Showing 36001 words to 39000 words out of 78655 words
Chapter 13 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
kina sammanin ko shekara goma zakiyi kina min aiki zai fanshe kud'in da
nake bin Alhj Musa ne,
million 30 nake binsa ba dubu talatin ba!!."
D'an sassauta shakar da yayi mata ya yi ganin yanda take ta fafutukar neman numfashi, kana
yazare hannunsa a wuyanta tare da angizata tagaru da jikin kujera.
SEEDRAH kuwa da gab'aya ta d'auke wuta tayi saurin dafe wuyanta inda take ji kamar ba a
jikin ta yake ba dan tsananin azaba, ta janyo numfashi dakyar tana mai da shi.
Cikin muryar fushi sosai ya ce
"Sai na rage miki numfashi duk ran da kika kuma tsayuwa a gabana kina fad'a min maganganun
da suka fito daga karamin kwakwalwar ki!."
ya juya da sauri yanayin yadda yake taku kad'ai zai tabbatar maka da fusatar sa afili dan hatta
cikin parlour'n amsa sautin takunsa yake, dip-dip-dip! haka yake tafiya kamar namijin zaki cike
da KARSASHI!.
can gefe cikin parlour'n in da
na'urorin motsa jikin sa suke ya nufa,
cike da zafin nama yashiga wujijjiga jikinsa bisa na'urar yad'au tsawon mintuna 30 kafin ya
sakaita motsa jikinsa ya sauka.
fridge dake zaune gefe a gurin ya bud'e ya d'au gorar ruwa mai sanyi, kan kujerar silve da
suke jere a gurin ya zauna yabud'e gorar tare da d'aura shi kan lips d'in sa.
saida ya shanye ruwan duka kafin ya d'ago gorar tare da yin wurgi da shi cikin parlour'n.
numfashi yashiga maidawa a hankali yayin da yake share gumin da yake tsastsafo masa da
wata karamar towel,
ya zaro sigari a aljuhunsa ya kunna yashiga zuka da d'an sauri-sauri.
A razane SEEDRAH ta d'ago jin fad'uwar abu dan har lokacin tana cikin tsoro, bakin nan nata
ya mutu musurus sai zazzare ido take, dan har lokacin bata dawo hayyacin ta daga shakar da
yayi mata ba.
yad'au tsawon mintuna 10 zaune sai a lokacin yaji zuciyarsa ya d'an sanyaya.
ya mike a sannu ya jefar da ragowar sigarin hannunsa saman wani table dake gurin, kana ya
tako cikin parlour'n,
ya zauna kan kujerar da d'azu ya tashi.
kasa tayi da idanunta,
shiko murmushi mai sauti ya yi tare da shafa d'an karamin gemun sa irin wan da 'yan kwallo
suke bare,
"Gargad'in ya shigeki kenan bakiga komai ba ma tukun."
ya yi maganar idanunsa a kanta.
lumshe idanunta tayi tare da kuma bud'e su a lokaci guda tad'an tauni gefen lips d'in ta.
magana ya soma ya yin da idanunsa ke kanta
"Gargad'i game da aikin gidan nan ina mai tabbatar miki da duk randa nasami wata kusku ranar
zaki fuskanci fushi na,
kaf fad'in gidan nan daga sama har kasa kama daga cikin kowani bedroom's da bathroom's
zuwa parlourn sama da kasa zaki rika gyara shi akowata safiya da maraice, girki safe rana
dare,
wankin kaya, sharar farfajiyar waje baiwa fulawa ruwa wankin mota, sune aikin ki,
sannan kuma da karfe 11 nake tashi daga bacci kuma ina tashi nake bukatar abin da zansa wa
cikina, kada ki kuskura lokacin ya wuce batare da kin tana da min abinci na ba,
sannan kuma brekfast a sama nakeyi sauran lokutan cin abinci kuma a kasa,
da karfe 11 nan kuma ki tabbatar da kinzo kin gyara min d'aki zuwa bathroom d'ina kafin gyaran
kawani bedroom's,
idan kika kuskura aka sami matsala aduk cikin abun da na lissafa mikin nan to ina mai tabbatar
miki
Alhj Musa shi zai fuskanci matsala!,
karfe 11 kin gama komai ko minti 1 kika kara a kai to kiyi kuka da kanki."
Shiru tayi tana nanata ayyukan daya lissafo mata a ranta, sai kace tazamo jaka to ma taya
zatayi ta iya duk wad'an nan ayyukan daga asuba zuwa karfe 11,har da aikin da yakamata
mazane suyi duk dasu zatayi.
kai ta jinjina zatayi bauta ko dun ta tseratar da mahaifinta daga tozarcin S.MAN.
Maganar sa tajiyo yana fad'in
"Da nayi niyyar can waje kusa da d'akin karnuka zaki zauna kirika shigowa kina aikin,to amma
kinci albarkacin zan iya bukatar abinci cikin dare dan haka ga d'aki can kishiga kizauna ciki."
ya nuna d'aya daga cikin d'akunan cikin parlour'n.
kwayar idanunta ta juya izuwa kofar d'akin da yake nuna mata kana ta dawo da kallon ta a
kansa sannan ta ce
"Nawa ne albashin aiki na?."
"Me yasa sai kin sani."
"Ko aikin gwamnati kaje nima ka samu ana sanar maka da iya albashin da za a rika baka, ka
d'auka hakanne,
zan fara lissafi daga kan yau da zanfara aiki, nakuma san adadin hakkina da za a rika cirewa
cikin bashin da kake bin Babana."
ido ya bita da shi wato bakin ta dai bazai tab'a mutuwa ba. ya ce
"Idan kika masa da tambaya amsar ga Alhj Musa zai isa, tashi ki b'ace min da gani, ki kai jakarki
ciki kifito da shirin fara aiki."
bata kuma magana ba jin ya sanyo Baba cikin maganar tasan ba mutunci gareshi ba sai ya iya
zuwa yaci mutuncin Baba.
ta mike a hankali taja akwatinta tanufi kofar d'akin daya nuna mata.
ta tura kofar a hankali takusa kanta ciki, a hankali tashiga takowa cikin d'akin yayin da take bin
d'akin da kallo.
d'aki ne babba komai na bukata yana ciki,
kama daga lafiyayyen gado babba da wardrobe wan da yacike b'arin bango guda, a gaban
gadon wata kujera ce ta alfarma t.v manne jikin garu-bango yana fuskantar gado ga fridge a
gefe bedside da ramb'asheshen mirro, da dai sauran su.
kayan d'akin duk irin na kasar waje tsaruwar sa yakai tsaruwa,
sai dai d'akin yad'anyi kura alamar dai babu mai rayuwa cikin sa.
a hankali ta isa ta aje akwatin ta kana ta cire mayafin kanta.
nan ta shiga kad'e d'akin ta gyara shi tsaf ta goge ko ina, kana ta sauya zanin gado data gansu
jere cikin wardrobe dan na kan gadon shima yayi kura.
ta d'auki wan da ta ciren ta shiga bathroom dan ta wanke, nan ta tadda washing machine ciki,
shima kansa bathroom d'in abin kallo ne dan kuwa yasha kayan alatu kamar ba band'aki ba.
da washing meshing d'in tayi amfani wajen wanke bedsheet d'in,
takuma yi amfani wajen busar da shi da goge shi, kana ta wanke bayin tsaf, sannan tayi wanka
tare da d'auro al'wala ta fito.
tana fita ana kiran sallar la'asar tagabatar.
ko da ta idar akwatinta ta bud'e ta ciro kayayyakin ta tashirya su cikin wardrobe dan tagama
sawa ranta zatayi zaman aikin da zata fanshi mahaifinta duk wuya duk rintsi.
tana saka akwatin cikin wardrobe taji ana bugun kofa sai kuma muryarsa data jiyo ya na fad'in
"Ba kwanciya yakawo ki gidan nan ba maza ki fito."
tsaki ta ja ta ce
"Sai kace kwanciya akace masa nayi."
Ko da ta fito parlour baya nan ciki, nan ta shiga tunanin ta in da zata fara.
nan ta talub'o kichin ta shiga
tasoma kiciniyar d'aura girki cikin awannin da basu fi uku ba ta shirya lafiyayyen girki, kan kace
me gaba d'aya gidan yakaure da kamshin daddad'an girkin ta.
S.MAN da tun fitar sa bai dawo ba sai daf magriba yana sanya kafarsa cikin parlour yashaki
wani daddad'an kamshi ba shiri ya lumshe idanunsa yana mai dad'a shakar kamshin.
SEEDRAH nagama gyara kichin d'in ta tarkaso kulolin data shirya abincin ciki tafito.
jin karar bud'e kofa yasashi bud'e idanunsa tazo tawuce ta gaban sa zata ta nufi dinning. ya ce
"Ke-ke-ke tsaya waya baki ikon girka abin da kikaga dama batare da kin tambaye ni ba, me ma
kika girkan tukun?.
cigaba da tafiyar tayi batare da ta tsaya ba ta ce
"Idan kazo ci zaka gani ai."
ta haura dinnig ta aje tray'n data jero kulolon ciki, gani ya dumfarota da sauri yana fad'in
"Ke ni kike cewa haka?." da sauri ta sauko daga kan dinning d'in ganin yana ta kokarin zuwa
inda take yana kokarin cafko ta aiko da sauri cikin had'awa da gudu tashige d'aki ta mai da kofa
ta rufe.
numfashi ta sauke tana fad'in
"D'an rainin hankali kabar kakuma sa hannu a jikina."
Shiko bayanta yabi da kallo tare da yin kwafa ya haura dinning, in da kamshin girkin ke ta
fisgarsa.
kular farko ya bud'e wani kamshi ne yabigi hancinsa babu shiri ya lumshe idanunsa ya yin da
yaji yunwar cikin sa yad'a karuwa.
had'edden jalof ne dayaji busasshen kifi da nama da kayan ganye sai fidda sihirtaccen kamshi
yake.
d'aya kular ya bud'e ferfesun kaza ce dataji kayan d'and'ano dana kamshi, tanuna luguf.
sai kofi mai d'an girma mai d'auke da kunun aya mai sanyi a ciki.
da d'an sauri ya zauna dan ba shakka yunwar cikin sa ta motsa.
sosai yaci abincin cikin matukar jin dad'in sa, yana ci yana tsiyayar kunun ayar nan yana korawa
da shi.
sai da yacika cikin sa tam sannan ya mike yad'au kular ferfesun kazar had'e da kofin kunun aya
ya haura sama da shi..
SEEDRAH kuwa bata kuma fitowa ba sai wajen karfe goma na dare nan ma sai da ta tabbatar
da babu motsin sa cikin parlour'n.
ta wuce kitchin ta zubo abinci ta koma d'aki.
tana gama cin abincin kiran Kamal ya shigo wayarta ta haye gado suka shiga soyawan su...
Washegari tana idar da sallar asuba ta fito
can gurin motsa jikinsa ta hangosa yana ta faman gudu bisa na'ura.
hararar bayan sa tayi a fili ta furta
"D'an wahala kamar wanda akasa dole Allah ubangiji yasa ka fad'i ka karya kafa da kugu, ko
idan kazo d'aga wancan katon karfen yafad'o ma a kirji."
takarashe maganar da jan guntun tsaki had'e da murgud'a baki kamar yana gaban ta.
ta shige tafara aiki.
gyaran parlourn kasa ta fara zuwa cikin bedroom's d'in cikin parlour'n kana ta wuce kitchin
tashiga kiciniyar had'a brekfast.
tana kammalawa tashirya masa nasa kan tray, da sauri ta nufo waje ganin lokaci nata tafiya.
ko da ta fito daga kitchin baya gurin motsa jikin, da sauri tashiga haurawa kan steps har ta kai
karshe, kana ta bud'e kofar dazai sadata da parlour'n sama da sallama ta shige ciki.
cak ta ja ta tsaya bakin kofar.........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 13
Ganin tsaruwan parlour'n mai kamada aljannar duniya shi yasata jan burki a bakin kofar.
idanunta ya sauka kan katon hoton sa da ke manne jikin garun parlour'n yana sanye cikin kayan
kwallo, a tsakiyar filin kwallo ya d'aga kafarsa zaiyi shot da ball aka d'aukesa a hoton, yayi
matukar kyau sosai.
idanunta ta janye daga kallon hoton nasa da kuma tsararren parlour'n nasa.
sai kuma ta d'an batsar tana tambayar kanta to ma ina wani abun burgewa a wannan gida da
mai gidan yakansace mutum mara d'a a.
taja gajeren tsaki kana tasoma takowa izuwa cikin parlour'n.
ta isa ta aje tray d'in saman table d'in sakiyar parlour'n.
nan tasha d'ammara da gyalenta ta shiga gyara parlour'n.
cikin mintuna kalilan ta tsaftace shi tas duk da dama dai bawani datti yayi ba.
tana gama gyaran parlour'n tad'ago ta na kallon kofofin bedroom's guda hud'u dake d'auke cikin
parlour'n tana tunanin ta in da zata fara,
idanunta ne yatsaya kan d'aya daga cikin kofofin
wanda dizainin d'in kofar ma daban ne.
anyi rubutu ajikin kofar wan da ga dukkan alamu ba mannashi akayi ba da shi aka kera kofar.
ido tad'an tsurawa kofar tana son gane abinda aka rubuta duk da da manyan harufa akayi
rubutun sai dai d'aya cikin d'aya akayisu,
kuma da yanayin kwalliya idan ma ba ka luraba zakayi zaton kwalliya ce kawai.
bata kaiga tantace ma'anar rubutun da take ji da wuya ma ta iya gane abin da ake nufi a ka
bud'o kofar.
waya na sakale a kunnensa yana magana, sanye yake da singilet da 3qrt ya karaso cikin
parlour'n, lokacin da yake sauke wayar a kunnen sa.
zama ya yi kan kujerar dake kusa da table d'in data d'aura kayan brekfast.
batare da ya kalli inda take ba ya ce
"Tsayuwa kalle kalle kikazo yi ko aiki?,
ai babu hutu cikin rayuwar ki acikin gidan nan, ko hutun sama da minti 10 bana kaunar naga
kinyi sa a cikin gidan nan,
wuce yanzu kije ki gyara min bedroom da bathroom sannan ki wanke min kayana ki goge."
wucewa tayi cikin d'akin da ta ga yafito daga cikinsa batare da tace komai ba, duk yanda
idanunta keta son janta izuwa kallon katafaren makwancin nasa zuciyarta kuwa yaki bada
damar hakan.
duk abin da yace tayi shi tayi kafin ta fito a d'akin.
yana nan zaune in da ta barshi yagama yin brekfast d'in.
tana kokarin barin parlour'n tajiyo muryarsa yana fad'in
"Kin gama duka aikin?."
kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta gyad'a masa kai.
"Baki da baki ne? da bazaki amsa min da bakin ki ba."
yafad'a yana jefinta da mugun kallo.
"Idan haka ka d'auka to hakan ne, ka tambaya kuma na baka amsa ai ba sai na amsa da baki
na ba, amsa magana da baki baya daga cikin jadawalin aikina, sannan kuma duk abin da ka
lissafo na aikina na gama ko a kwai abin da ya yi saura ne."
ta karashe maganar tana d'aga hanci sama cike da tsiwa.
da d'an mamakin jin zata iya kuma tsayuwa gaban sa yana fad'a tana fad'a dan zaton sa
gargad'insa na jiya daya shakota ya shige ta, sai yaga akasin haka.
idanunta tarmazai take jera masa zance.
afusace ya mike yana fad'in
"Kin gama kike cewa kin wanke mota da zubawa fulawa ruwa da gyarashi."
ta ce "Ban iya ba sai dai ka fad'o wasu aikin a madadin su."
"Su zakiyi idan kuma ba haka ba zan kira Alhj Musa nan yazo ya yi,tun da ya iya cin bashi dole
ya iya aiki ma."
"Ka iya bakinka ka dai na jefin mahaifina da miyagun kalamai zan iya jure komai amma ban da
cin mutunci wa mahaifina, ai bashi hanji ne yana cikin kowa,
yafi karfin yazo ya yi aiki a karkashin ka tun ya haifa gani nan a gabanka yawuce tozarci."
ta karashe maganar da murgud'a masa baki tare da binsa da kallon sama da kasa.
batayi aune ba sai ganin sa tayi a gabanta, baiyi wata-wata ba yakai mata bugu a bakin ta da
bayan hannu.
da sauri ta dafe bakin cikin jin azabar zafi.
ya ce "Fasa shi zanyi sai na fasa bakin ki aduk san da nake magana kina mayar min,
wuce maza yanzu kije ki wanke motar sannan ki gyara fulawar ki zuba musu ruwa yanzun nan
ko na kirawo sa yazo yayi!."
Baya ta shiga ja yayin da ta d'ago hannuta data kai baki tana kallon d'an guntun jinin daya fito a
gefen bakin ta.
shiko komawa yayi ya zauna yana fad'in
"Yanzu karfe 11 saura minti 25 mintuna 25 ne kad'ai suka rage miki, ki tabbatar da kin gama
komai kafin cikar mintuna 25."
Kuma duban d'an guntun jinin dake hannunta tayi kana ta dube sa sannan ta ce
"Ba a haifowa katon gardi jaka ba wlh Allah ya'isa mugu wlh kasake kuskuran kai hannunka
jikina sai kayi dana sani."
a fusace ya mike ganin haka yasata zurawa da gudu tana had'a steps tasauka a guje tayi cikin
d'aki ta murza key.
a jikin kofar takasa kunnenta jin dai shiru bai biyo ta ba tabud'e kofar asulale tayi waje.
Tsayuwa tayi a farfajiyar gidan tana karewa fulawowin da sukayiwa gidan kawanya kallo,
wai su zata zubawa ruwa sannan ta gyara
"To ma taya?." tayi wa kanta tambayar, ga kuma motoci can guda uku cikin parking lot
wai duk ita zata had'a ta wanke su.
kugu ta rike saita kalli motocin takuma kalli flaw's d'in.
sai kuma a sannu tashiga takowa zuwa in da ta hangi tiyo da irin abin da ake rage tsawon
fulawa da shi, ta d'au abin tashiga yanke kan flaw's d'in nan sai da ta kusa cire rabin na gurin,
kana ta yi gaba shima sai da ta cire ganye jiki tas..
mai gadi dake zaune can bakin get yahango abin da take da gudu ya taho yana rabka uban
salati da fad'in
"La-la-la waya saki wannan aikin wace b'arna kike yi haka, kin san kuwa daga ina oga yataho
da wannan fulawar? tun daga kasar turai ya taho da su, shine zakiyi musu aski irin haka waya
fad'a miki haka akeyi."
ta ce
"Oho ba bashi ya ce a gyara ba."
S.MAN dake sama yajiyo salatin da maigadi yake rabkawa ta windo ya leko ya hango su,
ido