Showing 45001 words to 48000 words out of 78655 words
Chapter 16 - KARSASHI Part 1 Complete Hausa Novels by Rasheedat S Director .pdf
ya ce
"Yanzun nan nabar kofar gidan Yayan mu nayi rashin sa'ar samunki nayi kuma farin cikin
had'uwa da kwarzon mu har sai da muka d'au selfi da shi, dama nazo ne na sanar miki gobe
idan Allah ya kaimu zamu d'an yi tafi da Alhajina."
numfashi ta sauke jin dai S.MAN bai gwada masa bakar halin sa ba.
tayi masa fatan isa lafiya nan suka lula duniyar masoya tana like da waya a kunne suna ta zuba
love d'in su...
Bayan kwana biyu.
SEEDARH ce kwance cikin d'aki tana kallo a t.v hamma ta yi tare da yin salati, a hankali ta mike
ta janyo kular da ta saka abincin breakfast ciki wan da take ajewa tarika ci har dare ta zauna
bakin gado ta soma ci.
taci yadda cikin ta zai iya d'auka kana tarufe sauran.
fuska ta yamutsa dan yanzu ruwa kawai take da bukata, dama ruwan pampon kichin take tara
cikin kofi ta kawo d'aki tarika sha duk da sam baya kashe mata kishi haka take maneji da shi,
gashi kuma gaba d'aya ta mance bata tari ruwan ba lokacin da ta gama girki, gashi ya kulle
kichin d'in yatafi da key d'in. tsaki taja tare da fad'in
"Dole ma in nemo ruwa dan wlh bazan mutu da kishi ba."
tamike da d'an sauri tafita, cikin sauri ta nufi steps dan taji fitarsa d'azu a mota bata kuma ji
dawowar sa ba.
tana shiga parlour'n sama in da fridge yake ta nufa ta bud'e, babu ko gorar ruwa aciki drinks ne
kad'ai a ciki.
rufe fridge d'in tayi tana fad'in
"Ruwa nake jin kishin sa ba lemo ba."
da sauri ta juya tanufi kofar bedroom d'in sa ta tura kofar a hankali............!
Mommyn Twins ce
í ¼í¼º *ƘARSASHI!* í ¼í¼º
*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR*
( _Book 1_)
~Free page~
_
*____________________________________*
*í ¼í¼ˆí ¼í·°AINUWA í ¼í·¼RITER'Sâœí ¼í¿¼*
*í ¼í·¦SSOCIATIONí ¾í´í ¼í¿»*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*í ½í±‡í ¼í¿»
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
page 15
Tashiga ciki da sauri ta isa inda fridge yake ta bud'e, cikin hanzari ta d'au babban gorar ruwa har
hannunta na b'ari tabud'e shi dan bakarami kishi take ji ba.
sai da ta sha kusan rabin gorar kana ta sauke gorar ta mai da marfinsa tarufe, takuma d'aukar
wani babban gorar ruwa sannan ta rufe fridge d'in
tana fad'in
"Zan shaku har dare."
ta juyo tare da d'aga kafarta zata bar d'akin aka turo kofar.
da sauri cikin rawar jiki tayi baya da hanunta tab'oye gorunan ruwan a bayan ta.
Ido S.MAN ya zuba mata ganin ta tsaye cikin d'akin sa cikin yanayin nuna rashin gaskiya, sai
kuma yasoma d'aga kafarsa ya tako zuwa gabanta yayin da yake cigaba da binta da kallon
tuhuma.
"Me ya kawo ki cikin d'aki na lokacin zuwan aikin ki baiyi ba, sata kika zo min ko?."
ya jefa mata tambayar ya na mai cigaba da tsare ta da ido.
d'an dibirbircewa tayi sai kuma ta saita nutsuwar ta ta ce
"Ni bana sata ban tab'a yi ba bazan kuma faraba da yardar Allah."
tayi maganar had'e da murgud'a baki da d'aga hanci sama cike da tsiwa.
ya ce "To idan ba sata kika zo min ba me kike b'oye shi a bayan ki."
yafad'a tare da miko hannunsa ya cafko hannayen ta da suke b'oye a bayan ta,
ba shiri tasaki gorunan kasa, sabo da yan da ya ruko hannun nata da salon mugunta.
bin gorunan ruwan ya yi da ido kana ya mai da duban sa gare ta ya ce
"Okay satan ruwa kika zo min a d'aki?."
baki ta turo ta ce "Kai nifa ba b'arauniya bace kishin ruwa nake ji dan kuma na d'auki ruwa na
sha baizama nayi sata ba,
idan kuma hakan sata ne to kowa ma b'arawo ne tun da kowa yakan iya shan ruwa a duk in da
ya gansa, ruwa kuma ai na Allah ne bana d'an mutum ba."
"Idan kuma mutum ya siya da kud'in sa ne ya ajiye wani yad'auka fa shima ba sata bane, to
bazaki sha wannan ba akan ba ruwa cikin bathroom d'in d'akin da kike ne, ko da a gidan ku
ruwan gora kike sha, wani samin guri kawai wuce ki bar min nan na daina ganin ki."
yayi maganar tare nuna mata kofa yana yi mata alamar ta fita.
baki ta turo gaba ta ce
"Allah bazan sha ruwan bayi ba ni ko a gidan mu ma bana shan ruwan pampo dan baya kashe
min kishi, sauyin rayuwa ce kawai amma muma ruwan gorar muke sha a gidan mu da, yanzu
kuma da Allah yaso ganin mu a haka bai hana mu kud'in da zamu siyi ruwan fiyowata ba, ni
ban iya shan ruwan pampo ba dan baya kashe min kishi."
Ya ce "Zaki b'ace min da gani ne ko sai na murd'e wannan bakin rashin kunyar, tun da bazaki
sha na pampo ba sai ki zauna haka."
fita tayi tana kunkune da fad'in wlh bazata sha na pampon bayi ba kam...
Haka kuma bata sha bathroom ba har sai da tazo girkin dare kafin tasha a kichin ta kuma d'iba
ta kai bedroom d'in kwanan ta.
shan ruwan kawai take bawai ko dun yana kashe mata kishi ba,
SEEDRAH ma abociyar shan ruwan dare ce.
duk nauyin baccin ta kishin ruwa na tadata cikin dare.
hakan ne ta kasance da misalin karfe biyun dare kishin ruwa ya tashe ta, ta mike cikin magagin
bacci ta isa in ta aje ruwan da tad'ibo a kichin aikuwa garin gigin baccin ta tamika hannu zata
d'au kofin ta tureshi ruwan ya kife a kasa.
sai a lokacin ta gama bud'e idanunta da bacci ke cike fal cikinsu.
tsaki taja cikim muryar bacci ta ce
"Shine ka zube."
sai kuma ta nufi bathroom dan ji take bazata iya bacci idan bata sha ruwa ba.
pampo ta kunna ta kafa kanta tasoma sha babu kakkautawa cikin ta yacika tam sai dai bata
fasa jin kishin ba.
mikewa tayi tana yamutsa fuska dajin yanda lokaci guda taji zuciyar ta na tashi,tasan za ayi
hakan dan tana kyankyanin shan ruwan bayi babu in da ta iya ne kawai.
da sauri ra sunkuya kan toilet tashiga sheka amai daya taho mata, sai da ta amaye ruwan data
sha duka kana ta mike ta wanke bakinta tana mai da numfashi.
sai da ta gyara in da ta b'ata kafin ta fito.
abakin gado ta zauna tana cigaba da maida numfashi.
wani irin mugun kishin ruwa takeji yin aman da tayi tamkar dad'a kara mata kishi ya yi, zuciyar
ta kuwa sai hurewa yake da azabar kishin ruwa.
da kyar ta iya tattaro yawun bakin ta ta had'iye. ta mike da sauri ta d'au hijabin sallarta ta saka
tafita a d'akin dan yanda take ji har idan bata sharuwa yanzu ba tana ji kamar bazata wayi garin
gobe ba.
direct sama ta haura rike da wayarta tana haska hanya dan duk wutan cikin side d'in a kashe
yake.
ko da ta shigo parlour'n sama gurin fridge
ta nufa tabud'e da tunanin ko ya saka ruwa aciki, amma sai taga babu sai drinks d'in ne kawai
aciki.
da sauri tashiga waige-waige ko Allah zai sa taga ruwa amma babu ko alamarsa.
numfashi ta fizga da kyar takuma had'iye miyau tare da rumtse idanunta da karfi tana jin yanda
zuciyar ta ke dad'a hurewa da ƙishin ruwa.
bud'e idanunta tayi ta sauke su kan kofar bedroom d'in sa idan har tana son tasha ruwa tofa
babu makawa dole sai tashiga d'akin sa.
sannan ta rokesa ya sammata.
bata da zab'in da yawuce hakan a hankali tashiga d'aga kafarta har ta tako bakin kofar.
Ta d'aura hannunta jikin handle sai kuma ta tsaya da tunanin har idan taje tarokesa tofa jin
kansa zaiyi kamar yafi kowa, sannan kuma yakara kaimi kan wulakantata da yake,
to amma tana jin kishin da bazata iya sarrafa kanta ba dole sai ta sami ruwan da zatasha.
kashe tocin wayar ta tayi kana a hankali ta murd'a handle d'in ta tura kofar a hankali cikin sand'a
tasa kai cikin d'akin.
cikin d'akin duhu babu haske ko tafin hannunta bata iya gani.
a hankali tasoma d'aga kafarta duk da bata ganin gaban ta amma takan iya hasko in da fridge
yake acikin zuciyarta, tana jin zata iya isa gurin batare da haske ba.
wani irin garuwa tayi da jikin abu da sauri ta dafe goshinta datake sammanin fashewa ma ya yi
dan bakaramin azabar zafi taji ba, gaba d'aya jikin ta ya d'au b'ari ga zafi ga tsoro bata kai ga
dai-dai ta nutsuwar ta ba taji hannun mutum a kafad'ar ta.
wani uban kara ta sake mai cike da tsananin tsoro tayi baya da sauri takuma garuwa da wani
abun, tana kokarin d'ago wayarta ta kunna tsabar b'arin da jikin ta yake wayar ta fad'i kasa, sai
kawai takuma sakin wani karar.
"Ke rufamin baki me yakawo ki d'aki na a tsohon daren na me kika ajiye anan kika zo d'auka
sata kikazo min?."
taji maganar sa daf da ita, wutar d'akin ya kunna yaci gaba da fad'in
"Alhj Musa ne ya turo ki ki kasheni ko."
kai tashiga girgizawa sai kuma ta ce
"Nifa ruwa zansha ba wani abu yakawo ni ba, ni kuma ba b'arauniya bace ka dai na dangantani
da sata, sannan kuma mezaisa Baba yaso kasheka."
"Ke ba magana nace ki jera min ba, bance kije ki sha ruwan bathroom ba d'azu, yanzu ma ki
koma kije kisha."
"Allah ni bazan iya shan abin da zai kusa kashe ni ba."
tayi maganar tana janye idanunta daga kansa dan babu komai ajikin sa sai gajeren wando
kawai.
ya ce "Oya wuce ki fita in kinje ki mutu."
a hankali ta juya harta kai bakin kofa tajiyo muryarsa yana fad'in
"Zo ki d'auka zan cire kud'in sa acikin kud'in aikin ki dan kin dai na cin abinci kyauta acikin
gidan nan, duk wani abun da zakici acikin kud'in aikin ki."
da sauri ta juyo dan sosai take jin kishin ta d'au babban gorar ruwa tafita, a parluor'nsa tasha
kusan rabin ruwan kana ta koma d'akin ta sai alokacin ta sami bacci mai dad'i yadda take so..
Washegari kamar kullum tana yin sallar asuba bata yadda ta koma ta kwanta ba sanin kalar
baccin ta ba lallai bane tatashi dawuri.
kichin tatafi tafara d'aura breakfast kafin ta fito can ta hangosa gurin motsa jiki tawuce ta haura
sama.
ko da ta gama gyaran saman tasauko shikuma lokacin yahaura sama,
tashiga kichin ta kammala aikin kana ta d'auki nasa breakfast d'in ta kai masa nasa, tadawo
kichin d'in ta d'auki nata tashige d'aki tana zama tajiyo sa yana kokarin kulle kichin da sauri ta
mike tuno da wayarta ta mance shi a cikin kichin d'in.
tana fitowa yana zare key da sauri ta karaso in da yake tana fad'in
"Na mance wayata aciki bani key d'in na d'auka."
jefa key'n ya yi cikin aljuhunsa kana ya juya yasoma tafiya yana fad'in
"Sai ki jira idan lokacin bud'e kichin d'in ya yi sai ki d'auka."
da sauri tasha gaban sa tarike kugu ta ce
"A wani dalili wayata ce ina bata wani ba kabani key nad'auki abina."
"Anki badawa idan kina da karfi ki kwata."
hararar sa tayi sama da kasa kana taja tsaki mtttss ta juya.
hannu ya miko zai cafko ta ai ko ta d'aga kafa tasa gudu nan jigidan jikin ta yafara bada sautin
kacau-kacau.
tsayuwa ya yi tare da zubawa bayanta ido yalura duk san da tayi masa tsamin baki zata gudu
sai yaji wannan karar ajikin ta.
har ta shige d'aki yana tsaye kana daga bisani yahaura sama..
Yana gama breakfast yazari makullin mota yabar gidan, bai dawo ba sai bayan sallar isha.
SEEDRAH kam yau tasha baccin ta ma'ishi wan da tun da tazo gidan bata samu tayi irinsa ba,
kasan cewar key d'in kichin na gurin sa be dai isa yakamata da laifin rashin yin girki ba.
tana zau ne kan sallaya yaturo kofa, tad'ago ta dube sa sai kuma ta kawar da kanta tacigaba da
lazumin da take.
daga bakin kofar ya ce
"Ke ina abinci na?."
batare da ta d'ago ba ta ce
"Kaba da key ne?." key'n ya wurgoshi jikinta ya ce
"Tashi ki dafo min tea yanzunnan ki kawo min."
ya janyo kofar ya fita.
sai da ta gama dukkanin addu'o'in ta kafin ta fita taje ta dafo tea d'in.
ad'an karamin flas tazubo tad'aura shi kan d'an madaidaicin tray had'e da cup tafito ta haura
sama..
yana zaune a parlour yana busa hayakinsa,
fuska tashiga yamusawa tana kakkawar da fuskarta gefe,
tazo ta gefen sa ta aje tray'n kan table d'in da ke gefen sa dai-dai lokacin da ya huro hayakin
sigarin.
da sauri takai hannu ta toshe hancinta, d'aya hannunta kuma tana kore hayakin da shi tana
wani yamusa fuska cikin yanayin da kamar zatayi amai.
tajuya zata bar parlour'n tana mai cigaba da yamutsa fuska cikin kasa da murya sosai ta ce
"Mutum bashida aikin yi sai shaye-shaye da halin y'an kwaya mttss."
taja gajeren tsaki
Maganar da tayi tamkar a kunnensa.
wani irin mikewa ya yi tare da fizgota har sai da ta garo da jikin sa.
bakaramin tsorata tayi da ganin yanayin da ya shiga lokaci guda ba,
ta lura aduk sannda ta ce masa d'an kwaya d'an shaye-shaye irin wannan yanayin fusatar take
gani tattare da shi.
sigarin ya kai bakinsa yazuko hayakin daya cika bakin sa kana ya jefar da sigarin kasa sannan
ya kuma yanyota jikinsa sosai kana ya tallofo kanta da hannunsa d'aya d'aya hannun kuma ya
matse bakinta,
ya d'aura lips d'in sa kan nata yahura mata hayakin sigarin cikin bakinta duka sannan yad'ago
kansa yasa hannu ya toshe bakinta.
yadad'a tallafo kanta sosai da sosai.
SEEDRAH ko ido tashiga zazzarewa tana juya kai da fizgar numfashi, yayin da hayakin yashiga
kokawa da makoshin ta, tuni idanunta suka kad'a sukayi jajir.
sai da ya tabbatar da tahad'iye hayakin kafin ya sake ta tare da angizata tazube kan kujera.
yabita yashako wuyanta cikin fusatacciyar murya ya ce
"Ni ba d'an shaye-shaye bane ban tab'a shan kwaya ko kayan maye ba, iya sigari nake sha
shima nafi shansa alokutan da nake jin b'acin rai, duk san da kika kuma dangantani da d'an
kwaya na rantse saina canza miki kamanni wawuya kawai!!."
ya hankad'a ta tagaru da jikin kujera ya mike yana huci yashige bedroom d'in sa.
Itako tari take babu ko kakkautawa tanayi tamkar zata shid'e da kyar ta mike tana cigaba da
tarin ta sauka kasa tana shiga d'aki bayi ta wuce tarika kela amai kamar zata amayar da hanjin
cikin ta.
da kyar aman ya tsaya ta mike tana mai da numafshi a daddafe ta gyara in da ta b'ata kana tayi
wanka ta fito,
tana saka kaya ta haye gado ta kwanta tana
jamasa Allah ya isa a haka bacci ya d'auke ta.
Washegari da kyar ta iya tashi sallar asuba sakamakon wani baccin da ke cike fal idanunta,
tamkar batayi bacci da daddare ba.
bayan tayi sallan kwanciya tayi kan sallaya jin yadda bacci ke fizgar idanunta ai kuwa ba b'ata
lokaci bacci yatafi da ida.
ba ita tafarka ba sai wajen karfe 10 da rabi.
da sauri ta mike ganin yanda lokaci yatafi har haka, sanin kalar baccin ta shiyasa tun da tazo
gidan bata yarda ta kwanta baccin asuba gudun kada ta ketare lokacin aikin daya zana mata
saboda kare wulakancin sa ga Baba.
da sauri ta fito numfashi ta sauke ganin sa can gurin motsa jiki.
a ranta ta ce
"Allah ya taimaka shi ma dai makaran ya yi."
waige-waige tashiga yi tama rasa ta ina zata fara sai kawai ta juya da sauri ta haura sama.
cikin hanzari ta shiga gyara parlour'n nan da nan ta gama kasancewar babu wani datti,
da sauri ta shige cikin bedroom d'in sa ta na fad'in
"Allah yasa har na gama kada azzalumin nan ya shigo."
d'an tsayuwa tayi cikin d'akin tana tunanin tafara daga cikin bathroom ne ko daga bedroom, sai
kawai ta yanke hukuncin ta fara daga bayi sannan ta fito tagyara d'akin, da sauri ta nufi kofar
bathroom ta murd'a handle ta shige ciki ta maida kofar ta rufe kana cikin hanzari ta juyo.
Wani irin waro ido tayi ganin mutum tsaye cikin bayin babu kaya jikin sa yayin da yake ta
kokarin wanke kumfar sabulu a fuskansa,
kara ta calla sai kuma da sauri ta kai hannayenta tarufe fuskarta da shi tashiga ja da baya.
da sauri S.MAN ya wanke kumfar fuskarsa kana ya janyo towel ya d'aura a kugun sa,
jin ta garu da jikin kofa ta juya da sauri tana kokarin bud'e kofar sai ji tayi ya danne kofar da
hannunsa kana yakuma murza key ya kulle kofar da key.
ido takuma warowa batare da tajuyo ba ta ce
"Allah bansan kana cikiba kuma ai can na hangoka gurin motsa jiki to taya akayi na ganka a
nan kuma."
fuska ya d'aure tamau ya ce
"Karya kike kin sani sarai ina ciki shiyasa ma kika shigo, wannan fisararrun idanun naki ga
dukkan alamu kinsan maza shiyasa ma kika biyoni bayi yanzu!."
ya yi maganar cikin tsawa har sai da tad'an zabura.
kai tashiga girgiza wa tana fad'in
"Kada kayi min kazafi wlh Allah ban san kana ciki ba a gurin motsa jikinka fa na ganka dan Allah
bud'e min kofa na tafi."
"Ai ba ki isa ba tun da kika ganni to yazama dole