Showing 39001 words to 42000 words out of 78655 words
Chapter 14 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
ya waro kan b'arnar data tabka masa cikin d'aga murya ya ce
"Ke!."
maigadi yad'aga kai sama yana fad'in
"Oga basai ma ka sauko ba
amma dai tayi b'arna wanna ganyen turai d'in tasha tsinka yo ko kwad'o zakiyi da shi ai iya
kaci."
ganin ya rufe glaas d'in windon tasan saukowa zaiyi ai da gudu tayi ciki, tana shiga parlour
shikuma yana step d'in farko na sama yana kokarin sauka.
kafin ya sauko tuni tayi cikin d'aki ta murza key.
kofar yashiga bubbugawa da karfi yana fad'in
"Ki bud'e kofar nan!.
ta ce " Wlh bazan bud'e ba bazan bud'e kayi min bugun uban wani ba, ni ba 'yar ka bace kajira
ka haifa tukun ka buga."
bugun kofar yake yana cigaba da fad'in
"Na rantse idan kika shigo hanuna sai na ɓaɓɓalla ki na taraki anan."
"Ai wlh baka isa ba zakaga gatana kuwa, aiki ka sani kuma nayi maka baka da bakin wata
magana."
naushin kofar yayi da kafa kana ya juya yabar jikin kofar.
SEEDRAH ko ido ta zazzare dan ta gama zaton kofar ta b'alle dan ba naushin wasa yayi wa
kofar ba.
jin shiru bai kuma wata motsi ba sai ta koma bakin gado ta zauna tana mai da numfashi da
fad'in
"Haka kawai dukan da bazaka iya ramawa ba,
ai wlh da baka fito bama da kaf saina yanke fulawan nan nazubar da su, ba aiki kace ba."
(AFWAN NASAMI KORAFI GA WASUN KU SUN CE SU BASUSAN MEYE GARU BA KUMA
DUK LITTATTAFAI NA DA KALMAR NAKE YAWAN AMFANI TO YA ZANYI TUN DA HAUSAN
GARIN DA NAKE KENAN KUMA NA SABA AMMA ZANYI KOKARI ZAN RIKA RUBUTO
MUKU IN DA ZAKU FAHIMTA. GARU BANGO KENAN KO KATANGA SHIMA DUK GARU NE
KURIKE SUNAN DAN BAZANYI MUKU ALKAWARI A KODA YAUSHE ZAN RIKA SAKO
MUKU BANGO BA KU DAI RIKE SUNAN SA GARU KAWAI DAN YA KAMA BAKI NA)
Ranar SEEDRAH wasan b'uya tashiga yi da S.MAN ko ai ki take idan taji motsin sa saita gudu
d'aki ta kulle kanta ciki
a haka suka kwana.
washegari kuwa data fito ta hango sa yana gurin motsa jiki, sai ta fasa gyaran parlour'n ta sulale
tayi kichin sai da ta kulle kofar kichin d'in kafin ta soma aikin.
ko da ta gama ta bud'e kofar a hankali ta leko kanta can ta kuma hango sa yana ta uban gudu
bisa na'ura, cikin sand'a ta fito a hankali tahaura sama.
tana aje kayan brekfast d'in ta shiga gyaran parlour'n da sauri-sauri tana kammalawa ta shige
bedroom nan da nan tagama ta fito da sauri tanufi kofar da zata sauko kasa.
wani irin wawan burki taja sakamakon ganin sa ya sako kai zai shigo.
tad'an tsorata da had'uwar da batayi zato ba sai kuma ta wayence ta had'e fuska ta masa gefe
ta bashi hanya dan ya wuce.
hannuta ya cafko da karfi ya murd'e hannun.
tasaki uban kara tare da fad'in
"Wayyo Allah na wayyo hannuna ya karyamin hannu."
takuma sakin wani kara jin yanda yake cigaba da murd'e hannun wane zai karya shi.
ido ya zubawa fuskarta batare da ya saketa ba burin sa kawai yaga hawaye cikin idanunta, duk
ihun da take d'in nan kuwa babu d'igon hawaye a idanunta.
sulalewa kasa tayi yabita batare da ya saki hannun nata ba yasaka guiwansa d'aya a kasa yana
mai cigaba da mud'e hannun nata.
cike da jin azaba tafashe da kuka cikin muryar kuka da tuni hawaye yashiga zubowa idonta ta
ce
"Wayyo Allah na wayyo hannuna wayyo Mama ya b'allamin hannu, wlh idanka karya ni kaima
sai an karya ka."
sakin hannun nata yayi kana ya mike tsaye tare da karkad'e hannunsa ya dube ta da kyau kana
ya ce
"Da ma burina naga hawaye a cikin wad'an nan marasa kunyar idanun naki, duk san da kika
kuma yi min b'arna acikin gidan nan sai na sauya miki kamanni."
yajuya ya shige d'aki ya yafito rike da key d'in mota yafice ya bar gidan.
da kyar ta iya mikewa ta sauko kasa, a parlour'n kasa ta zauna bata iya shiga d'aki ba tana
tallafe da hanunta datake ji kamar baya amfani.
tajima sosai zaune a gurin sai da taji hannun yad'an rage mata zugi kana ta mike ta shiga d'aki.
kwanciya tayi a kan gado ta d'aura hannun kan pilo.
wasu zafafan hawaye ne zuka zubo mata takai hannunta mai lafiyar ta share haushi da tsanar
S.MAN cike fal cikin zuciyarta
"Lallai wan nan zai iya kashe mutum dan babu imani atare da shi."
tayi maganar a kasan ranta, tana nan kwance a haka har baccin wahala ya d'auke ta.
Ko da S.MAN yafita gidansu ya je, suna zaune a parlour gaba d'aya hankalin Ummi na gare sa.
ta d'an numfasa kana ta ce
"Amma Usaman meyasa ka zab'i ajiye 'yar aiki a gidanka akan mata?, madadin kayi aure ka
ajiye mata agidan sai ka d'auko wata 'yar aiki, duk da ita d'in 'yar uwar ka ce amma ai itama nan
bada jimawa ba zata iya yin aurenta,
shikenan sai dai karika d'auko 'yan aiki bazakayi aure ka ajiye mata cikin gidan ka ba."
"Bana da lokacin ajiye mace yanzu duba da abun da nasa gaba, Ummi bazai yuwu ma nayi
aure yanzu ba har sai na nutsu guri guda."
"Usman harsai yaushe ke nan girmafa kake 'yan kwallo nawani suke da mata kuma suna tafiya
ko wani kasashe, kayi aure zanfi samin kwanciyar hankali ni ma naga jikokina."
"Allah yakawo lokaci."
yafad'a yana mikewa, wai shi da baya da ko budurwa ma ake masa wani zancen aure, dan shi
dai har yanzu baiga mace cikin matan da suke bibiyarsa ba.
ya yi wa Ummi sallama ya tafi...
SEEDRAH da bacci kamar kasa har wajen karfe 2 na rana bata farka ba.
S.MAN da yanzu dawowan sa daga masallaci ya yada zangonsa a parlour'n kasa,
ya zauna tsawon wasu 'yan mintuna yana daddana waya daga bisani ya aje wayar kana yakai
hannu yashafi cikin sa daya fara jin yunwa. bin parlour'n yayi da ido baiga alamar wata kula na
abinci a gurin ba,
ya maida dubansa can kan dinning shima babu komai.
d'an shiru yayi yana tuna tun zaman sa a nan baiji motsin ta ba ko a kichin ne, sai ya mike ya
nufi kichin d'in ya leka baiga kowa ciki ba, babu kuma alamun an d'aura girki.
juyawa yayi yanufi d'akin da take yatura kofar, can ya hangota kwance kan gado tana ta sharar
baccin ta.
daga bakin kofa in da yake tsaye ya ce
"Ke bacci ne yakawo ki gidan nan wa kika ajiye da zai miki girkin."
nauyin bacci irin na SEEDRAH batama san yana yi ba,
shiko ganin kamar tana jinsa tayi burus da shi ne yacigaba da magana a hatsale amma har
lokacin bata ko matsa ba.
a hatsale ya tako bakin gadon yana cigaba da fad'in
"Ke wai ni sa'an ki ne ina magana kina kwance zaki tashine kosai na sauya miki kamanni a
nan!."
yayi maganar cikin d'aga murya sosai kuma cikin tsawa.
sai a lokacin tad'an motsa tare da yin mika ta juya kai tare da cigaba da baccin ta dan ita bata
ma san yana yi ba.
cikin matukar jin haushi yarasa ma me zai mata sai ya juya yaje in da fridge yake ya bud'e
yaciro gorar ruwa mai sanyi har wani turiri yake tsabar sanyi, ya dawo bakin gadon kana
yabud'e marfin gorar ya saiti dai-dai fuskarta yashiga tuttud'a mata ruwan.
a gigice ta farka tare da kwalla kara ta mike zaune tana ware ido a kansa dan ba karamin firgita
tayi ba.
shiko ragowar ruwan yakarasa sheka mata a wuya ya gangara cikin kirjinta, kuma zabura tayi
tamike ta saka guiwawinta saman katifa tana fad'in
"Wayyo Allah sanyi me namaka Allah bazan yafe ba."
ya ce "Idan da baki tashi ba d'aukar ki zanyi nasakaki cikin fridge d'in na kulle ki ciki, ke har kina
da wani ikon yin bacci ne a gidan nan, idan na sake ganin ki kin kwanta kina bacci kamar
mushe sai na sauya miki kamanni,
tukun na ma ina abincin rana?."
baki ta turo gaba tare da d'an murgud'a shi tana d'an jajjan rigarta da ruwan yasa ya lafe ajikinta
sosai, har ana iya hango shatin bakin ababen jirjinta da bata saka musu bra ba, ga kuma wuyan
rigar daya d'an zamo.
ya ce
"Zaki tashi kije ki d'aura girkin ne ko ya."
baki takuma turowa tare da sakar masa karamar harara ta ce
"To ka fita mana ba ka fad'a ba zan fito ai."
tayi maganar tana janyo hijabinta dake kan gadon ta rufe jikin ta.
tsaki yaja kana ya juya yafita yana fad'in
"Ki b'ata lokaci ki gani."
Sauka tayi a gadon tana jan tsaki da fad'in
"Mugu azzalumi kuma Allah ya isa."
bayi ta shige
ta tub'e jikakkun kayan tayi wanka tare da d'auro al'wa ta fito,
sai da ta gabatar da sallar azahar kana ta sauya wasu kayan sannan ta fito.
yana zaune a parlour'n rike da sigari yana d'an zuka yayin da idanunsa ke kan t.v
tazo zata wuce shi ta nufi kichin dai-dai lokacin da ya buso hayakin sigari ya ce
"Sai kinyi ra ayi ne ma kafin ki fito, aduk b'ata lokacin da zakiyi a kan wani aiki acikin kud'in aikin
ki dan ko wace karya doka sai anyi mata kud'i."
kai ta kawar gefe tare da yamutsa fuska tana kore hayakin sigarin da hannunta kana ta toshe
hanci da sauri tabar gurin.
sai da ta shiga kichin kafin ta saki hancin ta tana sauke numfashi, a fili ta furta
"D'an kwaya ma da ban yake."
Ko da ta gama girkin ta d'ibo ta kawo masa sannan ta d'ibi na maigadi ta kai masa kana ta d'ibi
wan da zataci tayi d'aki...
Bayan kwana biyu
SEEDRAH ce zaune cikin parlour bayan ta gama duk kanin ayyukan ta tana huta gajiya.
wayarta ce tayi kara da jin sautin dake tashi na musamman wan da mutum d'ayane ke da
wannan sautin, murmushi ta sake tare da d'aga kiran ta
kara wayar a kunnen ta tare da yin sallama.
a b'angaren Kamal kuwa numfashi mai sauti ya sake tare da amsa sallamar kana ya ce
"Me yasa hakan?."
ido ta d'an lumshe tare da bud'e su lokaci guda takai bayan ta jikin kujera tana mai dad'a manna
wayar a kunnen ta sannan ta ce
"Me ya faru?."
ya ce "Gani a kofar gidan ku Mama ta ce min wai kina gidan yayan ku yau kwana nawa ma,
amma shine babu ko labari ashe duk wayar da muke da ke ma kina can da ban zo ba da baza
ma ki fad'a min ba kenan."
to taya ma zatayi ta iya fad'a masa taje gidan wani aiki akan bashin da ake bin Baban ta, duk da
tasan Kamal mutum ne mai fahimta amma ina bazata iya fad'a masa sirrin gidan su ba.
ta ce "Ayya wai dama bamuyi magabar ba ai na d'auka na fad'a maka nazo gidan sa ayya na
sha'afa ne to gaba d'aya, ayi min afwa."
ya ce "Da nayi fushi amma yanzu na hakura."
ta ce "To godiya nake."
Nan suka shiga hirar su na kauna da soyayya cikin hirar yake tambayarta
"Wai wani yayan ku ne ma?."
ta ce "S.MAN yaron kanin Baba." ya ce
"Oh S.MAN wannan d'an kwallon ko ai ina matukar son buga wasan sa dan wlh ya iya kwallo
sosai dawowan sa ma daya ciyowa Nigeria kwallo ai damu akaje a ka cashe a hall."
hab'a ta rike ta ce "Wai rawa kukayi?."
dariya ya yi kana
ya ce "Shagali ne kawai amma an d'anyi rawan ma, daga nan kuma mukaje muka buga kwallo
saboda farin cikin kasarmu tayi gaba."
"Wai dan Allah kaima kana wannan aikin wahalan ne."
"Ke kwallon ne aikin wahala kinsan kwallo kuwa, to duk wanda kika gansa yana kwallo ki
girmamashi daga yau ma ki kara girmama S.MAN fiye da da,
dan shi d'in a can saman-sama yake babbane."
baki ta tab'e a ranta ta ce
"Ina abin girmamawa a tare da shi mutumin da baisan darajar mutane ba Allah ya sawaka."
a fili kuwa dariya kawai tayi.
maganarsa ta jiyo yana fad'in
"Ashe ya yi aure ma amma dai auren sirri ya yi dan banji labarin ba ko a kafafen yad'a labarai,
kai manyan nan fa yanzu sun dage da auren sirri babu mai sani zasuyi abunsu sululu su shige
da matansu ciki,
da gaskiyarsu su killace matansu ba suyi ta nunawa duniya tana gani ba, yafi ai suyi kishin
kayansu, kai nimafa irin wannan auren zamuyi dan babu wani bikin da za'ayi daya wuce
walima."
d'an shiru tayi tana nazarin maganar tasa, wato shi tunani ya ke S.MAN d'in yana da mata, shi
yasa ma tazo gidan nasa,
to ma taya zatayi tace masa bashida mata kuma take zaune a gidan.
maganar sa ta kuma sinkayowa ya na cigaba da fad'in
"Ki gai da Aunty'n namu watarana zaki rako ni na gaida ta idan basu koma ba, amma dai yau
zaki koma gida ko?."
kai ta girgiza kamar yana ganin ta sai kuma ta ce
"A'a ba yau ba."
ta fad'a a takaice
"Sai yaushe ko sai zasu koma tukun?."
ta ce "Eh." ido ya waro ya ce
"To gaskiya bazan iya jure rashin ganin kiba tun da bansan yaushe zasu tafi ba zan dai zo
narika ganin ki a can d'in, kar kumafa su d'auke min ke sutafi min dake kasar turawan nan ace
sai nayi kud'in jirgin d'auko ki."
dariya tayi ta ce "Haba dai sai ka tara kud'in jirgi kenan."
shima dariyar ya yi ya ce
"Da gudu ma kuwa."
jin karar bud'e kofar parlour tasan S.MAN ne ya shigo dan haka tayi saurin cewa Kamal bari tayi
wanka anjima zasuyi waya.
ya ce to. sukayi sallama ta sauke wayan dai-dai lokacin da yake karaso wa cikin parlour'n
yad'an kalle ta tare da fad'in
"Zan fita yanzu kije ki wanke min mota ki goge yanzun nan."
ya wuce yafara haurawa step's, mikewa tsaye tayi sannan ta ce
"Ban iya ba."
sai da yakai karshen matattakalar sannan ya ce
"Alhj Musa kam dole zai iya dan nasan bashi da kud'in da zai iya kai gura-guran motar sa gurin
wanki sai dai idan fashi zai koma so dole shi yake wanke sa da kansa, bare kuma wad'an nan
motoci masu tsada wankin su ai bazai bashi wuyaba shi zai zo ya wanke su yanzu."
Cikin d'aga murya ta ce
"Ya ishe ka ka dai na kokarin rika aibanta Babana dan uba baifi uba ba."
cak yaja ya tsaya tare da juyowa kana ya maimaita kalmar "Uba baifi uba ba."
tarar numafshin sa tayi da fad'in
"Kwarai kuwa amma ka sani duk yanda kake son ka kaini bango bazan tab'a iya fad'ar
mummunar kalma akan Abba ba, dan har gaba da abadan yana da kima da darajar uba agareni
dan abun da ya yi Baba shi ya yi Abba, duk nasan darajar su ba kamar kai d'an kwaya d'an
shaye-shaye ba."
Wani irin waro idanu ya yi kan kace me idanun nasa sun sauya kamanni,
b'acin rai fushi tafasar zuciya kake iya hangowa cikin su,
ganin yan da ya d'aga kafa cike da KARSASHI tamkar zai duro daga saman matattakalar izuwa
kasa.
ai ko ta d'aga kafa dagudu kafin tace zata shiga d'aki ya iso ta ya samata kafa ta zube kasa.
bin ta yayi kasan tare da shako wuyarta.
wani irin tsoro ne ya baibayeta, idanunta tarufe da karfi dan ji take bazata iya bud'i idanunta a
kansaba dan ya koma mata abin tsoro.
cikin fusatacciyar murya mai nuni da zallar tafasar zuciya ya ce
"Ni ni ne d'an kwaya d'an shaye-shaye a ina kika tab'a ganina da kwaya a ina kika gansu!."
yayi maganar cikin tsawa tare zuba mata gigitaccen maruka biyu da sai da suka d'auke mata jin
ta na wucen gadi,
yashiga nuna ta da hannu yana fad'in
"Zan sauya miki kamanni sai na b'allaki na taraki anan."
ya angiza ta kanta yagaru da kasa,
ya mike ya haye sama yana huci.
fizgar numfashin ta tayi da kyar ta tattaro ragowar karfin ta ta mike zaune da kyar ta iya mikewa
tsaye ta shige d'aki a bakin gado ta zube, sai a lokacin taji wani kuka yazo mata ta fashe da
kukan tare da kife fuskarta jikin pilo tashiga rera kukan cike da kuna dad'acin rai.
kamar an zabure ta tamike tsaye tare da share hawayen ta tafito da sauri ta shiga kichin.
in da ta tab'a ganin soson waya taje ta d'auka ta fita ta dasauri ta nufi parking lot.
gindin pampo dake gurin taje takunna ruwa cikin boket d'in data gani a gurin ta d'auko ta kawo
sa kusa da motocin,
sai da ta dubi mota mai kyan ciki kana ta d'ibi ruwa a kofi ta wasa masa wannan soson wayar
data fito dashi tashiga dirza jikin motar da shi.
ta dage sosai tarika dirzan motar nan gefe da gefen sa gaba d'aya ta goga soson wayar ta
zazzana motar gaba d'aya tayi kaca-kaca da fentin motar.
mikewa tayi tana haki tare da rike kugu, ta girgiza kai tare da ciza baki ta juya da sauri ta
bargurin.
tana shiga ta ganshi yasauko cikin sabuwar shiga da d'an sauri yake tafiya ga dukkan alamu dai
fita zaiyi.
bin ta da ido yayi ganin duk ta jike ya ce
"Kin wanke motar ne ko ya?."
ta ce "Ah sosai ma kuwa har na gama."
tawuce da sauri ta shige d'aki, bin bayan ta yayi da kallo ganin yan da tayi saurin shiga
bedroom, sai kuma ya juya yafice waje..
Tun kan ya karaso parking lot d'in yake hango motar kamar an shafa mata wani abu, da d'an
sauri ya karaso gurin, wani irin waro ido yayi kan motar da yake ganin abin mamaki ajikin sa,
hannusa