ta sun matsa sun bata guri..
Kabir mijin Nabila da yanzu ya iso gurin d'aukar matar sa shima yayi ta taya Kamal d'in kamfen,
ita dai SEEDRAH bata saurare su ba har ya d'au matar sa sukayi gaba.
da kyar ta amince Kamal ya d'auke ta a mashin d'in sa, dan cewa tayi abin hawa zataje ta nima
ya kaita gida bazata hau mashin d'in sa ba. a hanya yayi ta fallasa mata irin son da yake mata
da ke kunshe a zuciyar sa tun ranar da kaddara ta had'asu.
ita dai tana jin sa suna isa kuwa ta sauka ta shige gida ta barsa nan tsaye a kofar gida...
A b'angaren amarya da ango kuwa kamar yanda Mukhtar yasha alwashin samarwa zuciyar
Naseeba salama da cire kiyayyarsa da kuma mantar da ita abun da ya faru cikin kwanakin da
basufi bakwai ba.
ya samar wa zuciyarta nutsuwa had'e da tarin kwanciyar hankali da santsar kauna da soyayya
da kulawar da yake nuna mata, ba shi kad'ai ba har da mahaifiyar sa da kuma kanwar sa.
a yanzu amarya Naseeba zamu iya cewa bata da wata matsala a rayuwar ta dan mijin ta
yazame mata bango majingina, ga uwa uba kular mahaifiyar sa da kanwarsa gare ta.
cikin wata d'aya ta mance da wani mummunar abu yatab'a faruwa da ita, har take jin farin
had'uwar su da shi shine yazamo first night d'in su kamar yanda Mukhtar d'in ya datsa mata jin
hakan a zuciyarta.
sai dai muyi fatan d'aurewar farinciki ga wannan family....
A d'an wannan saikon kuwa Kamal ya sami nasarar sace zuciyar SEEDRAH amma fa sai da
yasha wuya dan sai da yayi dagaske wajen iya sato zuciyar nata,
wani zazzafar sosaiya ce ke gudana sakanin su me cike da fahimtar juna.
SEEDRAH ce zaune tsakiyar d'akin Mama tana duba wasu litattafai, dan wata mai kamawa zata
fara zuwa, Kasu open university, poly d.s, university Kaduna.
Mama ce ta shigo rike da flaks da laida a hannunta ta dire shi tsakiyar d'akin.
SEDDRAH ta ture littatrafan gefe tare da gyara zama ta mika hannu ta d'au cup tana fad'in
"Allah dama yunwa nake ji."
"Me ya hanaki tashi kinimi abincin."
cewar Mama tana zama gefen ta.
ta ce "Mama karatu nake kin san wani wata me kamawa Baba ya ce zan fara zuwa makaranta."
Mama ta ce "Uhm Allah ya nufa." kallon ta SEEDRAH tayi jin yanda ta amsa mata, sai kuma
ta d'au flaks d'in ta tsiyaye ruwan zafi tafe da bud'e laidar, ido tad'an tsura cikin laidar ganin
biredi da lipton da siga ne kad'ai a ciki.
ta ce "Mama ina sauran kayan tea d'in?."
baki Mama ta tab'e kana ta ce
"Sha abunda ya sauwaka ki godewa Allah hakan ma an samu, kijira samuwar na rana ma tukun
dan bamuda tabbacin samun sa."
kai SEDDRAH ta jinjina kana tashiga had'a lipton da siga.
Alhaji Musa wato Baba ne tsaye cikin parlour'n sa, kallo d'aya zakayi masa kasan yana cikin
muguwar damuwa da tashin hankali.
a yaune karshen yarjejeniyar su da banki kan bashin banki daya ci, tun shekarun baya da suka
wuce, lokacin da aka kwashe masa kud'i na farko a accaunt d'in sa, hannun jarin sa yayi kasa
sai da yaje yaci bashin banki kafin ya d'an farfad'o.
gashi yanzu ankuma yi masa mai gaba d'aya, duk kaddarorin da yake da su ya d'auka ya siyar
yazuba kudin cikin asusun sa na banki wasu da baisan ko su waye ba suka kuma kwashe masa
kud'i cikin account duka basu rage masa ko sisi ba.
gashi yayi sintirin banki har ya gaji ba'a gano wad'an da suke aikata masa hakan ba.
gashi yau banki ta nemesa kan kud'in ta daya ci, an kuma bashi wata guda yadawo da kud'in.
hankalin Alhaji Musa bai dad'a dugunzuma ba sai da yaga wata gudan da a ka bashi ya
kare.
da sassafe tun bai tashi daga bacci ba yasami kira daga banki.
ko da yaje banki suke shai da masa sun sami masaniya kan yasai da kaddarorin sa daya ajiye
musu a mazaunin jingina kafin su bashi bashi, suka kuma nuna b'acin ransu a kan hakan,
sannan suka ce masa sun bashi awa ashirin da hud'u yadawo musu da kud'in daya karb'a, idan
kuma ba haka ba zasu sa gidan sa da yake ciki da motar hawan sa a kasuwa yau kuma zai bar
gidan.
cikin matukar tashin hankali yabaro bankin
da tunanin in da zai sami kud'i, bashi da su bashida dalilin su,abun da yayi masa saura daga
gidan da yake ciki da iyalinsa sai motar da yake hawa, hatta abincin da zaici da iyalinsa nason
fin karfin sa dan ma d'an'uwan sa na tallafa masa da abincin.
hankali tashe ya nufi gidan kanin sa Alhaji Sulaiman...........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada
ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
í ¼íµ¿ï¸6
Ko da Alhaji musa ya isa a parlour'n kanin nasa suka yada zangon su, nan Baba yake shaidawa
d'an uwan sa abun da ke faruwa. Alhaji Sulai
ya jinjina lamarin matuka. ya gyara zaman sa ya ce
"A gaskiya wad'an nan 'yan yawu d'in basu kyauta mana ba sakanin mu da su sai sakayyar
Allah, wlh Yaya Musa duka-duka kud'ina da suke cikin account d'ina basu kai kud'in da banki
suke bukata ba, kuma nasan tun da suka d'au zafi ba lallai bane su karb'i kad'an ba, amma dai
muje ko Allah zai sa su karb'a su kara mana lokaci har Allah yasa mu samu a kaimusu sauran." Baba yashiga yi masa godiya da irin rufin asirin da ya yi masa suka d'unguma zuwa banki, sai
dai sukayi rashin sa'a banki sun d'au zafi sosai bisa karya musu yarjejeniyar da sukayi kan siyar
da kaddarorin daya nuna musu a matsayin jingina.
suka ce bazasu karb'a kud'in da ya yi kasa da abunda suke binsa ba, haka suka baro bankin
cike da matukar damuwa.
gidan Alhaji Sulai suka dawo da tunanin mafita, suna zaune sunyi jugum-jugum Abba wato
Alhaji Sulai yad'an zaburo tare da d'aukar wayar sa da yake kara alamun shigowar kira.
ko da ya gamai kiran nasa zaman sa yagyara tare da d'aukar kiran ya kara a kunnen sa yana
amsa sallamar da ake tacikin wayar.
daga cikin wayar akace
"Ina kwana Abba ya gida dasu Ummi?."
Abba ya ce "Lafiya lau sai dai mu yanzu rana ce ba safiya ba, ya harkokin dai?."
ya ce "Alhmdllh."
"To masha Allah Allah ya taimaka."
ya ce "Amin amma Abba yanaji muryar ka haka gidan lafiya dai ko?."
kai Abba ya girgiza cike da alhenin halin da suke ciki ya ce
"Gaskiya kam a kwai damuwa dan har nafara tunanin neman ka ma sai ga kiranka."
bayanin abun da ke faruwa yashiga zayyana masa, daga cikin wayar yad'an ja numfashi kana
ya ce "To basai ya basu gidan da motar ba kawai yaje ya kama haya."
Abba ya ce "Gidan haya kuma Usman? da tarin iyalai ai gidan haya bazai yiwuba Allah dai ya
kawo mana mafita kawai amma muna cikin damuwa."
"Amin." yafad'a a takaice tare da kashe wayar sa.
jugum su Baba sukayi kowa da kalar tunanin sa..
A can kasar Spain USMAN SULAIMAN inkiya S.MAN
kyakkywan saurayi ne ajin farko, yahad'a duk wani abun da cikakken namiji yake takama da
shi, S.Man d'an kimanin shekaru 30 da 'yan d'ori, dogo ne me faffad'an kirji yana da haske sai
dai ba can ba, yana da zubin karfafan maza zaratan maza.
juyi ya yi daga kwancan da yake a kan wata lafiyayyen gado,
yana kwance ruf da ciki kafafunsa suna ririto a kasa yayin da kafafun nasa suke sanye cikin
takalmi sau ciki irin na 'yan kwallo.
yana sanye da kayan kwallo a jikin sa.
cikin rashin damuwa da halin da wan mahaifinsa yake ciki da yanzu Abba yagama sanar masa
abun da ke faruwa, ya wurga wayar can gefe kana
ya mike tsaye.
yashige bathroom dan yanzu ya dawo daga gurin kwallo gaba d'aya a gajiye ya dawo.
bayan wasu mintuna yafito d'aure da farar towel a kugunsa yanufi gaban gado wayar sa ya
d'auka tare da dannawa lambar Abba kira.
Abba da suke zaune har lokacin shi da Baba ya d'aga kiran tare da sallama.
cikin ko oho ya ce "Har yanzu zaman jiran mafita kuke?."
Abba ya ce "To ya zamuyi Usman yanzu a bun da nake tunani shine na had'a kan takardun
kaddarorina muje bankin abasu idan kud'in bai kai ba in yaso sai a cire na accaunt d'ina nasan
dai zasukai."
ya ce "No Abba hakan baiyi ba taya za a yi ka aikata hakan bayan nan gaba idan rai yayi
halinsa kaddarorin namune, baka tunanin hakan zai haifar da matsala yau she kake ganin zai
samu wad'annan kud'ad'en ya biya a ina ma zai samu tukun, bayan ya rigada ya dawo talaka."
Abba ya katse shi da fad'in
"Kai kasan gawan fari ne wato fatan mutuwa kake min ko? kanka d'aya kuwa Usman kasan me
kake fad'a kuwa nafa fiskanci zaman kasar arnan nan nason mai daka wani iri, a shekaran nan
zaka dawo kasar nan dan babu abun da zaman can ke tsinanawa sai rashin daraja, tun da ka
kammala karatun ka kadawo gida imma kasuwancin ne a kasar mu ma anayi, idan aikin
gwamnatin ne ma duk akwai a nan in kwallon ne ma duk anayi, idan ba ka kira ka bada taka
gudumawar bane to ka kashe wayar ka."
baki S.Man ya tab'e tare da d'aga kafad'a cikin halin ko oho ya ce "To Abba ai dai gaskiya ce
kuma ni ba fatan mutuwa nake maka ba,zan bashi aron kud'in idan yana bukata amma da
sharad'in zai dawo min da kud'i na duk san da na duro Nigeria."
da sauri Abba ya ce "To..to...to ba damuwa turo..turo mana."
Abba ya juyo yana duban Baba cike da murnar samun mafita ya ce
"Yaya kaji ko Usman zai bada aron kud'in."
cikin murna mara misaltuwa Baba ya washe baki yana fad'in
"Kai masha Allah Allah yayi albarka Usman kai madallah ai to mutashi muje bankin sai ya turo a
can." kuma tab'e baki
S.Man ya yi kana ya kashe wayar sa dan duk abin da yake fad'a yana ji..
cikin hanzari suka mike suka tafi banki, a can S.MAN yaturo musu kud'in direct bankin.
ranar Baba yasamu yayi bacci mai dad'i dan tun da banki suka sashi