Showing 27001 words to 30000 words out of 99740 words
Chapter 10 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf
wajen irin wannan halitta? Ai sai ku
kyawawa, masu mota 'ya'yan attajirai. Khadija
tace kin hutawa kanki wallahi kina burge ni
yadda kike tafiyar da rayuwa, ba kya jajubo wa
kanki abun da zai wahalar dake. Nima nayi
nadama ba zan sake shiga irin wannan hatsarin
ba. Yanzu mun bata da malaman nan
makaryata, wai yaga aurenmu har da haihuwar
'yan biyu. Shine ai na saki jiki nayi ta tura
musu kudi suna cemin zai zo da kafarsa
nemana ga mutum kamar zai yayyaga ni cikin
waya don masifa. Bani ba wani malami ai
yanzu na rufawa kaina asiri nace mohd ya aiko
da iyayensa muyi aure. Ina laifinsa yaro
matashi, yana da mota da gidan kansa da aikin
bankinsa, nima da aikina ya ishe mu rayuwar
duniya. Sai naji hankalina ya tashi, dana sani
ta afko min. Na gyara zama nayi tagumi ina
duban khadija na rasa in da zan saka raina, sai
yanzu na fara gane kuskuren da na tafka a
rayuwa. Ummi ta cuce ni. Na fada a cikin
zuciyata yayin da hawaye ya cika min ido.
Nace da khadija kina so kice min gaba daya
asirin da malamanki suka sha zabgawa ko
daya bai taba shi ba, asiri baya cinsa kenan?
Tace baya cinsa tunda bai ci shi ba, babu abin
daya yi masa. Malamina daya ne ya fada min
gaskiya tun da farko naji haushinsa, daga
karshe na gane gaskiya ya fada min. Yace dani
yaron nan da kike so gaskiya ya rike adduar
neman tsari dare da rana, da wuya a jefe shi ya
taba shi, sai dai kawai kije kiyi addua in da
alkhairi Allah Ya hada ku ta wata hanyar, a
dadin rai yazo, kuma ina so ki sani ba'ayiwa
Allah dole. Khadija tace aiki ma daina damuwa,
Allah Ya ganar dani har na dade ina istigfari.
Su maryam anmad ne suka rage suma Allah Ya
ganar dasu. Shiyasa aka ce wani kyau bala'I
ne, sai a dilmiyar da kai in bakayi taka tsan
tsan ba. Yanzu dr shureim in ba don Allah Ya
sa nutsatte bane da mata sai sun halakar
dashi. Haka ma mace mai kyau idan baatayi a
hankali ba maza su halakar da ita, su rude ta
da kudi tabi su koda kuwa tana da aure. Ke dai
Allah Ya sa mu gane gaskiya. Sai naji khadija
ta burge ni, tafi ni gaskiya. Ina ma a llokacin
da naje neman shawara wajen ummi khadija na
samu ta fada min abinda ta fada yanzu, da ba
wa zuciyata hakuri, da ban je na jefe kaina a
rigima ba. Yanzu gashi komawa gida ya
gagareni. Da me zan biya wannan dimbin
bashin na kaina gashi babu alamar nasara a
aikin malamin. Khadija ta katse min tunanina
tace duk inda ya kai da takama da kwalliya, da
yanga karshen alewa dai kasa. Dole mace zai
aura, ba auri kansa da kansa ba. Kuma dole
yayi 'yar murya kafin a bashi ita, dole ya kashe
kudi ya bauta mata saboda Allah Ya wajabta
masa ciyarwarta, sutura, kula da lafiyarta,
muhallinta da duk wata dawainiyarta. Daman
dai ance DUK KYAN TAKALMI dole kafa ce zata
saka sannan a taka kasa. Lallai zanso inga irin
macen da zai aura, karshenta fa ya kare a
mummuna, baka, 'yar talakawa, kinsan karshen
irinsu kenan. Nace yana da mata fa har da 'ya,
kema kinsan dr shuriem ba zai auri kucaka ba.
Khadija tace ke aisha farida wa ya fada miki
wannan? Nayi murmushi nace matarsa ma
baturiya ce a london suka hadu, a london take
zaune. Da bakinsa naji yana fada. Kuma a
gabana sukayi waya da ita cikin harshen
turanci ko hausa bata ji. Khadija ta gyara zama
tace don Allah da gaske kike? Ni da kin fada
min haka tuntuni ai da ban wahalar da kaina ba
wallahi. To wai ina kika ganshi ne har kika ji
yana waya, nifa tun ganin nan nasa da mukayi
yana motarsa ban sake ganinsa ba. Ko dai ba
shi kika gani ba? Nace shine wallahi, abokin dr
lukman ne, likitan kwakwalwa wanda matron
maryam take aikena wajensa. Kinsan tana da
kanwa mai matsalar kwakwalwa, to yana duba
to ko ba ranar clinic ba. Khadija tace lallai ba
zai saurari kujari-kujari irinmu ba, mai mata
baturiya mai zaiyi damu? Naji zuciyata tana
kokarin bugawa, sai na mike na tayar da sallar
la'asar daman da alwalar azahar dina bamu
dade dayi ba. Nayi sallama nayi addua, Allah
Ya biya min bashin da yake kaina. Na yunkura
zan mike in tashi, sai khadija tace dani aisha
farida gaskiya akwai abinda yake damunki,
saboda duk jikinki yayi sanyi, yanzu ko yanayin
sallarki ya canza ba irin na da ba, ba kya
samun nutsuwa wajen yin sallh, kin daina
doguwar addua bayan kin idar da sallah. Nayi
shiru ina tunani nace a raina yanzu son dr
shureim har addinina zai taba, bayan karatuna
da ya tava ga zaman lafiya dana rasa. Sai na
zuba wani zazzafan hawaye nayi sauri na boye
fuskata don kada ta gane. Na dauki jakata na
rataya nace mata zan tafi gida. Ta rako ni har
bakin titi na hau acaba na tafi, ita kuma ta
koma gida. Sai a hanya na fara tunanin halin
da zan fada idan naje gida, don haka nace dan
acaba ya kai ni zango gidan ummi kenan. Ina
isa cikin gidan na tarar da kofarta a kulle
alamar bata nan, sai naji banji dadi ba don
haka na leka bangaren faccalarta na
tambayeta. Tace min bata nan tun jiya ta tafi.
Sai naji zuciyata ta buga na dafe kirji na
tambaya kafiya? Ta tafi unguwa tun jiya bata
dawo ba? Amsar da ta bani itace babu komai.
Na sami kujera na zauna nace da ita ki fada
min gaskiya, ummi kawata ce bata boye min
komai. Sai tace to kiyi mata waya mana sai ta
fada miki da bakinta tunda aminiyarki ce. Na
jikina a sanyaye nace to sai anjima na tafi. Sai
naga ta bini da kallo alamar tausayawa tace
dani gaskiya ummi tana gidansu mijinta ya
sake ta. Kuna fita shekaran jiya ya kai mata
takardar sakinta gidansu, ashe bai bata izinin
fita ba ta biki kuka fita har ina cewa ku jirani in
shirya kuka ki. Na dawo na tsuguna a gabanta
nace innalillahi wainna ilaihir rajiun. Yanzu
yassar saboda dan wannan dalilin ya saki
ummi? Tace a'a ba wannan kadai ba, daman
akwai wata kasa. Ummi bata da kunya, ga ta
da bin bokaye da 'yan tsubbu kowa yasani,
mijinta ya sani saboda yana tono binne binnen
da takeyi, da kuma barbade barbade da takeyi
masa a abinci. Da zarar sun fada mata karya
sai ta zai tana habaici ta bata da kowa, har
uwarsa da ta haife shi bokanta yace uwar
mijinta bata sonta. Yanzu ya dace ace ummi
tazo ta zazzageni? Jiya ita da kannenta da
kyar aka fitar dasu daga gidan nan wai sai sun
dake ni. Har da cewa yadda na raba zamanta
da mijinta nima zamana da mijina sai ya kare,
sai in babu malamai a kano. Kinga kenan
malaminta ne ya fada mata ina yi mata asiri.
Ta tabe baki ta harareni tace to ai fitar da
kukayi gidan boka kuka je, saboda yassar
yabiku a baya har yaga inda kuka nufa, shi
yasa ya kai takardar sakinta gidansu. Ko kin
dauka ban gane ki bane munafuka kin san inda
take. Aiko ki tayi kizo ki barbada min wani abu
ko? Na zabura na mike tsaye na dafe kirjina
nace ni?? Wallahi bansan ummi ba ta nan ba
da bazan zo ba. Ba na irin wadannan halayya
kuma ba da wata manufa nazo ba. Tace dani
fita daga gidan nan kafin in tara miki jama'a.
Kuma duk ranar da kika kuskuara kika hadu da
yassar yace sai ya balla miki kafa, tun a
sakandire kike yi mata hudubar tsiya, yasan kin
tsane shi, shine kika biyo ta har gidan aurensu
kika kai ta gidan boka, wato a kashe shi kuci
gado ko? Tunda nake a duniya ba a taba yimin
cin mutunci, kazafi da wulakanci irin na
wannan ranar ba. Duk irin gulmace gulmacen
nan da ake yi a lungunmu tun ina yarinya ba
ataba cewa ga abin da aisha farida tace ba.
Lalli na jefa rayuwata cikin wani mawuyacin
hali saboda son dr shureim imran. Na gaggauta
ficewa daga gidanta kafin ta tara min jama'a
kamar yadda ta fada, kuka nake wiwi na hau
acaba ba tare da nasan inda na nufa ba. Sai da
dan acaba ya tambaye ni sau uku hajiya ina
zan kaiki? Sannan nace ka kaini gadon kaya.
Gidansu maryam ahmad kenan. Ita ma inje inji
halin da take ciki da dr shureim dinta. Duk da
haka ban daina sonsa ba. Maryam ahmad tayi
mamakin ganina, amma ganin ina fara'a ta san
lafiya kalau kenan. Tace dani shegiya aisha
farida umar daga ina kike, ba ki koma gida ba
ne har yanzu na ganki da uniform a jikinki?
Nace ke dai bari, yau bana jin komawa gida da
wuri, zumunci nake ji, zuwa nayi in gaishe da
su mamarki. Sai taji dadi taja hannuna har
dakin mahaifiyarta muka gaisa, na gaisa da
kannenta da 'ya'yanta biyu wanda Allah Ya
yiwa mijinta rasuwa ya barta dasu amma fa da
dimbin dukiya. Muka koma dakinta muka zauna
akan wani makeken gado, ta kunna mana AC
yayin da ta dinga kwallawa 'yan aikin gidansu
kira suna kawo min abubuwa kala kala kamar
su juice, kayan marmari, cincin da cake. Sai
taga duk na kasa ci sosai, ina yawan yin shiru
idan tana magana kamar hankalina baya tare
da ita. Sai ta zungureni nake dawowa
hankalina, na rasa yadda zan dauko mata
maganar dr shureim domin kada ta zargi wani
abu ta gano saboda zancensa na zo gidansu.
Domin ban taba zuwa ba gidansu haka kawai
ba, sau daya na taba zuwa kuma daga
makaranta muka zo muka yi mata gaisuwar
mijinta, da yake gidanta na kallon gidansu ne.
Muka shigo nan ma muka yi mahaifiyarta, to
anan na san gidansu. Da kanta ta dauko min
hirarsa tace baki tambayeni likitana ba dr
shureim. Sai na zauna dai dai nace yaya akayi?
Ki bani labari, akwai cigaba ko? Tace wanne ci
gaba ni da tun kafin aikin da na rabawa
malami bai je ko ina ba abu ya dagule gaba
daya, nace to su daina adduar yafi karfina. Dr
shureim yafi karfin ya kwanta in taka shi da
takalmin kafata, kinji. Anya mutumin nan
haifarsa akayi ba tikowa yayi daga sama ba?
Ace mutum ya hadu ta ko ina babu aibu a
tattare dashi? Sai naji na kara tsanar kaina, na
fada cikin shamulalliyar murya, me ya faru?
Tace mutuminki na same shi a ofis dinsa
wancan sati, malamina ya bani laya na kunshe
a karkashin harshena wai in dai da layar nan
duk abin da nace masa ya zauna babu musu.
Bayan turarukan da na dume jikina da goshina
dasu, wasu masu wari kamar na 'yan bori, ni
kaina sun isheni da wari balle shi dan gayu. Ina
shiga kaina tsaye ko fargaba banayi saboda an
bani tabbaci, ni kuma na yarda da cewar na
same shi na gama kamar yadda suka bani
tabbaci. Shi da wata likita mace ina jin dai
daliba ce, bata gama ba. Ta cika tayi taf kamar
zata fashe saboda fushi. Ta wani galla min
harara nima na harare ta saboda abin da ya
kawo ta shi ya kawo ni. Da na gaishe su babu
wanda ya amsa sai na sami kujera na zauna a
kusa da ita, shima yana zaune a kujerarsa. Ya
juyo ya dubeni sarai sannan ya dukar da kansa
yaci gaba da rubuce rubucensa. Ya gama ya
mika mata takarda, gami da cewa Allah Ya
sawake jeki. Ta tabe baki ta dubi takardar da
alama magani ya rubuta mata sai tace inje in
sha wannan kenan? Ya ce eh In sha Allah
kurajen zasu warke. Sai tace doctor muje ka
kaini chemist din mana, nina fi so ka tabbatar
masu kyau ne. Sai ya bata rai yace ba aikina
bane in rubuta miki magani, kuma in raka ki
zabar miki wanda zaki saya ba, komai a rubuce
yake zasu karanta su baki. Tace kaki zuwa ka
duba ni a gida, kwanana biyu ban fito ba har
waya nayi na fada maka. Na turo maka sakon
adireshina kaki zuwa. Sai ya harare ta yace
bani da lokacin zuwa duba dalibaina don basu
da lafiya. Ta sake turo baki tace amma ai
daliban daban daban ne, ba daya nake da
sauran ba. Ya daka tsawa ya zazzare mata ido
yace dalibaina dukka daya suke, daidai kike da
wannan. Ya nuna ni, ita kuma ta wurgo min
harara, nayi murmushin jin dadi nima na harare
ta sama da kasa. Yace idan baki da abin da
zaki fada min mai ma'ana game da karatunki ki
tashi ki tafi, kada ki kara shigo min ofis. Ta fice
sai ya juyo wajena ya tambaye ni cikin fushi,
ke kuma fa? Menene? Ina fitowa na kira
malamin da ya bani laya da turaren nan mai
daga hankali don wari kamar na 'yan bori.
Yana daukar wayar sai yace malama an sami
nasara kuwa? Nace nasarar me mutum kamar
zai mare ni? Sai yace to an sami kuskure ne
daga wajenki ina ganin baki yi yadda nace ba.
Nace komai daidai nayi banyi kuskuren komai
ba. Yace yaushe zaki zagayo sai in sake
bincikawa muga ta hanyar da zamu sake
bullowa kuma? Nace Allah Ya sawake in sake
kashe wani kudin bayan wanda na tula maka
na baya har da yankan rago amma a banza.....
Kafin in rufe bakina ya kashe wayarsa, nayi ta
kira har yau a kashe. Ko yau ma na gwada a
kashe, yaga na gane shi dan damfara ne babu
abin da ya iya. Haka nabi duk sauran malaman
naci musu mutuncu sukayi ta kame kame, sai
yanzu na gasgata cewar malaman zamanin nan
sun raina wa mata wayo, sun mayar dasu
jahilan karshen zamani. Idan kura tana
maganin zawayi tayi wa kanta, ke kina ganin
malaman kinga wahalallu masu matsala sun
kasa maganin matsalarsu, wai suce zasuyi wa
wani maganin matsalar su, sai suyi ta canke
canke don basu ma san ya ake duban ba. Ai ni
na dawo daga rakiyarsu na goge lambar
kowannensu, ko sun kira ni tsuye su nakeyi, sai
su waya da sauro. Ko wata na gani zata bata
lokacinta wajen bin malamai zan hanata sai dai
idan taki yadda in kyale ta, idan taje taga uwar
bari zata dawo da kanta tayi min bayani. Duk
wadannan bayanai da maryam keyi tuni sun
ragargaza min zuciya, kwakwalwata ta riga ta
dau gobara, na rike kai kawai tamkar mai
ciwon kai yayin da na sulale na kwanta akan
gadonta tamkar sumammiya. Na yarda da
cewar komai ya sami bawa rubutacce ne, in ba
haka da ya za'ayi tun farko inji wadannan
labarai akan malamai kuma in dauki
zunzurutun kudi in kai wa wani? Nace a raina
me yasa na fara zuwa gidan ummi neman
shawara banzo wajen khadija da maryam sun
fada min halin malaman zamani ba? Tun daga
lokacin na tabbatar kudin sun mula kuma ba
zan sami dr shureim ba. Maryam labari take
bani kala kala, amma bana fahimta ina can ina
tunanin abin da zanje in tarar a gida, haduwata
da uwani mai adashe da sauran makoftan da
na ciyo bashi, sannan bayanan da zanyi wa
yaya hussaini in da naje na kai dare bayan tun
karfe biyu na rana muka tashi.
A gidan su maryam nayi sallar magriba, na yi
ishai muka ci abincin dare. Taga bani da niyyar
tafiya sai ta fara mamaki, tana jero min
tambayoyi iri iri kasancewar ta sanni ba mai
bin gidan kawaye bane kwata kwata balle tace
na saba daman. Sai da na fuskanci har ta fara
gyangayi , tara da kwata na dare sannan na
fara haramar tafiya gida ba don naso ba,
saboda niyyata sai karfe goma sha daya na
dare zan koma gida kafin nan kowa yayi bacci.
dole na fito ta raka ni kofar gidansu na hau
babur na tafi. Ina tafe ina adduoi har na isa
unguwarmu, daga nesa da gidanmu nace mai
acaba ya sauke ni, don bana so 'yan gidanmu
suji karar babu na san idonsu yana kan hanya
suna zuba idon dawowata. Na biya dan acaban
kudinsa yayin da nake tafiya tamkar hawainiya
ina yi ina waige waige tamkar barauniya. Da
sanda na shiga zauren gidanmu naci sa'a babu
'yan matan gidan masu zance a zaure da
samarinsu. Sai na leka tsakar gidan, nan ma
ban ga kowa ba. Sai na cire takalmana na rike
a hannuna ina sanda dana zo giftawa ta
windown dakin uwani sai na tsugunna nayi
duku duku na wuce don kada taga giftawata,
najiyo motsin mutum a daki ina kyautata zaton
ba ta yi bacci ba. Da yake babu wuta sai
hasken fitilar kwai da kyandira zaka dinga
hangowa a dakunan don haka na hango kyallin
kyandir a dakin abida ina hango inuwarta a
tsaye jikin labule, sai dai ba zan tantance abin
da takeyi a tsaye ba. Na duba kofar dakin sai
naga takalman yaya hussaini da alama ya
dawo, nan da nan tsoron da nake ciki ya karu.
Nayi maza na tura kofar dakina na shiga na
iske ta shimfidar da 'ya'yanta ta rage hasken
fitilar kwai a gefe. Shiga ta dakin ke da wuya
ko jakata ban ajiye ba naji motsi a kofar
dakinmu, nan da nan na tsuguna na takure a
lungu. Sai na sankare saboda firgici. Abida ce
ta shigo hankalinta a tashe, tana ambaton
subhanallahi, yaya zanyi yau. Tana rufe bakinta
sai muka hada ido yayin da zaka dinga hango
mamaki a cike da fuskarta gami da firgici. Ni
kuma ina tsugunne ina kokarin daidaita
numfashina domin na shide, don tsoron yaya
hussaini da uwani a tunanina daya daga
cikinsu ne. Aisha farida lafiya? Yaushe kika
dawo? Ina kika shiga yau tun safe? Abida ce ta
jero min wadannan tambayoyi masu wuyar
amsawa. Na mike tsaye a sanyaye ba tare