Showing 9001 words to 12000 words out of 78655 words
Chapter 4 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
baki gaba tana wani mammatse ido,
ta ce "Wato shine kuka ki dawowa ko?, sabo da mugunta ai da kuna nan da duk haka bai
faruba."
dariya SEEDRAH ta yi ta ce "Ayya sannu kin ga in da idanunki suka kunbura kuwa."
baki ta kuma turo wa ta ce
"To ba dole ba mutum bayajin dan Allah."
dariya takuma yi mata a kasan ranta kuwa tana ayyana, ita tama sami rarrashi da kima a gun
mijin ta, ga kawar su can abin tausayi, wani katon banza ya turmushe ta batare da biyan sadaki
ba.
SEEDRAH ta ce "Je ki kawo min jakan mu da wayoyin mu natafi, yan zu zamu wuce gida
zazzab'i na damin Nasiba."
"Ayya yanzun tafiya zakiyi madadin kuzo da Nasiba'n nan kafin ku wuce, kibari sai anjima ki
tafi."
Nabila ta fad'a kamar zatayi kuka.
SEEDRAH ta ce "Tap gida zamu wuce yanzu, kin san bamuyi da Mama zan kwana ba nasan
zatayi ta min fad'a gara na koma da wuri."
Nabila ta ce "To shike nan amma yaushe zaku zo?."
ta ce "Sai kin kwana biyu zamu kara zuwa."
Nabila ta d'auko mata jakar su badun taso ba suka rabu tana kwalla.
Gidan su Maman Zeey SEEDRAH ta bi da sallama tashiga gidan, Maman Zeey ta amsa
sallamar da murmushi dan ta gane ta.
bayan sun gaisa Maman Zeey take fad'in
"Shine jiya kika tafi babu sallama?."
murmushi SEEDRAH tayi, Zeey ta fito suka gaisa kana ta mika mata laidar data sako kayan da
jiya suka bata, Zeey ta karb'a taje ta d'auko mata nata da ta barshi a nan, ta amsa tare da yi
musu godiya tayi musu sallama ta fita.
a bakin kofar gidan suka had'u da Kamal, ta d'auke kai tayi gaba..
kamar zaiyi mata magana sai kuma ya yi shitu, yabi bayan ta da kallo har ta b'acewa ganin sa.
sakai ya yi ya shiga gidan.
Zeey ya tarar ita kad'ai a tsakar gidan,
ta gaishe shi ya amsa tare da tambayar ta ina Mukhtar?, dan tun jiya yake neman sa bai gansa
ba, ya yi masa kiran duniyar nan a waya baya d'aga wa.
ta ce "Ai ni rabo na da Ya Mukhtar tun jiya da kuka fita sallar magriba, kai d'aya ma kazo ka ci
d'anwake na baka kushe ba, kuka fita da yarinyar jiyan nan, wai wace ce ita ne Ya Kamal ko me
iya girkin ne ka samo?."
ta karashe maganar tana dariya. shima dariyar ya yi mata yanufi d'akin Mukhtar yana fad'in
"Bari na duba shi ko yana ciki ina zuwa dai."
ya na zuwa bakin kofar d'akin Mukhtar ya tura kofar yajisa a rufe gam, har ya yuya
zai wu ce ta jikin windon d'akin yajiyo karar wayar sa.
ya maso jikin windon tare da zuge glass d'in windon ya leka. can ya hango sa kwance saman
katifa rigingine fuskarsa na kallon sama.
kofar ya dawo ya shiga bubbugawa yana fad'in
"Mukhtar kazo ka bud'e min kofar nan."
sai da ya yi ta bubbuga kofar kamar zai b'alla kafin ya taso yazo ya bud'e masa, baya ya yi ya
koma ya zube kan katifar yana mai dafe kansa.
Kamal ya shigo d'akin tare da mai da kofar ya rufe, ya tako gaban sa yana mai kare masa kallon
tuhuma, hannunsa ya zura cikin aljuhunsa ya zaro agogon Mukhtar d'in da jiya ya gani yafad'o
daga jikin Nasiba, ya mika masa yana fad'in. "Ga agogon ka da ka mance da shi jiya."
kai Mukhtar ya sunkuyar yana mai taunar lips d'in sa na kasa, tabbas yana mai danasani da
nadamar aikata wa yarinyar nan fyad'e, wan da shi kansa baisan ta yan da akayi zuciya ta kaisa
ga ai kata hakan ba, tun bayan faruwar haka jiya yarasa ina zai tsoma rayuwar sa ya shigo gida
babu wan da ya sani ya kulle kansa har yau. Kamal ya dube sa da kyau ya ce
"Me ka aikata kenan kasan girman laifin abun da ka aikata kuwa Mukhtar?!, yaushe ne halin ka
ya juya izuwa halin banza Mukhtar? mu da muka biyo su domin share tantamar mu ko matan
banza ne, shine kai zaka nuna halin banza a kan ta, yaushe halinka ya koma haka ne
Mukhtar?." da sauri Mukhtar ya d'ago tare da ruko hannun Kamal murya a raunace ya ce
"Aboki na kafi kowa sanin halina, kasan wannan ba halina bane, wlh tun jiya da hakan ta faru
nakasa samin sukuni a rayuwa ta, ban san yan da akayi har na kai ga aikata hakan ba,
tabbas na yar da idan mace da na miji suka keb'e guri guda to shaid'an ne cikon na ukun su, shi
ya angiza ni izuwa aikata hakan, wlh ban san ta yadda akayi na sinci kaina cikin aikata hakan
ba."
d'an shiru Kamal ya yi bashakka yasan ko waye abokin nasa, tabbas shaid'an ya sami galaba a
rayuwar sa a karon farko.
ya ce "To sun ce bazasu kyale ba zasu shigar da kara kotu."
da sauri Mukhtar ya ce
"Ina maraba da karb'ar duk wani hukuncin da za a yi min, wata kila hakan zaisa zuciyata tasami
sassauci daga halin da nake jin kaina yanzu, Kamal zuciya ta kamar zata fashe dan zafi."
ya janyo hannun Kamal ya d'aura shi dai-dai kahon zuciyarsa.
Kamal ya jinjina kai cike da alhenin abin kana ya ce
"Bakaci abinci ba tun jiya har yau taso kaje kayi wanka muje kaci abinci."
kai ya girgiza cike da jin zafin da zuciyarsa ta ke ya ce
"Ina jin kunyar had'a ido da Maman Zeey, bansan da wani ido zan kalle ta ba."
Kamal ya ce "Maman Zeey bata san komai ba kuma nasan zata fahimce ka dan tasan wani irin
tarbiyya ta baiwa d'an ta, je kayi wanka kazo muje kaci abinci."
ya mike jiki a sanyaye yashige bayi...
SEEDRAH tana komawa gidan Goggo Larai, ta sami Nasiba har tayi wanka.
babu laifi jikin ta ya dad'a warwarewa suka saka kayan su suka ajewa goggo nata sukayi mata
sallama suka tafi.
sai da SEEDRAH ta raka Nasiba har gida kafin ta wuce gidan su dan ga gida ga gida ne
sakanin gidan su da gidan su Nasiba.
ta shiga da sallama direct d'akin Mamarta ta wuce.........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada
ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690734_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
í ¼íµ¿ï¸4
Mama da ke zaune cikin d'aki tana ninke kaya ta amsa.
SEEDRAH ta karaso ta aje jakarta tana cire mayafin ta ta ce
"Barka da gida Mama ina kwana."
batare da Mama ta amsa gaisuwarta ba ta ce
"Amma ai bamuyi dake zaki kwana ba kikasa babun ku yazo yana ta yimin masifa."
zubewa SEEDRAH tayi kan kuje ra tana fad'in
"Ayya Mama jiya baki ga ruwa ake da daddare ba shi yahana mu dawowa, a gidan goggo Larai
muka kwana da Nasiba."
"Shi ne bazaki kira gida ki fad'a ba? kin san halin Baban ku sarai idan ya shigo bai ganki ba
yarika kira kenan."
"Yi hakuri Mama, wayar tawa a gidan Nabila na barta jiya sai yau naje na d'auka." SEEDRAH ta
fad'a tare da gyara zama tashiga taya Mamar tata ninke kayan su data wanke musu da safen
nan.
Mama ta ce "Sabo da shashanci irin naki waya ya kwana wani guri ke a wani gurin, Allah ya
shirya, sai ki tashi kije ki d'aura girki da ma yanzu nake da shirin shiga kitchen d'in wankin kayan
ki ya sai da ni."
ta ce "To me za'a girka Mama?."
Mama ta ce "A kwai shinkafa a store da Abba'n ku Sulai ya aiko da shi d'azu, ina ga akwai
ragowar manja da yaji a kitchen sai ayi mai da yaji, dan Baban ku baice komai ba game da girki
ga rana tana ta yi."
kai SEEDRAH ta jinjina ta ce
"Mama haka za'a girka zallar mai da yaji babu wake?."
"To ina kika ga waken waken daya kare tun ba yau ba, je ki girka abin da ya samu kawai."
a hankali SEEDRAH ta mike tana jinjina lamarin dake dad'a ta'azzara game da mahaifin nasu.
abun kamar wani kariyar arziki gida kamar gidan su babu wan da zai ga gidan ya ce basufi
karfin komai na rayuwa ba. sai gashi abun da zasuci ma yana kokarin fin karfin su, wai har ya
kaiga d'an uwan mahaifin su ke aiko musu da abinci, wanda a da mahaifin su yana daga cikin
masu kud'in unguwar su,
rayuwa kenan.
takuma jinjina kai tana fita daga cikin d'akin Mama.
A sakar gida ta tadda su Suhailat da Halimatu yayun ta wan da suke uba d'aya da Umma wato
mahaifiyar su kishiyar Mama.
Suhailat rike da waya a kunnen ta tana daga d'an can gefe, Halimatu tana yiwa Umma tsifa.
"Ina kwana Umma."
SEEDRAH ta fa d'a tana karaso in da suke.
Umma ta ce "Lafiya lau kawayen amarya andawo ne?."
ta ce "Eh." Halimatu ta dube ta ta ce "Baba sai tambayar ki yake ko d'azu ma sai da yayi
magana."
"Ai yanzu Mama take fad'a min jiya ruwa ne yahana ni dawowa nakwana a gidan goggo Larai."
SEEDRAH tayi maganar tana wuce wa kitchen, tashiga kiciniyar d'aura abinci.
tana gamawa ta zuba a kula mai d'an girma ta kai d'akin Umma kana ta d'au na d'akin su takai,
sannan ta dawo ta d'auki na Baba ta nufi d'akin sa.
da sallama ta shiga d'akin nasa,
Baba da ya ciro hular kansa yana kokarin ajiwa da alama yanzu yashigo gidan, ya amsa
sallamar.
takaraso ta aje tray'n data dauro kular abincin da plt da cokali, ta d'ago tana fad'in
"Sannu da dawowa Baba."
ya ce "Yauwa SEEDRAH yanzu Maman ki take ce min wai gidan goggon ku kika kwana."
ta ce "Eh Baba ruwa ne ya tsare mu shine na biya gidan ta."
ya ce "To a rika kiyaye wa dai, je ki kirawo min Maman naki."
ta ce "To Baba."
ko da taje ta sanar wa Mama Baba na kiran ta hijabin ta ta d'auka ta ce wa Mama zata shiga
gidan su Nasiba ta duba ta jiya sun kwana tana zazzab'i.
Koda ta shiga gidan su Nasiba a tsakar gida ta tadda Mama Kubura kishiyar Maman Nasiba
wacce a hannunta take tun bayan rasuwar Maman Nasiba, ta gaishe ta tana tambayar Nasiba'n
ta na ciki ne?.
ta ce mata Eh.
ta shige d'akin a kwance ta iske ta tayi shiru kamar me yin bacci,
tana ganin SEEDRAH tayi mata murmushi, SEEDRAH ta dube ta da kyau daga jiya zuwa yau
kawai tayi wata y'ar rama, girgiza kai tayi cike da tausayawa tana zama kusa da ita.
a hankali Nasiba ta mike zaune, tana mai cigaba da k'wak'ulo murmushin yake da bai kai ciki ba
dan b'oye damuwar ta.
SEEDRAH ta ce "Yajikin dai Nasiba Allah yasa dai bata gane komai ba."
ta ce "Ta so ta gane dan tun fitar ki d'azu dana fita zan shiga bayi tarika bina da kallo, har tana
tambayata wai ko ciwo naji a kafata taga kamar ina d'ingishi, na ce mata a'a babu abin da
yasame ni a kafar, SEEDRAH ina tunanin ranar da zata gane bazata tab'a yar da kan anyi min
fyad'e bane, za ta ce maza nake bi da ma can tasaba fad'a shike nan zata sami hujjar da zata
kafa har Baba ya yarda."
kukan da ke son kwace mata ne yasa ta yin shiru tana mai zubda kwalla.
da sauri SEEDRAH ta rike hannunta yayin da tuni itama hawaye yafara zuba a idon ta ta ce
"In sha Allah bazata tab'a ganewa ba kidage da sarki da ruwan zafi har gurin ya gama warkewa
gaba d'aya, yanzu tun da ta fara kawo zargi kan tafiyarki to zata saka miki ido ne sosai dan
gano abun da take zargi,to kada kibata kofa kiyi kokarin ganin komai yayi normal ta inda zaki
jirkita mata tunanin ta takasa gane komai, kuma bazata ganen ba in sha Allah."
kai Nasiba ta gyad'a kana tashiga share hawayen ta, itama SEEDRAH hawayen nata ta share
nan suka shiga d'an tab'a hira sai wajen karfe 3 kafin ta koma gida...
Da yamma SEEDRAH na share d'akin Mama wani yaro yashigo ya ce "Wai SEEDRAH ta zo inji
wani a waje."
Mama dake zaune sakar gida ita da su Umma ta ce
"Inji wa kenan kuma izinin wa ya nema daya zo gurin ta? je ka ce masa an bashi izinin zuwa
wajen ta ne."
Umma ce ta dakatar da yaron da fad'in
"Je ka ce ta na zuwa." kana taci gaba da fad'in
"Idan ma ba'a bashi izini ba yanzu idan ta fita in tasan shi takuma aminta da shi sai ta bashi
izinin zuwa wajen mahaifinta ya nemi izini sai ya cigaba da zuwa."
Mama ta ce "To ai sai ki zo ki je kiga ko waye ne, ai yanzu haka ma ita tasa shi ya zo zaiyi
zuwan gashin kansa ne."
mayafi SEEDRAH taja ta fito tana turo baki gaba
"Ni wlh ban san da zuwan kowa ba koma wane ne zan je nasa me shi ni."
tayi waje tana cigaba da turo baki da kunkuni, dan ita ba'a tab'a zuwa gurin ta haka kai tsaye ba
hasali ma bata hira ko a waya ne dan ko saurayi bata da shi bawai kuma babun bane saurarar
su ne bata yi.
da mamaki take kallon wan da ke tsaye a kofar gidan nasu yana jin gine a jikin mashin d'in sa.
b'ata fuska ta kumayi taja tatsaya jikin get, tana mai mamakin yan da a kayi yasan gidan su har
ya zo.
Kamal kuwa na ganin ta yasaki murmushi kana yata ko in da take.
"Madam barka da warhaka, suna na Kamal." ya fad'a yana mai cigaba da sakar mata
murmushin sa mai sanyi.
fuska takuma had'e wa ta ce "Me kazo yi gidan mu ko kazo ne har nan d'in ma kakirawo d'an
uwan naka ku kuma aiwatar da mugun nufin ku a kan mu?."
kai ya jinjina kana ya ce "Kizamo mai yafiya mana, wlh bai aikata abun da ya aikata da gangan
ba sharrin shaid'an ne."
wani irin murmushi ta sake wan da ya dad'a bayyano da ainahin k'yan fuskarta kana ta gimtse
ta ce
"Wai ku mutane bakwa da kunyar yiwa shaid'an kazafi ne? ranan gobe kaje ka tsaya gaban
ubangiji ka ce shaid'an ne ya sashi, shikuwa shaid'an zaifito yakare kansa dan baka da hujjar
dazaka kuma dogara da shi kan shed'an ne yasaku aikata ba dai-dai ba, dan baka tab'a ganin
sa da ido ba, ya tabbata kuwa kune shaid'anun kanku." ido ya zuba mata yana ji da kallon yanda take zuba zance y'ar karama da ita da iya tsara zance
kamar wata babbar mace.
murmushi ya yi ya ce
"To Allah dai yana son me yafiya, da ma nazo ne naga ya jikin nata, dan Allah ko zaki kirawo
min ita nagaishe ta da jikin?."
baki ta tab'e ta ce "Bazata zo ba bata bukatar gaisuwar taka kaje ka da abin ka mun yafe."
ta juya tana kokarin shiga gida ya yi saurin datakar da ita ta hanyar shan gaban ta ya had'e
hannayen sa biyu alamun roko ya ce
"Dan Allah kuyi hakuri kuyafe wa aboki na wlh abokina mutumin kirki ne sharrin shaid'an ne
kawai da kuma kaddara, idan kuka bashi da ma zai zo har nan ya nemi gafarar ta shi kansa
yanzu haka yana cikin mawuyacin hali da matukar damuwa da tashin hankali had'e da nadamar
abun da ya aikata, amma ki sani babu bawan da ya wuce kaddara na tabbata shi yafita shiga damuwa da tashin
hankali acikin halin da yake yanzu, yakuma shiryawa karb'ar duk wani hukuncin da za'a yanke
masa."
wani kallo ta wurga masa ta ce
"Yafita shiga damuwa da tashin hankali?,
bayan ita ya yi wa mugun illa a rayuwar ta, shi me yaragu a jikinsa?."
tayi masa tambayar tana k'afe sa da manyan idanunta.
d'an lumshe ido ya yi tare da kuma bud'e su a kanta jin yadda idanunta ke yawo cikin jikin sa. ya
ce
"Sanin ita ya raunata shiyasa ya shiga damuwar dan Allah kizamo mai dai-dai ta lamura dan
suffarki yafi kama da mutanen kwarai, nafuskanci har yanzu baki huce ba zamu dawo nan da
kwana uku da shi kan nan nasan kin dad'a hucewa kibamu damar ganin ta."
k'wafa tayi tare da shige wa cikin gida batare da ta kuma ce da shi komai ba, shima ya haye
mashin d'in sa ya yi gaba.
ko da ta koma gida Mama ke tambayar ta wane ne?, ta ce daga cikin abokan ango ne.
ta fad'a mata hakanne dan bata so ta tsananta bincike a kansa.
Washegari da safe bayan SEEDRAH tayi sallah a d'akin su