Showing 54001 words to 57000 words out of 78655 words
Chapter 19 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
d'an nonuwan sa tana kuma manna masa kiss a gefen wuya had'e da shinshinar gefen wuyan
nasa.
sai mammanna ababen kirjin ta take a bayansa duk da suna cikin riga.
shiko gaba d'aya ya mai da hankalinsa kan gyaran gashin sa da yake.
daga cikin mirro SEEDRAH suka had'a ido da shi.
da sauri tayi baya tare da janyo musu kofar tasauka kasa gaba d'aya tana Allah wadai da hali
irin nasa..
ta koma d'aki tayi kwanciyar ta har bacci yafara d'aukar ta tajiyo magana a kanta,
ta bud'e idanunta a kansa ya ce
ta tashi taje ta gyara masa d'aki yana fita itama ta fito, can ta hangosu suna fita shi da
Teema.........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08088110090 ko
08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 17
Yau SEEDRAH ta tashi bata jin dad'in jikinta tanajin zazzab'i a daddafe tagama aiyukan safe.
kwance take rab'uke a jikin pillow idanunta a lumshe.
kiran Kamal ne yashigo wayarta ta janyo wayar batare da ta bud'e idanunta ba ta d'aga kiran
tare da kai wayar kunnen ta.
jin muryar ta hankali tashe yake fad'in
"Me ya faru me ya same ki me ke damin ki?."
ya jera mata tabayoyin cike da kulawa hankali tashe.
idanunta takuma lumshewa tana dad'a manna wayar a kunnenta ta ce
"Zazzab'i zazzab'i nake ji."
da sauri ya ce "Subhanallah bari nasa Mukhtar yazo ya kaiki asibiti sannu kinji yanzunnan
zaizo."
kai ta girgiza tare da fad'in
"A'a nasha magani zai sake ni."
"Anya kuwa kin tabbata kawai yazo ya kaiki."
"Na tabbata zai sake ni, yaushe zaka dawo?."
numfashi ya sauke ya ce "Gaskiya ni hankalina bai kwanta ba ko dun ciwon nan naki ma zan
dawo."
murmushi tayi ta ce
"A'a ka tabbatar da ka gama taya Alhajin Mu aikin daya kai ku tukun."
"Amma dai ki kulamin da kanki sosai dan wlh sai na iya guduwa na dawo, dan ma
Alhajin mu ya fahimci halin da nake ciki ya ce muna dawowa zai zo asa mana rana, bana so a
sa yakai ko wata ne so shine samu sati biyu zuwa uku."
ta ce "Allah ya kaimu yadawo min da kai lafiya da Alhajin mu."
ya amsa da amin amin.
nan suka d'an tab'a hira irin na masoya kad'an ya ce tayi bacci anjima zai kira yaji jikin nata.
tana kashe wayar kiran Mama na shigowa.
da sauri ta d'aga dan tun shekaran jiya rabon da suyi waya da Mama.
ta kai wayar kunnenta da sallama daga cikin wayar tajiyo yan da Mama take amsa sallamar
tana jan numfashi da kyar.
ido ta waro tare da mikewa zaune cikin rawar murya ta ce
"Mama lafiya me ke da mun ki ciwon ki ne ko!?."
tayi maganar hankali a mugun tashe.
dakyar Mama ta iya furta
"SEEDRAH magani na ya kare babu kud'in siya kizo ki d'au wani abina ki siyar ki siyo min
magani."
wani irin dirowa tayi a kan gado cak ta nimi zazzab'in da take jin tarasa, da sauri ta d'au hijabi
had'e da wayarta tanufi kofa da sauri har tana had'awa da sassarfa.
gabaki d'aya kwakwalwarta ya tsaya cak burin ta kawai ta ganta cikin d'akin Mamarta, idan
kafin taje ta siyar da wani abunsu a sami kud'in siyan magani ai ciwo yagama galabaitar da
Mama, mafita kawai zata nima ta in da zata samo kud'i kafin siyar da wani abun nasu,
da wannan tunanin tafice cikin d'akin.
can ta hango S.MAN zaune cikin parlour yana daddanna seystem nashi da sauri ta isa in da
yake ta zube a gabansa tayi zaman dirshem a kasan carpet.
cikin matukar tashin hankali ta ce
"Dan Allah dan annabi kabani wani abu daga cikin kud'in albashina nawannan watan, Mama ta
ce batada lafiya zan siya mata maganin ta, idan wani watan yayi sai a soma lissafi kan kud'in da
kake bin Baba,
dan Allah ka taimaka ciwon Mamata ya tashi."
ido yad'an zuba mata ganin yanda gaba d'aya ta firgice tsananin damuwa da tashin hankali ya
bayyana a gare ta,
nan da nan kuma hawaye yashiga zuba a idanunta.
sai kuma ya tab'e baki yad'an ture seystem d'in gaban sa gefe kana ya ce
"Kin san nawane albashin naki da kike cewa wani watan acire cikin kud'in da ake bin Baban
ki?."
kai ta girgiza da sauri ta ce
"Ko ma nawa ne ni dai dan girman Allah kabani mahaifiyata tana bukatar taimako na dan
Allah."
tayi maganar tamkar zata zubda kwalla.
kai ya jinjina ya ce
"Dube ta kamar mutumiyar kwarai to yau ina shegen bakin rashin kunyar nan take,
kinci albarkacin abu biyu girman Allah da manzonsa da kika had'a ni da su,
sai kuma darajar ciwo badun su ba babu abun da zaisa na bada."
sunkuyar da kanta kasa tayi batare da ta ce komai ba, dan bazata iya cewan bama a yan da
take jin kanta ciki, tasan kalar ciwon Mamarta idan ya tashi tamkar zai tafi da ranta haka yake
mata, to har yaushe zata zauna zaman yin fad'a da wani, bataje ta kai mata agaji ba.
Mikewa yayi ya haura sama jim kad'an yadawo ya zauna kan kujerar daya tashi, in da ya barta
nan ya dawo ya taddata.
d'aurin kud'in dake rike a hannunsa ya nuna mata kana ya ce
"Nan 50k ne shine albashin ki."
sai ya kirga dubu goma a cikin kud'in ya zare su ya aje gefe sannan ya ce
"Wannan shine kud'in abincin ki nakwana goma, kin ga idan akayi lissafi kowani kwana d'aya
kinacin abincin 1k kenan a ihisanin da zan miki."
yakuma kirga wasu dubu ashirin yakuma had'asu da wannan dubu goman sannan ya ce
"Haka ya kama kud'in abincin da kika ci na wata guda kenan kinga albashin ki yarage saura 20k
kenan dan haka wannan shine kud'in aikinki."
ya nuna mata naira dubu ashirin d'in dake hannunsa sannan yazare dubu goma daga ciki ya
mika mata yana fad'in
"Ga wannan kije ki siya mata maganin wannan kuma zan ajiye idan kikayi aikin wani watan sai
na d'aura a kansa,
sai kiyi lissafi shekaru nawa zakiyi kina aiki kafin ki gama biyan bashin da Baban ki yaci."
tsananin mamaki ne ya kamata sai dai a yanzu bata da lokacin tsayuwa biye masa, ta karb'i
dubu goman da sauri har hanunta na b'ari ta mike da sauri ta nufi kofa.
muryarsa tajiyo yana fad'in
"Kitafi da shirin dawowa yin abincin rana."
bata iya cewa komai ba tayi waje, can ta hango maigadi na gyangyad'i bakin get batabi ta kansa
ba ta bud'e kofa tafita.
tana jiyo muryar sa yana fad'in
"Oga ne ya ce ki fita?."
bata saurare sa ba tayi gaba abin ta.
tana tafe kan abin hawa sai gani take kanar baya sauri, suna isa tunkan ya dai-dai ta parking ta
duro tayi gida da gudu dan tun shiganta napen tabiyasa kud'insa.
direct d'akin Mama ta shiga a guje tana kiran sunan ta.
a sakiyar parlour ta iske Mama kwance a kasa tana sauke numfashi da kyar,
a guje ta iso gunta tazube guiwowinta a kasa tana fad'in
"Innalillahi sannu Mama, ke d'aya ce ba kowa ne a gidan ina su Umman suke?."
tayi maganar arikice tana d'ago kanta ta d'aurashi kan cinyarta tana cigaba da yi mata sannu.
Mama ta ce
"Basu jima da barin nan ba suma sunyi bakin kokarin su."
kai kawai SEEDRAH ta girgiza kana ta ce
"Mama ta shi mutafi asibiti jikin nan naki magani kad'ai bazai wadatar ba."
Mama ta ce "Bani magani tukun nasha gashi can."
ta nuna mata wani laida dake gefe, da sauri ta mike tad'au laidar ta bud'e magungunar da
Mama take sha ne a ciki masu yawa,
da sauri taje ta d'ibo ruwa a kofi tana mamakin a ina aka samu kud'i aka siyi magunguna masu
yawa haka.
ta bud'e maganin ta ciro yanda take sha ta tallafo kanta tasaka mata maganin a baki had'e da
ruwa tasha.
kana ta gyara zamanta da kyau tayiwa Mama pillo da kafarta dan tasan yanzu bacci zai d'auke
ta, ai kuwa ba a d'au wani lokaci ba bacci yad'auke ta.
Shiru SEEDRAH tayi tana kallon fuskar Mama wani irin tausayin ta ne ke shigarta, ganin yanda
ta rame tayi duhu mai da kwallar daya ciko mata ido tayi tare da sauke numfashi.
a hankali tashiga kunce kitson dake kanta tana kitsa mata su da d'ai-d'ai harta gama.
SEEDRAH na zaune harsai da Mama ta farka da kanta, tana ganin ta bud'e ido tashiga jera
mata sannu ya take jin jikin nata.
Mama ta mike zaune ta dubi SEEDRAH tana fad'in
"Ke ai kafarki sai tayi tsami yabaki saka min pillow ba kawai."
ta ce "Mama bazaiyi tsami ba tashi muje asibiti kawai adubaki."
"Da wani kud'in SEEDRAH maganin dana sha ma ya wadatar."
ta ce "Ga wasu 'yan kud'i a hannuna S.MAN ne ya bani su cikin kud'in aikina muje asibiti kawai
Mama."
da kyar ta lallab'a Mama ta yarda suje asibiti dan cewa tayi ta barta kawai ita tasha magani ta
warke.
asibitin da dama can Mama ke zuwa suka tafi nan da nan kuwa suka sami ganin likita, bayan ya
duddubata ya ce zai sauya mata magani wan da in sha Allah sai tafi jin dad'in sa fiye da wanda
take sha.
bayan ya rubuta maganin SEEDRAH ta karb'i takardar suka fito sunayi wa likitan godiya.
gurin sai da magani dake cikin asibitin SEEDRAH ta nufa bayan ta ce wa Mama ta zauna kan
wani kujera ta jirata taje tabiya kud'in gwaje-gwajen da akayi mata takuma siyi maganin da likita
ya rubuta musu.
ko da ta mika takardan aka bata magungunar ta karb'a kana ta dubi matar dake bada maganin
tana fad'in
"Yauwa nawane duka kud'in mu ya kama?."
matar taduba takardan maganin kana ta dubi SEEDRAH ta ce "Am akwai wani maganin da aka
sako ta ciki wan da bamu da masaniya a kansa shi kud'in sa d'ari tara ne shike nan kud'in."
SEEDRAH ta ce
"To sauran fa da kud'in gwaje-gwajen duk bamu biya ba."
ta ce "Iya kud'in dai kenan."
da mamaki SEEDRAH ta ce
"Asibitin yadawo na gwamnati ne?."
murmushi matar tayi mata batare da ta ce mata komai ba.
ta juya tana mai mamakin yanda akayi asibitin ya koma haka dan dai ita a sanin ta ma,
kud'in data zo dashi sai dai suyi maneji bazai kai kud'in zuwa suga likita har ya siya musu
magani ba.
bare kuma wannan maganin da aka canza basai an fad'a ba kasan mai tsada ne.
tazo in da Mama take ta zauna gefen ta tana fad'in
"Mama yaushe asibitin nan ya koma na gwamnati kigafa iya d'ari tara suka karb'a,
naga ko asalin asibitocin gwamnatin ma sai ka siyi magani da kud'in ka."
Mama ta ce "Ikon Allah ko dai sun yi rafkanuwa ne."
"A'a wlh Mama haka ta ce min iya kud'in kenan."
Mama ta ce "Ikon Allah to Allah ubangiji yasaka musu da alkhairi."
ta amsa da amin kana suka mike suka fito daga cikin asibitin suna mai mamakin lamarin har
suka komo gida.
Ko da suka dawo gida bayan su Umma sun shigo sunyi wa Mama ya jiki sun fita, SEEDRAH
tabaiwa Mama maganin kamar yanda tagani a rubuce.
sannan ta shiga kichin ta girka mata abin da tasan zata d'anci da marmari cikin kayan abincin
da 'yan uwan ta suka turo mata.
SEEDRAH na zaune a gefen ta tana cin abincin suna d'an tab'a hira, Mama ta dube ta cikin kula
ta ce
"Ke ban ga kinci komai ba."
murmushi SEEDRAH tayi ta ce
"Zanci sai nayi sallah."
kai Mama tajinjina.
hannu SEEDRAH ta mika ta janyo laidar magani wan da d'azu zuwan ta tagani cikin d'akin ta
baiwa Maman ta sha tana fad'in
"Yanzu Mama ya za'ayi da wannan maganin tun da an canza miki wasu, gashi da yawa kuma
maganin,
Baba ne yasiyo ya mayar kawai yayi musu bayani subashi kud'in."
Mama ta ce
"Bana tunanin shi ya siyo dan tun da farar safiya ma ya fita,
d'azu ne ina kwance yaro ya yi sallama ya kawo ya ce kuma wai inji Falalu mai kyamis,
to ban sani ba ko Baban nakune yayi masa magana ya basa bashi ban dai sani ba kam
watakila shi d'in ne,
kokuma Halimatu dan naji kafin fitarsa yana ce mata tabashi bashin kud'i dan jiya saurayin ta
yazo ya mata kyauta."
kai SEEDRAH ta jinjina tare da fad'in
"Tun da Falalu ne bari na kai masa nasan zai bada kud'in idan an bashi, in kuma ba a basa ba
sai ya karb'i abin sa."
Mama ta ce to, ta d'au mayafin ta da laidar maganin tayi waje.
Ko da ta isa gurin Falalu bayan sun gaisa ya ce
"Kwana biyu ina kika shiga ne SEEDRAH ko kinyi tafiya ne?."
Eh kawai ta ce masa kana ta d'aura da fad'in
"Maganin da ka bayar a kaiwa Mamana ne nadawo maka da shi, munje asibiti d'azu ancanza
mata magani, shin Baba ya baka kud'in maganin ne?,
idan ya baka to dan Allah ka karb'i maganin ka bamu kud'in idan kuma bai baka ba to gashi ka
rike abinka."
ya ce "Eh anbani."
ya ciro kud'i ya kirgo ya mika mata. ta karb'a tare da yi masa godiya ta juyo gida ta baiwa Mama
kud'in ta ce ta ajiyewa Baba in agun Halimatin ya karb'a in ya dawo ya maida mata.
Har yamma lis SEEDRAH na gidansu cikin walwala tana kusa da Mamarta,
ganin bata da niyyar tafiya ne yasa Mama ce mata ta tashi ta koma gurin aikin ta dare nayi.
ta ce ita kwana zatayi bazata iya tafiya ta barta bata da lafiya ba.
Mama ta ce ita kam ta sami sauki ta tafi abinta, da fari tuburewa taso yi sai da Maman tayi da
gaske kafin tayarda zata tafi amma wai sai in Baba ya dawo sun gaisa tukun.
Mama ta ce tatafi abinta kawai sa gaisa a waya dan bayanzu zai dawo ba sai dare.
acikin kud'in da ta zo dashi kud'in abin hawan da zai komar da ita kawai ta cire ta bawa Mama
sauran ta ce ta ajiye tarika amfani da su.
tayiwa y'an gidan sallama ta tafi badun taso ba, Mama ta rakata da addu'a da sanya wa rayuwar
ta albarka.
Tana fita Suhailat ta biyo ta ta ce
"Yauwa SEEDRAH kina da lambar Ya S.MAN ki bani?."
kai ta girgiza cike da takaicin 'yar'uwar tata ta ce
"Ni kuma me zai had'ani da lambarsa aiki kawai nake masa ba a dana lambarsa ba."
tsaki Suhailat taja ta ce
"Jeki ba cewa nayi ki gaya min magana ba samo lambarsa ai bazai bani wuya ba."
"Da dai yafi kam ki samo da kanki ko ba komai kya kulla kawa da wulakanci."
cewar SEEDRAH tayi gaba abinta.
A b'angaren Maman ma ita ma kanta batason rabuwa da d'iyarta d'aya tilo duk da karancin
shekarun ta takan iya jajircewa wajen kula da lamuranta, sai dai babu yanda ta iya hakan ne
kad'ai zaisa su tsira da mutuncinsu.
SEEDRAH na fita ba da jimawa ba Baba ya dawo Mama tayi masa bayani kan kud'in maganin
da SEEDRAH ta karb'o,
ya ce baima karb'i kud'in Halimatu ba hasalima bai ma je shagon Falalu ba, yadai fita niman
kud'i ne yasamu yazo ya siya mata maganin sai yanzu ke nan dawowansa.
amma bari ya huta zaije gurin Falalun yaji ta in da kud'in yafito.
SEEDRAH nashiga gidan S.MAN ana kiran magriba, tana shiga parlour shikuma yana sauka
daga sama cikin shirin zuwa masallaci.
wani kallo ya watsa mata cikin gimse fuska ya ce
"Bari na dawo daga masallaci zaki fad'a min dalilin daya sa kika karya dokan dana sa miki."
bata kula shiba ta shige d'aki shiko yayi waje, tana shiga kuwa ta kulle kofar da key bata kuma
bud'e wa ba sai washegari..
SEEDRAH ce tsaye jikin mirro d'aure da towel a kirjinta fitowar ta daga wanka kenan.
bra da pant ne rike a hannunta ta saka pant d'in da sauri-sauri dan batayi sallar magriba ba ga
shi kuma har an fito daga sallar isha.
kana
ta zame towel d'in a kirjinta tana kokarin saka bra aka turo kofa.
da sauri tayi wurgi da bra'n tayi hanzarin jan towel d'in kirjinta dai-dai lokacin daya sako kansa
ciki batakai ga karasa d'aura towel d'in ba.
baki ta turo gaba tana wurga masa harara cikin jin haushin yanda ya fad'o d'akin kai tsaye babu
sallama ta ce
"A gaskiya bai kamata karika fad'o min cikin d'aki haka batare da sallama ko niman izinin
shigowa ba, ko ma mene ne karika fad'a min daga wajen bakin kofa ai dai zanji."
"Ni da gida na har sai na nimi izinan shiga wani guri a cikin sa,
duk in da nake son shiga zan shiga batare da niman izini ba, ke baki isa ki kafamin doka a gida
na ba."
baki ta murgud'a cike da tsiwa tana fad'in
"Gidan ka ne d'akin nan kuma gurin zamana ne' kamata yayi idan zaka shigo karika yimin
sallama, ba karika fad'omin cikin d'aki kai tsaye ba."
a hatsale yasoma takowa cikin d'akin yana fad'in
"Doka zaki gindaya min cikin gida na ke zaki fad'a min abin da zan yi a cikin gida