Showing 75001 words to 78000 words out of 78655 words
Chapter 26 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
zasuyi aure akara kulla dankon zumunci, nan take yakira Ummi ya sanar mata.
Ummi tayi matukar farinciki dan a yanzu bata da burin da ya wuce taga auren d'an nata duk da
kuwa auren yazo musu a bazata cikin rashin shiri.
nan take ta d'aga waya ta kira S.MAN ta ce yazo yanzu tana niman shi.
ko da ya iso gidan farincikin Ummi yagaza b'oyuwa
kamar ta goyashi haka ta ke ji.
ta dube shi fuska d'auke da murmushi ta ce
"Usman kana takan shiri kuwa? ya kamata yanzu mushiga Kano muje mu had'o lefe tun da
abun yazo a kurarren lokaci da da sauran lokaci da a Dubai za aje had'o lefen nan,
to Allah ma yasa anan gida Nigeria muna da kayayyaki masu inganci kamar na kasashen
ketaren."
baki ya tab'e ya ce
"Ummi wani lefe kuma auren nan da d'an wani lokaci."
ta ce "Ban fahimta ba kamar ya?."
kai ya d'an sosa kana ya ce "To ni me na sani game da hakan, duk abun da ya kamata sai kiyi."
baki ta washe ta ce "Ah to yanzu naji zance,
wlh kamar ka shiga raina na dad'e ina fatan hakan SEEDRAH yarinyar kirki ce."
zaman ta tad'an gyara kana ta ce
"Amma Usman me yasa bakayi magana tuntuni kana son SEEDRAH ba, sai yanzu da auren ta
yarage kwana biyu me kake ganin mutane zasuce a kammu."
kafad'a ya d'aga alamar ko oho ya ce
"Ko me ma suce." Ummi kam shiru ta d'anyi kana ta ce
"To Allah yasa hakan shine mafi alkairi."
shiko mikewa ya yi tare da d'aga kiran da yashigo wayar sa yafice yashiga motarsa ya bar
gidan.
nan da nan Ummi tashiga kiran 'yan'uwanta da abokan arziki tana sanar musu.
daga karshe takira lambar Sagir bugu d'aya a na biyu ya d'aga,
cike da girmamawa yashiga gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da farincikin da ke d'awainiya da
ita.
kana ta ce
"Sagir zan shigo Kano anjima zakayi mana jagora zuwa kasuwa had'o lefen Usman."
cike da mamaki Sagir ya ce
"Lefe kuma na S.MAN?."
dariya Ummi ta yi ta ce
"Eh na shi kaima abun yazo maka a bazata ko bai sanar maka da auren nashi bane."
"Bamuyi maganar da shiba."
nan ta labarta masa ranar auren da kuma wacce zai aura.
Sagir ya girgiza da jin wacce S.MAN d'in zai aura ya ce "To ai ina ma kadunan dama yau zan
wuce Kanon da yamma sai mu wuce kawai."
Ummi ta ce "To shike nan bari na fara shiri."
Sagir suna gama waya da Ummi cikin hanzari yanufo gidan S.MAN, tun kafin ya iso yakirasa a
waya ya tambayesa ko yana gidan, ya ce yana nan babu in da yaje.
yana isa gidan a parlour'n kasa ya iske shi yana zaune yana kallon sa cikin kwanciyar hankali.
Sagir ya karaso cikin parlour'n ya zauna kan kujerar da ke fuskantarsa tun kafin ya karasa zama
ya ce
"S.MAN da gaske auren yarinyar nan zakayi?."
d'an dubansa ya yi kana yamai da idanunsa kan TV
"Tantama kake?."
"Amma dai S.MAN kana son yarinyar nan? idan kasan ba sonta kake ba pls kabarsu suyi auren
su, kada ka cutar da su."
baki ya tab'e kana ya ce
"I don't think I love this girl, even if we get marry I will divorce her."
"What! amma meyasa zakayi hakan dan Allah ka fita a sha'anin yarinyar nan, ka barta ta auri
wanda yake son ta."
wani kallo ya wasa masa kana ya mike tare da fad'in
"Idan ka gama zaman zaka tafi ka kashe min TV."
ya haye sama yabar Sagir agun baki bud'e.
haka nan Sagir ya bar gidan yana alwadai da son kai irin nan S.MAN..
Baba musamman yayi tattaki zuwa gidan su Kamal yasa akayi masa sallama da mahaifin
Kamal.
nan Baba yashiga shirya masa zance cikin hikima da dabara daga karshe ya d'aura da fad'i.
ai tun da dad'ewa dama da alkawarin aure sakanin S.MAN da SEEDRAH tun mahaifinsu na da
rai.
sai da wannna auren ya taso kafin aka tono maganar da aka jima da binne ta, dan haka suke
son cika alkawarin da suka d'auka, sucika burin mahaifinsu.
ya maido masa da kud'in sadakin su, kud'in da ya dawo musu da shi kuwa yacire ne cikin kud'in
da S.MAN ya bashi.
wani d'an uwan Baban Kamal ya buga kasa ya ce
ba a isa ayi musu wannna aikin ba sai da suka tara jama'a tukun za a tozarta su.
Baban Kamal daya shiga rud'ani sosai ya ce yabar maganar, kana ya ce wa Baba shike nan
Allah yasa hakan shine mafi alheri.
Baba ya koma gida a kunyace dan kuwa mutane sunyi ca a kanshi kowa yana fad'in ba ayi wa
dangin Kamal da shi Kamal d'in adalci ba.
amma ya gwammace jin wannan kunyar da kunyar da S.MAN zai janyo masa...
Ko da labari yashiga kunnen Kamal tamkar zai haukace sabar kid'ima.
ya yi ta kiran lambar SEEDRAH bata d'agawa hankalin sa yakuma mummunar tashi, saiga
Kamal kuka wui-wui da idanunsa, yaso yaje gidansu SEEDRAH amma Baban sa ya hanasa. ya
ce har idan shi ya haifesa bai yarda ya taka kafarsa a kofar gidan su SEEDRAH ba.
yana zaune a d'akin sa Mukhtar da wasu abokansa sai bashi baki suke, shikam ina baya jin su
sai aikin kiran wayar SEEDRAH ya ke wan da har lokacin yana ringin ba a d'agawa, lokaci zuwa
lokaci kuma ya share hawaye.
yana mikewa tsaye ya yanki jiki ya fad'i, nan aka garzaya da shi zuwa asibiti.
A b'angaren SEEDRAH kuwa har yanzu bata san abunda yake faruwa ba, dan 'yan uwan Mama
da ita Maman kanta babu wanda ya sanar mata abun da ke faruwa.
ta nimi wayarta kuma ta rasa Aunty Rashida ce ta d'auke wayar ta b'oye dan tasan dole ne
Kamal d'in zai kira ta.
Yau juma'a da misalin karfe 11 na safe Aunty Rashida tagama zizarawa amarya SEEDRAH jan
lalle, mai matukar kyau da tsaruwa irin na amare.
abun ka da farar mace ba karamin kyau jan lallen ya yi mata ba.
SEEDRAH ce zaune gaban Mama da 'yan uwan Maman da suka zagaye ta.
jikin ta ya yi sanyi sosai dan zaton ta nasiha zasuyi mata dan tun da akasa ranar auren kullum
acikin yi mata nasiha ake.
Umma Bishira tad'an nisa cike da fargabar abunda zaije ya dawo ta ce
"SEEDRAH kiyi hakuri da abunda zai fito daga bakin mu, amma idan kikayi nazari zakiga
dacewar sa duba da halin yau da babanki ya ke ciki, SEEDRAH kizamo 'ya mai biyayya wa
iyaye hakika zaki sami dace wa da rahamar Allah kiyi hakuri kiyi biyayya wa iyayen ki da kuma
mijin ki, kiyi hakuri ina mai baki hakuri kizamo 'ya mai biyayya wa iyaye." shiru tayi kanta a kasa tana sauraron ta. a kasan ranta take fad'in
"Yau kuma nasihar har da biyayya wa iyaye ne."
muryar Umma Bishira ta sinkayo tana fad'in
"SEEDRAH a yau auren da za a d'aura miki bada Kamal za a d'aura ba da Usman wato S.MAN
za a d'aura, yasami mahaifinki ya sanar masa ya na sonki ankuma juya auren yadawo kansa,
dan haka kiyi biyayya wa iyayenki ki karb'i kaddarar data zo miki a haka."
duk suka shiga yi mata nasiha tayi hakuri ta d'auki dangana.
wani irin duuummm haka taji kunnuwan ta sunyi mata
ido ta ware kan Mama da tuni idanunta suka cuko da kwalla cikin harhad'a kalma da sarkewar
numfashi ta ce
"Ma..Ma..Mamaaa wai.wai..me.mee..suke fad'a ne!."
cikin matukar tausayi Aunty Rashida ta riko hannunta cikin nata ta ce
"Kiyi hakuri SEEDRAH haka Allah ya hukunta miki S.MAN ne mijin ki ba Kamal ba wannan
rubutacce ne tun ran gini ranzane."
Mama ko hawaye ta share cikin jin tausayin d'iyar tata.
d'ipp jinta da ganin ta suka d'auke sai fafutukar fizgo numfashin da yake kokarin barinjikin ta
take.
a kid'ime duk sukayi kanta Aunty Rashida da tafi kusa da ita ta janyo ta jikin ta ganin tana
kokarin sulalewa kasa,
nan take numfashin ta ya d'auke.
ruwa aka shiga yayyafa mata amma ko gizau batayi ba.
Mama kam tama rasa me zatayi sai gefe taja ta zauna tacigaba da sharar kwalla.
hayaniyar da Umma tajine had'e da salati yasata shigowa d'akin Mama da sauri, ganin halin da
SEEDRAH ke ciki tafita tacewa Halimatu tayi sauri taje ta kirawo Dr Maryam wata makociyarsu.
sai a lokacin Umma ta sami labarin abun da ke faruwa ta tausayawa SEEDRAH matuka, sai dai
a wani b'ari na zuciyarta bataji dad'i ba dan tasan irin kaunar da 'yarta take yi wa S.MAN tajima
tana mata fatan samin sa, amma ina yanzu kam ya dad'a mata nisa.
Dr Maryam tazo ta duddubata nan tashiga bata taimakon su irin na likitoti.
ta ce musu dogon suma tayi amma zata farfad'o insha Allah.
ta d'aura mata ruwa da zai taimaka mata wajen dawo hayyacinta had'e da allurai.
ta ce kada a rika surutu kusa da ita sukayi ta mata godiya kana tayi musu sallama ta tafi.
nan aka ragu a d'akin kamar yadda likitar ta ce.
nanfa gidan biki ya kacame kowa da fad'i albarkacin bakinsa,
masu san barka sunfi yawa dan a cewarsu a yanzu samin miji kamar S.MAN yana da wuya ga
dukiya ga kuma d'aukaka.
Suhaita da Halimatu kuwa kamar su kashe kansu dan bakinciki.
musamman Suhailat dake mahaukacin son S.MAN SEEDRAH tasha tsinuwa yafi cikin kwando
a gurin ta.
har cewa tayi wai dama ashe sonshi take shiyasa tayi ruwa tayi saki wajen ganin taje gidan sa
aiki.
har kuma fatan mutuwa tayi mata wai Allah yasa kada ta farka daga wannan suman sai dai ta
farka cikin kabarin ta.
A b'angaren Kamal kuwa 'yan uwa ne tam kansa a asibiti bayan ya farfad'o, abin tausayi da
kuka ya farka kamar karamin yaro.
sai baki ake basa yayi hakuri ya bar wa Allah komai.
Maman Zeey da ta shigo d'akin da aka kwantar da shi hankali tashe labari ya isketa, Zeey na
biye da ita.
cikin matukar tausayawa Maman Zeey ta maso bakin gadon taruko hannunsa tana fad'in
"Yi hakuri Ya Kamal."
hannunta ya kankame yana wani irin kuka.
duban Alhj Tahir mahaifin Kamal Maman Zeey tayi kana ta ce
"Aje a cigaba da shagalin biki baza a fasa komai ba idan lokacin da aka saka na d'aurin aure ya
yi aje a d'aura da Zainab."
tayi maganar tana nuna Zeey dake tsaye duk tausayin Kamal ya cikata, sai sharar kwalla take.
Alhj Tahir da maganar yazo masa a bazata ba shiba duk wanda ke cikin d'akin, musamman
Kamal da Zeey.
Alhj Tahir zaiyi magana Maman Zeey ta ce
"Alhj yanzu ba lokacin tsayuwa magana bane an tara jama'a aje a ji da jama'a kada kuma lokaci
ya kure."
Bayan sallar juma'a dandazon jama'a suka shaida d'aurin auren Usman Sulaiman S.MAN da
amaryarsa SEEDRAH.
kamar yadda aka shaida d'aurin auren Kamal da Zeey.
Bayan d'aurin aure kuwa wasu 'yan'uwan Ummi da Goggo Larai suka kawo akwatuna set uku
ko wanne cike ya ke tamtam da kaya nagani na fad'a.
jama'a sai yabawa suke kowa sai fad'in albarkacin bakinsa ya ke, wasu na cewa ina ma a ce
'ya'yansu ne suka sami irin haka.
Gaggo Larai bataji dad'in ganin halin da SEEDRAH take ciki ba.
sai yamma lis SEEDRA farfad'o Hafsat da Yusrah ne a gefenta, ganin ta bud'e ido suka dad'a
matsowa kusa da ita har suna had'a baki wajen ce wa
"SEEDRAH kin ta shi sannu kinji."
da sauri ta rirrike hannayen su murya na rawa ta ce
"Dan Allah kuce min mafarki na ke, kuce min duk abun da naji mafarki ne ba gaskiya ba ku fad'a
min haka dan Allah!!."
tausayin ta ya bala'in kama su Yusrah har da kwalla duk da S.MAN d'an uwan tane tana daga
cikin na gaba-gaba masu farincikin aurensu.
amma bata so auren nasu yazo a haka ba, taso a ce babu wani wanda SEEDRAH ta ke so, ko
da ace bata son yayan nata ta tabbata zaman su zaifi d'an gwanda-gwanda.
SEEDRAH taci gaba da fad'in
"Dan Allah ba a d'aura auren ba ko kuce min ba a d'aura ba."
kai Hafsat ta girgiza ta ce
"SEEDRAH hakuri zakiyi amma an d'aura."
wani uban ihu ta saka da gudu mutane suka shigo d'akin.
ta birkice kamar mai tashi aljanu da kyar da rarrashi aka samu tayi shiru.
Aunty Rashida taja hannunta suka shiga bathroom, ta dubeta ta ce
"Kiyi wanka SEEDRAH zaki dad'a jin dad'in jikin ki."
ido tap da kwalla ta ce "Aunty Rashida yanzu da gaske anraba ni da Kamal ke nan."
kai Aunty Rashida ta girgiza ta ce
"Ki nason ciwon Maman ki ya tashi?."
da sauri ta girgiza kai
"To yi wanka ki fito kinji kiyi shiru ki dai na kukan, ga ruwan wanka nan na had'a miki."
ta nuna mata ruwan wasu had'in sinadaran kamshi.
kai ta gyad'a Aunty Rashida tafita taja mata kofar bayin.
kaya ta cire mata had'e da babban hijabi ta feshe su da turare, tana fitowa ta bata ta saka
lokacin har an fara kirare-kirayen sallar magriba, bayan ta gabatar da sallar magriba da wad'an
da ake binta.
Aunty Rashida ta kamo hannunta suwa nufi d'akin Baba acan ta dadda Mama.
nasiha sosai Baba ya yi mata tare da ban hakuri Mama ma haka tana yi tana sharar kwalla.
SEEDRAH kam sai kuka yanzu kam ta fara yadda da gaske S.MAN aka aura mata.
Goggo Larai taruko hannunta ta d'agota suka fito jin ana cewa afito a tafi Aunty Rashida na rike
da d'aya hannunta.
Kuka sosai SEEDRAH take kamar ranta zaifita haka aka shigar da ita motar Aunty Rashida da
Goggo Larai suka sata a tsakiya.
Sagir ne ke jan motar Bashir na gefensa suna jiyo sautin kukan ta, Sagir tausayin ta ya kamashi
"Tabbas S.MAN bai kyauta ba."
ya yi maganar a kasan ransa.
Har suka isa gidan SEEDRAH na kuka su Aunty Rashida na aikin rarrashi.
Bashir ya faka motar yafito ya bud'e musu su Goggo Larai suka sauko SEEDRAH kam taki
sauka sai ma sautin kukan ta data kara.
da kyar suka samu suka lallab'ata har da su Sagir d'in kafin ta sauko.
d'akin kusa da wanda ta tab'a zama ciki aka shiga da ita, tun da take gidan bata tab'a shiga
d'akin ba.
sosai d'akin ya tsaru ko mai nacikin sa blue and white.
'yan kawo amarya sunyi kallo a wannan duniyar S.MAN d'in, wasu ko sun nuna kauyancin su
kamar irin su Aysha JB marubuciyar Mijin Babata aminiyar Rasheedat S Director har tuntub'e
ake sabar anga daula.
nan fa aka shiga kwashe mutane ana maida su inda aka d'auko su.
aka bar amarya daga ita sai kawayen ta biyu Hafsat da Yusrah.
Da misalin karfe goma motar S.MAN ne yashigo gidan, a farfajiyar gidan ya tadda su Bashir
kallon tuhuma yabisu sa dashi kana ya ce
"Me ya sai da ku baku tafi ba me kuke jira?."
Bashir ya ce "Jiran ka muke mana muraka ka gun amarya."
wani kallo ya wasa musu ya ce
"A kan bana da kafa ne ko bansan hanya ba."
Sagir ya ce "To siyan bakin kuma fa wazai siya maka."
tsaki yaja kana yasoma tafiya yana fad'in
"Kun gama kwashe mutanen cikin gidan ko da saura?."
"Akwai Yusrah da wata kamar amarya."
cewar Sagir ya ce
"To kujira su ku maida su gida suma."
dariya Bashir ya yi ya ce
"Amma dai a barta tahuta gajiyar bikin nan dai tukun."
bai kulashi ba ya wuce abin sa.
Direct sama ya haura yarage kayan jikin sa. kana ya d'au wayar sa ya lalub'o lambar Yusrah.
tana d'agawa ya ce
"Ku fito su Bashir su kaiku gida."
ta ce "To."
ya jefa wayar kan gado kana ya fad'a bathroom.
Yusrah ta dubi Hafsat dake shirin kwanciya ta ce
"Wai mu fito a maida mu gida."
ido Hafsat ta ware ta ce
"Inji wa?."
"Inji Ya S.MAN ke nan."
"Kam bala'i lallai wannan ba sauki."
cewar Hafsat tana mike wa ta d'au mayafinta, ta dubi SEEDRAH da ke zaune zuwa yanzu kam
zuciyarta yagama bushewa kukan ma yatsaya da kansa, ita kad'ai tasan abun da take kisawa a
ranta.
ta ce "To amarya angonki ya kore mu sai gobe in munzo cin kaza."
wani uban harara ta galla mata kana taja dogon tsaki.
dariya duk suka tuntsure da shi sukayi mata sai da safe suka fice.
Suna fita ta mike taje ta sawa kofar key, kana ta shige bathroom taje ta d'auro al'wala ta fito sai
a lokacin tasamu tagabatar da salla isha.
tana idarwa tamike taje tacire kayan jikin ga tasa wani doguwar rigar bacci pink ta haye gado.
lamo tayi a kan gadon ya yin da tunani iri da kala suke ta zuwar mata
"Ko Kamal yana cikin wani hali?."
wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata ta share kana takuma gyara kwanciyarta, tana shirya
kalar zaman da zatayi a cikin gidan nan yazama dole ta d'au fansa.
idanunta ta rumtse tana jin yanda kanta yake wani irin sara mata.
da sauri ta d'ago jin an bud'o kofa taya akayi haka dan ita dai a sanin ta tarufe kofar, da sauri
kuma ta kalli saman mirror tagama mancewa ma da tazare key d'in a jikin kofar sabar damuwa.
da sauri ta mike ta zauna tana jifansa da wani irin mugun kallo mai cike da zallar tsana.
yana sanye cikin rigar bacci fari sol mai mad'aurin igiyoyi ta gaba,
rigar tad'an wuce guiwarsa kad'an, ya mai da kofar ya rufe kana ya tako cikin d'akin.
ya karaso ya zauna bakin gado yana fuskantar ta.
cikin nuna isa da takama ya ce
"Oya ta shi ki tub'e kayan jikin ki."
wani kallon sama da kasa tayi masa kana ta ce
"Allah ko ah lallai kayi kokari ba shakka!,
wannan jiki mallakin Kamal ne shine kad'ai ke da ikon ganin sa, bawani katon gardi ba,
Allah bazai