Showing 15001 words to 18000 words out of 99740 words
Chapter 6 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf
gawarsu aka kwakulo. Tun daga
lokacin idan naga mutum akan acaba sai kaga
na bar abun da nakeyi na rike kai, ina taya shi
da addua har sai na daina hangensu.
Musamman mace sai inji kamar in fasa ihu ince
ga motarta nan zo ki hau na tafi da kafa.
Wadanne irin maza ne zasu bar matarsu taje
ta hau acaba, ko bashi da mota ai sai ya bata
kudin drop har inda zata je a mota. Sai a
lokacin na tabbatr da dalilin da yasa yake
hararata rannan ashe, don na sauko daga kan
acaba ne. Ya tayar da sallah, dr lukman ya
miko min file biyu da wanda nazo dashi da
wanda yayi cike cike yace in mayar mata ince
bashi ba, koren file din zata bayar. Na durkusa
na karba na fito da sauri, yayin da zuciyata ta
cika da murna saboda yau taga abinda take
muradi. Sai ya sake burge ni dana ga yana
sallah, naji dadi danaji dalilin hararar da yayi
min rannan ba tsana ta yayi ba. Sai na fara
tunanin hanyar da zanbi in shiga harkarsa ba
tare da yayi min wulkanci ba. Naci sa'a kuwa
ina zuwa nayi mata bayani sai ta miko min
koren file din da yace ta bani in kai masa. Na
taho hanya ina farin ciki hade da fargabar abun
da zanje in tarar. Na isa ofishin sai faduwar
gaban da nake ji ta karu, na fara karanta
ADDUAR WANDA YAJI TSORON MUTANE
"Allahummakfinihim bimaa shi'ita" (Ya Allah Ka
isar mini dasu da abin da kaso). Ina tura kai
sai nayi sallama. Dr lukaman ne ya amsa, har
yanzu gogan nawa yana kan abin sallah ya idar
amma yana jan carbi. Na dago ido na dube shi
a hankali, sai muka hada ido ni dashi, bansan
wanda ya fara kawar da kai gefe ba. Na matsa
lungu ina jiran dr lukman ya gama dubawa sai
da na tabbatar lungun da na shige ko ya daga
ido ba zai ganni ba. Na nutsu kai kace a gaban
sarki nake, yadda nake sanda kai kace da
kayan sata aka kamani, za'a yanke min
hukunci. Wayar dr shuraim imran ce take ruri,
kidan ringing tone din yana tashi a hankali,
wakar soyayya ce ta celen dion mai taken come
bake to me, sai ya danna amsa. Kalmar da ya
fara ambato a cikin harshen turanci ita ta
gigitani, tasa na dimauce sai na tsinci kaina
har da kwalla mai radadin fita saboda kishi.
Daga ji ba sai an fada min ba da matarsa yake
magana, wacce yake tsananin so da kauna fiye
da kowacce 'ya mace a duniya. Tunda nake a
rayuwata ban taba jin namijin bahaushe da ya
fadawa matarsa wannan kalma, ko da yake ni
'yar gargajiyace na tashi cikin 'yan gargajiya
tsakanina da matansu sai ke zo nan, dauko,
dafa, wanke, goge. Kullum sai hantara dube ki
ballagaza, kazama, kwadayayyiya. Haka na
saba ji tun tashina tsakanin miji da matarsa.
Amma dr shuraim imran yace da abar
kaunarsa, salam my dear, my heart, my life
how are you and how is your trip? Hope cool.
Duk da ban jiyo abinda zata fada ba itama da
daddadar kalma ta mayar masa. Ya juye
harshe sai turanci yake zazzagowa ya tambaya
kuna ina yanzu? Sai ta bashi amsa, banji
amsar ba sai yace ok kun bar london yanzu
kuna amsterdam? Awa nawa zaku yi transit
din? Ta fada masa, sai yace karfe goma dai dai
zaku iso kano, ni kuma karfe tara a airport zata
yi min da izinin Ubangiji. Ina kewarki, ina
babyna? Can sai naji ya fara magana cikin
muryar yara yana yiwa yaro wasa, sai na
tabbatar 'yarsa ce itama da turancin yake mata
magana. Kalmar da ya fada ta karshe daga ita
ya kashe waya itace "I love u baby, I miss u
too, I am eager to see ur beautiful face. Take
care bye". Na dinga dauki ba dadi da zuciyata
don so take ta tsinko fado kasa ta ragargaje
don tashin hankalin da ta shiga. Dr lukman ya
dube shi yayi dariya yace madam ce? Ya
lumshe ido tace madam ce ita da baby sun
taho yanzu suna amsterdam sun baro london.
Kaji matar da take makaranta shine ta bar
karatunta ta biyo ni. Dr lukman yace ah da
gaskiyarta, yaushe zata zauna a can mijinta
yana nan? Dr shureim imran yace toh ai
matsalar ba zata iya zaman bane a nan, tana
yin sati biyu a daddafe zata fara magiya inzo
mu koma london, ita ba ta zauna tayi karatunta
ba a can, ita bata bar yarinya tayi karatunta
ba. Dr lukman yace ai da ta dinga barin
yarinyar a gidan iyayenta ba suma a london din
ba gidansu yake? Sai iyayenta su rike muku
'yar kai da ita ku karaci walagiginku tsakanin
london da Nigeria. Dr shureim imran yayi dariya
yace toh ai yarinyar harta fi uwar damuwa ai
ita tace take so uwar tace sai an kawo ta ta
ganni, sai tasa uwar tayi min waya fiye da sau
goma a rana ace min ga baby tana kuka, wai
tana son magana dani. Ina daukar wayar kasan
abinda zata ce min? Daddy I miss you, sai ta
kashe waya shikenan. Su dukka suka kwashe
da dariya, dr lukman yace gaskiya ku canza
tsari, ko kai ka hakura da zaman nigeria ka
koma can ku zauna, daman a can kuka hadu.
Dr shureim imran ya rike baki yace cafdi! Ai ba
zai yiwu ba, ka manta halin babana ai ba zai
bari inyi aiki a can ba, kasan shi da kishin
kasar nan, babu dansa da bai dawo nigeria ba
yanzu. Karatu kadai ya amince muje muyi, aiki
kuwa dole mu dawo mu bautawa kasarmu, mu
taimaki alummar hausa, fulani, musulmai 'yan
uwanmu, bai damu da yawan albashin can ba.
Dr lukman yace haka ka fada min, gaskiya ya
burge ni. Ina ma za'a sami dattijan arewa
irinsa masu kishin YARENSU DA ADDININSU da
kasar nan, da kasar nan ta gyaru. Dr shureinm
yace ai kuwa sanda zanyi aure hana ni yaso yi,
dana dage ina so ni da ita ya shimfida mana
sharudda masu tsauri. Tace taji ta gani zata bi
duk abinda yace. Sharadi na farko da ya
shimfida mana shine dole ta biyo ni nigeria mu
zauna dindindin idan munje london hutu muka
yi da zarar hutu ya kare mu dawo. Sannan dole
ta bar shigar dan siket da wando ta saka
atamfa ko leshi da mayafi don shi ya tsani
english wears. Tace ta yarda yanzu ma zaman
da ya bari tana yi na dan shekaru ne saboda
karatu, ta kusa kare makarantar da zarar ta
kare yace ta hado kayanta kakaf ta kaura kasar
nan, dole anan kasar zatayi aiki ba a can ba.
Tags :
Itama kuma bata iya zaman kasar na, tsoron
sauro takeyi, ko kuda ta gani sai ta hau kuka
ta tashi da gudu. Baby kuwa tana burge ni
babu abinda ba taci, kuma babu in da bata
shiga ta zauna lafiya a kasar nan, bata
damuwa da duk wani canji kuma itama a can
aka haifeta kamar yadda aka haifi uwar a can.
Dr lukman yayi dariya yace ah wannan ita ta
biyo kakanta alhaji, komansu na gargajiya ,
babu zancen cewa ma kai ta biyo, don kai ma
bature ne. Dr shureim imran yace ai kuwa baka
san bature ba, ai ni ko a gidanmu sun san nina
biyo alhaji sak, saboda ko wajen abinci bana
cin su shinkafa, taliya , cake, macaroni da
sauransu. Idan aka ga naci irin wadannan toh
a london nake, ko abj don babu yadda zanyi.
Nifa har kwano nake bawa direbana ya dauka
ya tafi cikin gari unguwar su wani abokina
neman danwake, dambu, ko gurasa mai
kulikuli. Dr lukman ya kwace da dariya yace har
da yawon neman dambu kake sawa ayi? Lallai
dagaske kake. Ni kuma abinda ba'aci kenan a
gidana ko tuwo zasu yi sai dai suyi min
abincina daban, haba ai an wuce wannan
lokacin ina yaro in nadi dambu da tuwo, yanzu
da wayona da 'yan canjina a aljihi inci dambu?
Ko ba haka ba 'yar boko, har yanzu kina cin
dambu? Ya tambayeni, sai nayi sauri na dubi
dodona dr shuriem, domin shi nake tsoro.
Gogan nawa sai yayi dif bai sake magana ba,
yaji an dako dani a zancensu. Jikina ya sake
yin sanyi, nayi murmushi nace bana cin dambu
nima. Dr lukman yace yawwa ashe bani kadai
ne na gaji da cin tuwo ba, muna da yawa.
Daga lokacin hirar ya koma ni da dr lukman
kadai, dr shureim yaki tsoma baki. Dr lukman
yace dani ke 'yar gidan matron maryam ce,
naga kuna kama? Wannan karon ne ma naga
dr shureim ya dubeni kasa kasa, sai yayi wuf
ya mike tsaye yana nade abin sallah, ya linke
ya ajiye sannan ya shiga daura neck tie a
wuya, ya saka bakar suit dinsa. Cikin sanyi jiki
nace a'a ni ba 'yarta bace, malamata ce kawai,
muna shiri sosai. Dr lukman yaci gaba da
rubutu yana magana yace ke ba 'yar gezawa
bace kenan. Tunda matron maryam 'yar
gezawa ce. Nayi dariya nace a'a ni ba 'yar
kano nace ba ma, ni 'yar shagamu ce. Sai ya
tsaya da rubutun ya dube ni ta cikin gilashinsa
yace da gaske kike, ko kanwar yahaya umar
ce? Babban abokina ne, ajinmu daya a
sakandiren da muka yi a yobe. Sai nayi caraf
nace yayana ne, babanmu daya. Sai ya fasa
rubutun ya ajiye biro yace yanzu dan Allah
yahaya umar yayanki ne? Na gyada kai nace
yayana ne. Yace llallai kuwa naga kama, kina
cewa ke 'yar shagamu ce sai naga fuskarku iri
daya daman tun sanda na fara ganinki na rasa
wanda kika min kama. Yana ina yanzu? Yana
nan lagos yana aiki a tasha dan union ne. Yace
subhanallah! Yanzu duk kokarin nan na yahaya
umar bai cigaba da karatu ba a aikin tasha ya
kare? Kinsan fa ni dashi muka kudiri niyyar sai
munyi karatun likita. Tunda muka gama
makaranta a. Yobe na dai ganinsa, naje
gidansu a nan yobe nemansa ban same shi ba
aka ce ya koma garin babansu shagamu, ashe
dangin mahaifiyarsa ne a yobe ko? Shikenan
rabuwarmu dashi, sai dai duk sanda aka
ambaci shagamu sai na tuno shi, saboda dan
shagamu muke ce masa. Mun shaku sosai
dakinmu daya, ajinmu daya. Nayi murmushi
nace eh dangin mahaifiyarsa ne suka rike shi a
yobe, tun yana yaro, daya gama sakandire sai
ya koma gida shagamu, bai cigaba da karatu
ba kuma. Ina rufe bakin dr shureim ya shirya
tsafa, ya dauki jakar laptop dinsa ya dubi
abokinsa dr lukman. Yace ni na tafi sai kuma
gobe. Dr lukman yace aini ma na tashi, ka jira
ni yarinyar nan zan sallama kawai, ka ga ashe
ma ni kanwata ce, haba tun sanda nake
ganinta nake ganin kamar na san fuskar, ashe
kanwar abokina ne childhood frnd yahaya umar.
Ya tabe baki yace a'a ni dai nayi gaba, sai ka
taho kawai. Ya fice ya bar mu. Bai ma bada
amsar labarin da ya bashi ba saboda a kaina
ne ba zai tsoma baki ba, sai na fara dankarawa
zuciyata zagi akan ko taki ko taso sai ta rabu
da son wannan marar mutuncin. Me yayi zafi?
Dan kawai Allah yayi masa baiwa kala kala,
yayi masa farin jini, ana sonsa sai ya dinga
wulakanci, shi waye? Namiji ne fa kamar
kowanne namiji, gasu nan birjik a titi suna bin
mace tana musu yanga kafin ma ta kula su.
Suna 'yar murya suna yi mata wahala, don ta
saurare su. Haka na dinga kushe shi a zuciyata
don in samu sukuni, duk yadda zanbi in raba
zuciyata da sonsa bi nake yi don shine samun
saukina. Dr lukman ya rufe file ya bani,
tambayi lambar wayar abokinsa yayana yahaya.
Nace bani da waya, amma zan karbo masa
lambar a wajen yayana hussaini gobe zan kawo
masa. Sai yayi mamaki don nace bani da waya,
sai ya tambaye ni, yace faduwa wayar taki tayi
ne? Kuma baki hadda ce lambarsa ba? Na
amsa da eh faduwa tayi. Saboda sauri nake in
fice daga ofishin saboda abin kaunata baya
nan, daman saboda shi naji tsayuwar da nake
yi bata isheni ba tun dazu, yana barin ofishin
sai naji duk ofis din ya gindure ni. So nake in
fito inga in daya nufa, kuma da wacce irin mota
yazo yau. Nayi wa dr lukman sallama na fito
bakin barandar da sauri, na waiga kowacce
kusurwa sai ban ganshi ba, ko alamunsa babu,
sai naji haushin dr lukman ya rufe ni, da bai
bari na fito da wuri ba, gashi nan har ya tafi.
Sai zuciyata tace ke da kike yi min fada in rabu
dashi, ina ke ina takaicin don baki gan shi ba?
Nayi ajiyar zuciya mai karfi naci gaba da tafiya
maimakon inbi doguwar baranda sai na sauko
na dinga kutsawa ta kasa cikin motoci. Ban sa
ran ganinsa ba ko kadan amma dai nasan dole
ta nan ya bi, idan zai dauki motarsa ko sawun
takalmansa na taka ai naji sa'ida a raina.
Kamar daga sama naji wata murya mai shige
da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa
shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na
sake fada miki don Allah ki daina damuna da
waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na,
bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada
mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki
ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne
haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni
har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika
nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako
ya bani? A wanne dalile zakiyi min sayayya ki
kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa
tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na
dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke
a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai
ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana
cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta
magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har
ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na
kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba.
Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji
dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce
hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado
kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na
dauko mata na mika mata, sai ta dube ni
jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min
thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr
shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle
ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye
kyam yana dubana. Na harare shi sama da
kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na
bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai
ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina,
ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa
kaina wulakacin da yayi min da sauran
wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa.
Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu
sabida na san ba zan same shi ba kamar
sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu
same shi ba. Kamar daga sama naji wata
murya mai shige da tasa daga gefena, abin da
yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na
fada miki na sake fada miki don Allah ki daina
damuna da waya cikin dare, yau matata zata
zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala.
Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga
aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa.
Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A
asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina?
Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai
gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi
min sayayya ki kai min gida? Zaki jefa
rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata,
da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina
kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya
bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa
a bace yake magana cikin matsanancin fushi,
sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da
fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin
uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan
sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace
shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a
fusace tana sharce hawaye, yayin da farin
gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita.
Na karaso da sauri na dauko mata na mika
mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta
karba gami da ce min thank u very much. Ta
wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake
bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar
yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na
harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na
kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai
daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na
san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika
tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi
min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana
masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya
daina hada mu sabida na san ba zan same shi
ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau
basu same shi ba. Da na koma gida, dare yayi
sai bacci ya gagare ni, na shifa zulumi da
fargabar kallon da nyi masa. Naji kwata kwata
ban kyauta ba, tausayinsa ya rufe ni, yayin da
sabon sonsa ya tsatsafo daga cikin zuciyata.
Na dora hannu aka ina fadinn na kashe kaina
da kaina, me ya kaini yi masa wulakanci ni da
nake addua, ina saka ran zan same shi
watarana? Na shiga adduar Allah Ya sa baiji
haushina ba. Gari na wayewa na shiga
shiryawa, na tsaya na tsarawa fusakata
kwalliya yadda zanyi kyau sosai. Nayi sauri na
tare yaya hussaini zai fita