Showing 45001 words to 48000 words out of 99740 words
Chapter 16 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf
aiki ne samun
shuraim amma kin biyea maganar qawaye
duk sun tsorata farida ta girgiza kai tace ba
zai yiwu ba nan da nan farida ta juyo ta
dube ta cike da mamaki marar misaltuwa ta
fada a bayyane ikon Allah yai naga abunda
yafi qarfina sai suka kwashe da dariya su
duka abida ta gyara zama taci gaba dayi
mata tsifa yayin da har yanzu farida na
kwance ta dora kanta akan cinyarta abida
tace idan dai har yanzu kina son shuraim
bana so ki fitar da ran sumunsa domin Allah
yana bawa bayinsa duk abin da suka roqe
shi;farida ta girgiza kai tace aunty na
haqura da dr shuraim ko maganarsa bana
so ayimun abida tace kin haqura akan dole
ko kin daina sonsa ne kwata-kwata?Aisha
tayi shiru yayin da hawaye ya cika mata ido
idan ta matse sai wani ya sake tsattsafowa
abida ta shafa kanta tace kiyi haquri kukan
naki zai koma dariya da izinin ubangiji idan
baki manta ba na umarce ki daki riqe abu 5
wannan abu 5 din zai kaiki da samun nasara
ki sami shuraim cikin ruwan sanyi uhmmm
farida ke ambato tana kwance ta kasa
magana sai bugun zuciyarta ke tsananin
yi.Abida tace bazaki tambayeni abu 5 din
bane? cikin sanssayar murya tace meye
abun 5 da zan riqe? abida tayi murmushi
gami da jiyar zucia tace Alhamdulillah a
cikin 5 din nan zan fara fada miki 3 daga
baya inga miki saura 2 a hankali.Aisha ta
daga kanta a hankali ta dubi Abida zuciyarta
cike da fargaba abun da abidar zata fada
tana tantama ko zata jure su don ta qudiri
aniyyar ba zata sake yin wahala ko zubar da
ajinta ba wurin shishigewa dr shuraim abida
tayi daria tace kada ki tsorata zaki iya ba
wani abun wahala bane.farida tayi ajiyar
zucia ta dafe qirji ta lumshe ido gami da
qirqiro wani basashen murmushin da bai
kai zuci ba ita dai a ranta tafi son abar
maganar dr shuraim kawai shi yafi
sauqi.abida tace abu na farko dana keso ki
riqe a rayuwarki itace addu'a idan kika
yawaita addu'a akan dukkan lamuranki zaki
ci nasara Aisha ta gyada kai tace ina addu'a
sosai ma kuwa abida tace wannan ta
musamman ce a tsakaninki da shuraim ki
roqi Allah ya zabar muku abinda da yafi
alkhairi amma ke alkhairin wajenki shine ki
sami soyayyarsa tunda kina sonsa,babu
hijabi tsakanin ubangiji da bawansa ki roqi
duk abunda kike nema a dunia da lahira
idan dai halak ne ki zayyano masa duk
yadda kike so babu kunya Allah mai karbar
addu'a ne idan kika riqe addu'a ki yarda
Allah zai amsa miki kin cika abu daya.Aisha
ta gyada kai naji menene na 2?
Abida tayi ajiyar zucia tace abu na 2 da zaki
riqe bayan addu'a shine kizama mai
tsananin haquri sai mai haquri ne yake cin
ribar rayuwa ki daure ki jure duk abunda
zaki gani haka duk nisan lokacin da za'a
dauka ki daure kada ki qagu ko ki girgiza ko
ki razana ba'a yiwa Allah dole kuma
gaggawa daga shaidan take ma'ana duk
tsawon lakacin da za'a dauka kafin shuraim
ya karkato gareki kada ki gaji kiyi fushi kice
kin haqura.sai na 3 shine ki riqe
mutumcinki. Kada ki fito da maitarki fili ya
gane halin da kike ciki na sonsa ma'ana kaja
ajinki.Aisha ya yamutse fuska alamar nuna
rashin fahimtarta a fili abida tayi murmushi
tace zaki fahimce sai a hankali.farida ta
tashi zaune ta dubi abida zuciyatra cike da
quna tace aunty abinda kina nufin inyi ta
bin shuraim ina zubar da ajina yana
wulaqantani shine haquri? idan ba haka ba
yaushe shuraim yasan dani balle yasan ina
haquri dashi wata rana yaso ni?kin kasa
gane waye shuraim idan ba office muka je
ba bama ganinsa abun da ya fiye min sauqi
shine na rabu dashi ni yanzu ko a hanya ma
bana so mu hadu bawai na tsane shi bane
ko yayimun wani laifi aa ko kadan bana
zarginsa don bai ma san abun da anke yi ba
sai dai don na samarwa zuciya ta
salama.abida ta girgiza kai ai wannan itace
juriyar da haqurin da nake kiyi ki taka inda
yake ki ganshi ya ganki sannan kija masa aji
Aisha taji tamkar abida ta dora mata dunia
akanta don nauyin da kanta yayi taji
hawayen takaici ya tsatsafo mata ta girgiza
kai tace aunty abida zancen jan aji kuma a
nan in har naje inda yake? ai na sayi
wulaqanci da kudina abida tayi murmushi
tasa gefen hannunta ta gogewa farida
hawaye tace ki biyo ni a sannu a hankali
zaki fahimce ni kuma zaki ga canji a wajen
dr shuraim insha'allah ke dai kija mu je ki
riqe matakan 3 addu'a.haquri da riqe
mutunci.farida ta koma ta kwanta akan
cinyar abida a sanyaye yayin da hawaye
yayi ta zuba ta tuna mata abinda taci gaba
dayi mata tsifa tana zayyano mata dadadan
kalamai game da yadda zata sami shuraim
idan har zata riqe addu'a zata riqi
haquri.Aisha farida tana yin duk abun da
abida ta shawarceta ta duqufa da yin addu'a
safe da rana harda tsakar dare dama can ita
gwanar yin addu'a ce tana da juriyar yin
addu'a sai dai lokacin taji a ranta kamar
abun ba zai yiwu ba bata lokacinta kawai
takeyi sai ta tuno abubuwan da abida ta
fada mata cewar ta roqi Allah duka abinda
take so kada ta boye babu hijabi tsakanin
bawa da ubangijinsa sai taci gaba dayi bata
gajiyawa.tafi ambaton Allah kasan ina son
shuraim idan da alkhairi shima ya soni.
A CIKIN ASIBITI Aisha farida ce ke zaune
akan wata doguwar kujera tana jiran
matron maryam ta fito daga duba mara
lafiya a babban dakin mata, zata bata sakon
data aike ta ta karbo. Duk da ita ma daliba
ce zata iya shiga, amma security ta hanata
wucewa tace sai dai ta jira anan kasancewar
shugaban asibitin aminu kano ne yake
zagaye. Don haka manyan likitoci sai
tururuwar wucewa ciki suke yi. Tana zaune
tana jira har ranta ya fara baci, don ba don
sakon nan ba da babu abinda zai rabota da
karatunta, ita yanzu bata so a wuce ta koda
dakika daya ne. Taji tamkar ta barwa
security sakon inta fito ta bata, sai ta tuna
zai iya bata kuma sakon yana da
muhimmanci, don ba dan faridar ba ma da
matron ta yadda da ita babu wacce zata
aika ta karbo mata. Kudi ne da wasika ta
karbo mata daga wajen matron aisha, a
dakin 'yan awo. Aisha farida taja dogon
tsaki sannan ta harari security din da ta
jawo mata wannan dogon bata lokacin,
sannan ta duba agogon dake daure a
tsintsiyar hannunta. Karfe goma da rabi na
safe daidai, ta daga ido zata kalli kofar dakin
da matron ke ciki. Kicibus idanuwanta
sukayi da abin da ya gigitata har sai ta
zuciyarta ta daki allon kirjinta don firgici.
Bata manta da ambaton innalillahi wainna
ilaihi rajiun ba, yayin da ta daure bata nuna
razanar da tayi a fili ba. Dr shuraim ne ya
tunkaro inda take a zaune, yana tafe
tamkar dawisu, cikin kyakkyawar shigarsa
wato bakar suit, hannunsa rungume da file.
Kallo daya tayi masa tayi saurin dauke
idanuwanta, haka nan da nan ta kawar da
fuskarta gefe daban, ko da ya karaso
saitinta sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta
kasa har ya wuce bata dago ba. Wucewarsa
ba dadewa sai taji wata sassanyar murya
wata mata tayi mata sallama, da ta daga kai
ta dubi matar sai taga wata zankadediyar ce
fara sol, doguwa 'yar gayun gaske, mai
kamshi na alfarma. Gefenta kuwa wata 'yar
budrwa ce ke goye da yaro a baya, da
alama dai mai aikinta ce ke goye da danta.
Aisha farida tayi murmushi gami da amsa
mata sallamar. Ta zauna kusa da aisha
farida, sannan ta umarci mai aikinta ma
tazo ta zauna, yayin da ta dubi aisha farida
ta gaishe ta hade da tambayarta. Sai dai
fargabar da farida ke ciki ta sake karuwa,
don wannan zankadediyar matar dr
shureiim take tambayarta. Aisha farida tayi
sauri ta girgiza kai tace a'a bansan shi ba,
sai dai ki tambayi security, nasan dai duk
manyan likitoci suna ciki.
Sai matar tace ai naga kamar security din
nan bata da mutunci, bari kawai in kira shi
a waya, da zan fito daga gida munyi waya
yace min yana nan female medical ward,
naga kuma ba a bari a shiga. Ta jawo
wayarta sabuwa dal kirar blackberry ta
matso sunan dr shureim idanuwan aisha
farida na kai yayin da taci gaba da zazzare
ido tana tunane tunane kala kala daban a
ranta. Shin wannan wacece take neman
abin kaunata? Toko matarsa ce? Cikin
harshen turanci tayi masa magana tace
faridarka ce ina nan female medical ward,
an hana ni shiga. Aisha farida ta maimaita a
zuciyarta. Faridah! Faridah!! Daman yana
da wata farida bayan ni? Lallai abida tana
so ta kaini ta baro ni, domin wahala kawai
zansha babu alamar nasara a nan. Sai ta
tuna da abubuwan da abida tace cewar tayi
addua kuma tayi hakuri. Farida ce ta katse
tunanin da aisha farida keyi, ta dube ta tace
gashi nan zuwa ashe, baya ciki ya dan fita.
Aisha farida ta gyada kai tace okay! Matar
ta sake duban aisha farida tace yaya na
ganki a nan zaune, ke ba ma'aikaciya bace,
ko wani kike jira? Aisha farida tayi
murmushi tace wata matron nake jira, ta
shiga ciki aini daliba ce. Security ta hana ni
shiga. Kuma dai yau ne ake hana mu shiga
shima saboda shugaban asibitin yana
zagaye.
Haj farida tace toh shiyasa naga duk an
koro 'yan zaman jinya a waje? Alla dai Ya ba
wa kowa lafiya. Nima wallahi yarona na
kawo bashi da lafiya, kwana yayi zazzabi
kuma ga amai. Aisha farida tace
subhanallah, ko hakori ne? Haj farida tace
anya kuwa hakori ne? Bana jin hakori ne,
don ya gama hakoransa, shekarunsa fa biyu
da rabi, don kin ganshi a baya ne kamar
jariri. Ina ga canjin yanayi ne, kinsan sauron
kasar nan. Aisha farida ta gyara zama tace
daga wacce kasa kukazo? Haj farida tace
daga london, ai can nake aure. Nan da nan
jijiyoyin jikin aisha farida suka rike, ta kasa
cewa komai, babu makawa itace matar dr.
To amma sai dai in 'ya'yan nasa guda biyu
ne babbar mace ce, kuma tayi wayo don
tana amsa waya radau. Cikin sanyin murya
aisha farida ta tambaya shi kadai ne danki,
ko akwai wasu? Haj farida tayi murmushi
tace akwai yayarsu na baro ta a gida.
Tabbas matar dr ce wannan, amma Allah
yayi kyau da gayu a nan. Ai ruwa ma ba
sa'an kwando bane, ina ni ina jera kishi da
wadannan mata masu shigen kama da
matan hurul ain? Aisha farida ta fada a
ranta.
Taji gaba daya bata da sauran wani tunani,
kuma tasan shuraim yayi mata nisa. Rashin
sanin shuraim na hakika ne abida take
wannan daddagwar tana cewa sai anyi. Haj
farida ta dubi aisha tayi murmushi tace
yaya sunanki? Aisha farida tayi jim kadan,
can tace sunana farida. Wow! What a
coincidence is that? Sunanmu daya ai nima
farida sunanan. Matar ta fada yayin da
takeyin dariya, fararan hakoranta suka dau
walkiya. Aisha farida ma tayi dariya tace oh
haka ne kuma naji sanda kina waya kin fadi
sunanki. Yaya sunan yaronki? Tace rislan.
Aisha farida ta gyada kai tace rislan suna
mai dadi, yaya sunan yayarsa ta gida? Tace
sunan mamanmu ne aka saka. Aisha amma
muna kiranta da momi. Aisha farida tace
Allah Ya raya su. Haj farida tace amin.
Yawwa ga dr shuraim nan zuwa. Aisha
farida tahi wuyanta ya sage, har ba zata iya
juyawa ta dubi bangaren da ya taho ba, don
haka can gefe ta juyar da kanta har ya
karaso gabansu ya tsaya. Kamshin turaren
jikinsa mai sanyi shine ya daki hancin aisha
farida, yayin da tattausar muryrasa da
hadadden turancinsa yake ta dukan dodon
kunnuwanta a inda aka hau dambe tsakanin
zuciyarta da idanuwanta, idanu suka su juya
su kalle shi, yayin da zuciyar ke son kallon
abin da take kauna. Idanu suka rinjayi
zuciyar aisha farida taki dagowa ta kalle shi
Me yake damun dana ne? Oh my God rislan
ciwo ne ya taba min kai? Inji dr shuraim a
lokacin da yake shafa kan rislan. Haj farida
tace jiyya bamuyi bacci ba wallahi, sai naji
kamar yau in yanki ticket in juya london. Dr
shuraim yayi murmushi yace no kar ki
damu, mu nan asibitin muna da kwararrun
likitocin yara, bari in kira kawata dr
rukayya. Ya dauko hadaddiyar wayarsa kirar
blackberry ya matso sunan dr rukayya ya
fara da sallama, sannan ya gabatar da
kansa. Yace dr shuraim imran ne yake
magana, nasan baki san wannan layin nawa
ba ko don sabo ne? Dr rukayya tayi
murmushi tace ai kowa ya sanka da canje
canjen layi kullum. Ya aiki? Dr shuraim yace
alhmdlh, dama ina so in turo miki patient
dinku, sister tace farida imran yaronta bashi
da lafiya nake so ki duba shi, duk wani
taimako da ya kama kiyi musu. Dafatan dai
kina cikin asibitin? Dr rukayya tace haba
meya abin yi min magiya, kanwar ka ai
kanwata ce, to ka turo ta razo ina nan
speciality yanzu. Dr shuraim yace nagode,
gata nan zuwa. Sannan ya kashe wayar ya
mayar aljihunsa
DUK KYAN TAKALMI 2* 5
Aisha farida taji wani irin sanyi a ranta da
Allah Ya sa kanwarsa ce ba matarsa ba, sai
a lokacin kamanninsu suka bayyana. Tabbas
kamarsu daya tamkar an tsaga kara. Har
yanzu bata kallonsa ta juyar da kanta can
gefe, amma fa kunnuwanta radau a bude
tana sauraronsu. Dr shuraim ya dubi 'yar
uwarsa yayi murmushi yace kinga ni yanzu
ina tsakiyar aiki, bari in samo wacce zata
raka ku speciality don nasan baki san kan
asibitin nan ba, da sai in kwatanta miki,
kuma ma da nisa. Ya dade yana kallon aisha
farida, sai taji a jikinta kamar ana kallonta,
tana dago ido sai suka hada ido dashi, nan
da nan ta bata fuska, har da murguda baki,
ta kawar da kanta gefe, don kada ma yaga
fuskar aikenta. Shima yayi saurin dauke
idanuwansa daga kanta ya bata fuska, ya
juya ya nufi wani office ba jimawa ya fito
tare da wata daliba likita na biye dashi a
baya. Suka iso inda aisha farida ke zaune.
Haj farida kuwa sai takalo aisha farida
takeyi da hira, yayin da ita kuwa bata cikin
hayyacinta. Dr shuraim ya kade mata
hankali gaba daya ta rasa me yake
damunta, sai da ta sake ganinsa ta tabbatar
har yanzu sonsa na nan dankare a zuciyarta
sai taji haushin zuciyarta da take jawo mata
masifa iri iri.
Dr shuraim yace ga dr zainab dalibata ce
zata raka ku, kuma zata tsaya ki gama
komai, sannan ta dawo. Dr zainab farin ciki
fal a zuciyarta fara'a cike a fuskarta saboda
yau dr shuraim ya kula ta har ya zabe ta ta
raka kanwarsa, don haka ji take tafi kowa
samun shiga. Tayi sauri ta duka ta gaishe da
haj farida yayin da ta hau shafa kan rislan
tana ta faman iyayi. Tanayi tana satar kallon
dr shuraim, shi kuwa gogan abin da yafi
tsana kenan, irin wannan shishigin sai ya
fara bata fuska. Aisha farida tayi murmushi
a zuci tace a ranta wayyo zainab ina
tausaya miki indai dr shuraim ne zaki hadu
da tsagewar zuciya bama bugun zuciya ba.
Muma nan munyi mun warke. Haj farida da
mai aikinta suka mike suka dunguma suka
fara tafiya har haj farida ta wuce sai ta tuna
ba tayiwa aisha farida sallama ba, sai ta
waiwayo da sauri. Tace af kawata,
takawarata na tafi ko, sai Allah Ya kara sada
mu da alkhairi. Aisha farida ta dube ta, tayi
dan murmushi ta gyada kai. Tace yawwa sai
anjima Allah ya sadamu da alkhairi, Allah Ya
bashi lafiya. Yayin da dr shuraim ya dubi
kanwarsa ya juya ya dubi aisha farida da
alama yana mamaki kuma daga dukkan
alamu akwai alamomin tambaya a tattatre
da bakinsa. Abin da kunnen aisha farida ya
jiyo mata bayan sun juya suna tafiya shine
ya dubi kanwarsa yace a ina kika san
wannan yarinyar har ta zama kawarki, kuma
takwararki? Haj farida tayi murmushi tace a
nan na santa, yanzu ma na taba ganinta a
duniya. Dr shuraim yayi dariya ya girgiza kai
yace hmm mata, akwai kwashe kwashe,
daga dan zaman da kukayi tare shikenan
har kunsan juna, har da dogayen lanarai da
sanin sunan juna. Suna ta maganar har
sukayi nisa ta daina jiyo abin da suke cewa
Aisha farida tayi ajiyar zuciya yayin da farin
ciki ya rufeta, tasan dr shuraim yanzu ya
santa duk inda suka hadu zai shaida
fuskarta sannan zai tuna da sunanta tunda
dai ba zai mance sunan kanwarsa ba uwa
daya uba daya ba. Ko ba komai aisha farida
taci riba tunda har ya damu yake yi wa
kanwarsa tammbayoyi akanta. Ta fara Allah
Allah a tashi daga asibiti taje gida ta bawa
abida labrin cigaban da aka fara
samu......bata gama tunanin da takeyi ba
taji karan takalmi ana tahowa a baranda, ko
da ta daga ido dr shuraim imran ta hango
yana tahowa. Kallo daya tayi masa sai tayi
sauri ta kawar da kai gefe, sai da ya wuce
ta sai ta sake juyar da kai wani bangaren ta
rantse shi dinne dai ba zata kalla ba. Abin
mamaki sai taga ya wuce yana kallonta har
da waiwaye. Don son ya gasgata abun da
yake gani, sai ya dawo ya sake wucewa ta
gabanta, wannan karon ma can gefe ta
muskuta bayan kan ma har da jikinta ta juya
ta nuno masa keya. Ya fice ya sake
dawowa, sai yaga ta juya daya bangaren
gaba dayanta. Tabbas ya shaida dashi take
ba zata kalle shi ba. Baifi minti uku da
shiga ba dakin marasa lafiya ba, sai gashi ya
fito a karo na uku yana ta waya, amma fa
yanayi yana duban aisha farida donya ga
abun da zata yi. Sai tayi saurin dangwafar