Showing 6001 words to 9000 words out of 78655 words
Chapter 3 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
ne, da kuma na biyo ku naga kun gudu sai na dad'a
gaskata hakan a raina, shi yasa muka biyo ku, amma wlh bada mugun nufi muka biyo ku ba,
sabo da yawai tan irin wad'an nan 'yan titin masu shashanci shine muka kafa kwamiti duk wan
da muka gani bamu yarda da shi ba mukan tuhume shi musan gaskiyar sa, shi yasa muka biyo
ku domin sanin ko ku suwaye."
wasu zafafan kwalla ta share
ta ce "Kwamitin yiwa 'yanmata fyad'e? ai ba 'yan titi bane 'yan'iska kune manyan 'yan'isakan,
kun san me ya saida mu a gurin?."
sai kuma ta kuma sakin kuka mai d'aci ta ce
"Tai mako na take, ni na ce ta cire min rigan ciki na sabo da ruwa daya tab'a ni yake min
kaikayi."
juyo wa tayi ta sunkuya hawaye na cigaba da wanke fuskarta ta taimakawa Nasiba ta mike
tsaye ta gyara mata d'aurin zanin ta.
ido Kamal ya zubawa wani agogon daya fad'o kasa lokacin da Nasiba ta mike tsaye,
ya sunkuya tare da d'aukar agogon yana juyashi a hannunsa,
a kasan ransa ya furta
"Mukhtar me yasa zakayi haka!!.........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada
ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690734_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
í ¼íµ¿ï¸3
Hannun Naseeba SEEDRAH ta ja tana hawaye ita ma tana hawaye, da kyar Naseeba take iya
d'aga kafar ta sabo da azaba, har suka fice cikin gidan.
jiki a sanyaye Kamal yabiyo bayan su.
SEEDRAH ta dube ta cike da matukar tausayawa ta ce
"Naseeba ki daure mufita bakin titi mu sami abin hawa ya kai mu gidan goggo tun da duk bamu
fito da kud'i ba idan mukaje gaggo sai ta biya sa, duk da babu nisa gidan daga nan amma
nasan bazaki iya tafiya da kafa ba, dan Allah kiyi hakuri Naseeba duk ni na janyo miki da bance
mu tafi ba da duk haka bata faruba."
takarasa maganar tana mai dana sanin cewa su fito cikin daren nan.
da sauri Kamal ya iso su ya ce
"Ina ne zaku je kuzo na sauke ku in da zakun, kin ga tafiyar wahala yake bata."
wani uban harara SEEDRAH ta banka masa, kana ta cigaba da jan Naseeba da ke d'aga kafa a
hankali kamar mai koyon tafiya, sai yarfe hannu da zubda kwalla take cikin jin azaba.
gaban su yasha da sauri ya ce "Da dai kin tsaya na sauke ku tana bukatar taimako."
a hatsale SEEDRAH ta ce
"Bama son taimakon naka ku har wani taimako kuka iya ban da zalunci, ma ha'inta wlh zakuga
karshen ku."
kai ya girgiza ya ce "Eh..Eh naji amma dai dan Allah kibari na kaiku duba fa kiga yadda take
tafiya tana bukatar taimako kibari a taimake ta, kiyi hakuri zo ki hau mashin d'in na sauke ku in
da zakuje kin ji."
yayi maganar yana duban Naseeba da fuskar tausayawa. shiru SEEDRAH bata kuma magana
ba, tasan kawar tata tana bukatar taimako a irin halin da take ciki yanzu tafiyar kafa bazai yuwu
a gare ta ba,
tsayuwa tayi batare da ta ce komai ba,
ganin haka yasa Kamal saurin hayewa nashin d'in sa yana fad'in
"Yauwa kuzo ku hau muje."
hannun Naseeba ta ja zuwa gurin mashin d'in ta taimaka mata tahau, cikin b'ata fuska take yi
masa kwatancen in da zai kaita wato gidan goggon ta, sakanin su da gidan babu nisa sosai.
ya ce ya gane gidan to tahau bayan Naseeba
su tafi tare mana,
wani harara ta dalla masa ta ce bazata hau ba.
bai kuma magana ba yaja mashin d'in suka soma tafiya a hankali dan yaga ita wancan tad'au
zafi da yawa ga dukkan alamu kuma masifar tsiwar tsiya ce da ita.
bayan su ta bi a kafa, sun isa suna tsaye a kofar gidan SEEDRAH ta karaso.
ta ja hannun Naseeba suka shige cikin gidan, suka bar Kamal tsaye a gurin yana yi musu
magana bata ko saurare shi ba...
jiki a sanyaye Kamal yaja mashin d'in sa yatafi, duk in da yake zaton zai sami Mukhtar ya je
baya gun, gaba d'aya lissafin sa ya jagule sai gani yake kamar mafarki yake,
wai Mukhtar ne da aikata haka, shi a sanin sa tun da suka taso bai san sa da irin wannan halin
ba...
A can gidan su Maman Zeey kuwa jin fitar su Kamal yasa Maman Zeey fitowa daga d'aki, tana
tambayar Zeey ina yarinyar take,
Zeey ta ce "Sun fita da Ya Kamal ni fa ina ga su suka biyo ta, dan naji yana ce mata dama yayi
zaton nan ta shigo."
Maman Zeey ta rike hab'a tana fad'in
"Jimin tsiya ina ruwan su da ita da zasu biyo ta yara da niman magana haka."
A b'angaren su SEEDRAH kuwa
Yanayin dare gidan shiru side d'in goggo suka nufa, shiru side d'in babu motsin kowa ciki, direct
d'akin goggo Larai suka wuce, goggo Larai bata ciki tana can side d'in maigidan ta, kasan cewar
'ya'yan ta duk maza ne suma suna nasu d'akin.
a bakin gado SEEDRAH ta ce wa Naseeba ta zauna kana ita kuma ta wuce cikin bathroom,
ruwan zafi ta had'a mata cikin
Bathtub kana ta fito ta taimaka mata suka shiga cikin bayin.
tagasa jikin ta sosai, Naseeba na masar kwallar wahala SEEDRAH kuma na zubda kwallar
tausayin ta tare da jin d'acin rasa wani kima mafi girma da daraja a rayuwar ta.
sosai ta taimaka mata ta gasa jikin ta dan sai da ta sauya mata ruwan zafi har sau uku.
kana ta sarkake jikin ta suka fito,
babu laifi taji dad'in jikin ta sosai dan ko tafiyar ta ma ba irin na d'azu ba.
Wardrobe d'in goggo Larai ta bud'e ta ciro mata wasu kaya wan da take ga bazai mata girma
sosai ba tabata ta saka, natan daya gama cukurkud'ewa a turb'aya ta koma bayi ta wanke mata
ta shanya shi cikin bayin.
ko da ta fito bakin gado ta matso in da Naseeba ke kwance shiru bawai ko dun tana bacci ba,
ta zauna gefen ta cike da tausaya mata cikin murya mai rauni ta ce
"Kiyi hakuri Naseeba narasa da wani irin baki zan baki hakuri, wlh in da nasan haka zata faru da
ban ce mu fito zuwa nan ba."
hawaye ne yafara zuba a idanunta tana mai ci gaba da baiwa kawar tata hakuri.
ta ce
"Sai naji ina ma ace a kai na hakan yafaru bawa ke ba."
hannunta Naseeba ta rike ta ce
"Haba SEEDRAH ki dai na d'aura alhakin haka a kanki duk abin da kikaga ya sami bawa to da
sanin ubangiji, tawa kaddarar kenan dama Allah ya hukun ta ni tawa budurcuin a haka zai tafi,
amma sam baki da laifi ki dai na d'aurawa kan ki laifi, dan ina da tabbacin bazaki tab'a so abin
da zai cutar da ni ba bare ya tab'a min kima." zafafan hawaye SEEDRAH ta share ta ce
"Wlh baza a kyale su ba sai an gurfanar da su gaban shari'a azzalumai."
kai Naseeba ta girgiza yayin da take jin d'aci cikin ranta cikin rawar murya da kuka ke son
kwace mata ta ce
"A'a SEEDRAH kirufa min a siri bana son maganar nan ta fita
nasan zan zamo abin nunawa a gari, gara naji da abu guda kyara da tsangwama gurin mijin da
zan aura a lokacin da yagane bani tare da budurci na."
kuka ne ya kwace mata, sai kawai suka had'a kai sukayi ta rusar kuka, babu mai iya baiwa
d'an'uwan sa hakuri,
sai da suka gaji dan kansu kafin sukayi shiru.
sai da dare ya raba kafin bacci ya sami damar d'aukar su.
Washrgari da asuba goggo Larai ta dawo d'akin ta, turus tayi ganin mutane kwance a kan
gadon ta suna bacci,
da mamakin ganin SEEDRAH ce da kawar ta. ta karaso bakin gadon tashiga bubbuga su da
fad'in.
"Kai ku tashi kuyi sallah wai yaushe kuka zo ne ma kada a ce a nan kuka kwana."
SEEDRAH me nauyin bacci mika tayi had'e da yin juye ta kuma gyara kwanci.
Naseeba ce ta mike zaune tana mussuke ido,
goggo Larai ta ce "Wai yaushe kuka zo ne Naseeba? wannan kasar in ba ruwa a ka yayyafa
mata ba, batashi zatayi nan kusa ba."
tayi maganar tana mai dad'a bubbuga SEEDRAH da ta koma baccin ta.
Naseeba ta ce "Jiya muka zo da daddare."
sai a lokacin SEEDRAH ta bud'e ido cikin magagin bacci sabo da bubbuga ta da goggo Larai
take tayi, tana fad'in ta tashi suje suyi sallah.
da kyar ta mike zaune tana tura baki gaba, hamma tayi had'e da salati ta ce
"Allah sai nake ji kamar yanzu na kwanta."
goggo Larai ta ce
"Yo ke kam in tun magriba kika kwanta bacci kika tashi yanzu ai haka zaki ce, irin wannan
baccin naki sai a sace ki ma baki sani ba, maza sauko kuje kuyi al'wala kuyi sallah."
goggo Larai tayi waje.
Naseeba ce ta fara shiga bayin sai da tayi sarki da ruwan zafi kafin tayi al'wala ta fito,
SEEDRAH ma ta shiga, suna idar da sallan, Naseeba ta koma gado ta kwanta dan zazzab'i
take ji tun daren jiya.
gefen ta SEEDRAH ta zauna tana yi mata sannu cikin tausayawa.
goggo Larai ne ta shigo da flaks d'in ruwan zafi data girka ta aje,
suka gaida ta ta amsa tare da fad'in
"Shine baku kirani ba da kuka zo jiyan, me ya sa mi wannan take dunkulewa da rawar sanyi?."
SEEDRAH ta ce "Ba waya ne a hannun mu mun baro shi gidan Nabeela, nan aka kawo ta fa
saman layin ku, zazzab'i ne ya dami Naseeba shine muka zo nan."
goggo Larai ta ce
"Subhanallah ta karya ta sha magani, ai ku yaran yanzu kun fiye sako bidi'a cikin hidimar biki
ku, zirga-zirga ma kad'ai ya ishi mutum yayi ciwo, ki karya sai ki sha magani."
shiru sukayi basuce komai ba, gaggo Larai ta had'a mata tea me kauri ta ce tata shi ta sha, tana
tsaye har sai da ta shanye,
kana tafita jim kad'an ta dawo da faracetamol ta bata tasha, sannan ta ce ta kwanta kafin gari
ya dad'a waye wa a siyo mata magani.
babu jimawa kuwa bacci yayi gaba da ita.
goggo Larai ta fita domin yiwa y'ay'anta abin kari sutafi gurin aiki.
SEEDRAH kuwa ganin ta koma bacci ta mike ta shiga bayi,
kayan jikin ta da aka bata jiya agidan da ta shiga b'uya, tacire, sai da ta wanke shi tsaf kafin tayi
wanka ta fito d'aure da towel d'in da tagani cikin bayin,
babban hijabin goggo Larai ta saka, kana ta fita can sakar gida ta shanya kayan domin iska ya
busar da su dawuri.
ko da ta dawo d'akin kayan goggo Larai ta saka, ta isa gaban mirro ta shafa mai had'e da d'an
murza pauda, dariyar kanta tayi ganin yan da take yawo cikin kayan dasukayi mata yawa.
kitchen ta nufa in da goggo Larai take had'a Breakfast nan ta iske Zaraddin da Faisal yayan
goggo Larai,
tana shiga kitchen d'in Zaraddin ya fashe da dariya yana nuna ta cikin zolaya irin na d'an kawu
da d'an goggo ya ce
"Wai kin gan ki kuwa kamar an rataya miki kayan ne."
baki ta murgud'a masa tana aika masa da harara ta ce
"To ina ruwan ka d'an sa ido."
bugu ya kaiwa bakin ta cikin wasa yana fad'in
"Ni sa'ar ki ne kike murgud'a min baki?."
kauce wa tayi batare daya same ta ba ta ce
"Wai manya manya da ku wai sai goggo ta shiga kitchen ta girka muku abinci bazakuyi aure ba,
kowa sai yazo ya tsaya wai sai an girka an bashi yaci yatafi gurin ai ki, ai na rantse goggo ki dai
na musu girki duk wan da bazai yi aure ba yarika fita yana zuwa restaurant yana cin abinci."
Faisal daya d'auki plt d'in soyayyen dankali da kwai da goggo ta zuba masa, ya kai lomar kwai
bakin sa ya ce
"Zan je na kai wa Kawu ko da dubu ashirin ne na lallab'a da ke a maneji."
ido ta waro tare da fad'in "Allah ya yi min tsari sabo da na zamo kaza dole a bada dubu ashirin a
kaina, ko miliyon ne ma bazaka samu ba, na kai ka ina zuu ko wasan gona?."
"Kaji yarin yar nan za'a taimake ki kike wa mutane zakin baki."
cewar Zaraddin yana rike hab'a.
hararar su tayi duka kana ta d'au plt ta mikawa goggo Larai tana fad'in
"Ni duk kun cika ni da surutu har kunsa junwan da nake ji ya karu."
goggo Larai ta zubo mata dankali da kwai tana fad'in
"Je ki karya rabu da su sai akace muku kai muke nima da ita da za mu karb'i dubu ashirin ai me
biyan sadakin ta sai ya shirya."
dariya tayi cike da jin dad'i
ta ce " Fad'a musu dai goggo na."
Faisal ya ce
"Ai ashirin d'in ma a hakan tai mako za'ayi mata."
waje tayi tana fad'in Allah ya sawake mata..
Tana gama yin breakfast ta mike ta fito, har lokacin Naseeba na bacci bata farka ba, kayan da
ta wanke ta duba sun bushe ta kwaso, ta dawo d'akin tasaka cikin laida, tasaka hijabi ta fito dan
kaiwa masu kayan kayan su.
a bakin kofar fita daga side d'in suka had'u da goggo Larai, ta ce
"Ina zuwa?." SEEDRAH ta ce zanje na d'auko mana kayan mu ne a gidan Nabeela."
ta ce "Yauwa to ga wani yana sallama da ku a waje."
d'an shiru tayi tana tunanin to waye?, sai kuma tasa kai ta fita tana ce wa goggo sai ta dawo.
a tsaye jikin mashin ta tadda Kamal a kofar gidan, kallo d'aya tayi masa ta d'auke kai zata wuce,
da sauri ya sha gaban ta tare da fad'in
"Barka da safiya antashi lafiya ya mai jiki?."
gajeren tsaki ta ja takuma sa kai zata wuce batare da ta ce da shi komai ba.
yayi saurin kuma shan gaban ta ya ce
"Da ma magani na kawo mata dan nasan zata bukace sa, wannan kuma kayan ku ne daku
zubar jiya garin gudu."
yayi maganar yana nuna mata d'aya laidar dake d'aya hannunsa.
a hatsale ta ce "Tunanin ku kenan sai dai kun mance magani bazai tab'a dawo mata da kima da
martabar da kuka zubda mata shi ba, wlh bakuci banza ba kujira sammaci daga kotu."
da sauri ya ce "Mun ji a yi hakuri muna jira kuma zamu karb'i hukuncin mu, amma dan Allah ki
kai mata maganin nan."
kamar bazata karb'a ba tuno da kawar ta tana bukatar magani dan jikin ta yayi tsami sosai sai ta
fizge laidar maganin a hannunsa had'e da laidar gyale da bra d'in ta da jiya suka watsar da shi
garin gudu,
ta juya ta koma ciki.
a d'aki ta tadda goggo Larai tanayiwa Naseeba sannu da jiki da alama farkawar ta kenan, ta
karaso itama tana yi mata sannu,
jin goggo tana fad'in bari takira almajiri meyi mata shara ya siyo mata magani,
SEEDRAH ta mika mata laidar maganin tana fad'in "Ga magani nan ma ankawo mata,
abokin ango ne angon ne ya aiko sa da maganin shine yake sallama a wajen nan."
goggo Larai ta ce "Ai ko ya kyauta dama hidimar bikin sa ne yasa ta zazzab'in, to bari taci abinci
sai ta sha."
goggo ta fita zuwa kitchen domin samo mata abinci.
Naseeba tayi kasa da kanta jin hawaye ya ciko idon ta tuno da halin da take ciki.
SEEDRAH ta maso ta tare da dafa kafad'ar ta ce
"Wan da yakawo ki nan jiya shine yakawo maganin."
kai Naseeba ta jinjina tayi saurin kai hannunta karkashin idanunta ta taro hawayen da suke
kokarin zubo mata, batare da ta bari SEEDRAH ta gani ba, dan ta san idan tagani sai ta fita yin
kukan har kuma goggo Larai ta fahimci abin da ake ciki.
SEEDRAH ta ce
"Da ma zan je na d'auko mana jaka da wayoyin mu ne a gidan Nabeela daga gurin na biya na
kaiwa matar data bani kaya jiya na amso tawa."
Naseeba ta ce "To sai kin dawo kada ki jima kiyi sauri."
ta ce to.
tana fita Naseeba ta sami damar fitar da hawayen da yake ta cin ta a zuciya...
Gidan Nabeela SEEDRAH ta fara zuwa, a kafa ta tafi sabo da babu wani nisan kirki sakanin su
da gidan goggo Larai, duk unguwa d'aya ne layi ne dai ba d'aya ba.
a parlour ta tadda Nabeela da angonta K'abir sai faman rarrashi yake.
suna gaisawa ya shige cikin bedroom, Nabeela da ta turo