Showing 42001 words to 45000 words out of 78655 words

Chapter 15 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf

Advertisement

ya d'aga ya naushi iska ya kai hannayen sa duka biyu yacusa cikin sumar kansa ya
yamutsa. sai kuma yashiga kai koma a gurin yama rasa me zaiyi.
sai kuma da sauri ya zaro wayar sa tare da lalub'o lambar Baba ya dannan masa kira
Baba ya d'aga da sallama batare da ya amsa sallamar sa ba ya ce
"Kud'in motata naira million 80 kazo ka had'a kabiya...........!

Mommyn Twins ce









🌺 *ƘARSASHI!* 🌺




*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*




( _Book 1_)

~Free page~



_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*🇦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*

```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




page 14






Da sauri Baba cikin matukar shiga tashin hankali ya ce "Wata motar kuma?."
S.MAN ya ce "Motar da 'yarka ta la'anta shi yanzu kud'in motar na fad'a maka kazo yanzu ka
biya ni."
ya na gama fad'in haka ya kashe wayar sa.
Baba kuwa cikin matukar tashin hankali yafito a bujajan ganin yan da yafito daga d'akin sa
hankali tashe yasa su Mama tambayar sa abun da ke faruwa, bai iya tsayuwa basu amsa ba
yayi waje yaja motar sa ya yi new G.R.A gidan S.MAN.

S.MAN kuwa na kashe wayar yajuya da sauri sai huci yake yaje yarika bubbuga kofar
SEEDRAH taki bud'ewa yarika buga kofar yana fad'in
"Wlh yau sai na canza miki kamanni ki bud'e kofar nan."
ta ce "Bani bud'iwa kuma ina mai tabbatar maka a duk san da ka sake kuskurin kai hannunka
jikina da sunan duka ko shaka wlh karika yin na kud'in ka kenan, kad'an ma ka gani."
naushin kofar yayi dakarfi har sai da ta ja da baya cikin matukar tsoro, dan gani take kofar ma ta
b'alle.
cikin fusatacciyar murya ya ce
"Kin jawa wanjan tsohon."
jin shiru bai kuma magana ba yasa ta komawa ta zauna jiki a d'an sanyaye dan tasan gurin
Baba yanufa yanazu, Allah ne kad'ai yasan cin mutun cin da zai je ya yi masa.

A b'angaren Baba kuwa cikin mintuna kalilan yakawo shi gidan S.MAN yayi hon maigadi ya
bud'e masa get.
yana faka motar da sauri ya fito, can yahangi S.MAN a gurin hutawan shi na musamman a cikin

gidan wan da aka kawata shi tamkar a turai.
yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun da suke zagaye da gurin ya d'aura kafarsa d'aya kan
d'aya yana d'an girgiza kafar, sigari na rike a hannunsa yana sha, idanunsa kuma suna lumshe.
da sauri Baba ya karaso in da yake yana fad'in
"Usman ina motar take ina kuma ita SEEDRAH?."
Baba yayi maganar cikin nuna tsantsar damuwa.
hayakin sigari ya zuko tare da buso shi kana ya bud'e idonsa d'aya ya kalli Baba da shi cikin
kanne ido da rashin daraja ya ce
"Ka taho da kud'ad'en?."
hannu Baba ya rungume jiki a sanyaye.
S.MAN yakuma mai da idonsa ya lumshe yana fad'in
"Au na mance ashe kai fakiri ne, to ni ko fashi zakaje kayi kaje kayi kakawo min kud'ina wan da
kaci bashin sa naira million 30 da kuma wacce 'yarka ta la'anta motar million 80."
Baba ya ce
"Dan girman Allah Usman kayi hakuri a ina zan sami wad'an nan kud'ad'en?."
da sauri S.MAN yabud'e idanunsa ya ce "Anya ba kaika sata ba ma kuwa? dubi yadda ta goge
min mota ta b'ata shi, kai komai akayi ma da sa hannunka, duba fa dubafa ka gani."
yayi maganar yana nuna parking lot can in da motar take.
Baba ya ce "Haba Usman taya zanyi na sata tayi maka b'arna wlh sam banda masaniya a kan
haka, ina SEEDRAH take?."
"Tana ciki kaje ka fito da ita dan wlh yau sai na saita mata tunani."

Da sauri Baba ya shiga ciki yana waigen motar da SEEDRAH ta goge fentin sa kamar zata
sake masa wata fentin.
tun daga bakin kofa Baba ke kiran ta har ya shiga ciki.
S.MAN daya biyo bayansa yakaraso yana fad'in
"Can kofar zakaje ka fito da ita in ba hakaba kuma na b'alle kofar ni naje na same ta."
ya nuna masa kofar d'akin da SEEDRAH take ciki.
Baba ya matsa bakin kofar da sauri shiko S.Man ya haura sama.


Tana nan zaune cikin zullumi da tunanin rashin mutuncin da yanzu S.MAN yaje yake kanyiwa
Baba tajiyo ana bubbuga kofa.
a d'an firgice ta mike tazo bakin kofar
Baba yakuma bubbuga kofar tare da fad'in
"Ke SEEDRAH bud'e kofar nan hauka kikayi ne wani shashanci ne wannan kin san kuwa
barnan tulin dukiyar da kikayi? maza bud'e kifito nan."
jin muryar Baba yasata bud'e kofar tafito tana rarraba ido tare da turo baki.
Baba ya ce "Zonan maza."
yafad'a yana nufar in da kujeru suke ya zauna, ta karaso ta zauna kasan carpet gefe da shi.
Baba ya dube ta hankali tashe ya ce
"Meyasa hakan meyasa zaki sa abu ki goge masa jikin mota kin san kuwa kud'in motar nan
SEEDRAH?, ta ina ne zan iya samo kud'in motar nan SEEDRAH ata ina ne zan iya samo

miliyan 80 ban da kud'in da yake bina iye SEEDRAH, meyasa zakiyi haka."
"Baba ai nace masa ban iya wankin mota ba ya ce sai nayi."
"Tafi can da'alla sai kuma dan baki iya ba sai ki saka abu ki goge motar har sai kin cire fentin
jikin sa, yanzu ko kud'in fentin motar ce ma a ina zan samu nabiya sa asake yi masa fenti bare
kuma kud'in motar."
baki ta kuma turowa zatayi magana sukajiyo muryarsa yana sauko wa daga matattakalar bene
"Ko da kana da kud'in fentin ma bazan karb'aba sabuwar mota nake bukata."
yakaraso ya zauna kan kujera tare da d'aura kafa d'aya kan d'aya.
Baba yashiga basa hakuri kamar zai zuba guiwowinsa kasa yana had'asa da Allah da manzon
sa, shiko sai wani cika yake yana batsewa daga bisani yad'aga wa Baba hanu ya ce yaje amma
fa zai neme sa aduk san da bukatar hakan ta taso dan bai hakuraba.
Baba ya tafi yana mai jaddadawa SEEDRAH ta kiyaye kada wata matsala takuma faruwa.

SEEDRAH nakokarin mikewa ta bar parlour'n ya dube ta yama rasa me zaiyi wa yarinyar, yaso
yimata dukan da gobe idan akace takuma b'arnata masa wani abun bazatayi ba.
ya ce "Kizauna da shirin ki dan wlh sai nayi miki dukan kud'in motata."
wani kallon sama da kasa ta bisa da shi kana ta ce
"Ni kuma wlh ka kuskura ka tab'a ni sai nayi maka b'arnar da har ka mutu bazaka manta ba, duk
ranar da ka sake kuskuran kai hannu jikina sai kayi da na sani, ba wankin mota kace ba'
shiyasa nikuma nayi masa wankin da zai dad'e bai yi datti ba ko gobe kakuma sani haka zan
yiwa sauran motocin."
ta murgud'a masa baki tayi wucewar ta d'aki.
baki ya bud'e da mamaki yake kallonta harta shige d'aki sai kuma da sauri yabiyo bayanta yana
fad'in
"Me zaki yi, me zaki iya yi?."
ta ce "Komai ma idan kuma kana ganin wasa ne to ka gwada."
tayi maganar ne cikin dakiya ganin yadda yake dad'a maso ta, ya mika hannu da zummar cafko
ta, ta ja da baya tare da d'aukar plt dake kan mirro ta ce
"Idan ka kuskura ka tab'ani sai na buga maka."
murd'e ta yayi ya kwace plt d'in tare da angizata tagaru da jikin gado.
kana ya ce
"Baki isa ki b'ata min mota kici banza ba,
kinyi abakin abincin da kike ci a cikin gidan nan, dan nasan Alhj Musa bashi da kud'in da zai iya
biyana b'arnan da kika min,
daga yau abinci sau d'aya zaki rika ci a gidan nan iya na safe kawai sai kuma wata safiyar,
sannan kuma ruwan gidan nan ya haramce ki sai dai idan zaki rika shan nacikin bathroom."
baki ta murgud'a masa ta ce
"Sai me."
ganin yana kokarin kuma maso ta taruga da gudu tayi cikin bayi ta murd'a key..

Bata fitoba sai da ta tabbatar da yatafi, tana fita kiran wata 'yar ajinsu mai suna Firdausi na
shigowa wayarta.
bayan sun gaisa Firdausi take cewa

"SEEDRAH kina da labarin gobe za a shiga yajin aiki kuwa?."
ido ta waro ta ce "Dan Allah fa wlh bani da labari."
Firdausi ta ce "Wlh nima d'azu K.B yake fad'a min zuwa yanzu kuwa ai labarin ya baza ko ina."
"Wayyo ban ji labarin ba Allah dai yasa adawo da wuri."
"Amin ya Allah."
nan sukayi sallama..

Tun daga ranar S.MAN bai kuma sa SEEDRAH wankin mota ko baiwa fulawa ruwa da duk
sauran ayyukan daya shafi sakar gida ba.
aikin cikin side d'in kawai takeyi,
sannan kuma ya kwashe duk wasu kayan sha dake cikin fridge d'in parlour'n kasa zuwa kichin
bedroom d'inta duk ya kaisu sama.
kamar yadda ya ce sau d'aya zata rika cin abinci kuwa hakan akayi duk san da zatayi abincin
rana dana dare zama yake a parlour har sai ta gama tana gamawa kuwa zaice ta kai masa
sama sannan yakulle kichin d'in yatafi da key d'in.
ganin haka kuwa idan tayi breakfast sai ta zuba da yawa cikin kula shi zatayi ta ci har dare.
a haka har ta shafi tsawon sati uku a gidan.
duk yadda taso zuwa gida yahanata yakuma ce mata idan ta sake ta fita to sai ya cire kud'in
fitar cikin albashin ta,
tun da tazo aiki tofa aikin kawai zatayi babu fita.
idan tayi yunkurin fita kuma maigadi yaki bud'e mata kofa ya ce Oga ya ce kada ya barta ta fita.
duk san da tayi waya da Mama takan cewa Mama itafa ta gaji tana so ta zo gida ta ganta
yakuma hanata fita.
Mama ta ce tabari kawai takula da aikin ta duk gidan suna nan lafiya.
haka SEEDRAH tayi ta mita wai sai kace tazamo matar kulle sai yarika nuna mata wani
busasshen iko, ko shi a su wa oho,
dan tana aiki a gidan sa sai ya zamo ko waje bazata leka ba dan rainin tsintsi ma wai harda
gidan su yahanata zuwa.

A B'angaren Kamal kuwa yagaji da zuba idon ganin komawarta gida,
gashi yana son ganin ta duk san da yace mata zai zo, sai ta ce masa yabari tukun.

Kwance take akan gado like da waya a kunnen ta suna waya da Kamal,
cikin hirar tasu yake ce mata
"Nifa yau hakurina yakare ganin kyakkyawar fuskarnan taki kawai nake da bukata."
murmushi tayi tare da fad'in
"Um bagashi kana jin muryata kullum ba."
"Inaa jin murya kad'ai bai wadatar ba ganin ki nake son yi, na dauren na daure dauriyar takasa
kai ni ko ina, yau zan zo kawai naganki."
"To ai baka san gidan ba."
tafad'a cike da d'an zullumi da tunanin zuwan nasa, bakomai yasa taki barinsa yazo gidan ba
sai dun gujewa wulakancin S.MAN dan tana da tabbacin zai iya wulakanta sa idan yazo dan
abune mai sauki a gurin sa.

ya ce
"To tun da abun kauna ta tana ciki me zaisa sai na sani nemo sa kawai zanyi, in ban da abunki
gidan jarumin namu ne zai gagare ni sani,
yanzu idan na bukaci hakan za'a kai ni har kofar gidan."
murmushin yake tayi
"Ni dai ka huta kawai bance ka wahalar min da kanka ba, kuma gobe ma zanje gidan Nabeela
ta haihu daga gun zan wuce gidan Naseeba can zan wuni."
ya ce "Da gaske."
ta ce "Eh mana." "To shike nan Allah ya kaimu."
nan sukayi sallama.
numfashi ta sauke tana aje wayar a gefen ta, fatan ta kada Allah yasa yazo gidan dan bazata
iya jurar ganin tozarcin S.MAN agare shi ba.
mikewa tayi ta nufi kofa dan lokacin d'aura abincin rana yayi.
tana fito wa cak taja ta tsaya nan bakin kofar,
da d'inbin mamaki take dad'a ware idanunta kan S.MAN dake zaune kan kujera wata budurwa
na zaune a kan cinyarsa tawani sakalo wuyansa da hannayen ta, takawo fuskarta daf da nashi
tana yi masa magana.
shiko hannunsa d'aya ya saka ya tallafo bayan ta ya yin da d'aya hannunnasa kuma ke rike da
waya yana daddannawa.
baki bud'e SEEDRAH ta ke kallon su sai kuma tayi saurin janye idanunta tare da yin gyaran
murya.

Da sauri budurwar mai suna Teema ta waigo tana bin SEEDRAH da kallon mamakin yadda
akayi ta ganta a nan bayan tasan shi kad'ai ne cikin gidan.
SEEDRAH ko tafiya ta soma tazo ta wuce su ta shiga kichin, a ranta take ayyana girman
lamarin nasa ashe dai ba iya shaye-shaye ya tsaya ba har da neman mata.

A parlour kuwa kallon tuhuma Teema take yiwa S.MAN mikewa tayi a jikin sa ta zauna gefen sa
tare da ruko hanun sa sannan ta ce
"S.MAN wace ce kuma wannan?."
batare da yad'ago daga kallon wayar da yake ba ya ce
"Ƴar aiki ce." ido Teema ta waro tare da fad'in "Ƴar aiki, wannan ce 'yar aikin?
haba S.Man kada ka cigaba da rainamin hankali mana, ashe dama kayi aure ne shiyasa dana
bukaci nazo kace min baka kasar, yaushe kayi aure S.MAN?."
gabaki d'aya ganin SEEDRAH yasa hankalin Teema mugun tashi tabi ta rikice.
d'an kallon ta yayi kana ya ce
"Na ce miki 'yar aiki ce."
cikin rashin gamsuwa da maganar sa tayi murmushi wan da yafi ihu ciwo, ganin rainin hankalin
da yake mata yadubi wannan zankad'ed'iyar yarinyar ya ce wai ita ce 'yar aiki. sai kuma ta
girgiza kai tare da fad'in
"Basai ka b'oye min ba ni ban damu da kayi aure ba zan cigaba da jiranka idan ka gama more
amarci idan kana bukatar karin wani amarcin zaka iya nima ta, ko yanzu ne ashirye nake."

A cikin kichin kuwa SEEDRAH na d'aura girki tafito, bata kuma kallon in da suke ba tazo zata
wuce su tajiyo muryarsa ya na fad'in
"Ke ba kiga bakuwa bace ki kawo mata abun sha."
cak ta ja ta tsaya tare da juyowa da zummar ce masa baya daga cikin jadawalin aikin ta
kawowa karuwa abin sha.
sai kuma ta juya ta hanyar tausar zuciyar ta tahaura sama domin kawo mata, dan duk
yakwashe duk wani abin sha ya kaisu sama.
Teema ko baki bud'e take binta da kallo harta haura sama tana ta son ta gaskata wai shin da
gaske ne 'yar aiki ce.
sai da takawo drink's d'in yasata ta bud'e ta zuba mata a kofi kafin ta gaskata cewa 'yar aikin ce
dai da gaske,
sai dai tana ta shan mamaki ace kamar wannan takasance a 'yar aiki, dan tayi imani har idan da
matar sa ce ko auren kiyayya akayi musu dole sai taga kishi a kan idonta a yanda tafito ta
samesu d'in nan, bare kuma har taje ta kawo mata abin sha.
ko da SEEDARH ta juya tanufi d'aki bayan ta Teema tabi da kallo har ta shige ciki.
gabaki d'aya tasha jinin jikin ta wai ace wannan ita ce 'yar aiki, ba sai wani yafad'a mata ba
tasan SEEDRAH tafita komai da kamai kyau diri da komai ma na tsarin zubin halitta.
wannan itace S.MAN ya aje amatsayin 'yar aiki matarsa kuma to ya zata kasance kenan?.
tayiwa kanta tambayar acikin zuciyar ta, sai yanzu ta samo amsar da yasa yaki aurenta sannan
kuma yaki amsar tayin bukatarta na mallaka masa kanta koda bai aure ta ba.


Wace ce Teem?.
Teema d'iya ce ga wani hamshakin d'an siyaya a Nigeria ta jima tana d'awainiya da dakon son
S.MAN a zuciyar ta,
saboda tsabar son da take masa duk kasar da zaije buga kwallo sai ta bi jirgi taje ta same sa.
duk yan da taso ta juyo hankalinsa gareta ta garara dan har kanta ta ce zata bashi tasha tub'e
kayan ta a gaban sa amma ko kallo bata ishe saba, wasu lokutan yakan tab'a jikin ta sai dai
baya wuce gona da iri.
duk da S.Man yarayu cikin turawa baisashi mu'amalar banza da mata ba, ya kanyi iya bakin
kokarin sa wajen kame kansa, ba Teema kad'ai ba akwai mata da yawa masu kawo masa
kansu baya sauraran su.
wannan kenan...



Ko da SEEDRAH ta kuma fitowa duba girkinta basa cikin parlour'n yanzu, dan haka ta wuce taje
tacigaba da aikin ta.

Da yammacin ranar tana zaune cikin d'aki bayan tayi wanka ta shirya cikin riga da siket na
atamfa, tana zaune a bakin gado tana d'an daddanna wayar ta, gabaki d'aya kad'aici ya ishe ta
kewar Mama da 'yan uwan ta duk sun addabe ta.
a hankali ta d'ago kanta jin an turo kofar

Ganin shine sai ta maida idanunta kan wayar tacigaba da abun da take.
yana tsaye rike da kofar daga nan bakin kofar ya ce
"Wa kika gayyato mun shi gida na?, kefa kawai 'yar aiki ce, baki da ikon da zaki shigomin da
wani cikin gidan nan, na ce masa yatafi na aike ki."
da sauri ta d'ago tana duban sa akasan ranta ta ce
"Kamal kazo kenan."
"Kada ki kara gaiyato min wasu 'yan iska cikin gida daga yau."
ya juya yana kokarin fita
da sauri ta ce "Shine zakace masa ka aike ni alhalin ina nan, shi ba d'an iska bane kamilin
mutum ne, ko waccan karuwar da tazo ba'a ce mata baka nan ba bare kamilallen mutum."
kofar ya janyo batare da yayi magana ba sakamakon kira data shigo wayar sa.
da sauri ta mike zatayi waje kiran Kamal ya shigo wayar ta, cikin hanzari ta gad'aga
Kamal

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login