Showing 57001 words to 60000 words out of 78655 words

Chapter 20 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf

na ko da Alhj
Musa muka had'a kud'i muka gina gidan."
ganin haka yasa ta juyawa da sauri tayi kofar bayi tatura kofar da sauri tasako kafarta d'aya
cikin bayin aikuwa tsamtsin tais yajata tatafi suuuuuu tafad'i timmm a kasa.
wani irin gigitaccen kara tasake tare da fad'in
"Wayyo Allah na wayyo bayana kafata kaina wayyo Allah na."
tsaki yaja yajuya yana fad'in
"Kifito yanzu idan ba hakaba sai na canza miki kamanni ki b'ata lokaci kigani."

SEEDRAH ko kukan wahala ta sake tayi-tayi ta iya d'aga ko da hannunta ne ta kasa, dan ba
karamin fad'uwa da buga kanta tayi ba, nan da nan guri yashiga juya mata a take ta sume a
gurin..

S.MAN na zaune a parlour ganin shiru bata fito ba yamike a kufule ya nufi d'akin yana fad'in
"Yarinyar nan idan ba dukan sa'a nayi mata ba bazata dai na sab'a magana ta ba."
ya tura kofar da karfi yashiga, tsayuwa ya yi cikin d'akin yana waige-waige ganin bata ciki,
can ya hangota kwance cikin bayi kasan cewar kofar bayin abud'e take.
ya tako ya iso bakin kofar yana fad'in
"Ke wai baki tashi ba okay nan yazamo miki gurin kwanciya ma kenan, zaki tashi ne ko sai na
tattakaki anan."
ido yad'an tsura mata ganin duk maganar da yake ko motsi batayi ba,
sosai yad'an tsura mata idon nan ya lura da gaba d'aya bata motsi.
a hankali ya sunkuyo kanta yakamo hannunta d'aya ya d'ago yaji sa a sake, sakin hannun yayi
kasa, kana ya kai yatsun sa biyu dai-dai santin hancinta d'ip babu numfashi.
ido yad'an waro kana a hankali ya kai hannu jikin ta yashiga bubbugata nan ma ko motsi batayi
ba, tsaki ya ja yamike har ya kai kofar fita daga d'akin sai kuma ya juyo ya dawo cikin bathroom
d'in da take kwance a sume, ya sunkuya ya sunkuceta cak ya d'agata yafito da ita yana zuwa
bakin gado ya wurgata a kan gadon yana jan tsaki. duk da irin wurgota da yayi a kan gadon nan ko gizau batayi ba sai a lokacin ya gaskata
dagaske bata hayyacin ta.
kugu yarike yana binta da kallo a fili ya furta

"Wai mutuwa tayi ko suma?."
sai kuma ya juya da sauri yaje ya bud'e fridge yaciro gorar ruwa mai sanyi sosai, yadawo bakin
gadon ya bud'e gorar yashiga tsiyaye mata ruwan a fuska da bakin gorar.
wani uban numfashi ta ja a kid'ime kuma a razane sakamakon jan ruwan da tayi a hancinta, ta
jujjuya kai cikin azabar jin ruwan ya wuce mata cikin kwakwalwa duk da bata cikin hayyacin ta
sai da hawaye ya zubo idon ta.
a sannu a sannu tashiga sauke numfashi .
kana a sannu tashiga bud'e idanunta har ta bud'e su duka,
a hankali ta juyar da kanta gefe sai dai da kaga yanayin yan da take yi kasan ba'a cikin
hayyacin ta take ba.
sai kuma tashiga maida idanun nata a hankali ta lumshe su duka asanu-asannu tashiga sauke
numfashi yayin da bacci yasami nasarar d'aukarta cikin halin da ta ke ciki.

Shiko na tsaye a kanta ganin alamun bacci tayi, sai yaja tsaki tare da wurgar da gorar hannunsa
kasa yana mai janye idanunsa daga kallonta,
dan gaba d'aya towel d'in jikin ta daga kasa ya tattare ya yi sama kusan duka cinyoyin ta a waje
suke.
yanayin kwanciyar ta daya jefo ta kan gadon kafarta d'aya a lankwashe yake d'ayan kuma a
mike sai dai a ware yake har ana iya hango pant d'inta ta tsakiyar cinyoyinta.
daga saman kirjin ta kuma kusan rabin ababen kirjinta a waje suke dan d'aurin towel d'in ya
kunce.
juyawa ya yi zai fita harya kai bakin kofa sai kuma ya dawo bakin gadon yana fad'in
"Yarinyar nan rainin wayon ta ma da yawa yake, ke wai bacci ma kikayi dan tsabar rainin wayo
wai kullum sai an fad'a miki aikin ki zaki tashi ne ko sai na canza miki kamanni."
SEEDRAH kam da ma ya ya gwanace a gurin bacci bata ma san yana yi ba.
wani irin fizga idanunsa ya yi lokacin da ya d'aura idanun nasa a kanta dai-dai lakacin da tayi
wani irin mika tare da kuma bajewa ta gyara kwanciyar ta da kyau.
da gyar ya iya tattaro yawun bakin sa ya had'iye mututt.
bin santala santalar cinyoyin ta farare tass yayi da kallo,
a hankali yake yin sama da idanunsa har zuwa kan ababen kirjinta da yanzu sukafi na d'azu
fitowa fili,
tantsan-tantsan d'in nonuwan ta farare soll suna cike tup-tup atsaye kem gwanin bansha'awa
masu tsole idon mai kallonsu.

Wani irin fizgo numfashi yayi tare da yarfe hannunsa had'e da tankwashe yatsunsa biyu wan da
ya tab'a kokarin cusasu cikin HQ d'inta dayaji sun yi masa wani irin fizga wane kurar karfe.
a hankali yashiga ja da baya har ya isa bakin kofa da sauri ya bud'e kofar ya fita har yana had'a
step ya haura sama...........!

Mommyn Twins ce


🌺 *ƘARSASHI!* 🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~





_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

page 18




Direct bedroom ya shige yazube kan kado ya kwanta ruf da ciki, kafafunsa suna rito a kasa,
cike da tsananin mamaki yake jin yanayin da ke shigar sa sai kuma yakai hannu zuwa kan
wandon sa, ido ya waro jin yanda bananar sa ta kumbura ta mike samb'al wane zata faso
wando ta fito. dogon tsaki yaja tare da dunkule hannunsa ya naushi karifa da karfi kamar zai burmata.
da sauri ya mike yanufi bathroom yana jajjan rigarsa yana bud'a ta ta kasa yana rufe abartasa
data mike ta turo wando har rigar.
yana shiga bayi yasakarwa kansa ruwa mai sanyi batare da ya cire kayan jikin sa ba.
numfashi yashiga saukewa a hankali a hankali kana yashiga tub'e kayan jikinsa yana mai
cigaba da matukar mamakin ganin yadda bananarsa tayi wani irin uban kumburar da bai tab'a
sanin yana da kalar halittar ba,
har wani zafi-yafi yake masa.
ya d'au tsawon mintuna 20 a tsaye ruwa na sauka a kansa a hankali yaji abu mai d'umi nabin
gefen cinyarsa.
kasa ya yi da idonsa zuwa gurin, ruwan cikin bakin sa ya furzar had'e da iska mai huci, kana ya
saka hanu yashiga wanke gurin in da ruwan madarar sa ta malala har zuwa kasan kafarsa yana
yi yana jan tsaki,
daga nan ya sarkake jikin sa ya fito.

Ko da yasaka kaya ya haye gado daga zarar ya rufe ido sai ya rika hango surar SEEDRAH na
masa yawo a gido,
kokarin gusar da faruwan hakan yayi sai ya matse idanunsa da karfi dan son bacci ya d'auke
sa, amma me nan ma surar tata ya kuma gani.
zumbur ya mike zaune tare da bud'e idanunsa cike da takaicin yanayin ya ce
"Anya yarinyar nan ba mayya bace kuwa?."
sai kuma yakuma komawa ya kwanta aransa yake ayyana imma mayyar ce sai ya cire mata
maitancin da duka.
da kyar bacci ya d'auke sa da taimakon addu'o'in daya rika tofawa...



A b'angaren SEEDRAH kuwa ba ita ta farka ba sai da aka fito daga sallar asuba.
mika tayi had'e da salati ta mike zaune tana mamakin yanda akayi ta kwanta bacci da towel
bata sa kaya ba a hankali ta zamo bakin gadon tamike tsaye
"Wash."
ta furta lokacin da ta mike tsaye jin zafi a kafarta sai kuma lokaci guda kanta ya sara mata.

da sauri ta koma ta zauna bakin gado, a hankali tashiga tunano abun da yafaru da ita jiya ta san
dai ta fad'i har tayi ihu daga nan kuma bata iya kuma tuna komai ba.
tunani ta soma to ma taya akayi har ta tashi tazo kangado ta kwanta,
ganin bata da amsar tambayarta sai ta yunkura a hankali ta mike tana d'ingisa kafa ta shige
bayi.
sai da tayi wanka kana ta d'auro al'wala ta fito.
bayan ta idar da sallah a hankali ta mike taje ta saka kaya tanufo waje dan lokacin gari ya yi
haske.
a daddafe ta gama ayyukan ta na kasa dan jikinta ciwo yake mata musamman ma kafarta da
kuma kanta dake ta yi mata ciwo.
ta d'au tray d'in data shirya masa kayan breakfast ciki,
ta nufi step's a hankali take d'aga kafarta harta haura.
a sakiyar parlour ta dire tray d'in saman table kana tashiga gyaran parlour'n koda ta gama
gyaran parlour'n kofar bedroom d'in sa ta kalla sai kuma ta juya da niyyar sauka kasa sai idan
ya gama abunda zaiyi yafito kafin tazo ta gyara,
dan bazata shiga ta je ta ganewa idanunta abin da bai da ce ba.

Tana juyawa tajiyo karar bud'e kofa a hankali ta waigo, ya mai da kofar ya rufe sanye yake da
singlet da 3qrt yana rike da sigari a hannunsa yana d'an zuka ya yin da d'aya hannunsa kuma
yake cikin aljuhun wandonsa.
a sannu yake d'aga kafarsa har ya karaso cikin parlour'n ya zauna kan kujera yana mai cigaba
da shan sigarin.
fuska ta yamutsa tana kawar da kanta gefe tare da kore iskar dake had'uwa da hayakin sigarin
da hannunta.
cikin kuma yamusa fuska ta d'an kalli gefen da yake ta ce
"Zan shiga nayi aikina ko zaka iya ce mata ta fito tajira awaje nagama."

Bayansa yajingina da jikin kujera kana a hankali
yad'an zuba mata narkakkun idanunsa da basu sami
bacci jiya ba.
"Tambaya ne yakawo ki gidannan ko ai ki?."
ya yi maganar yana kokarin janye idanunsa a
kanta sakamakon jin yan da idanunsa ke fizga sai yanayin yan da yaganta jiya ke dada zuwar
masa sabo.
Sarai ya fahimci abinda take nufi tana tunanin Teema tana cikin d'akinne baki yabe tareda
maida idanunsa ya lumshe.
Fuska ta yamusa akasan ranta tana ayyana bazata shiga d'akin taganewa idonta ba dai-dai ba.
shiko
da sauri ya ware idanunsa sakamakon ganin surar jikinta b'arob'aro tamkar alokacin ne hakan
yafaru.
"Ke mayya ce ko!?."
Yajefo mata tambyar idanunsa a kanta.
Ido tad'an waro ganin yanda ya tsareta da ido yana

wani muzurai.
manyan kwayar idanunta ta kad'a sannan ta ce
"Eh mutane 99 na cinye inata kan niman cikiton na d'arin kenan."
A hatsale ya ce
"To ni nafi karfin ki sai dai kici kanki wuce ki bace min da gani mayya kawai."
yanayin yanda yake maganar yaso yabata dariya sai kuma ta gimtse ta juya tasoma tafiya
tana fad'in
"Katab'a ganin in da maye yaci kansa da kansa dole dai ya samo abokin tafiya."
tayi gaba tana murgud'a masa baki ta juya tabar gurin.

Dogon tsaki yaja yamike tsaye ya yi wurgi da sigarin hannunsa.
ya dunkule hannu ya naushi iska tare da furzar da huci mai zafi sai kuma ya juya da sauri
yanufi steps.
ko da ya sauko kasa gurin motsa jikin sa ya nufa yahaye kan machine d'in motsa jiki yakure
masa gudu.
gudu yake babu ko kakkautawa baya jin kuma yagaji.
yashare tsawon awa guda yana gudu kafin yakashe na'urar ya sauka yana maida numfashi.

Makullin motar sa ya zara yabar gidan, dan ji yake idan yacigaba da zama a gidan zata iya
cinyesa da maitar ne da gaske dan shi yan da yake ji da ganin suffarta a idon zucinsa da gaske
maitar take.
Wunin ranar baiyi a gidan ba.
dan gani yake zaman su tare a gidan ne yake sashi ganin ta cikin kwakwalwa da zuciya da
idanunasa, cikin suffar da ya ke hargisa masa lissafi.
bai dawo gidan ba kuwa sai dare yau ko niman tea d'in daren ma baiyi ba...

Washegari yatashi da shirin barin kasar zuwa Kanada buga wani wasan da za a gudanar.
da sauri ya sauko cikin shigar kana nan kaya da suka amshi jikin sa ba kad'an ba tamkar dan
shi akayi su, yana tafe cike da Karsashi yake taka kasa tamkar namijin zaki.
a parlour ya taddata tana gyara, tana ganin shi ta d'auke kai tacigaba da abin da take tana yi
tana bin sansanyar wakar soyayya da ke tashi a wayan ta,
a hankali tana jin wani irin shauki da son Kamal dake dad'a ruruwa cikin zuciyarta.
d'aga kiran daya shigo wayarsa ya yi bayan ya gama magana ya sauke wayar da d'an sauri ya
dube ta ya ce
"Ke saurare ni zan yi tafiya, saura kuma kiga bana nan ki ajiye ayyukan gidan nan nadawo na
sami datti da kura, naga wani abu ba dai-dai ba zaki had'u da b'acin raina."
yana maganar yana tafiya da alama dai sauri yake.
baki bud'e tabi bayansa da kallo haryakai kofa
"Wai zama zanyi a gidan nacigaba da bautatawa gidan da ba kowa ciki, na rantse bazan
zaunaba ka nimo wata ma'aikaciyar ba ni ba kam."
ta shige d'aki da sauri ta d'au mayafinta kana tashiga washe kaya tana sawa cikin jaka ta janyo
akwatinta tayi waje.

Koda ta fito farfajiyar gidan bataga d'aya daga cikin motocinsa ba har ya tafi kenan.
tawuce bakin get tana kokarin bud'e karamar kofa taji sa a kulle.
kallon in da maigadi ke zaune can gindin wata fulawa yana ta uban goge baki da asuwaki tayi ta
ce
"Malam zo ka bud'e min kofa na fita."
da sauri ya furzar da abin bakin sa ya ce
"Rufamin asiri zo ki koma ciki oga ya ce ba shiga ba fita, ki koma kawai abinki kije ki more daula
kafin ya dawo kasar, anjima ki kunna mana TV zan shigo mu kalli wasan da zai buga amma dan
Allah karkice masa nashigo."
wani uban harara ta wasa masa cikin masifa ta ce
"Dalla malam kazo ka bud'e min kofa kana fad'a min wasu abubuwan da basu shafeni ba na
rantse idan baka bud'e ba sai na kirawo masu b'alla kofar nan."
ya zari buta yayi hanyar bayi yana fad'in
"Hajiya kirawo su su b'alla amma ni kam bazan bud'e da hannuna ba."

Duk uban masifar da take yana jin ta yaki fitowa daga cikin bayin,ta janyo jakarta ta koma ciki ta
d'aga waya takira Mama.
ko sallama batayiba sabar yanda take jin kanta
"Mama wai kiji mutumin nan wai ya yi tafiya wata kasar yasa a ka kulle ni a gidan, wa aljanu zan
cigaba da yiwa aikin, Mama ku kirasa yasa a bud'e min kofa, idan ba haka ba Allah sai na sa an
b'alla kofar nan da get d'in gaba d'aya yadawo ya same sa a ajiye,
wai wani in zauna in cigaba da yin aiki meye nufinsa, ina dama aikin washi akeyi ba wa fanko
ba, tun da baya nan meye amfanin aikin."
"A'a SEEDRAH ki saurare ni kada kiyi yinkurin yin wani abu kibi sa a sannu arabu rafiya da
Usman, kada ki kuma jawo mana wata matsalar kiyi hakuri ki zauna d'in kici gaba da yi har ya
dawo."
"Mama mutumin nan fa ba mutunci yake da shi ba sai ya iya cewa aikin da nayi bayanan
yazama ziro baza a cire kud'in acin kud'in da yake bin Baba ba, wahalar banza kenan fa nayi."

Mama ta ce "Watakila ba jimawa zaiyi ba kicigaba dayin aikin naroke ki SEEDRAH arabu lafiya
da Usman."
kai kawai ta girgiza ta kashe wayar batare da takuma cewa komai, bakin ciki had'e da haushin
S.MAN ne kawai ke cinta a zuciya.
taji ta yarda zata zauna tayi aiki a karkashinsa ko dun ta tsare mutuncin iyayen ta, daga kaidin
S.MAN da baisan in da mutunci yake ba.

Kwanan sa biyu da tafiya bayan tagama dukkanin ayyukan ta tana zaune a parlour, manne da
waya a kunnenta suna soyewa da habibinta Kamal daya dawo jiya.
cikin hirar tasu yake cewa
"Baby nifa na gaji da rashin ganin ki naso a ce jiya dana dawo garin nan, dake nafara tozali ban
san me yasa kike son horani da rashin ganin ki ba,
kibarni nazo na ganki please."
kai ta kwantar jikin kujera cike da shaukin so ta ce

"Kai da ka kusa mallakata gaba d'aya saurin me kake."
"No nasani kibari na ganki zanfi samin sukuni."
ido ta d'an lumshe tana tunanin ta inda zata fara tasan maigadi bazai tab'a barin sa ya shigo ba
ita ma kuma bazai barta ta fita ba.
muryar sa tajiyo yana fad'in
"Zanzo yanzu please kada ki hanani ganin ki, nasan S.MAN baya kasar dan jiya duk da gajiyar
dana kwaso na hanya bai hana ni zama kallon wasan sa ba, yanzu ma haka ina gaban TV ina
kallon maimaicin wasan nasa na jiya."
to ta ya zatayi ta fad'a masa ya kulle ta ya hanata fita yakuma hana wani ya shigo gidan, murya
a marairaice ta ce
"Kabari zan zo gida gobe sai mu had'u."
"Har gobe!."
yafad'a cikin nuna damuwa sosai.
"Yi hakuri mana da yau da goben ai duk d'ayane."
duk yan da yaso yasan dalilin hanashi ganin nata taki sanar masa ammsar dai d'aya ce yabari
goben zasu had'u.
a haka dai sukayi sallama tana jin ba dad'i dan ita kanta ba karamin missing d'in sa tayi ba.
numfashi ta sauke lokacin da take aje wayar,
ta d'au rimut ta canza tashar da take kallo bawai ko dun tana fahimtar abin da akeyi a TV ba
gaba d'aya lissafin ta a jagule ya ke.

Nan ko idananuta ya sauka kan S.MAN da ke zuba uban gudu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login