Showing 66001 words to 69000 words out of 78655 words
Chapter 23 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
jikin kofar tare da dafe kirjin ta.
"Fyad'e fyad'e zaiyi min innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,
lallai wannan ya tabbata tabbataccen mara imani mugu azzalumi."
ta furta murya na rawa cike da mugun tsoro.
a b'angaren S.MAN kuwa tana fita yazube bakin gado tare da jan tsaki,
hannu yasaka yad'an matse kasan marar sa dake murd'a shi, tsaki yakuma ja ganin yan da
MAN d'in sa take ta wani irin zillo wane zata tsinke.
wani tsakin yakuma ja tare da fad'in
"Mayyar yarinya kawai."
A daren ranar duk bacci irin nata sai da ta raba daren kafin bacci ya d'auke ta. shima d'in cikin
tsoro da fargaban kada ya yi jingina bango yakuma shigowa kamar yanda ya shigo rannan, ta
kwanta da shirin goge zatabar gidan dan bazata cigaba da zama tana ji tana gani ayi mata
fyad'e arage mata kima ba, yazama dole ta tseratar da kanta daga faruwar hakan. washegari guri nayin haske tafito da sauri dan tasan zuwa yanzu yagama motsa jikin sa.
Da sauri ta isa bakin get bataga maigadi ba addu'a take Allah yasa kofar a bud'e take, ai ko
tana tab'awa taji ta a bud'e da sauri tasa kai tafita.
tana jin mai gadi yana fad'in
"Hajiya dawo wa ya ce ki fita."
Shafa gefen fuskar sa S.MAN ya yi dake kallon duk abin da ke faruwa daga can saman bene ya
juya yana cigaba da zukar sigarin sa cikin kwanciyar hankali..
Tafiya take da sauri har lokacin zuciya da jikin ta basu dai na cirawa.
sai da tayi tafiya mai d'an nisa kafin ta d'an sami nutsuwa kana ta tsari adai-daita zuwa unguwar
su Nasiba.
a hanya ta kira Kamal ta ce su had'u a gidan su Nasiba.
tana isa ta ce wa mai adai-daitar yad'an jira bari ta karb'o masa kud'i dan bata fito da ko sisiba.
ta shiga ta karb'a kud'i gurin Nasiba ta kawo masa.
Kamal daya hango saukarta daga can kofar gidan su yakaraso.
murmushi suka sakarwa junan su sai kuma ta b'ata fuska.
a d'an marairaice ya ce "Me kuma nayi?."
ta ce "Dan ya ce katafi sai ka tafi ko da ma ba son gani na kake da gaske ba, kabi ka ishe ni da
kana son ka ganni."
murmushi ya yi yakama kunnuwan sa ya ce
"Ayi min afuwa amma tabbas babu ko shakka ke nake muradin gani, sai dai gaba da gabanta
shid'in babban wa uba ne, ayi hakuri kar a cinye ni da tsiwa."
hararar wasa had'e da so da kauna ta sakar masa kana ta juya ta nufi ciki.
da sauri yabi bayan ta yana fad'in
"Ranki shi dad'e kimbiya ayi hakuri mana."
maman Zeey dake sakar gida tana aiki ganin Kamal nabiye da ita had'e da hannu alamun roko
tayi murmushi, tana jinjina girman so irin wannan.
fuska ya marairaice kamar karamin yaro ya dubi Maman Zeey ya ce
"Maman Zeey tayi fushi ki ce baki yardaba idan ta bari zuciyar d'anki ya fashe."
murmushi mai sauti Maman Zeey tayi.
Zeey dake wanke-wanke kuwa waka ta soma musu
"A hayye soyayya ruwan zuma masoyiya tana wahalar da masoyi masoyiya kara wahalar da
masoyi idan yana so haka zai jure."
harara ya wurga mata ya ce "Yar sa ido kawai."
tintsirewa da dariya tayi ta ce
"Oh Ya Kamal ni kuma meye nawa."
"Yi fama da wanke-wanken ki." cikin muryar dariya ta ce "Ina kai ma kuwa."
Murmushi SEEDRAH tayi tawuce sashin Nasiba bayan ta kuma gaida Maman Zeey dake ta
zolayar ta tawuce sashin Nasiba cike da jin kunya Kamal ya biyo bayan ta.
Tana shiga Nasiba ta taho ta rungume ta cike da murnar ganin ta.
ido SEEDRAH ta waro ta ce
"Ke wai oyoyon naki baya kare wa ne ina shigowa ta d'azu kinyi min so kike ki murkushe mana
baby."
dariya Nasiba tayi ta ce
"To ai duk murnar ganin ki ne rabon da nagan ki wata nawa, ga Nabila can ta kullace ki fushi
sosai take da ke, har ta haihu taje wankan gida tadawo bakije jin dubata ta."
kai kawai ta girgiza akan ranta ta ce
"Bazaku gane bane wancan bakin mugun daya maida ni matar kulle a gida kamar wacce aka
bashi ni abakin bashinsa ya siyeni haka ya maidani."
taja kwafa a fili.
kusa da Nasiba ta zauna inda Kamal ya zauna kusa da abokin sa Mukhtar ke zaune.
SEEDRAH ta dubi cikin ta daya d'anyi girma ba cancanba irin dai girman cikin fari ta ce
"Wai yaushe ne zaki haihu ne kam?."
fuska Nasiba ta marairaice ta kalli Mukhtar fuska a marairace ta ce
"Abban Seedrah yaushe ne zan haihu."
murmushi ya yi ya ce
"Kin kusa saura kad'an Ummie'n Kamal."
baki da hanci SEEDRAH ta bud'e ta ce
"Wai sunan baby's d'in ke nan sunan mu?."
Nasiba ta ce "Eh ai Kamal ne ya saka ya ce idan aka haifi mace sunan ki za a saka mata idan
kuma na miji ne sunan sa, jimin son kai fa ni da ma Mukhtar zan saka idan najimi ne."
dariya duk sukayi SEEDRAHA ta ce
"Kai amma naji dad'i sosai My Kamal gaskiya ka burge ni."
ido ya kashe mata ya ce
"Wani abun ma sai kin shigo hannuna zakiga abubuwan burgewa."
hararar sa tayi ta ce "Kafara ko ni bari ma naje gidan Nabila naga baby."
"Sai dai kirika zuwa kina ganin baby'n mutane ke bazakiyi zuciya aga baby'n mu ba ko."
Kamal ya fad'a yana dariya kasa-kasa.
harara takuma wurga masa. Mukhtar shima dariyar ya yi yana bugun kafad'ar sa kana ya ce
"Yakamata kam ayi duba da lamarin nan gimbiya SEEDRAH."
ita dai mikewa tayi Nasiba ma ta mike ta ruko hannunta cikin yin kasa da murya ta ce
"Ya dai naganki haka tun d'azu nake ta karantar yanayin ki kamar ba a dai-dai kike ba."
"Uhm ba komai kawai bana d'an jin dad'i ne."
shiru Nasiba tayi bawai ko dun ta yarda da abin da kawar tata tafad'a ba sai dai dun bata son
yawaita yi mata tambaya gaban su Kamal ne amma tabbas ta fahimci tana cikin damuwa.
itako SEEDRAH bata jin zata iya sanar mata da abun da ke faruwa dan tana ganin abun kunya
ne a gare ta duk da kuwa Nasiba aminiya ce a gare ta.
tayiwa Nasiba sallama suka fito da Kamal, Mukhtar zai bisu Kamal ya ce ya zauna basa bukatar
rakiya bare yaji abun da zasu fad'a.
suna fita kofar gidan SEEDRAH ta dubi Kamal da kyau ta ce
"Kamal kana so na kuwa?."
da sauri ya waro idanunsa ya ce
"Anya kinsan me kike fad'a kuwa amma sam banji dad'in fitar kalmar nan daga bakin ki ba, ko
makaho ne ya dafa zuciya ta na tabbata zai fahimci irin girman so da kaunar da nake miki."
ido ta rumtse da karfi kana ta bud'e su a kansa ta ce
"To gobe kaje ka kai kud'in aure na gidan mu."
wani irin tsalle ya tuma tare da fad'i
"Yes yess yesss."
sai kuma ya d'an dai-dai ta nutsuwar sa yana son karantar yanayin ta kana ya ce
"Are you okay."
kai ta girgiza ta ce "Yess I'm okay kayi yadda nace."
"Insha Allah." ya fad'a kana suka nufi gidan Nabila a kafa suna d'an tab'a hirar su.
ko da suka isa da fari Nabila ta nuna fushin ta kan rashin zuwan SEEDRAH da ta haihu,
SEEDRAH tayi ta bata hakuri har ta huce ta d'auki babyn data ci suna Ishmat tayi ta mata wasa
kana daga bisani tayi mata sallama suka baro gidan, Kamal ya d'auko mashin d'in sa ya kaita
gida.
Tayi missing d'in Mama bata tsaya hira da shi a waje ba ta ce anjima ya dawo, ta shige gida da
sauri a sakar gida ta tadda su Mama da gudu tafad'a jikin Mama tana fad'in "Oyoyo Mama."
murmushi Mama tayi dan tayi kewar d'iyar tata ba kad'an ba.
SEEDRAHA ta mike jikin Mama ta zauna gefen ta kana ta gai da Umma sannan ta gaida
Maman.
duk suka amsa cikin sakin fuska suna tambayar ta ya aikin nata.
Suhailat da Halimatu kuwa har rige-rigen tambayar ta ya S.MAN ya ke.
mikewa tayi tana fad'in
"Me zai hana kuje gidan ku gano sa."
"Mara kunya halin naki na nan dai."
Halimatu ta fad'a tana hararar ta, bata kuma bi ta kansu ba ta shige d'akin Mama tana shiga ta
haye gado tayi kwanciyar ta, ai ko ba jimawa bacci yasami nasarar sace ta, nan tashiga rama
baccin da bata samu tayi shi yadda ya kamata ba jiya.
sai wajen karfe biyar da rabi ta farka, tashiga bayi ta yi al'wala ta fito tagabatar da sallar la'asar.
tana zaune kan sallaya Mama ta shigo ta dube ta cikin kula ta ce
"Kin ta shi?."
kai ta gyad'a ta ce "Eh." kana ta langwab'ar da kai gefe ta ce
"Mama yunwa ban karya ba."
zama Mama tayi a bakin gado tana fad'in
"Ga ragowar kunu can da jiya na dama sauran gari daddare nasha na rage,
da safe nasha naso sha da rana naji kirjina na suya sai na hakura ganin zai tada min olsa."
murya ta mararirace ta ce "Kunu kuma Mama abinci dai."
"Uhum SEEDRAH ke nan muna dai kan jiran Baban ku har yanzu bamuga aike ba."
jikin ta ne ya mutu ya yin da taci wasu zafafan kwalla sun ciko mata ido, wato dai Mama bataci
abinci ba kenan tun safiya bayan kunun da ta sha wan da jiya ma haka shi d'in ta sha.
"Innalillahi wa Inna ilaihirraji un ya Allah ka kawo mana mafita cikin lamuranmu."
a hankali ta rarrafo ta kwantar da kan ta kan kafar Mama ta ce
"Mama bakiyi waya da su kawu Yusufa bane."
kanta Mama ta shafa ta ce
"Banyi musu waya ba SEEDRAH nauyin tambayar su nake ji duk da nasan bazasu tab'a son
gani na cikin wani haliba, amma abaka yau a baka gobe yawuci wasa, wan da ya haliccemu
shine kad'ai baya gajiya da bamu kuma munakan rokon sa zai warware mana lamuran mu,
ki tashi ki koma bakin aikin ki ga magriba ta kusa kada dare ya yi miki a hanya."
hawayen da suka zubo mata ta share kana ta d'ago ta gyara zaman ta kan sallaya sannan ta
ce..............!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 20
"Mama nifa bazan koma ba na dawo gida ke nan, yafad'i wani abun da za ayi masa ya fanshi
kud'in sa, ni nagama yi masa aiki, ga su Aunty Suhailat da Halimatu su je suci gaba da yi masa,
tun da duk suna son zuwa gidan sa da ma."
"SEEDRAH kasa zaki wasa min a ido, ina kawazucin iyayen nan da nake gani tare da ke?, idan
baki taimake ni ba wazai taimaka min SEEDRAH, ke yake da bukatar yi masa ai ki basu
Suhailat ba."
suka jiyo muryar Baba daya fad'o cikin d'akin yana sauke waya a kunnen sa, ko ba a fad'a ba
tasan S.MAN ne yakira sa yaku yi masa barazanar daya saba.
Baba yacigaba da fad'in
"SEEDRAH ko mai na dad'a tab'arb'arewa ko dubu talatin bana da shi nawa na kaina bare
miliyan 30,
a ina zan samu na biya sa, zaman ki cikin gidn shi kina yi masa aiki shine rufin asirina, idan kika
ce zaki bar aikin nan to tabbas muma zamu bar gidan nan, ko kud'in d'akin haya d'aya bani da
shi sai dai mukoma titi rayuwar mu ta kare a can."
ido ta rumtse da karfi ya ilahi ya lillahi me yake shirin faruwa da ita ne kam.
Baba ya fita ya na fad'in
"Kiyi tunani dai SEEDRAH."
Mama ta ce "Hakuri zakiyi ki koma hakan shine kad'ai rufin asirin mu."
sai a sannan ta bud'e idanunta wanda kake iya hango damuwa had'e da tsoro da fargabar
faruwar wani abu cikin su. ta ce
"Mama shin bakwa tunanin me duniya zasu ce a kanmu, ina gidan wani da bashi da mata ina yi
masa
ai ki kada kusa duniya tafara zargin mu mana, Mama ina jin tsoro ina jin tsoro Mama, kuyi
hakuri ku barni na zauna a nan kusa Halimatu ko Suhailat suje suciga da yi masa aikin dan
Allah Mama."
ta karashe maganar da rike hannun Mama gam.
shiru Mama tayi tana nazartar ta, sai kuma ta girgiza kai sannan ta ce
"Ko ma mene ne kisa Allah cikin lamuranki ki tabbatar da tsoran sa gare ki,
duniya kuwa zasu fahimci cewa kima da darajar mahaifinki kika tsare,
kije Allah ya kareki, a kullum da ko yaushe ban gushe ba ina kan yimiki addu'a, ina da tabbaci
da yakini a kan tarbiyyar dana baki."
shiru Mama tayi da tunani irir-iri a zuciyarta, sai dai bata bari mugun tunani yasami matsuguni
cikin zuciyarta ba, addu'a take ubangiji ya tsare mata d'iyarta aduk inda tasa kafarta.
Mikewa tayi ta ce "Mama makaranta na fa?."
"SEEDRAH a wannan halin da muke ciki, kuma haryanzu ma ba a dawo daga yajin aiki ba."
kai ta girgiza kana ta d'au wayar ta ta dubi Mama zuciya a raunace ta ce
"Mama na tafi." jiki a sanyaye Mama ta ce
"Ubangiji Allah ya tsare ki da tsarewarsa ya kare ki da kariyarsa, a duk inda kike ki kasance da
tsoron Allah, domin shi Allah baya bacci ko cikin kasa katona ka shiga ka aikata sab'on Allah
yanaji kuma yana ganin ka, zakuma kaje ka tarar da shi."
kai ta jinjina kana tayi mata sallama ta fito sakar gida.
Mama tabi bayan ta da kallo yayin da wani irin rauni ya ziyarce ta, 'yarta d'aya tu
tilo a duniya bata da ikon magance mata damuwar da take gani tattare da ita.
hannu biyu ta d'aga sama ta ce
"Ya Allah dan isarka da buwayar ka dan girman al'arshinka ka tsare min 'yata aduk in da take."
ta mike tashige bathroom domin yin al'walar sallar magriba da ake ta kiraye-kirayen sa yanzu.
A sakar gida kuwa SEEDRAH tayi wa Umma sallama, ta shiga d'aki gun su Halimatu suma tayi
musu sallama, Suhailat ta ce
"Yauwa SEEDRAH tsaya dan Allah in tambayeki."
SEEDRAH ta tsaya daga bakin kofar.
Suhailat ta karaso in da take ta ce
"Dan Allah wasu irin abinci S.MAN yafi so."
kallon shekeke SEEDRAH tabi ta da shi sannan ta ce
"To ni kuma ina zan sani, nawa a wanne."
"Dakata da Allah ni irin wannan bakin halin taki ce take had'a ni da ke, zaki ce baki san abincin
da yafiso ba akan bakya yi masa girki ne."
sai kuma ta d'an sassauta murya
"Kina ji ko SEEDRAH friend's d'ina ne suka bani shawara daga girki ma kad'ai zan iya karkato
da hankalin S.MAN gare ni, dan Allah kiyi min wani taimako a matsayin ki na 'yar'uwata zanyi
masa girki gobe na kawo masa."
baki bud'e SEEDRAH ta ke kallonta ta ce
"Amma lallai Aunty Suhailat bakiyi dogon nazari ba, yanzu a ce gidan nan akwana ba a d'aura
tukunya ba, bazaki iya badawa ayi girki ba amma zaki d'au kud'i kiyiwa wani koton gardin banza
can girki, lallai kuwa aiki bai ishe ki ba,
to ni banma san wani irin abinci yafi so ba dan ni ko wanne ma girka masa nake."
"To bance kiyi min rashin kunya ba jeki basai kin fad'a ba zan bincika da kaina, da ma ke asu
wa ga uwarsa can ita tasan komai nasa ai zanje gidan gobe."
"Da yafi miki kuwa."
SEEDRAH ta fad'a ta juya tayi gaba abinta.
a can wajen get ta sami Baba ya bata kud'in abin hawa yanata sa mata albarka ta tafi.
Ko da ta isa knocking tayi maigadi ya bud'e mata kofa, ta nufi ciki zuciyarta na bugawa, wani irin
tsoro ne yake ta son danne jarumtarta duk da kokarin da take tayi wajen ganin hakan bai
faruba.
babu kowa a parlour'n taji dad'in hakan dan haka ta shige d'aki.
bayan ta idar da sallar isha kuma ta fito, ta nufi kichin ta had'a masa kayan tea ta haura sama, a
kan table d'in tsakiyar parlour ta aje masa dan batajin zata iya shiga cikin bedroom d'insa.
da sauri ta sauka kasa ta shige d'aki ta kulle.
A b'angaren S.MAN kuwa yana can gurin party da a ka gayyace shi, sai waje karfe 1 na dare ya
dawo gidan, ko da ya iske kayan tea d'in sa a parlour ya kwashe ya yi cikin bedroom da shi.
Tun daga lokacin SEEDRAH bata kuma yunkurin shiga d'akin sa kai tsaye ba, sai ta tabbatar da
baya ciki kafin ta shiga, da sauri-sauri kuwa zatayi abun da zatayi ta fita.
bata kuma yarda ta cakale shi da fad'a sosai