Showing 21001 words to 24000 words out of 99740 words

Chapter 8 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf

ESHAT   

23 Mar 2025

5444

fara,
sai ummi ta zaro dari biyu zata mika masa na
rike hannunta nace ba sai an bincika min ba
malam zan fada da bakina. Na koro masa
bayani tas, sai yayi dariya ya kyakyata yace
wannan karamin aiki ne a wajena, idan har zaki
sayi kayan aiki na baki kwana biyu inda dr
shureim imran ne kim gama samunsa. Ina jin
haka sai naji farin ciki ya lullube ni nayi dariya,
na tambaye shi me dame za a siya? Sai yayi
min zancen abubuwa daban daban, wasu na
sansu wasu ban sansu ba. Aka hada kudin ya
kama naira dubu ashirin da daya. Sai na dafe
kirji nace malam bani da kudi ko zaka yi min
bashi idan komai ya kankama sai in biya? Ya
dubi ummi cike da bacin rai yace ina kika samo
min wannan yarinyar? Baki fada mata dokar
aikina bane? Sabon shiga ce ko? Toh ni bana
fadar farashi a nemi ragi balle ace inyi a bashi,
a cikin kudin nan babu sisi nawa, duk na
rauhanai ne. Ummi tace ayi hakuri malam,
laifina ne ban fada mata dokokinka ba zamu
dawo gobe tare zamu nemo kudin mu kawo.
Mun goda. Banyi godiya ba na kada kai na fito,
hankalina ya gama tashi. Muna fita kofar gida
ummi ta hau yi min fada tana cewa me yasa
ban bari anyi min bincike ba inji bayani dalla
dalla ba, sannan me yasa nace ayi min aiki
bashi alhali tun a kan hanya na baki labarinsa?
Nace to bani da kudi ko naira hamsin ta kaina
bani da ita. Me zance? Tace ki sayar da
kadararki mana. Nace ai bani da ko barimar
gwal balle dan kunne. Ta tabe baki tace ni dai
shawarar da zan baki itace kije kisan abinyi
don nima nan da kika ganni bashi zanje in ciyo
in kai masa idan aiki yaci da kansa zai baki
kudi kije ki biya. Malamin nan fa aikinsa kamar
yankan wuka, sha yanzu magani yanzu. Kije
kiyi tunani zuwa gobe ki samo kudi, kizo mu
kai don ni ma daga nan gari zan shiga neman
bashi. Ta bani kudin mota mukayi sallama na
shiga motar unguwarmu, ita kuma ta shiga
motar dawanau ban san inda ta nufa ba. Ina

zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da
kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani
yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka
zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce
dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida
na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa
inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya
koma wajen inda zan samo rancen kudi in
kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da
batsewarta babu matar da zata iya fitar da
dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da
yamma na shirya na fita neman kudi gida gida,
da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce
kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai
yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni
lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa
cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da
lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a
asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya
dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami
dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan
samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda
yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya
shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi
kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare.
Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min
abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo
abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa
guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da
dubu uku har da doguwar wasika yana mai
bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici
gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min
kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba
na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan
in kai. Ina zaune a mota tamkar gunki ina
tunani, sai da kondasta yyayi ta magana
sannan na gane dani yake, na mika masa kudin
mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na
manta har aka wuce dani, sannan na ankara
nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga
gida a cakude, narasa inda zan saka raina,
tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan
samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin

unguwar nan da batsewarta babu matar da
zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye
saboda talauci. Da yamma na shirya na fita
neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen
dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da
musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar
mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni
a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar
kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar
karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana
neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace
aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a
yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan
anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a
bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza
kai nace babu zance bashi kuma dole in hada
kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida
zai aiko yaro ya kawo min abin da ya
sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya
samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi
ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku
har da doguwar wasika yana mai bani hakuri
abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da
nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman
soyayya ko gama karantawa banyi ba na
yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in
kai. Uwani uwar adashe ita kadai na tabbatr
zan iya samun rancen kudi a wajenta ko nawa
ne saboda itace naga koda yaushe mata suna
aiko mata da zubin kudin adashe, ina hango
shigarsu da fitarsu daga windon dakina domin
dakinta na kusa da dakina. Ina idar da sallar
magriba na tabbatar abida tana daki tana
wuridi ba zata fito tsakar gida ba, sai tayi
sallar ishai kamar yadda ta saba. Sai nayi
sanda na fito dakina na fada dakin uwani, sai
tayi mamakin ganina a wannan lokaci, naci
sa'a maigidanta bai dawo ba. Ta saka fitilar
kwai a gaba tana kirga kudi kashi kashi. Farin
ciki ya rufe ni da naga kudin nan sai na shiga
marairaice mata inayi mata dadin baki cewar
ta ranta min dubu goma sha bakwai zan biya
ta gobe da yamma. Ta tsorata matuka har da

dafe kirji ta tambaye ni, me zakiyi da kudi
haka? Na shaida mata kawata ce zata haihu a
asibitinmu ance ba zata iya haihuwa da kanta
ba sai an yi mata tiyata. Ga mijinta ba ya gari
yana lagos. Amma ya sako kudin ta banki, to
kasancewar asabar ce babu banki, lahadi ma
babu aiki ba za a iya fitar da kudin ba, sai
ranar litinin. Shine tace in ranto mata zuwa
litinin zata biya. Uwani tace a'a aisha farida
kinsan halin mutane kayi musu rana suyi ma
mutum dare. Ki zo ki taimake su suki biya, ko
kuma ni in taimake ki, kiki taimakona. Kinsan
dai kudin nan da kika gani kudin cizo ne, bana
kashewa bane da masu shi. Gobe haj rabi ce
zata dauki adashen nan dubu talatin. Mace
dayace bilki bata saka mata ba, na aika tace
gobe zata aiko yana aikowa sai in hada in
aikawa haj rabi daukarta. Yanzu idan na baki
aka zo aka sami matsala yaya zanyi? Kinsan
bani dashi, lada suke bani duk wata dubu daya
dan tarawar da nakeyi. Niko ikon sgiga
adashen ma bani dashi dan bani dashi. Nace
na sani uwani, idan Allah Ya yarda babu
matsala, ranar litinin da sassafe zanje bankin
da kaina in karbo miki. Tace to shikenan gashi
nan. Ta kirgo dubu goma sha bakwai tabani, na
karba na kirga sun cika cas, nayi godiya.
Sannan na roki arzikin ta rufa min asiri kada ta
fadawa kowa ko abida kada taji, salin alin zan
dawo mata da kudinta. Tayi min alkawari babu
wanda zaiji. Na shiga daki na hada kan kudina
na adana a jaka. Naira dubu ashirin. Farin ciki
fal a zuciyata, har sai da abida ta fuskanci
haka a daren, a da bana iya cin abinci sosai,
amma a daren taga har da kari nayi. Da bana
son magana sai taji na isheta da labari a ranar.
Ta san na daina fara'a amma a ranar na ishe
ta da kyakyata daria har da wake wake.
Saboda na riga na sami kudin da bana tantama
na gama samun dr shureim imran. Gari na
wayewa na shiga tunanin karyar da zan
shiryawa yaya hussaini wacce zai bari in fice,
domin ranar lahadi ce babu aiki, kuma kulle

yake min. Na shirya tsaf na kira abida gefe na
shirga mata karyar cewa zanje asibiti yau ma,
ana yiwa wata nurse bikin gama aiki, tayi retire
ance kowa sai yaje kuma da kayan gida. Na
santa da wayo ta san yadda zata fadawa
maigidanta ya aminta da ita. Ta shiga daki ta
tsaro shi sai ga ta da dari biyu kudin babur.
Naji tausayinsu ya kama ni saboda nafi su kudi
yanzu, da sun san kudin da yake jikina da basu
rabu da dari biyunsu ba. Nayi godiya na karbe
na tafi, abida ta rakani har zaure tana yi min
fatan alkairi. Tana jaddada min in ragowa
'ya'yanta kayan walima. Na amsa mata da zan
rago musu da yawa ma kuwa. Ina fita na hau
acaba sai gidan ummi kawata. Da yake sassafe
ne mijinta ma bai fita ba yana daki, tajani
zuwa falonta muka zauna muna magana cikin
sirri. Ta tambaya yaya ake ciki, na samo kudin
kuwa? Na ciro mata himilin kudin daga jakata
sai ta rike baki tace lallai kinyi kokari, nima na
hada dubu goma sha biyar bari inje inyi masa
karya inzo mu tafi. Yau lahadi ba zai fita da
wuri ba, gara muyi tafiyarmu. Ta shiga daki ba
dadewa ta fito a shirye da goyonta muka nufi
kofar fita, har mun kai zaure faccalarta ta biyo
mu da sauri. Tana cewa ummi unguwa zakije
baki fada min ba mu fita tare? Yau ne sunan
mariya 'yar jummai, ki tsaya in shirya mu fita
gaba daya mana. Ummi ta doka mata harara
tace dani aisha faida da Allah muje, dole ne sai
mun fita tare. Myka kada kai muka fice muka
bar ta a tsaye tana kallonmu har abin tausayi.
Muna fita nace da ita haba ummi ya za ayi kiyi
mata wulakanci? Ai sai ki bata amsa mai dadi
ko ba kya so tabimu. Ummi ta tabe tace ai na
daina raga mata tunda bincike ya nuna bata
kaunata. Ni da mutunci da ita har abada. Nace
to amma ai maganar malamai ce, babu tabbas
zaiyiwu kirkira yayi. Ta harare ni tace lallai kina
wasa da aikin malamin nan. Idan yayi miki
duba tabbas zaki ga komai a hankali daya
bayan daya. In bai gani ba zai fada ne ko da
ya taba ambato sunanta in ba yanzu ba, kuma

nima na lura tun sanda muka sayi generator ta
canja min, taga mun cigaba a rayuwa. DUK
KYAN TAKALMI 11 Bansake magana ba dai har
muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara
washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka
zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin
bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai
da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban
daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na
harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu
daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita
ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta
tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba,
goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu
kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin
komai zai daidai ta. Muka fito muna murna,
ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in
kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta
koma gidanta, na sake shirgawa abida wata
karyar tunda ban taho da kayan walima ba,
naso in siyo musu lemo da biskit amma na
juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na
karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban
damu da himilin bashin dake kaina ba, burina
aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana.
Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin
walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga
barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba
irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a
gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare-
dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna
tafe muna hirar soyayya. Na dade ina
tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da
mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa
zuciyata na sami dr shureim na gama kamar
yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara
saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na
shirya na karbi kudin babur a wajen abida.
Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita
ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta
tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga
banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta
kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in

aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan
aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku
na fara zullumin inda zan nemo wadannan
makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame
kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina
kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na
dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti
naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda
ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara
bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an
tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko
ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna
shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi
da dr lukman suna fitowa medical students
suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya
(ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai
naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba
murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr
lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa
yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana
biyu, rannan har yahaya umar yace in baki
waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya
nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a
wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne
sanda yake magana, har yakai barandar waje
banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake
bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe.
Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen
amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da
dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da
aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar
gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina
wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa
kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu
zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a
gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace
wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo
a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don
haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata
jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata
muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace
da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin
ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in

karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a
ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo
har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na
fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar
masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya
makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko
kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta
min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa
haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan
kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata
karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama
ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi
fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba.
Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na
shiga gidan mu har sai da abida ta shiga
damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta
tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan
naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da
kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji
sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa
makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na
wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani
ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan
zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi
turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce
abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa
yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan
bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar
kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa
sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce
zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr
lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce.
Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin
so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin
yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo
tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai
dai wannan abincin bana lasa bane, yafi
karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya
yana kamshi amma aka zazzaga masa guba
kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya
wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe
shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga
bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na

amshi wata galleliyar harara daga gareshi.
Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli
ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda
nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login