Showing 33001 words to 36000 words out of 78655 words
Chapter 12 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
gasu Halimatu ya ce basu yake bukata suyi masa aiki ba ita
SEEDRAH yake bukata."
"Alhj to karatun ta fah sai dai tarika zuwa da farar safiya ta dawo ta tafi makaranta ke nan."
hannuta Baba yakuma damkewa ya ce
"Nima nayi tunanin hakan amma ya ce zama zatayi acan gidan nasa, ai inaga babu wata
matsala in yaso daga can d'in sai ta rika tafiya makarantar."
"Amma Alhj.."
katse ta ya yi da afad'in
"Hakan ne kad'ai mafita kituna fa idan mukace zamuyi masa musu to fa babu makawa sai
munbar gidan nan,
dan Allah kada kikuma cewa komai ki kirawo SEEDRAH kiyi mata maganar ta shirya idan Allah
yakaimu gobe zan kaita gidan nasa."
Numfashi Mama tasauke kana ta gyad'a masa kai jiki a sanyaye, Baba ya mike ya fita, yana fita
Mama ta daga waya ta kirawo lambar SEEDRAH.
SEEDRAH dake kwance a d'akin su manne da waya a kunne suna waya da Kamal, ganin kiran
Mama yasa ta cewa Kamal d'in ya kashe bari taje kiran Mama, ta mike ta nufi d'akin Mama.
Mama na ganin ta tamike daga kan sallayan da take zaune ta koma bakin gado.
"Zo zauna nan." Mama tafad'a tana nuna mata gefe da ita.
SEEDRAH ta karaso ta zauna kusa da ita
Mama ta dube ta da kyau kana ta ce
"Yayan ku Usman yazo."
SEEDRAH ta ce "Waye kuma Yaya Usman Mama?."
"Usman d'in Abba'n ku Sulaiman S.MAN fa."
baki SEEDRAH ta tab'e ta ce
"Usman dai ko S.MAN d'in babu wani Yaya mutumin da baya ganin darajar Baba mezai sa
shima a daraja shi, yakuma zuwa ciwa Baban mutunci ne?."
kai Mama ta girgiza kana ta ce
"Ki shirya kayanki gobe Baba ku zai kaiki gidansa zaki je ki d'an rika kula masa da gida ne."
wani irin waro ido SEEDRAH tayi tare da d'an zabura tanuna kanta ta ce
"Ni nine zanje gidan sa kula masa da gida?!."
sai kuma ta shiga girgiza kai tana fad'in
"Mama kinsan me kike fad'a kuwa tayama hakan zata kasance, ina bazai yuwuba babu in da
zani, wato ta nan ya b'ullo, wata kofar wulakanta Baba ke nan ya samo ko, to wlh bazai tab'a
yuwuwa ba ni kam babu in da zani."
ganin yanda ta birkice gaba d'aya tana kokari mike wa Mama ta ruko ta tana fad'in
"Ke SEEDRAH ki nutsu ki saurare ni kiji, bijirewa hakan tamkar kuma rura wutar da akeson
mutuwa fetur ne,
a daren nan yazo yasami Baban ku da batun,
ya ce yanason kije kirika yi masa aiki a gidan sa sannan kuma zai rika biyan albashi wan da
acikin kud'in da yake bin Baban ku za a rika zarewa."
hannunta Mama ta dad'a rikewa da kyau kana taci gaba
"SEEDRAH mutuncin Baban ku da kike son karewa tanan ne zakibi domin dad'a kare masa
mutunci da kimarsa,
har idan kika bijirewa hakan tamkar kin dad'a bada kofar da Usman zaizo yarika ciwa Baban ku
mutunci ne daga karshe kuma ya karb'e gidan nan,
mu bazama yawon gidan haya haka zamuyi ta tsugune tashe,
kisawa ranki neman kud'i zakije domin ki kare mutuncin mahaifinki, ai wannan wata kofa ce
muma da muka samu ta in da zamuyi aiki a karkashin sa sannan kuma musamu mubiya wani
abu daga cikin bashin da yake binmu,
ko kin fi so yaci gaba da zuwa yana tozarta mahaifin kine iye SEEDRAH?."
Tuni hawaye yashiga sauka a idanun ta. bakinciki da takaici sune suka sata zubda kwalla wai
ita ce zata je gidan wani amatsayin 'yar aiki wanin ma S.MAN mutumin da tafi tsana a
rayuwarta.
Allah kad'ai yasan manufar sa na son ta kasance 'yar aikin gidan sa,
tama rigada da tasan wani tozarcin yake shiryawa Baba.
kai ta girgiza tace
"Bazai yuwu ba bazan tab'a zuwa karkashin sa nayi aiki ba,
ko da ace kuwa shi yafi kowa kud'i a duniya bazan je gidan sa a matsayin 'yar aiki ba, idan aiki
kuke so nayi to dan Allah Mama ga gidajen masu kud'i da yawa ku turani can narikayi musu
wanke-wanke da shara da wanki kai harma da girki,
murika tara kud'in ana rage masa bashin sa."
"SEEDRAH kina tunanin albashin da za a rika biyanki a wani gida dan kina wanke-wanke da
shara zai bada wani kwakkwarar gudumawa ne wajen biyan bashin da Usman ke bin Baban ku,
kinsan kuwa nawa yake binsa to ko albashin gwamnati kika fara karb'a sai kin b'ata tsawon
lokaci mai nisa kafin yakai adadin kud'in da yake binsa,
to amma tun da shi yace da kansa zai rika cirewa cikin kud'in da yake binsa shike nan wata kila
wata rangwami ya yi niyyar yi masa,na samun saukin biyan bashin da yake binsa."
Duk yan da Mama taso SEEDRAH ta amince sam taki, dan acewarta dataje tayi aiki a gidan
S.MAN gara taje tayi sharan titi.
kwana biyu a na abu guda,
Baba Mama Umma kullum sai sun tasata gaba. su Halimatu kuwa cewa sukayi tun da taki
amincewa su zasu je, musamman Suhaital da wutar kaunar S.MAN ke balbalar ta har kayan ta
ta had'a ta ce zata tafi gidan nasa,
Baba ne ya hanata dan bai mance da wacce S.Man d'in ya ce ita zata je aikin ba.
a daren ranar kwana na biyun kiran S.MAN yashigo wayar Baba,
yana d'agawa ya sinkayo muryarsa yana fad'in
"Tun da ka kasa sata tazo to ni bazan kasa zuwa karb'ar gidana ba, duba takardun gidan ka
gani anya suna tare da kai kuwa."
yana gama fad'in haka ya kashe wayar.
da sauri Baba ya mike yaje in da takardun gidan suke adane, wani irin bugawa kirjinsa yayi
lokacin da yaga basa gurin.
bincike yashiga yi cikin d'akin ta ko ta ina amma babu su babu alamun su.
ya fito daga d'akin sa yanufi d'akin Mama har yana cin karo.
SEEDRAH dake cikin d'akin tana kad'ewa Mama gado zata kwanta ta mike da sauri ganin
yanda yashigo d'akin.
Mama ma mikewar tayi tana tambayar sa lafiya.
Baba ya ce "Ina kuwa lafiya Usman ne yakirani yanzu, na tabbata har idan gobe yasa kafarsa a
gidan nan to tabbas munbar gidan nan kenan dan kuwa ina da tabbacin takardun gidan nan
suna hannunsa dan basa in da na ajiye su, bansan ta yadda akayi suka shiga hannunsa ba,
maganarsa ya tabbatar min da suna hannunsa." Maganar Mama taji ta na fad'in
"Shike nan SEEDRAH tun da bazakibi maganar mu ba abin da yafi tozarci da cin mutunci
Usman zaici gaba da zuwa yana mana tun da haka kika zab'a."
da sauri tashiga girgiza kai tana fad'in
"Zanyi zanyi aikin zanje gidansa nayi aiki a matsayin 'yar aiki dan na kare kima da mutuncin
mahaifi na, zanyi."
takuma fad'a tana sakin bedsheet d'in da take shinfid'awa ta fita da sauri zuwa d'akin su.
Wardrobe ta bud'e gefen da kayanta yake ciki ta janyo wani akwati wanda shima nata ne
tashiga ciro kaya tana karawa cikin na akwatin cikin sauri, yayin da takejin zuciyar ta ya bushe
tangaras ta sawa ranta zataje tayi aiki tukuru dan ta tseratar da mahaifinta daga tozarcin S.MAN
bama shi ba har wanin sa. Suhailat dake zaune tana kallon yadda take tura kaya cikin akwatin, ta yamusa fuska tare da
fad'in
"Tun da ke bakya bukatar zuwa basai abar masu bukata suje ba kamar S.MAN zai bukaci aje
masa aiki wai kiki zuwa, nifa ko gidan nasa yace nakoma gaba d'aya narika bautatawa gidan ko
bazai biyani ba wlh da gudu zanje ganin sa ma kad'ai yabiya kud'in aikin da zan masa."
bata kula ta ba sai aikin tura kayan ta take cikin akwati tana gamawa tarufe ta d'au mayafin ta
taja akwatin tayi waje.
A tsakar gida taga su Baba da Mama Umma duk a tsastsaye,
ta dubi Baba ta ce
"Baba na shirya ka kaini."
Baba ya dubi agogon wayarsa ya ce
"Goma da rabi ina ga kamar dare ya yi mubari sai gobe da safe."
kai kawai ta gyad'a taja akwatin zuwa d'akin Mama ranar a d'akin ta kwana.
washegari da sassafe Baba ya d'auketa a mota da kayanta suka d'au hanyar gidan S.Man.
suna isa ya yi hon maigadi ya wangale masa get yashiga ya faka a gefe, SEEDRAH ta fito Baba
ya fito tare da ciro mata akwatin ta.
bin gidan tayi da ido wan da tsaruwan sa yakai tsaruwa,
"Ga gida har gida amma babu mutum."
tayi maganar a kasan ranta tare da yamusa fuska a fili tana kuma murgud'a baki, kamar S.Man
d'in ne a gaban ta.
Maigadi yakaraso inda suke da sauri suka gaisa da Baba kana ita ma ta gaida shi.
maigadi ya ce
"Oga bai tashiba tukun amma yasanar min da zuwan ku dan haka zaku iya shiga daga ciki, ke
ce 'yar aikin ko?."
ya nuna SEEDRAH
Baba ya ce "Eh.eh.. itace eh itace."
kai SEEDRAH tajinjina wato ma tun kan tazo yagama yad'ata wai itace yau ake cewa 'yar aiki.
Baba ya ce
"A'a ita ce zata shiga ni zan koma daga nan tun da yana bacci, maza shiga ciki SEEDRAH, ni
zan wuce kasuwa."
kai ta gyad'a maigadi yad'au akwatinta yana gaba tana biye da shi, Baba kuma yaja motar sa ya
yi gaba.
Tsintar kanta tayi cikin wani dankararren parlour mai kyau da tsaruwa,
maigadi ya aje mata akwatin ta cikin parlour'n ya na fad'in
"Ki zauna ki jira fitowar Oga."
kai ta gyad'a tana zama kan d'aya daga cikin dankararrun kujerun parlour'n kana maigadi yayi
waje yana jawo kofar parlour'n.
a hankali tashiga bin cikin parlour'n da ido sosai parlour'n yatafi da ita matuka ta shagalta da
kallonsa.
tana nan zaune tana zuba idon ganin fitowar sa amma shiru, tashafi tsawon awanni biyu zaune
amma babu alamarsa.
tsaki takuma ja akaro na sau ba adadi a fili ta furta
"D'an rainin hankali sai kace wani mai sarauta da sai an wani zaman jiran fitowarsa."
kwafa tayi tare da kad'a harshe yabada sauti.
zuwa yanzu ta gaji da zama sai ta gyara kan doguwar kujerar da ta ke kai tad'an kishingid'a.
tana nan zaune harta fara jin kiraye-kirayen sallar azahar, ta mike tare da sakin doguwar
hamma had'e da mika tare da yin salati, gajiya junwa duk suke tare da ita.
waige-waige tashiga yi tana niman ta in da bayin parlour'n yake taje tayi al'wala.
can idanunta ya sauka kan wata kofa dake gefe shi kad'ai, ta nufi kofar dan shi take tunanin zai
iya kasancewa toilet.
a hankali ta murd'a handle ta tura kuwa taga toilet d'in ne, tsaf-tsaf yake babu datti sai kamshin
turaren toilet mai dad'i yake, tashiga tayi al'wala tafito.
akwatin ta tabud'e zaciro hijabi kana ta rufe, ta zare d'ankwalin kanta ta shinfid'a ta gabatar da
sallar a kai.
ko da ta idar jingina tayi dajikin kujera tana tasbihi a hankali da 'yan yatsun ta.
idanunta ne yasauka kan kwalin sigari dake kan kujerar da take jingine da shi,
cikin jin kyamar abin ta mike tana yamusa fuska ta d'aga waya da gyalenta dake kusa da shi ta
ajesu can gefe.
tad'au rimut d'in t.v da tagani a gun tashiga ture kwalin tabar cikin jin kyama ga yan da take ture
abin zaka san bam bata kaunar hannunta ya tab'a shi,
ko da ya fad'o kasa kusa da kafarta tayi d'an tsalle ta masa gefe.
kana ta mika hannunta dake rike da rimut d'in ta tura shi kasan kujera.
aje rimut d'in tayi tare da rike kugu ta sauke numfashi kamar wacce tayi wani babban aiki.
"Mttsss." taja dogon tsaki kana ta koma ta zauna.
zaman ta baifi da minti 5 ba tajiyo taku daga matattakalar bene
a sannu ta waigo da dubanta izuwa gurin.
yana sanye da jallabiya kalar ruwan madara yayi kyau sosai cikin rigar.
da d'an sauri yake saukowa yana kuma duba tsadadden agogon dake d'aure a hannunsa.
yanda yake sauka dasauri cikin zafin nama irin na zaratan maza, lallausar gashin kansa daya
sha gyara da wani d'an a don aski irin na 'yan kwallo iska ke kad'ashi yal-yal.
cikin hanzari yakarasa sauka daga step's d'in jin ana fad'in sahuu daga masallacin da ake jiyo
sautinsa rangad'au a cikin gidan.
yanufi kofa batare da ya kalli cikin parlour'n ba bare yama san da wata halitta agurin.
SEEDARAH ko baki bud'e tabi bayan sa da kallo cikin takaici tafurta
"Rainin hankali nashafe tsawon lokaci zaune a nan ina zaman jiransa sannan yafiyo ya yi tafiyar
sa,wato ma nacigaba da zaman jiran nasa kenan, ai wlh bai isa ba idan ban d'au jakata nayi
gaba abina ba."
d'an shiru tayi tana tuna tofa idan ta tafi tafiyar nata zai shafi Baba, da tunanin nan takuma
gyara zaman jiransa.
S.MAN bai shigo gidan ba sai wajen karfe 2 na rana, tana nan zaune cikin parlour'n ya turo kofa
ya shigo.
a sannu yatako izuwa cikin parlour'n
ya zauna kan kujerar dake fuskantar ta,
kafarsa d'aya ya d'aga ya d'aura kan d'aya.
yayin da ya maida bayan sa jikin kujerar yashiga kad'a kafar a hankali.
kana ya d'au rimut ya kunna t.v tare da mai da idanunsa kan t.v
SEEDRAH ta cika har wuya kiris ya rage ta fashe ganin rainin hankalin nasa nason yin yawa
yaganta sarai bawai bai gantaba amma yayi buris da ita kamar baisan da wata halitta agurin ba.
kwafa tayi a fili tad'an ja guntun tsaki kana ta ce
"Kafad'i abin da za'ayi maka idan kuma babu na tattara nayi gaba abina."
yatsa ya d'aura kan bakin sa ya ce
"Shiiiiit ni zan yi magana ba ke ba dan nan fadata ce........"!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSASHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciya salon labarin na daban ne. ku dai ku biyo ni cikin labarin nan kada ku mance
da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 12
Zaman sa ya gyara tare da kuma maida idanunsa kan t.v yana cigaba da karkad'a kafa.
SEEDRAH ko kallon shekeke tabisa da shi tare da yamutsa fuska.
sai da ya d'au tsawon mintuna 20 zaune batare da ya kuma cewa komai ba ya yin da idanunsa
kuma ke kan t.v har lokacin.
kamar an zamure sa ya sauko da kafarsa saman lallausar carpet d'in dake malale tsakiyar
parlour'n, yazamo bakin kujerar da yake kai yashiga nunata da yatsa sannan yasoma magana
cikin kakkausar murya
"Tun da nake babu wani wan da yatab'a tsayuwa a gabana yana fad'a min son ransa a kaina
sai ke da bakifi cikin kokali ba,
ko uban naki bai isa ya tsaya gabana ya yi gigin gayamin bakar magana ba,
shiyasa nasashi da kansa yakawo min ke domin nakoya miki tarbiyya dan naga karancin sa
atare da ke,
me ma kika ce?, d'an shaye-shaye ko!."
yafad'a cikin tsawa da har sai da ta d'an zabura ta matsa baya.
hannu yacigaba da nunata da shi ya yin da yakad'a yatsun sa suka bada sauti
"Zan nuna miki halin d'an shaye-shaye sai na kunttatawa rayuwar ki sai kinyi danasanin
kasantuwar ki a yanzu,
sannan ki sawa ranki bakima sanni ba babu wata alaka sakani na da ke, ke kawai 'yar aiki ce a
gidan nan."
Tarazana da jin kalaman sa sai dai sam bata bari ya fahimci hakan ba, tayi kokarin kawar da
tsoronta ta hanyar tattaro jarumtarta had'e da tsiwar ta ta shimfid'a su kan fuskarta.
Kafad'a ta d'aga alamun ko oho
kana ta wasa masa wani kallo sannan ta ce
"Kada kayi gigin aibanta mahaifina a gabana dan ko wuka aka kawo sa kan wuyata bazai bani
tsoro na lamunce cinmutunci wa mahaifina ba,
tarbiyya kuwa nasame sa dai-dai gwargwado sai dai godiyar Allah shiyasa ma nake tafe da
albarka ta,
yaushe tarbiyyar ta ishe ka da zaka bani,
kaima bawata tarbiyyar bace gare ka,
da kana da ita da bazaka rika aikata irin abubuwan da kake aikatawa ba,
sannan kuma ni dama ban sankaba idan dama dawata alaka na dangantaka sakanin mu kajima
da warwareta tun ranar da na fahimci rashin darajawarka ga mahaifina, babu wata alaka
sakanin mu kai da ni da duk wad'an da mukafito uba d'aya kamar bare ne wad'an da ke tafe a
kan titi, kaga babu wata alaka sakanin su, gidan nan kuwa nazo ne amtsayin 'yar aiki zanyi aiki tukuru domin dawo da kimar mahaifina,
zan yi aiki a karkashin ka ta hanyar biyana albashi karike kud'in da kake bin Baba."
Wani irin murmushin takaici ya sake a zafafe ya mike tsaye ya d'aga kafa zaiyi ball da ita, sai
kuma ya fasa, ya tsunkuyo tare da shako wuyarta da karfi, har sai da idanunta suka
firfito,sannan yasoma magana cikin huci
"Zan azabtar da ke ta yadda idan nayi magana baki isa ki amsa min ba!,
a karamin tunanin ki