Showing 3001 words to 6000 words out of 78655 words
Chapter 2 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
da 'yan uwa da abokan arziki, sai tashin gud'a kake ji,
wasu 'yammata ne suka shigo cikin shiga irid'aya wato anko, da ka gansu basai an fad'a maka
ba kasan kawayen amarya ne.
d'akin da amarya ke ciki suka shiga a gajiye wata kyakkyawar budurwa tazube kan gado tare da
fad'in
"Wash Allah wlh nagaji."
hararar ta amaryar dake zaune can kuryar gado tayi ta ce
"Ke kam SEEDRAH kin ga ta kanki da son jiki, sai kace tafiyar kafa kika yi ba'a mota ba."
hararar ta Seedrah tayi tana kwanciya kan gado tare da fad'in
"Ke kam ai bazakiji gajiyar ba tun da gidan habibin ki muka kawo ki, Nasiba ke dan Allah baki
gaji da jijjigar motar nan ba, da suke ta gudu da mutane kamar za'a tashi sama,
ni wlh addu'a na rinka yi ma dan na gama sadakar wa kifar da mu zasuyi."
dariya Nasiba dake zama kusa da Seedrah tayi ta ce
"Ai ango ne keta d'agawa direbobin hankali wai suyi sauri sai ka ce ance baza a kawo masa ita
bane ko saurin me yake oho."
sauran kawayen ne sukayi dariya suka shiga zolayar amaryar, da yanda angon ta keta d'okin
ayi a kawo masa ita...
'Yan uwa da abokan arziki da suka kawo amarya suka fara watsewa kasan cewar magriba ta
gabato,ciki har da wasu daga cikin kawayen amarya.
ko da Seedrah da Nasiba suka mike dan su koma gidan iyayen su, amarya Nabila ta tare su har
da yi musu kuka wai su bazasu tafi ba su kwana sai gobe.
ido Seedrah ta ware ta ce
"Mu kwana a ina ai sai angon ki yazo ya fidda mu a gidan nan da kansa, kinga kibar mu mu tafi
ga hadari ya fara taso wa kada ruwa ya tare mu a nan."
Nabila ta marairai ce fuska ta ce "Yau she zaku sami abin hawa daga nan zuwa unguwar rimi
yanzu dare yayi dan Allah ku bari gobe da safe sai ku tafi."
fir suka ki suka ce su tafiya zasuyi, dataga dai fa bazasu kwanan ba sai ta ce
to su bari idan Kabir ya shigo sai ya mai da su gida a mota.
da haka dai suka zauna har wajen bayan sallar isha, kafin Kabir ya shigo,
lokacin har yayyafi yafara sauka.
ko da ganin yayyafi ya fara Kabir ya ce musu su kwana gobe sai ya maida su gida, badun sun
so ba suka hakura.
Suna zaune a parlour ganin yan da Kabir ke ta bin amaryar sa da kallon kasa-kasa yasa sukaji
duk sun takura su, sun san cewa a yanzu yana matukar matar sa.
Kabir ya mike ya shiga bedroom yana fad'in bari ya d'an wasa ruwa,
yana shige wa ciki Seedrah ta dubi Nabila ta ce
"Je ki kula da mijin ki, Nasiba taso muje ki rakani gidan goggo na can kasan layin nan, bari muje
mu dawo."
tayi maganar tana mike wa Nasiba ma ta mike.
Nabila ta dube su tana fad'in
"A ruwan nan zaku fita ku bari gari yawaye mana."
"Yayyafi dai yanzu zamuje mu dawo."
cewar Seedrah tana janyo hannun Nasiba,
Nabila ta ce "To ku aje jakan ku da wayoyin ku, ai na gane so kuke ku gudu, daga nan har in da
zaku titi ne ga hasken wutan nepa da farin wata, Allah nifa tsoro nake ji."
dariya Seedrah da Nasiba sukayi ganin tsoro fal tare da kawar tasu.
Nasiba ta ce
"To meye abin tsoro gaki ga mijin ki."
duka ta kai mata a kafad'a tana fad'in
"Ai shine abin tsoron."
dariya sukayi ta mata suna zolayar ta da fad'in
tayi jarumta dai, sukayi waje.
Suna fita basuyi nisa ba ruwa ya fara karuwa,
Seedrah dake gyara gyalen kanta daya jike ta ce
"Kaji ruwan nan kamar jira yake mu fito ai kuwa zamuyi wanka, Allah ya so mu bamu fito da
wayoyin mu ba da sun jike."
Nasiba ta ce "Wai dagaske dawowo gidan nata zamuyi?."
kai Seedrah ta girgiza ta ce
"Haba dai amaryar yau me zai kaimu kwana gidan ta nafad'a ne kawai dan ta barmu mu tafi,
can gidan goggona zamu kwana gobe madawo mu d'auki jaka da wayoyin mu, dan nasan dama
ba bari zatayi mu tafi da shi ba."
Sunyi tafiya mai d'an nisa yayin da ruwan ke cigaba da karuwa, kamar yanda Seedrah ta fad'a
kuwa suna tafiya ne cikin saib'i ruwan yana musu wanka.
hannu SEEDRAH takai cikin rigar ta karkashin bra d'in ta tana sosawa, ta ce
"Wayyo kaikayi Nasiba zo ki cire min bra d'in narike shi a hannu wlh kaikayi yake min a jiki tun
san da ruwan nan yafara jika mu, gashi sai karuwa yake."
gefen wani shago ta tsaya,
babu kowa a gun shagon sakamakon ruwan sama da akeyi, kuma wan da ke bakin titi bazaigan
su ba dan gurin babu haske sai dai idan yazo kofar shagon da suke gefen sa tad'an baya
kad'an.
ta na cigaba da fad'in
"Yi sauri ki cire min wayyo Allah kamar wanda a ka zuba min karara a jiki."
Nasiba ta d'an zuge zip d'in rigarta ta baya kad'an tana kiciniyar cire mata bra,
ita kuma ta d'ago hannu da sauri tana kokarin susa in da taji yana kuma mata kaikayi, ai ko
'yankunnen ta ya rike gyalen ta data d'ago hannu sama gyalen yakuma rufe mata fuska.
kiciniyar raba gyalen da 'yankunnen take tana fad'in
"Wayyo nikam na shiga uku, Nasiba yi sauri ki ciremin dan Allah."
Nasiba na gama b'alle mata ma b'allin bra'n ta zaro shi ta bayan tana mata dariya ganin yan da
take yi kamar zata tuma tsalle, sai bubbuga kafa a kasa take tana kuma kokuwa da gyalen daya
rufe mata fuska ga kuma 'yankunnen ta daya rike gyalen ta gam tana ta kiciniyar rabasu.
dai-dai lokacin da Nasiba ta zaro bra d'in wani saurayi daya fito daga cikin shagon da suke
tsaye gefen sa ya hasko su da hasken tocilan wayan sa.
"Su waye anan?."
ya fad'a yana zuwa in da suke, da sauri Seedrah ta cire 'yankunnen gaba d'aya ganin bazata
iya cire shi jikin gyalen ba, ta had'o da gyalen ta rike shi a hannunta.
baya ta shiga ja ganin saurayin na dad'a masosu bai kuma fasa kashe musu toci a ido ba.
"Ku tsaya a nan!." yafad'a yana mai cigaba da masosu, ai sai suka juya suka rufa a guje,
Nasiba ta yadda bra d'in hannunta a kasa Seedrah ma tayi wurgi da gyale da 'yankunnen ta a
gurin, suka rufa a guje, da iya karfin su suke gudu ganin shima ya rufa musu baya a guje,
ta bayan layin suka shige a guje ta gurin kuma babu hasken wutan nepa sai dai farin wata daya
dad'a kara haske sakamakon ruwan da aka d'auke sai d'an yayyafi kad'an-kad'an.
Shiko wannan saurayi mai suna Kamal dake biyo su ya tsaya tare da juya wa da sauri ya koma
bakin kofar shagon,
ya d'ale mashin d'in sa dake fake a gun, cikin d'an d'aga murya yadubi wani dake tsaye bakin
shagon ya ce
"Mukhtar d'auko mashin d'in ka kazo mu bisu sun gudu, irin 'yan iskan 'yammatan nan ne suke
so su kawo mana iskanci unguwa."
yana gama fad'a yaja mashin d'in sa da sauri, Mukhtar ma ya rufa masa baya a kan nashi
mashin d'in.
A b'angaren su Seedrah kuwa ganin ya daina biyo su, suka tsaya suna mai da numfashi,
Seedrah data dafe kirji cike da tsoro ta ce
"Kai Nasiba Allah ya rufa mana asiri anya wannan ba mahaukaci bane?, daga ganin mutane ka
kama binsu."
Nasiba ta ce
"Ko kuma 'yan iskan layi ba."
bata kai ga rufe baki ba suka ji karan mashina a bayan su,
"Gasu can sune mu bisu."
sukaji an fad'a ai ko suka kuma zurawa a guje, suka sharo wata kwana.
kasan cewar su suna mashin su Seedrah kuma suna kafa, ganin suna daf da cin musu, ai ko
suka nufi cikin wasu gidaje biyu da suke hango su.
Nasiba ta shiga gida na farko wan da gida ne da ake gina shi ba'a karasa ba, amma ta ciki an
gama komai har da rufe.
Seedrah kuwa tsabar tsoro gaba ta kara a kid'ime ta shiga wani gida a guje.
mutanen gidan suna zaune a sakar gida ta fad'o ciki tana sauke numfashi, a birkice take fad'in a
taimake ta wasu ke binta. wata mata dake zaune
ta mike tana fad'in,
"Shiga nan." ta nuna mata d'aki, ai ko da gudu ta shige ta d'ale kuryar gado ta dukun kune tana
b'ari da maida numfashi.
A waje kuwa Kamal ne ya sai da mashin d'in sa dai-dai kwanan lungun da su Seedrah suka
shigo, yana ta d'an waige-waige.
Mukhtar daya iso in da yake ya ce
"Ina suke sun gudu ne?."
Kamal ya kalli gida na farko da suke tsaye a kusa da shi, ya ce
"Naga shigan d'aya nan gidan bita ciki d'ayan ce dai ban ga ta in da tayi ba, amma nasan ita ma
tana nan a nan eriyan bari na dudduba tacan."
ya sauko a mashin d'in ya kunna tocilar wayar sa yashiga haska gefe da gefen lungunan gurin.
Mukhtar kuma yashiga gidan da Nasiba ta shiga.
A can cikin gidan da Seedrah ta shiga, matar da ta ce ta shiga d'aki ne ta biyo ta cikin d'akin,
ganin yan da take ta kakkarwa ta iso bakin gadon tana fad'in
"Wai su wa suka biyo ki ne taso ga jikin ki duk a jike ai duk abunsu baza su biyo ki cikin gida ba
kam yanzu, zo ki cire kayan nan sanyi zai shige ki."
ta mike tana rarraba ido cike da jin tsoro wan da har yanzu tsoron bai bartaba ta zamo bakin
gadon,
tana fad'in "Haka kawai suka biyo mu daga ganin mu muna tsaye."
matar ta miko mata wasu kaya ta ce
"Saka wad'an nan kicire jikakkun, mata san mu na yanzu ai sai Allah, musamman zauna gari
banza suna nan suna harin 'yammata a hanya Allah ya shirya."
kar b'ar kayan tayi, matar ta fita ita kuma ta shiga tub'e jikakkun kayan jikin ta ta saka wad'an da
ta bata har da hijabi data had'a mata da shi.
tana gama sakawa matar ta shigo ta ce ta fito taci abinci,
jiki a sanyaye ta fito dan har lokacin jikin ta bai fasa b'ari ba ga tunanin ta da gaba d'aya yanzu
ya koma kan Nasiba, fatan ta d'aya Allah yasa ta sami mafaka kamar yanda ta samu.
a bakin kofar matar ta zauna kamar yanda matar tace mata,in da suke zaune suna cin abinci.
wata budurwar yarinya ce dake cin d'anwake ta turo mata plt d'in gaban ta tana fad'in
"Muci tare."
murmushi Seedrah tayi kana ta saka hannu cike da jin sha'awar d'anwaken wan da yaji mai da
yaji da kuma kayan ganye, suna ci yarin yar tana d'an jan ta da hira.
Sallama a kayi aka shigo gidan, matan gidan suka amsa, ya karaso ciki yana fad'in
"Maman Zeey nazo cin tuwon dare, amma idan ba Zeey bace tayi."
murmushi Maman Zeey tayi ta ce "To bismillah da kaina nayi abi na yau."
budurwar da suke cin d'anwake tare da Seedrah tayi murmushi da fad'in
"Yau Mama ita tayi abincin ta da kanta nima kuma nayi nawa daban duba ka gani Ya Kamal
d'anwake na girka abina."
karamar dariya yayi ya ce
"To gaskiya Zeey a zubo min d'anwaken nan dan naga alama zaiyi dad'i ga yan da kuke ta kai
loma."
yayi maganar yana zama kan dakale gefa da su Zeey d'in.
Zeey ta ce "Ah haba Ya Kamal kai da kace ban iya abinci ba sai jagwalgwale, ai ina jin ku jiya
kuna gulma ta kai da Ya Mukhtar wai ban iya abinci ba, ai zan ga kalar matar da zaku auro."
gefen fuskarsa ya shafo ya ce
"Ai kuwa zaki gani sai wacce tayi digiri a makarantar koyon girki, ke dai zubo min d'anwaken
nan naji ko ma yayi dad'i ko ganin sa kawai nake a ido kamar zaiyi dad'in."
Zeey ta mike ta nufi kitchen tana fad'in
"Kad'an zan zuba maka dan nasan yanzu zaka kushe."
Seedrah da tun shigowar sa kanta yake kasa jin muryar sa da yayi sallama yasa gaban kirjin ta
yanke wa, dan muryar yayi mata kama da na d'aya daga cikin wad'an da suka biyo su.
Zeey ta kawo masa d'anwaken ya gyara zaman sa tare da d'aukar cokalin data sako shi cikin
plt d'in d'anwaken yana fad'in
"Bari muji ko yau anyi abin kirki."
yakai d'anwaken bakin sa, Zeey ta ce "Ni dai Ya Kamal in kasan kushe min girki zakayi kaci na
Mama kawai."
"Ki dai tsaya yagama bin cikin baki na tukun zan fad'a miki in ma yayi dad'i ko baiyi ba."
Maman Zeey kam dariya tayi tana mikewa ta shige d'aki, dan ta saba jin rigimar su a kan abinci
shi da Mukhtar idan Zeey d'in ce tayi girki zasuci kuma sun rika kushe wa kenan wai bata iya
ba.
Loman d'anwaken yakuma kaiwa bakin sa kana ya dubi Seedrah da har lokacin kanta na kasa
bata kuma yi magana ba, ya ce
"Wai wace ce wannan ita kurma ce?."
Zeey ta ce "Bakuwa ce kai Ya Kamal wannan kyakkyawar tayi maka kama da kurma ce."
ya ce "Da alama, a kwai kyan d'an maciji ai dan ni tun zama ta banji tace kala ba."
d'agowa Seedrah tayi suka had'a ido da shi, plt d'in d'anwaken ya tura gefe, ya kara hasken
gurin ta hanyar kunna tocilan wayar sa ya d'ago wayar ya haska fuskanta
da shi.
ya ce "Ke ce?, dama hasashe na ya bani nan kika shigo."
mike wa Seedrah tayi a d'an hatsale dan kallamar dayiyi amfani da shi wajen jifanta da kalmar
k'yan d'an maciji, ya sosa mata rai.
ta ce "Eh ni ce!." sai kuma ta saka takalmin ta ta soma tafi ta nufi kofar fita, shima ya mike da
sauri yabi bayan ta.
Zeey kam baki ta bud'e tana kallon su har suka fice a gidan.
suna fita yayi saurin ruko hannunta gam ya ce
"Dube ki kamar wata mutumiyar kwarai wai a dole kin saka hijabi ta in da baza'a gane ko ke
wace ce ba, wuce muje sai kun fad'a min daga ina kuka shigo mana unguwa kuna son baje
k'olen iskancin ku a nan."
hannunta ta fizge da karfi ta ce
"Ina 'yar uwa ta take wlh duk abin da ya same mu kuyi kuka da kanku."
ta juya da sauri ta nufi gidan da d'azu taga Nasiba ta shiga sabo da birkicewar da tayi ita kuma
tayi gaba.
yabiyo bayan ta da sauri.
da sauri ta shiga gidan tana kiran sunan ta, kasan cewar gidan babu mutane ciki babu ko
hasken wutan nepa, tsayuwa tayi ganin gaba d'aya gidan da duhu, lokacin shikuma ya karaso in
da take, gurin yad'an yi haske sakamakon hasken wayar sa da ya ke kunne.
shesshekan kuka suka jiyo a cikin wani d'aki, da sauri har suna rige-rigen suka shiga cikin
d'akin,
Nasiba suka gani kwance a kasa jikin ta a rufe da zanin ta daga cikin ta zuwa cinyoyin ta, ga
kuma pant d'in ta a gefe, idanunta yayi luhu-luhu da alama taci kuka dai ta koshi, sai fidda
shesshekan kuka take irin na wan da ya gaji da kukan wahala.
hankali tashe Seedrah tayi kanta tana girgiza ta da fad'i.
"Naseeba me ya same ki me ya faru da ke?!."
tayi mata tambayar da karfi cikin matsanan ciyar tashin hankali, tana mai ci gaba da girgizata da
kokarin d'ago ta daga kwancen da take.
Jiki a d'an sanyaye Kamal ya zubawa Naseeba ido, kana ya kai duban sa ta kasa gurin cinyoyin
ta da zanin yad'an yaye yayi sama.
ido yakuma ware wa da karfi a kanta ganin jini a jikin cinyanta, dasauri ya janye idanunsa tare
da rufe idanunsa ya damke su da karfi, a fili ya furta
"Ya salam!."
sai a lokacin Seedrah ta lura da halin da take ciki, lokacin da ta janyo ta ta d'ago ta zaune sai
taga zanin ta ba'a jikin ta yakeba sannan kuma babu pant a jikin ta gashi a gefen ta, ga kuma
jini na fita daga gaban ta, Naseeba sai yarfe hannu take tana fad'in
"Wayyo Allah na."
wani irin kuka Seedrah ta fashe da shi cikin tsananin kad'uwa da firgicin gano halin da kawar
tata take ciki, cikin muryar kuka take fad'in
"Waya miki wannan aiki Naseeba wayyo Allah mun shiga ukun mu."
mikewa tayi da sauri ta rirrike rigar Kamal dake tsaye idanunsa a rufe yana jin kansa nayi masa
wani irin mugun nauyi.
cikin muryar kuka sosai tashiga bubbuga kirjin sa da hannayen ta duka biyu tana fad'in
"Me tayi muku zakuyi mata irin wannan zalincin mene ne gamin ku da mu da zaku rika bibiyar
mu, me yasa zaku zalince mu ku biyo mu ku idda mummunar nufin ku a kanta?,
kun cutar da ita cuta mafi muni,kun zalince ta kun raba ta da abu mafi muhimmanci a rayuwar
ta, to ina amfanin nawa tun da na kawa a miniya ta ya salwanta, nima kuyi min fyad'en gani a
gaban ka kayi min babu amfanin nawa budurcin tun da kuka illata nata."
kuka sosai take tana bubbuga kirjin sa.
Kamal yakuma rumtse idanunsa yanajin yanda kalaman ta da kukan ta ke dukan kwakwalwar
sa.
Seedrah kuwa hijabin jikin ta ta shiga kokarin cire shi tana cigaba da fad'in
"Jiran me kake kayi gaggawar yimin fyad'en nima azzalumai ma ha'inta tun da abun da yasa
kuka biyo mu kenan."
hannunta Kamal ya rike da sauri batare da ya bari ta cire hijabin ba, gaba d'aya lissafin sa ya
jagule bai san ta yan da akayi aka aikata mata wannan aika-aikan ba.
Ya ce "Wlh ba abun da yasa muka biyo ku ba kenan, dana ganku a tsaye kuna tab'a junan ku
wlh nayi zaton irin 'yan iskan titi nan