Showing 30001 words to 33000 words out of 78655 words

Chapter 11 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf

Advertisement

a kasuwa, kira yashigo wayar sa.
ganin mai kiran nasa yasashi shiga damuwa, jiki ba kwari yad'aga kiran.
daga cikin wayar S.Man ya ce.........!










Mommyn Twins ce



🌺 *ƘARSASHI!* 🌺



*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~


( _Bismillahirrahmanurrahim_)

_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_





_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_



*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




page 10






"Nazo gidan ka ji ina fata an fad'a maka, bazan kuma zuwa na uku nayi zuwan banaza ba, ka

tabbatar da ka ajemin kud'ad'ena dan yau babu afuwa cikin zuwa ta."
yana gama fad'in haka ya kashe wayar.
Baba ko numfashi ya sauke yana jinjina kai .
Mama dake zaune gefen sa idanunta akan sa ganin yadda ya zaro wayar jiki a sanyaye yana
juya wayar cikin matsanan ciyar damuwa ta ce
"Usman ne ko?."
kai yagyad'a mata alamar Eh. kana ya ce
"Bansan ta hanyar da zanbi na iya samo masa kud'insa ba sati guda nayi ina zuwa kasuwa da
iya karfi na nake gudanar da kasuwan cinnan amma yar yau ban had'a ribar da ta kai naira
dubu d'ari ba,
ina da tabbacin koda shekara zanyi bazan iya samun naira miliyon 30 ba."

Numfashi yaja kana ya ci gaba
"Idan ba gidan nan zan d'aga na siyar ba to bansan ta inda zanbi na samo masa kud'in sa ba,
kud'i yana da wuyar sha'ani kud'i ke sa karami ya raina babba, d'an d'an'uwana yake gaya min
maganganun da suka fito daga bakin sa, wan da ko shi Sulaiman d'in bazai iya duban tsabar
idona ya gayamin kwatankwacin sa ba." "Yanzu sai da gidan za'ayi."
Mama ta fad'a cike da damuwa.
"Baza a sai da gidan ba, idan aka sai da ina zamu je, idan kuma gidan haya zamu koma a
wanna lokaci da haya tayi tsada ga shekara yanzu babu wuyan ta zago, y'an kud'in da nake
juyawa bazasu wadacemu abiya haya sannan aciyar da kai ba."
kai Mama ta jinjina cike da tausayin halin da suka tsinci kansu ciki..
Wunin ranar Baba yayi ta zuba idon ganin da me S.MAN zaizo yau kuma,
amma har dare bai zoba, a daren ranar yakira Abba ya ce yaroka masa S.MAN d'in yakara
masa hakuri.
ko da Abba yakira S.MAN da batun kin dawowa gidan Abba yayi, yayi zaman sa a gidan sa.

Bayan kwana biyar har lokacin Baba na zuba idon ganin S.Man shiru sai dai shi S.Man d'in ma
baya kasar yatafi kasar spain sakamakon kiran gaggawar da yasamu kan buga wani wasan da
zasuyi.
watan S.Man guda da tafiya kenan
zuwa lokacin sosai Baba ya dage da niman kud'i duk da yasan kasuwan cin da yake yi in
shekara goma zaiyi bazai sami ribar da zai kai kud'in da yake bin sa ba, sai dai yasan hanyar
Allah tana da yawa.
in yaso sai ya bud'a masa a cikin rabin shekara yasami kud'in sa ya basa.
ya sanyawa ransa haka sai dai ina, jiya kamar yau wata guda bai ajiye kud'in da yakai dubu
d'ari ba...


Da sauri SEEDRAH ta fito daga d'akin Mama cikin shigar tafiya school tayiwa Mama sallama
tayi waje, da d'an sauri take tafiya dan ta d'an makara sai da ta haura can bakin titi kafin ta sami
abin hawa.

Yau Baba na gida bai fita kasuwa da wuri ba har wajen karfe shad'aya da rabi, yafito daga
d'akinsa, su Mama suna yi masa a Allah bada sa'a.
yana fitowa farfajiyar gida tsayuwa yayi da d'inbin mamaki ganin S.Man da wasu mutane ga
dukkan alamu shigowarsu kenan.
da kaga mutanen zakasan hukuma ne su dan ga alamun hakan a tattare da su.
Baba ya karaso in da suke jiki a sanyaye yana fad'in
"Usman kaine tafe sannunku fa yaushe ka dawo kasar?."
hannu S.Man yad'aga masa batare da ya amsa gaisuwar had'e da tambayar da yake masa ba.
kana ya dubi mutanen dake tare da su ya ce
"Shine wannan kusashi yanzu ya fita a gidannan nakulle shi."
cikin matsanan ciyar tashin hankali Baba ya ce
"Haba Usman dan Allah dan Annabi kayi hakuri idan kafitar damu a gidan nan ina zamu koma,
ka kara hakuri ina ta kokarin nima maka kud'in ka ko yanzu ma gurin niman zanje."
"Kuzauna a titi ma bai shafeni ba, yau zakabar gidan nan sannan kasani idan har nasiyar da shi
yagaza kud'in da nake binka dole zakayi min ciko, kana b'ata mana lokaci dukkanin mu muna
da abin yi kusashi ya miko min takardun gida, idan kuma ka hana yanzu ni me iya sawa ne a
buga min wasu." hukumar dake tafe da shi su suka ce
"Shiga ka d'auko takardun gidan sannan ka sa mutanen ciki sufito had'e da kayan ku."
hannu Baba ya had'a bibbiyu yashiga rokon su da magiya kan suyi masa hakuri su barshi a
gidan sa, amma me kamar dad'a ingiza S.Man ake yana kwararowa Baba rashin mutunci
sinki-sinki.

Hayaniyar da su Mama sukaji ne yasasu fitowa ganin abunda ke faruwa hankali tashe suma
suka shiga basu hakuri.
Suhailat da Halimatu sunyi jungum-jungum yayin da idanunsu ke kan S.Man...


SEEDRAH da ke tafi kan abin hawa zuwa makaranta har sunyi nisa ta tuna bata d'au wani
littafin ta mai muhimmanci ba, da sauri ta ce wa mai abin hawan
ya juya da ita tayi mantuwa zata kara masa kud'i.
suna isa kofar gida ta rika jiyo hayaniya da sauri ta sallami mai abin hawan ta shige gida cikin
sauri har tana had'awa da sassarfa.
turus ta ja ta tsaya daga bakin get tana kallon kowa d'aya bayan d'aya.
can ta hango Mama da Umma da Baba suna ta zuba magiya kamar zasu zuba guiwowin su a
kasa.
S.Man na jingine da jikin motarsa ya hard'e hannayen sa akirji yana girgiza kafa cike da rashin
daraja, wad'an nan mutanen dayazo da su kuma suna cewa su Baba suyi suje su fara fitowa da
kayan su.
Baba ya matsa gaban S.MAN cikin magiya da roko ya ce
"Usman ni fa wan mahaifinka ne kada ka mance da Sulaiman da ni uwa d'aya uba d'aya, ko
wani kagani zai yi min irin wannan tozarcin bazaka kyale ba sai kuma gashi kaine da kanka

kake kokarin tozartani, haba Usman ka farka daga baccin da kake mana."
hannu S.MAN ya d'aga masa kana ya ce
"Dangantakar ka sakanin kai da mahaifina ne ba da ni ba, idan kai yayansa ne bai zama kai
yayana bane so shine d'an'uwan ka bani ba, nifa a kan kud'i komai ma zan iya musamman
wanda na tara da gumi na, idan baza ku iya fitar da kayan ba yanzu nabiya afitar dasu!!."

"Wace doka ce tabada damar fitar da wanda ake bi bashi a gidan sa kai tsaye rana asaka
batare da bincike da yanke hukuncin wad'an da suka dace ba!!."

Maganar SEEDRAH suka sinkayo cike da amon sauti mai nuna zallar tafasar zuciya had'e da
raurin d'iya mace.
tattausar muryar ta mai zaki dake fitar da sauti cikin nuna zallar b'acin rai da takaicin tozarcin
da ta taras akeyiwa mahaifinta, tashiga d'aga kafarta tana dumfaro inda suke ya yin da tashiga
nuna S.MAN
da hukumar dake tafe da su da hannu tacigaba da fad'in
"Babu dokar da ta ce haka, dan haka baku da ikon da zakuce lallai sai ya fita a gidan sa ya
baku a bakin kud'in da ake binsa,
kuje kuyi sammacin sa a kotu idan kotu ta kirasa zai amsa kiranta dan acan ake zartar da
hukuncin daya dace, daga nan fa duk kud'in da yake samu a sati ko wata ko shekara aciki za'a
rika cirewa ana baka har bashin ka ya kare, baka da ikon da zaka zo da wasu kace sai yabar
gidan sa, babu in da zamuje muna nan, idan kud'in ka kake so kaje ka kai karan Baba kotu!."
ta karashe maganar da nuna S.MAN da yatsa had'e da murgud'a masa baki.

Tun da tafara maganar ya kafe ta da ido ganin kokari da karfin halin yarinyar.
cikin tsawa d'aya daga cikin d'ansandan da akazo da su ya ce
"Ke hukuma ne zakija dasu yanzu zakiji ki a cikin cell."
Mama ce tayi saurin ruko hannun SEEDRAH ta jata tana fad'in
"Ke SEEDRAH hukuma ne fa zo ki shiga ciki."
"Mama dan hukuma ne sai ayi shiru a kyale gaskiya bayan ga gaskiya ana gani a fili, tun da su
ba mala'ikun zare rai bane kibari a fad'a musu.."
da sauri Mama ta rufe bakin ta bata bari ta karasa ba,
S.MAN yabi bayan ta da kallo har suka b'acewa ganin sa.
da sauri yazura hannunsa cikin aljuhun wandon sa yana kokari zaro sigari sai kuma ya bari,
yakai hannu ya shafo sumar kansa tare da furzar da iska daga cikin bakin sa.
sai da Mama ta kaita har cikin bedroom d'in ta sannan ta sake ta ta kuma ce ta zauna anan
kada ta fito.
kuka SEEDRAH ta fashe da shi takifa kanta jikin pilo tana mai jin d'aci cikin ranta da mugun
tsanar S.MAN

Can waje kuwa har lokacin su Baba suna ta kan faman magiya da roko,
S.MAN ya dubi d'aya daga cikin d'ansandan dake kusa da shi kana ya yi masa magana
kasa-kasa.

kai d'ansandan ya gyad'a kana ya dubi 'yan'uwan sa ya ce
"Kuzo muje."
suka shige mota shima ya shiga yaja suka fice a gidan.
godiya wa Allah su Umma sukayi ganin sun tafi batare da sun ce komai ba.
jiki bakwari sukaja kafafunsu suka koma ciki.
Baba na shiga d'aki lambar Abba yakira sai yaji wayarsa a kashe ya ma gama mancewa da
Abba'n yatafi wani kasuwanci shida abokinsa a Japan.
Mama tashigo d'aki ta sami SEEDRAH zaune a bakin gado tagama kukan ta share hawaye ta
turo baki gaba.
ta dube ta tana fad'in
"Su Usman d'in sun tafi ma wata kila ya hakura ne, yakamata ki tashi ki koma makaranta me ma
yadawo dake ne ma?."
kwanciya ta gyara kan gadon Mama ta ce
"Sai kuma gobe yanzu kam."
Mama ta ce "Allah ya kyauta."
tayi waje.
A b'angaren Baba ma kasuwan da bai fita ba kenan ranar dan gabad'aya jikin sa yagama
mutuwa.

Da misalin karfe 8 na dare S.Man ne zaune cikin parlour'n sa dan yanzu yadawo zaman gidan
sa. in ka gansa gidan Abba to yaje gaishesu ne.
d'agowa yayi daga kallon System daya mai da hankalinsa sosai yake aikin latsashi,
sai dai fuskarsa sam babu walwala.
d'an shiru yayi da alama dai nazari yake rufe System d'in yayi ya mike da d'an sauri ya zari
makullin motar sa dake kan table d'in gaban sa yafita da d'an sauri.

Baba da ya fito daga masallaci sallar isha yazo zai shiga gida yaga mota tsaye a kofar gida.
ganin wan da yake tsaye jikin motar yasashi karasowa in da yake jiki a sanyaye, yana tunanin
da wani abun kuma yazo yanzu.
S.Man yagyara tsayuwar sa da kyau kana ya dubi Baba da duk jikin sa yagama sanyi yana
zaman jiran jin ta bakin sa ya d'an karkata kai kana ya ce
"Ina bukatar 'yar aiki da zata rika kula min da tsaftar gidana da girki zan rika biya duk wata, idan
kaso sai arika cirewa daga cikin bashin da nake bin ka."
tun kan ya karasa Baba ya ce
"To-to-to bawata matsala ai ga yarannan in kyauta kake so ma sai surika zuwa suna yi maka ai
bawata damuwa ai, ina dai shike nan abunda kazo da shi gobe sai suje su fara."
baki ya tab'e ya ce
"Ba gayya nake so ba mutum d'aya ma ya isa."
Baba yawashe baki da jin dai ba maganar kud'i ko gida bane dai yazo da shi cikin kuma washe
baki ya ce
"Au to shike nan ai tun da Suhailat itace babba sai ta rika zuwa."
katse shi ya yi da fad'in
"Ba ita ba d'ayar...........!

Mommyn Twins ce




🌺 *ƘARSASHI!* 🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~


( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya
zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin labarin nan mai suna ƘARSASHI
ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH da sauran littatafai na suka saba
zuwar muku🤗 ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai ƙwanƙwasa zuciya salon labarin
na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance da sunan sa ƘARSASHI!
ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_

_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




page 11





Baba ya ce "Ohoo Halimatu? ai ko gobe sai ta fara zuwa."
d'an shiru S.MAN ya yi alamun nazari, Baba ya juya zai shige gida yana fad'in
"In Allah ya yarda gobe da sassafe zata fara zuwa ai ba wata matsala kannen ka ne ai kana da
iko da su, idan akwai wani aikin ma nan gaba sai su tafi duka da Suhailat d'in dun su gudanar
da aikin da sauri, bawata damuwa ai gobe zata fara zuwa."
"Ba ita ba, sannan kuma bana bukatar zuwa a matsayin dangi na amatsayin 'yar aiki nake
bukata, kuma ba wacce zata rika zuwa tana dawowa ba sabo da kowani lokaci zan iya bukatar
a gudanar min da wani abin, idan zuwa zatayi tarika dawowa lokacin da na bukaci wani abu
bata nan fa?."
Tsayuwa Baba ya yi tare da juyowa ya ce
"To-to wa ke nan SEEDRAH kake fad'a?."
d'an shiru ya sake yi yana juya sunan cikin ransa yana son tuna sunan da yaji Ummi ta kirata da
shi randa yafara ganin ta a gidan su takai masa abinci.
kai ya gyad'a masa duk da baya da tabbacin sunan nata kenan dan baisan sunan ta ba bai

kuma tuna sunan da yaji Ummin ta fad'a ba.
Baba ya ce "To ba matsala shikenan bari na shiga ciki muyi magana."
Baba ya shiga ciki da sauri dan baya so ya tsaya har ta kaisu ga zancen kud'i ko gida.
aransa kuwa yana tunanin ta yadda za'ayi SEEDRAH taje ta zauna a gidan sa bayan tana tafiya
makaranta, kawar da tunanin ya yi da ayyana daga can d'in saita rika zuwa koma ta aje karatun.
dan shi yanzu yana jin duk abunda S.MAN ya ke bukata zai masa har idan zai sarara masa kan
maganar kud'i da gidan sa.
Direct d'akin Mama Baba ya shige ya taddata zaune kan sallaya tana jan jarbi, yazauna bakin
gado.
ta d'ago ta dube shi tana fad'in
"Barka da dare Alhj." ya ce "Yauwa."
kana ya muskuta da kyau ya gyara zaman sa sannan ya ce
"Usman ne yazo yanzu ina ga ma ya tafi."
kirji Mama ta buga a d'an razane ta ce
"Allah dai yasa ba da hukuma yakuma zuwaba,
yau idan yad'aga mu a gidan nan ina zamuje."
"Ba da kowa yazo ba, zuwansa na yanzu ya bambamta da zuwansa na ko yaushe,
yanzu yazo ne niman wacce zata rika yi masa aiki a gidan sa yakuma ce wai SEEDRAH ya ke
so taje tarika yi masa aikin."
ido Mama ta waro tare da kuma dafe kirji ta ce
"Meyasa sai gidan nan ne zai zo niman 'yar aiki meyasa kuma yazab'i SEEDRAH ita ce zatayi
masa aikin, Alhj ina jin tsowa nasan SEEDRAH ma bazata amince ba tun da ga su Halimatu
d'aya daga cikin su kawai tarika zuwa tana yi masa aikin."
Baba ya riko hannunta ya ce
"Haba meye kuma najin tsoro ai godewa Allah yakamata ma muyi tun da har ya tako kafa yazo
niman wani abu a gurin mu ko tanan zamusan yad'an hakura zaiyi mana jinkiri zuwa musamu
kud'in sa mu basa, zai kuma hakura yabarmu a gidan mu, har Allah ya kawo lokacin da zamu
samu kud'in sa murabu da shi, kuma ma ya ce zai rika biyan kud'in aikin, sannan kuma kud'in albashin acikin kud'in da yake
bina zai rika cirewa ai kin ga dai za'a d'an rage wani abin,
kuma nima sai da na ce masa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login