Showing 12001 words to 15000 words out of 78655 words
Chapter 5 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
d'akin Mama ta dawo ta kwanta
sabo da damin ta da Suhailat take da waya, duk da nauyin bacci irin nata har idan ana surutu a
guri sai tayi da gaske kafin baccin ya d'auke ta.
cikin jin dad'in baccin da take taji ana bubbuga ta da karfi, mika tayi cikin magagin bacci takuma
juye tagyara kwanciyar ta.
da karfi Halimatu ta d'aka mata duka a cinyar ta da zanin ta ya yaye tagefen santalelen cinyar ta
d'aya, ta na fad'in
"Banza mai shegen d'an banzan nauyin bacci har wani abun guduwa ya faru a gudu a barki kina
wannan shegiyar baccin naki."
a d'an razane ta mike tana susa gurin da Halimatu ta zuba mata duka tana fad'in
"Wayyo ni me nayi miki?."
Halimatu ta ce "Banza tashi dalla kowa ya fito ke kina d'aki kina baccin asara, gawasu can sun
kuma janyewa Baba kud'i a account d'in shi."
da sauri ta duro a gadon tana fad'in
"Yau ma kuma?." waje tayi da sauri Halimatu tabi bayan ta.
a can parlour'n Baba ta tadda duk y'an gidan tsaye curko-curko Baba ya na zaune yadafe kansa
da duk hannayen sa biyu.
hankali tashe tazube gaban sa tana fad'in
"Baba wai sun kuma kwashe maka kud'i!?."
hannunsa ya janye a kansa yad'an zuba mata ido kana ya gyad'a mata kai ya ce
"Wannan karon ko sisi basu barmin ba duka suka kwashe."
hawaye ne ya ciko idon ta kan kace me sun fara tsiyaya ta ce
"Baba katashi kaje banki mana su binciko maka masu ai kata maka haka ai dai dole zasu san
ko su waye ne."
kai ya girgiza ya ce "Ba na tunanin zasu yimin komai a kai dan wancan karon ma dasuka ce
zasu bincika har yau babu wata kwakkwaran amsa, nayi sintirin banki harna gaji, amma dai
zanje dan yau kam gaba d'aya suka kwashe ni, dan jiya da daddare aka turo min da kud'in dana
siyar da filaye da sauran kaddarorina kan zan gina wani masana'an ta, yau da safen nan kuma
suka kwashe duka da ragowar kud'in da ke cikin accaunt d'in."
ya mike ya na fad'in "Bari dai naje ko bankin basu fito ba zan jirasu har su fito."
yazari makullin motar sa ya yi waje..
Gaba d'aya y'an gidan yau basu da walwala duk wan da ka gansa kasan yana cikin damuwa,
gashi suna ta kiran Baba baya d'agawa.
tun safe sai wajen k'arfi uku kafin yadawo, gaba d'aya suka hallara a parlour'n sa, nan yake
sanar musu banki sunyi iya binciken su sunce basu gano wad'an da suka aikata masa hakan
ba, amma yaje wani sati yadawo kafin sun dad'a fad'ad'a bincike.
basuji dad'in jin hakan ba sai dai basu da yadda zasuyi..
Kamar yanda Kamal ya ce wa SEEDRAH zasu dawo da Mukhtar bayan kwana uku, hakan
kuwa akayi da yamma suka zo kofar gidan su SEEDRAH ya ai ka aka kirata, tana ganin sune ta
b'ata fuska a jikin get ta tsaya ta hard'e hannayen ta akirji.
murmushi Kamal ya yi suka karaso in da take.
Kamal ya dube ta da murmushi d'auke a kan fuskarsa ganin yanda tawani sha kunu, shi harga
Allah yarinyar dariya take bashi idan yaga tana wani b'ata rai ga iya zare zance kamar wata
babba, a kallon da yake mata shekarun ta bazasu wuce 17 zuwa 18 ba.
ya ce "Ranki shidad'e barka dawarhaka da fatan kina lafiya?.
kad'a kwayar idanunta tayi ta ce " Gashi dai kana gani."
kai ya girgiza Mukhtar daya d'an sunkuyar da kansa ya d'ago "Barka da yamma ya gida?."
batare da ta amsa masa ba ta ce "Kufad'i a bin da ya kawo ku nagode da gaisuwa."
Kamal yad'an gyara tsayuwar sa ya ce
"Ina fata zuciyarki tad'an sanyaya cikin kwanaki ukun nan, kamar yadda na fad'a miki zamu
dawo bayan kwana uku gani ga Mukhtar dan Allah ki kirawo mana kawarki munimi gafarar ta."
"Bama bukata kuje abun ku kudai cigaba da zaman jiran kira daga kotu."
da sauri Mukhtar ya ce "Please dan Allah kiyi hakuri ki kirawo mana ita dan Allah! badun niba,
a shirye nake da karb'ar duk wani hukuncin daya sauka a kaina amma kafin nan ina so na had'u
da ita nanemi yafiyarta dan Allah!."
baki ta tab'e kamar zatayi magana sai kuma ta juya ta nufi gidan su Nasiba.
a gurin wanke-wanke ta isketa tana wanke-wanke,ta sunkuyo kanta a hankali ta ce
"Mutanen nan ne suka zo wad'an da suka bimu a unguwar su Nabila, ranar d'ayan ne yazo wan
da yad'auke ki a mashin d'in sa ya kaiki gidan goggo wai shi Kamal yaso nakiraki naki, shine ya
ce zasu dawo bayan kwana uku ban fad'a miki bane,suna ta magiya wai dan Allah kifito hakuri
sukazo baki da niman yafiyar ki."
rau-rau Nasiba tayi da ido ta ce "Ki ce wan da ya yi min fyad'e ni babu in da zan je yatafi bana
ma son ganin fuskarsa."
SEEDRAH takuma rage murya ta ce
"Ki yi hakuri kizo wlh nayi ta musu kora da hali har nafito na ce musu bazan kirawo ki ba bakiga
yan da suke ta rokona ba, shi kamma Mukhtar d'in bakiga yadda yake yi ba kamar zai zubda
min kwalla."
kai Nasiba ta sunkuyar cike da d'acin rasa budurcin ta bata kuma yin magana ba.
SEEDRAH ta sunkuya ta shiga taya ta wanke-wanke dama saura kad'an ne ta gama, suna
kammalawa Nasiba ta mike taje ta d'auko hijabinta taleka d'akin Mama Kubura ta ce da ita zata
shiga gidan su SEEDRAH.
daga nan suka fito SEEDRAH na gaba Nasiba na biye da ita.
in da ta barsu nan suka iske su, tun kan su karaso gurin Mukhtar ya kafe Nasiba da ido yanajin
zuciyarsa babu dad'i.
nan take yaji kunnuwansa sun amsa da ihu da magiyar da take masa lokacin da yake kokarin
yimata fyad'e da kuma karanta mai tsananin karfi a lokacin da yashige ta yafasa budurcin ta.
rumtse idanunsa ya yi da karfi tare da kai hannunsa ya toshe kunnuwansa da karfi yana girgiza
kansa tare da taune lab'b'ansa.
jiki a sanyaye Nasiba ta tsaya d'an gefe da SEEDRAH, Kamal ya kai hannu yana d'an bubbuga
kafad'ar Mukhtar daya lura da halin da ya shiga ganin Nasiba, sai a lokacin ya bud'e idanunsa
da suka kad'a sukayi jajir.
da sauri Nasiba ta juya zata bar gurin ganin fuskar mutumin daya keta mutuncinta.
da sauri Kamal ya ce
"Dan Allah kada ki tafi ki saurare mu ko da na mintuna biyu ne,
ki sani akwai masu yiwa y'ammata fyd'e su gudu ko da kuwa an neme su baza a same su ba,
amma shi da kansa yakawo kansa domin ya nemi yafiyar ki kafin hukuncin da zai zartu a kansa,
ki sani Allah yana son me yafiya idan kayafewa d'an uwan ka sai shima yagafarta maka."
cak ta tsaya yayin da hawaye ke zuba a idon ta,
Mukhtar da gaba d'aya jikin sa yagama yin sanyi ya jawo kafafun sa da kyar zuwa gaban ta ya
zube guiwowinsa a kasa, tare da had'e hannayen sa biyu, murya a matukar raunace ya ce
"Dan Allah dan Annabin sa mai dubun daraja! ina mai rokon ki daki yafe min, ina mai nadama
da da nasanin aikata miki haka, hakan ba halina bane dan ban tab'a ai katawa ba sharrin
shaid'an ne, na roke ki kiyafe min daga nan kuma ki kaini in da zaki kaini aje a yanke min duk
kan hukuncin daya da ce da ni, amma kafin nan ina mai rokon yafiyar ki."
Yadda yake maganar cikin rauni sosai ga hawaye nabin gefen fuskarsa namiji kamar shi da
zuba goiwowinsa a kasa da kuka da magiya da roko.
yasa SEEDRAH jin jikinta ya yi sanyi, ta dafa kafad'ar Nasiba da ke hawaye ta dubi Mukhtar ta
ce
"Ka tashi zata yafe maka in sha Allah amma dai ka cutar da rayuwarta kam."
kai ya jinjina ya ce "Na sani shi yasa nake son gyara kuskure na, idan ta amince zata aure ni
nikuma a shirye nake nashare mata bakin cikin dana jefa rayuwar ta ciki."
wani irin d'agowa Nasiba tayi ta dube shi sai kuma ta juya da sauri had'e da sassarfa tanufi cikin
gida, tana mai zubda hawaye masu zafi.........!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
( _Bismillahirrahmanurrahim_)
_Alhamdulillah Ina yiwa Ubangijin buwaye gagara misali godiya daya kuma a ramin lokaci na
kuma dado wa a wannan karon a cikin littafi na mai suna ƘARSASHI kada ku manta kafin
zuwan ƘARSASHI HAMDAH ya zo muku masoya ku baza kunnuwan ku ku kuma biyo ni cikin
labarin nan mai suna ƘARSASHI ina mai yi muku albishir da faranta wa kamar yadda HAMDAH
da sauran littatafai na suka saba zuwar mukuí ¾í´— ƘARSADHI salon sa da banne labari ne mai
ƙwanƙwasa zuciyar masoya salon labarin na daban ne. ko dai ku biyo ni cikin labarin nan kada
ku mance da sunan sa ƘARSASHI! ƘARSASHI!! ƘARSASHI!!!_
_Littafin na kud'i ne 400 Account no 3170524141 Rashida Salihu first bank kokuma katin Mtn ta
wannan number 08034690723 a tura shaidar biya ta WhatsApp number ta 08034690723_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
í ¼íµ¿ï¸5
Da mamaki SEEDRAH ta ke kallon sa sannan ta ce
"Aure kuma?." kai ya gyad'a cike da tabbatar da gaskiyar sa.
Kamal ne ya dube ta ya ce "Ko bakya goyon bayan hakan ne?, Har idan ta amin ce shine hanya
mafi sauki da zai bi ya rarrashi zuciyar ta."
baki ta tab'e a kasan ranta ta ce "D'an shishshigi watakila ma kai ka tsara hakan ma." a fili
kuwa ce wa tayi
"An tab'a auren da babu so bare kauna? bugu da kari kuma yanzu a kullace take da shi a
zuciyarta ta ya ma hakan zai faru bayan shima ba son ta yake ba, kawai kuje ba lallai bane
hakan ta yuwu."
da sauri Mukhtar ya ce "Ina son ta da gaske tun ranar dana yi mata fyad'e zuciyata takamu da
son ta, son ta da damuwar abunda nayi mata sune suka had'u suke damuna, dan Allah ki
tabbatar mata da ce wa zuciyata tana tare da ita."
Kamal ya ce
"Kwarai kuwa dan aboki na baya karya dan Allah ki shawo mana kanta."
hararar sa tayi kana ta juya ta soma tafiya ta na fad'in
"Amma ya iya mugunta ai."
wani sassanyan murmushi Kamal ya bita da shi yana shafa gefen fuskarsa ya yin da idanunsa
ke kanta har ta shige gidan su Nasiba, sai sannan sukuma suka tafi.
A d'aki SEEDRAH ta iske Nasiba kwance a kan katifa tana kuka, ta zauna a gefen ta tare da
dafa kafad'arta kana tayi saurin mai da hawayen da taji sun ciko mata ido tayi kokarin rarrashin
kawar tata gudun kada ta kuma karyar mata da zuciya.
SEEDRAH ta ce "Naseeba kiyi hakuri nasan d'aci da kunar da kike ji a zuciyar ki amma ki sani
auren Mukhtar shine kad'ai rufin asirin mu, tabbas naga son ki cikin idanun Mukhtar kibashi
dama kawai."
mikewa Naseeba tayi zaune tare da share zafafan hawayen da suke zubo mata tarike hannun
SEEDRAH cikin zubda kwalla ta ce
"Ni ma hukuncin dana yankewa kaina kenan a yanzu haka na aminta da auren nasa,
dan nasan hakan ne kad'ai rufin asirina, dan babu wan da za'a kwashe masa ni a kaini gidansa
ya iskeni sauran wani yazauna dani cikin aminci, shi d'in daya rusa katangar budurcina da shi
zan rayu a haka ko da bana son sa."
kuka ne ya kwace mata takifa kanta a cinyar SEEDRAH tashiga rera sabon kuka.
duk dauriyar da SEEDRAH takeyi kan kada tayi kuka tacigaba da karfafa mata guiwa sai da ta
fashe ita ma da kukan suka cigaba da rera kukan tare.
jin motsin Mama Kubura a tsakar gida yasa su sassauta kukan nasu, SEEDRAH bata bar gidan
ba har sai da taga zuciyar kawar tata yad'an sanyaya...
A b'angaren su Mukhtar kuwa kullum sai sun zo unguwar su SEEDRAH watarana ta fito
watarana taki fito wa,idan har kuma ta fito taje kira musu Naseeba bata yadda tafito haga zasu
karaci tsayuwar su sutafi..
bayan sati biyu Mukhtar ne yakai kansa da kansa kotun musulunci dake nan cikin garin Kaduna,
yakuma fad'i laifin daya aikata harya kai ga zuwa da kansa kotu dan a yanke masa hukuncin
daya dace da shi a musulunce.
da fari alkalin yabukaci da azo da wacce yayi mata fyad'en Mukhtar d'in ya hana faruwan haka
ta hanyar fad'in, shi bai ma san ta ba.
yayi hakan ne kuma badun komai ba sai dun kare martabar ta a idon duniya.
a take a gurin a ka yanke masa hukuncin bulalu kamar yadda addinin mu ya shar'anta, bakuma
tare da tozarci ba, duba da irin namijin kokarin da yayi nakawo kansa da kansa domin a yanke
masa hukunci, wanda a zamanin mu na yanzu ba kasafai ake samun masu tsoron Allah irin
haka ba, su aikata laifi susan basuyi dai-dai ba har sukawo kansu gaban shari'a dan a yanke
musu hukunci ba.
sab'anin da yanzu ma mutum zai aikata laifin gashi a bayyane a na gani kiri-kiri ya aikata ya
kuma yi musu haka za'ayi ta tuka shari'a da shi karshe ma shari'ar tabi iska...
Bayan an gama yanke masa hukuncin yana kwance a kasa shame-shame yana sauke
numfashi a jikkace. da kyar ya iya d'aga wayansa da tun zuwan sa kotun ya kashe, ya kunnata
kana yakira Kamal da tun d'azu yake ta zaryar niman sa baigansa ba yakira wayansa kuma
baya shiga. Kamal na d'agawa ya ce "Mukhtar ina ka shiga ne tun d'azu nake ta kiran wayar ka baya
shiga?."
ido Mukhtar ya rumtse jin yadda jikin sa ke masa rad'ad'i da mugun tsami ya ce
"Kazo ka taimaka min muje gida."
jin muryar sa hankali tashe Kamal ke tambayansa meke faruwa yana kuma ina?.
ya shaida masa inda yake, hankali a mugun tashe Kamal yanufo koton cike da tunanin abun da
yakai Mukhtar d'in koto, dan Mukhtar bai fad'a masa zaizo kotu ba.
da tunanin ko iyayen Naseeba ne suka kaishi koton Kamal ya iso kotun.
ganin halin da abokin nasa yake ciki hankalin sa yakuma mummunar tashi.
da taimakon mahukuntan kotun Kamal ya iya d'aga Mukhtar da baya iya motsa ko da d'an
yatsansa, suka d'aurashi a mashin.
direct asibiti yanufa da shi,
da fari a kaki karb'an shi a kace sai yazo da hukuma, sai da Kamal ya yi ta had'asu da Allah
kafin suka karb'e shi suka shiga bashi taimakon gaggawa.
har yamma suna asibitin sai sanan Mukhtar ya farka daga baccin da ya ke, sakamakon alluran
baccin da a ka masa.
Kamal ya matso bakin gadon da yake kwance cike da tausayi yana yi masa sannu, kana ya
juya da sauri yana fad'in
"Bari naje na samo maka abun da zaka ci."
Mukhtar ya ce "A'a bana jin yunwa Maman Zeey fa tasan ina asibiti kuwa?."
shiru Kamal yad'anyi kana ya ce "Ni ma tunanin da nake tayi ke nan tun d'azu idan har ta ganka
cikin wannan halin me za'a cemata."
ido yad'an rumtse tare da bud'e wa ya ce
"Ka fad'a mata ina asibiti itama tazo ta yanke min hukuncin daya dace da ni."
ya yi maganar yana mai taune lab'b'ansa cike da kunar zuciya.
Kamal ya girgiza kai tare da zaro wayarsa ya lalub'u lambar Maman Zeey.
bugu d'aya a na biyu ta d'a, bayan sun gaisa ya ce da ita suna asibiti da Mukhtar.
cikin matukar tashin hankali take tambayar sa abun da ya sami Mukhtar d'in, bata iya nutsar da
zuciyarta bama taji amsar da zaibata ta ce masa wani asibitin?.
yafad'a mata sunan sa ta kashe wayar tare da d'aukar mayafinta da kud'i tayi waje.
Zeey tabi bayan ta da sauri tana tambayarta meke faruwa ta ce mata Mukhtar ne yake asibiti.
itama hankali tashe ta d'au mayafin ta tabi bayan mahaifiyar tasu, suka tsari napep suka nufi
asibitin.
Ko da suka iso ganin halin da d'an nata yake ciki yasa Maman Zeey nufar gadon da yake
kwance tana fad'in
"Me ya same ka haka Mukhtar b'arayi ne sukayi maka haka kokuma hatsari kayi?."
rumtse idanunsa ya yi da karfi yana mai cike da dana sani. tabbas baka da makiyi irin shaid'an
idan kuma kabiyewa zuciya da shaid'an ke tunzura shi izuwa aikata sab'on Allah hakika kana
cikin asara da tab'e wa had'e dajin kunyar duniya, idan baka hankalta ba kuwa har da ma
kunyar lahira data fi ta duniya. Maman Zeey ta ruko hannunsa tana cigaba da fad'in
"Mukhtar meya sameka haka!?."
tayi maganar hankali a matukar tashe kana ta juya ta dubi Kamal ta ce
"Kuyi min magana mana me ya same shi haka!?."
Zeey da itama hankalin ta ya mugun tashi ta ce
"Ya Mukhtar meya same ka haka?."
tayi magana hawaye na ciko mata ido.
sai sannan Mukhtar ya bud'e rinannun idanunsa ya zubawa mahaifiyar tasa kana yakankame
hannun ta dake rike da nashi sannan ya ce
"Maman Zeey kiyafe min kiyafe min dan Allah."
wasu zafafan k'walla ne suka zubo masa.
Kamal ya dubi Zeey da tuni hawaye ya soma zuba a fuskarta ya ce
"Ki d'an bamu guri zamuyi magana."
jiki a sanyaye taja kafafunta tayi waje.
hannun Maman Zeey
Mukhtar yakuma rike wa gam hawaye na wanke fuskarsa, gaba d'aya jikin ta yagama sanyi
tana tunin wani irin babban abu ne yasami d'an nata haka.
cikin rawar murya Mukhtar yake fad'in
"Maman Zeey kema ki yanke min hukuncin daya dace da ni kamar yanda suma suka kayi