Showing 24001 words to 27000 words out of 78655 words

Chapter 9 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf

Advertisement

tayi ta dube su ta ce

"Mu tafi ko nayi gaba ne? kunsan ina da islamiyya karfe 2 ga azahar ta kusa."
Ummi ta kalleta tana karanto rashin jin dad'in yadda yaron nata yayi musu a gareta, sai tayi
murmushi ta ce
"To ai da sauran lokaci yanzu."
murmushin yake SEEDRAH tayi ta ce
"Banyi guga bane zanje na goge Uniform d'ina kafin."
Ummi ta basu dubu biyu ta ce suyi kud'in napep sukayi mata sallama suka tafi.
a hanya SEEDRAH da har lokacin a cike ta ke taja tsaki tare da fad'in
"Amma wannan mutumin d'an rainin wayo ne."
Halimatu ta dube ta tace "Wani mutum kuma?."
ta ce "Wancan S.MAN d'in mana wai dan tsabar rainin wayo sunan Baba fa ya kira wai wani
Alhaji Musa, ai ko Baba ba yayan Abba bane zaici albarkacin girma tun da ya haifesa, idan ma
bazai iya kiran sa da Baba ba ai yana da yara sai ya kirashi da Baban wane."
tsaki takuma ja tare dayin kwafa ita har cikin ranta taji haushin hakan.
shekeke Suhailat ke kallon ta ta ce
"To meye nawani jin haushi shifa babban yaro ne ko Abba ma wani sa'in Alhaji yake ce masa, to
meye dun yacewa Baba Alhaji Musa akan ba sunan sa bane."
Halimatu ta ce "Gane min hanya meye najin haushin ki?, ai barashin kunya bane dan ya ce
haka."
da mamaki SEEDRAH ke kallon su kana ta ce
"Rashin kunya ne mana tun da bazai iya cewa Abba Alhaji Sulai ba, sai dai ya ce Alhajin kawai
ashe yasan ma wan da yake yi mawa sabo da shi ya haife sa ko Hmm."
kai ta girgiza.
hararar ta Suhaital tayi ta ce
"Kina da damuwa wlh, kiyi abin da yake gaban ki kawai mu dai bamu ga wani rashin kunyar sa
ba ai ba zaginsa yayi ba."
baki ta tab'e had'e da murgud'a shi sannan ta ce
"Na rantse duk san da yakuma kiran Baba da sunan sa, ni sai na tsayar masa, tun da shi dai ba
sa'ar sa ba ne tun da Aunty Hajara ma ta girme shi, ya haife shi ya juya."
ta karashe maganar had'e da kuma murgud'a baki.
Halimatu ta ce
"Kina da tsinannen rashin kunya shi d'in bana gaba da ke d'in bane."
shiru tayi bata kuma ce da su komai ba sai tsakin da take ta ja jefi-jefi har suka isa gida...........?




Mommyn Twins ce

🌺 *ƘARSASHI!* 🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~


( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada
ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_


_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090_ ko
08034690723



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*





🅿ï¸8






Da misalin karfe 5 na yamma S.Man ne ya shigo gida ya tadda Abba da Ummi zaune a parlour,
da murmushi Ummi ke duban sa har ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour.
Ummi ta ce "Sai yan zu Usman?."
cikin yanayin gajiyar daya kwaso ya amsa mata tare da gaida Abba.
Abba ya amsa yana fad'in
"Tun da ka dawo bamu sami zama mun gaisa sosai ba kullum kana hanyar fita."
zaman sa ya gyara tare da soma latsa wayar sa kana ya ce
"Ni ma nagaji da fitar nan mutane sun hanani sakat."
murmushi Abba yafad'ad'a ya ce
"To ai cigaban kenan."
baki ya tab'e bai kuma cewa komai ba yayin da hankalin sa gaba d'aya ke kan abun da yake a
waya. Abba da Ummi kuwa suna ta zuba masa zance, lokaci zuwa lokaci yake amsa musu.
zuwa can yasoma magana batare da ya d'ago ba.
"Abba ina bukatar kud'ina kace wa mutumin nan yabani kud'ina."
Abba ya dube shi tare da fad'in
"Wani mutumin kuma Usman?."
ya ce
"Kudi na dana bawa Alhj Musa aro nake so ya maido min dasu ina bukatar su."
Abba ya ce "To-to ai harna sha'afa, anya Yaya Musa ya aje wad'annan kud'ad'en ma kuwa, dan
a gaskiya samun sa ya yi kasa sosai ai kasan kud'in ma banki yabiya da su, sai dai bari dai na
tuntub'e sa naji ko da d'an wani abu ne yaba da a gurin sa kafin a samu sauran."
da sauri S.Man ya d'ago tare da da fad'in
"Duka kud'ina zai bani bada kad'an-kad'an
ba."
Abba ya ce "To idan kuma baya da shi fa sata zaije ya yi?, bari dai na tuntub'e sa naji in dai
babu kam ai dai dole zakayi hakuri."
mikewa ya yi tare da fad'in
"Bazan karb'i kad'an ba duka kud'ina zai bani jibi nake bukatar su."
yana gama fad'a yayi waje.

bayan sa sukabi da kallo, cikin d'aga murya Abba ya ce "Sha-shan cin banza kai,
idan baya da su na ce sata zaije ya yi, ai dole zakayi hakuri sai ya samu yabaka."
Ummi ko kai ta jinjina tasan halin d'an nata sarai tun da taji ya tsaya matsaya d'aya to kuwa
bazai tab'a canzawa ba.

S.Man na fita b'angaren sa ya nufa,yana shiga bedroom yajefa wayarsa a kan gado, kana a
sannu yashiga rage kayan jikin sa, yarage daga shi sai boxes.
murjajjen surarjikin sa irin na kakkarfan zaratan maza ya bayyana,
ainahin kyau na tsarin kyakkyawan halittar sa yabayyana a fili.
doguwar mika ya yi tare da lankwasa jikin sa gefe da gefe, irin dai yan da 'yan kwallo suke yi,
kana a sannu yanufi kofar bayi yashiga ya sakarwa kansa ruwa, wanka sosai yayi kana yafito.
ya shirya cikin kananun kaya wanda suka amshi jikin sa sosai, yana gama feshe jikin sa da
turarukan sa masu dad'in kamshi, yafito parlour d'auke da na'uwar sa,
sosai ya mai da hankalin sa cikin system da yake daddannawa.
wayar sa ya d'aga tare da lalub'o wata lamba.
magana yasoma yi ga dukkan alamu maganar sirri ce dan ni dai banji abin da yake fad'a ba.
sai gani nayi ya mike da laptop d'in yayi waje.

Bayan kwana biyu kamar yan da S.Man ya ce yakuma samin Abba da batun kud'in sa,ya ce
yana bukatar su a yau d'in nan.
bayan fitar S.Man daga d'akin Abba Abba yakira Baba bayan sun gaisa Abba ya ce
"Yaya yaron nan ne Usman yadameni da batun kud'in nan nasa tun shekaranjiya har yau ko a
d'an kwai wani abu a gurin ka abashi dai-dai a samu sauran."
Baba dake gaban teburin sa na aune-aune wan da sana'ar aune-aune ya koma da d'an kud'in
da Abba ya bashi kan yaja jari dan yasami yanda zai rika ciyar da iyalansa.
tun da yafara sana'ar nan baya wani ganin ci gaba madadin yasami riba sai fad'uwa, a duk san
da ya auno hatsi dan ya siyar dakyar uwar kud'in sa yake fita maganar riba kam dai babu ita,
bai kuma fasa sana'ar ba dan yana sa ran watarana zai samu.
damuwa ce sosai ta bayyana kan fuskar Baba a wannan lokacin a halin da yake ciki yanzu ina
zai sami naira miliyan 30 ko miliyan d'aya bashi da su bare miliyon 30.
cikin damuwa Baba ya ce
"Wlh Sulaiman kud'in dai basu samu ba, kabashi hakuri yad'an karamin lokaci zan nima insha
Allahu zan bashi kasuwan ne yanzu sai a hankali."
Abba ya ce "To bari na sanar masa Allah yarufa asiri."

Da misalin karfe 8 na dare S.Man yashigo parlour'n Ummi suna zaune ita da Yusrah.
guri ya samu ya zauna kan d'aya daga cikin kujerun parlour'n, Ummi ta dubesa da murmushi
tare da amsa gaisuwar da yake yi mata.
Yusrah ta dube shi tana fad'in
"Barka da dare Bro."
ido ya zuba mata yana mai jingina bayan sa da jikin kujera ya ce
"Bar wannan gaisuwar je ki kawo min abinci yunwa nake ji."
baki ta turo gaba dan ita bata so tayi gaisuwa a ki amsa mata, shi kuma baya wasa da cikinsa

yanzu idan ta b'ata lokaci bata d'auko masa abincin ba sai ya iya sab'a mata.
ta mike tanufi dinning tana magana kasa-kasa
"Wai ka gaida mutum yaki ammsawa ni bazan ma kara gaishe ka ba."
ta zubo masa abincin a plt ta kawo masa, tana aje abincin ya cafko kunnen ta yamurd'a.
hannu ta kai da sauri ta rike hannunsa tare da fad'in
"Wayyo Allah Ya S.Man kunne na zai tsinke."
dad'a murd'e kunnen yayi kana
ya ce "Tsinke shi dama zanyi me kike fad'a?."
murmushi Ummi tayi ta ce "Ai dai kasan bazai wuce rashin amsa mata gaisuwar da bakayi ba
kasan ta ai."
sakin kunnen ya yi tare da dungurin ta ya ce
"Wuce ki bar nan sai aka ce dole sai an amsa miki gaisuwar."
da gudu tayi hanyar d'akinta tana matse ido da shafa kunnen ta daya murd'e mata.

Ummi ta gyara zama tare da duban sa da kyau yana cin abincin sa cikin kwanciyar hankali.
ta ce
"Usman me zaisa bazaka kara hakuri har Yaya Musa yasami kud'in nan yabaka ba, tun da
bawai baka da kud'i bane a hannun ka, na tabbata kud'in da ka bashi kana da irin su sau ba
adadi, me zai sa ka damu da sai ya mayar maka da su yanzu ka kara hakuri har ya samu
mana." a hankali ya had'iye abincin daya kai bakin sa kana ya ce
"To ai bazai samu ba ko nan da shekara nawa ne."
Ummi ta ce "To ai abun da nake so ka gane kenan kayi masa hakuri har ya samu."
"Ya sai da gidan sa kawai ya biya ni tun da bashida wata kaddarar bayan ita, ai na fad'a musu
duk san da na shigo Nigeria zai dawo min da kud'i na, Ummi kiyi shiru kada ki kara cewa komai
game da maganar nan dan sai ya biya ni gobe goben nan dan ina da abun da zanyi da su."
ganin Ummi tana kokarin kuma jefo wata maganar yad'au plt d'in abincin sa yayi hanyar side
d'in sa...

Washegari da misalin karfe 2 na rana motar S.Man ne yashigo gidan Baba. yana dai-dai ta
parking yafito yana mai karewa gidan kallo,
a sannu ya jingina da jikin motar tare da hard'e hannunsa a kirji yana d'an kad'a kafarsa d'aya
daya sarkafe su guri guda.
hannu yasaka cikin aljuhun wandon sa yazaro wata sigari babba irin na rurawannan had'e da
makunnin sa.
ya kunna kana asannu yakai bakin sa yashiga zuko sa ya na buso hayakin, cikin nutsuwa.
sai da yasha tabar natsawon mintuna biyar kana ya jefar da ragowar kasa, yasa kasan
had'ad'd'en takalmin kafarsa ya murkushe.

A sannu ya mike daga jinginen da yake yasoma tafiya yanufi kofar da zai sada ka da cikin gidan
sannan ya tsaya batare da ya karasa bakin kofar ba.
tsayuwar sa ya gyra da kyau tare da bud'e baki yashiga kwad'awa Baba kira, batare da yin
sallama ba.

Kamar daga sama su Mama dake zaune a tsakar gida suka jiyo kiran da S.Man yake kwad'awa
Baba.
Mama ta ce "Waye kenan da irin wannan kiran mafarautar haka, babu ko sallama."
Umma ta ce
"Wlh kuwa wannan ai sai ya tsinkewa mutun gaba da irin wannan kira."
Suhailat da Halimatu na zaune ko waccen su na daddanna waya.
SEEDRAH na gefe tana wankin kayan Mama.
wani irin d'ago wa tayi jin yakuma fad'in
"Alhj Musa!".
a kufule ta mike tare da fad'in
"Wai wani irin d'an rainin wayo ne wannan daga jin wannan murya dai bana abokin Baba bane
sai dai in ko aiko sa akayi ya kira sa, sai ya rika yi masa irin wannan kira kajimin rainin wayo da
rashin tarbiya."
taja mayafinta dake kan igiya tanufi kofar gida tana cigaba da mita.
Suhailat ta mike zumbur tana fad'in
"Wannan muryar kamar na S.Man kada dai kuma shine kije kiyi masa rashin kunya."
bata saurare ta ba tayi waje ita ma ta bi bayan ta.

Tsabar jin haushi idanunta ya rufe tun kan ta kara fita tashiga fad'in
"Ka koma a koya maka tarbiyya ta yadda ake kiran babba, kai idan akaje gidan ku ana kiran
sunan Baban ka haka zakaji dad'i ne?."
ido ya tsurawa kofar cike da mamakin son ganin wata isasshiyar ce, tana sako kafarta waje
Baba na sako nashi.
dan tun kiran farko da ya yi masa kasan cewar yana zaune cikin parlour'n sa ne ya mike ya fito
bakin kofa dan tabbatarwa kansa da gaske shi d'in ake kira.
jin kiran da gaske ne da sauri yariga Suhailat bin bayan SEEDRAH.
da mamaki yake kallon S.Man dayake tsaye yana bin SEEDRAH da mugun kallo.
Baba ya maida kallonsa gare ta sannan ya ce
"Shiga gida SEEDRAH."
sai da ta wasa masa wani irin kallo daga sama har kasa sannan ta murgud'a masa baki cike da
tsiwa had'e da jin haushin sa ta yadda ya ke raina Baba wan mahaifinsa, tayi kwafa tare da
juyawa ta koma ciki.
Suhaita tun da taga shine har wani b'ari jikin ta yake,ta washe baki tana fad'in
"Kamar na sani kuwa na ce wannan muryar Ya S.Man ne ashe dai kai ne anwuni lafiya ya gida."
kallo d'aya yayi mata ya d'auke kai, batare da ya amsa gaisuwar da take mika masa ba.
itako ko a jikin ta bai dame ta ba da rashin kulatan da yayi, sai dad'a fad'ad'a annurin fuskarta
take.
Baba ya ce itama ta koma ciki har ta kule ciki tana waigen sa.

Baba ya dube sa ya ce "Usman barka da zuwa shine zaka tsaya daga waje ai da ka shiga ciki,
bismillah mushiga daga ciki."
girman idanunsa S.Man ya rage tare da fad'in

"No sauri nake kud'ina nazo karb'a d'auko min su na wuce sauri nake"
Baba ya ce "A ai munyi magana da Sulai bai fad'a maka ba, ka kara hakuri inata kan kokarin
neman kud'in kenan nasamu na had'a maka kud'in dan Allah ka kara hakuri."
fuska ya d'aure tamau kana yashiga kad'a makullin motar da ke rike a hannunsa sannan ya ce
"Bazan jira har sai an nima a bani ba yanzu nake bukatar su, nan da kwana uku zan dawo ka
adana min kud'ina."
yana gama fad'a ya juya yashige matarsa yabar gidan.
Baba yabi bayan motar da kallo kana jiki a sanyaye ya koma ciki.

S.Man na barin gidan gidan sa dake New G.R.A ya nufa, gida ne mai girman gaske ginin
zamani tsarin ginin turawa yatsaru iya tsaruwa.
ya bada kwangilar gina gidan tun yana kasar Spain, anjima da gina gidan anzuba kayan more
rayuwa babu abun da babu.
ankule gidan babu kowa cikin ta amma da ma'aikatan da suke zuwa gyaran gidan duk bayan
wata 1, shiyasa idan kaga gidan bazaka tab'a cewa babu mai rayuwa cikin sa ba.
kasancewar shi bawani zuwa Nigeria yake ba ko da yazo ma baya kwana a gidan sai dai yazo
d'an fisha ya tafi, wani lokaci kuma yakan zo da abonsa suyi hira.
koda yazo gidan bai wani jima ba yafita ya dawo gida a kitchen ya tadda Ummi tana aiki.
sannu da aiki yayi mata kana yayi kokarin wucewa.
Ummi ta dakatar da shi da fad'in
"Wai yau ina kaje ne Usman baka ko tsaya kaci abincin rana ba?."
hannunsa ya d'ago tare da duban tsadadden agogon da ke d'aure a hannunsa yaga karfe
3:30pm ya ce
"Gidan Alhj Musa naje daga gun nawuce gida na."
yayi maganar naya wuceta yabi ta kofar dake cikin kitchin d'in ya nufi side d'in sa.
da mamaki Ummi tabi bayansa da kallo, dan tasan maganar kud'in sa ne kawai zai kaisa gidan
Baba, dan haka siddan baya zuwa gidan idan yazo kasar nan.
kai ta girgiza a fili ta furta
"Allah shi kyauta."

A b'angaren Baba kuwa jiki a sanyaye ya koma gida Mama da Umma har suna rige-rigen
tambayar sa dalilin daya sa S.Man d'in tsayuwa a kofa ya na yi masa irin kiran da yayi masa
batare da sallama ba.
Baba yagirgiza kai cike da damuwa ya ce
"Kunsan a zamanin da muke yanzu mai nima baya fushi haka za idan ana binka dole ka jure
wulakanci,kud'i yake bina shine yazo karb'a."
nan Baba yashiga yi musu bayanin yanda a kayi yabashi aron kud'i yabiya bashin banki,
dan dama basu san ya amshi bashin banki ba basu kuma san da bashin bankin duka aka
kwashe a accoun d'in sa da akayi masa sata ba .
su Mama sun jinjina batun kwarai da gaske tare da tausayawa mijin nasu, sai dai sukayi ta
karfafa sa tare da yi masa fatan samin bud'in Allah yabiya sa kud'in sa,
duk da kuwa yawan kud'in da samun su zai iya d'au lokaci mai tsawo musamman a yanzu da
suke cikin halin rashi.

SEEDRAH da ta gama wankin da take tana shanya kayan taja tsaki wan da a zuciyarta tayi
bata sammaci fitowarsa ba,
tayi kwafa tare da kad'a harshen ta yabada sauti.
dukkaninsu suka juyo gare ta Halimatu ta ce
"Ke kuma da waye kk tsaki?."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login