Showing 30001 words to 33000 words out of 99740 words

Chapter 11 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf

Advertisement

ESHAT   

23 Mar 2025

5601

da
na san abinda zance mata ba. Ta sakke kallona
tace da ban ganki ba yanzu da kin jawo min
masifa yau, saboda yanzun nan yayanki ya
shigo ko minti biyar baiyi da shigowa ba, ya
shigo da ciwo a kafarsa sun fadi akan babur
shine yace in taso ki, ki rubuta masa allura ko
maganin da zai sha ko ki dauko akwatin
taimakon gaggawa (first aid box) ki zo kiyi
masa dressing. Na kasa ce masa bakya nan,
shine na shigo nan ina tunanin abin da zance
masa. Ina kika shiga kika sa hankalina ya tashi
ko abincin dare banci ba? Me yake faruwa
tsakaninki da uwani tayi ta zuwa nemanki
ranta a bace tunda rana? Na zazzare ido nace
me tace miki? Abida ta girgiza tace nayi nayi
ta fada min dalilin nemanki din da takeyi, sai
tace inkin dawo in tambayeki ita ba zata fa.
Ranta fa a bace har zage zage nake jiyowa

tanayi daga dakinki. Ke kuwa aisha farida me
ya hadaki dasu uwani ke da ba a zama a yi
gulmar wani dake, me ya kai ki tsoma baki a
maganarsu? Nasan wata gulma suka hado aka
ce dake a ciki, to ni shawarar da zan baki gobe
da sassafe kafin ki fita kije ki samu uwani ku
sulhunta, idan kinsan kin fada ki basu hakuri,
idan baki fada ba ki wanke kanki tun kafin
yayanki yaji abinda yake faruwa yaci miki
mutunci, kinsan halinsa. Duk kin susuce a
kwanakin nan kin canja halinki sai kiya ta nuku
nuku kamar mara gaskiya. Nayi shiru ina
sauraronta yayin da na cire kayan makaranta
na saka doguwar rigar baccina na saka katon
hijabi na dauko 'yar akwati na wuce gaba, tana
tsaye tana kallona cike da mamaki da takaici.
Nayi sallama a kofar dakinsu, yayi min izini na
shiga, na durkusa na gaishe shi yayin da ya
miko min kafarsa naga ciwon nayi masa sannu
da adduar Allah Ya kiyaye gaba. Sannan na
bude akwatin na shiga aikin saka iodine da
auduga. Ita kuwa abida tana can tana kinkimar
'ya'yanta daya bayan tana kai su fitsari. Naga
gama masa yayi min godiya na fito. Har yanzu
abida na dakina tana jirana bata gama jero min
tambayoyin da suka cika zuciyarta dam! Ta
dube ni ta yatsune fuska tace baki fada min ba
fa in da kika je ko daman kinsan da maganar
su uwani shiyasa baki dawo gida da wuri ba?
Na bata rai na turbune fuska nace ni ba
wannan bane ya tsayar dani, bayan mun tashi
daga asibiti aka ce mu dawo za'ayi mana
darasi daga karfe hudu zuwa shida, wani sabin
likta ne zai gabatar da wata sabuwar cuta
shine naga ba zan iya dawowa gida ba in sake
komawa da yamma ba, sai nabi khadija sani
gidansu da yamma muka koma, bamu baro
asibiti ba sai da karfe bakwai ana sallar
magriba, tace inzo gidansu idan nayi sallah sai
in wuce. Shine kuma muka zauna muna hira
bansan dare yayi haka ba. Abida ta tabe baki
da alama ba ta yadda da bayanai na ba. Ta
sake dubana tace aisha farida me ya hadaki da

musbahu kuma shima ya dinga aiko wani yaro
da wasika, zuwansa biyu. Nayi nayi ya bayar a
ajiye mike yace a'a, ance hannu da hannu zai
baki. Sai na sake gigivewa na hau kame kame
nace musbahu kuma? Meye hadina dashi? To
ina jin bani aisha faridar ba. Abida tayi
murmushin takaici tace kila na fara zama
kurma har a ambaci aisha farida inji ba daidai
ba. Babu abinda zance miki tunda boye boye
kike yi min tun yanzu. Sai dai kiyi hankali da
mutane, ki kuskuri bin shawarar batattun
kawaye, ki rike mairaici da talaucinki. Ta juya
ta fice ta rufo mana kofa. Na sulale na kwanta
na dora hannu aka ina juye juye, sai dai ban
fasa karanto innalillahi wainna ilaihir rajiun ba.
Yadda naga rana haka naga dare, barci ya
gagareni. Fargaba da tunanin haduwata dasu
uwani ta gallebe ni. Haka na kwana ban rintsa
ba saboda tashin hankali, don haka da asuba
kiran sallar farko na mike na shiga bandaki
nayi wanka, duk da sanyin ruwan ban damu da
saina dumama ba, na fito nayi sallar asuba na
kakaba kayan makaranta. Na dauki jakata na
dauko biro da takarda na rubutawa abida
wasika na ajiye takardar a bude akan
tabarmata yadda zata gani daga shigowarta.
Na fita daga dakin ina sanda tamkar barauniya
nayi sauri na fice, da yake kofar gidan a bude
take maza masu zuwa masallaci sun bude. Na
rufe fuskata saboda kada inci karo da mazan
gidanmu, duk da banji motsin fitowar yayana
ba, daga dukkan alamu kafar ta matsa masa
da ciwo tunda bai fito sallar asuba ba, dan
baya fashi in dai lafiyarsa kalau. Sai nayi ta
tafiya da kafata sabida rashin babura
kasancewar gari bai waye ba duku duku ne. Na
dade ina takawa da kafata sannan Allah Ya
jeho min mai babur na hau, mun dade da fara
tafiya ba tare da nasan inda zance ya kaini ba.
Ya sake tambayata malama ina zan kai ki? Da
farko nace masa asibitin aminu kano, har
munyi nisa na canza shawara nace ya kaini
jakara, umguwarsu ummi wato gidan iyayenta.

Muka isa kofar gidan na sauka daga kan acaba
sannan na biya shi kudinsa. Abinka da cikin
gari 'yan gargajiya basu san baccin safe ba
kowa ya tashi ya shiga safgoginsa. Mai kosai
ta ta fara suya, masu waina suna danawa.
Haka masu koko da masu shayi da biredi sun
fara tafasawa. Duk inda ka waiga yara ne
dauke da 'yan kwanuka a kansu an aiko su
sayan abin karin kumalllo. Na shiga cikin
gidansu ummi cike da fargabar abinda zanje in
tarar, ummin na iske a tsakar gida ita kadai ta
saka buta a gaba da alama alwalla za tayi,
tunani da damuwa sun hana ta sukuni. Ta
buga tagumi kamar mai tunani yayin da
idanuwanta sukayi luhu luhu. Tayi matukar
firgita data daga ido ta dubeni , ta cika da
mamakin ganina a daidai wannan lokacin. Ta
fada cikin firgici aisha umar lafiya? Sai na fara
zubar da hawaye shar shar shar daga
idanuwana. Ta mike tsaye da sauri taja
hannuna zuwa dakin da take kwana, a cike
yake da yara daga dukkan alamu kannenta ne,
yara 'yan kuci kuci da masu dan wayo.
Kowannensu barci yake da munshari yayi da
zarnin fitsarinsu da warin daudar jikinsu suka
daki hancina. Kamar inyi amai, na dai daure na
zauna akan wata dakwalkwalalliy ar katifa da
ummin take kwana don naga 'yarta a shimfide
a gefe. Anan tace in zauna bari taje tayi alwala
tayi salla sai tazo mu zauna. Kallonta kawai
nakeyi tamkar gunki na kasa magana, na dubi
yaran da suke linkaya a cikin fitsari babu
abinda ya dame su. Naji dama nice su nake
linkaya a cikin fitsarin nan da irin wannan
rayuwa da na jefe kaina. Ba jimawa ummi ta
shigo sanye da hijabi da alama ta idar da
sallah ko addua batayi ba sabida rashin
mutuswar dake tattare da ita. A firgice ta shigo
tana sauri kamar zata ci da kai, ta goya 'yarta
duk da himilin fitsarin da ta ci a napkin, zarni
kwar. Tace in taso mu tafi gidan malam. Na
mike da sauri muka fice ba tare da ta leka
dakin mahaifiyarta tayi mata sallama ba. Tafiya

muke fankam fankam tamkar fatake, muna tafe
muna tayar da kura kamar shanu, mu dukanmu
hankalinmu a tashe. Na juya na dube ta nace
ummi malamin nan kuwa yana da gaskiya?
Nifa har yanzu banga komai ba. Ummi ta tabe
baki tace uhmm ke dai bari. Ai shiyasa nake so
muje mu ritsa shi kafin ya gudu, macucin
banza. Kinsan mijina ya sake ni kuwa? Korar
kare yayi min fa. Na zabura na dafe kirji nace
au daman kinsan macuci ne kika kaini wurinsa.
Tace ke dai muje muji abinda zai ce mana. Na
fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun.
Allah ba Ya dorawa bawanSa abinda ba zai iya
ba sai dai bawa ya dorawa kansa. Ina zan
sami himilin kudin da na ranta in biya masu
shi, ummi yaya zanyi? Ummi ta dubeni a
fusace tace to ni kinsan irin zaryar da ake yi
min a gidanmu saboda bashi? Ke dai kawai
Allah ya rufa mana asiri. Na fusata nace babu
wanda ya taba saka ni a tozarci da tashin
hankali a rayuwata irinki. Ta harare ni tace dan
Allah aisha ki rufe min baki, gara kema baki
aure shi ba balle ya sake ki, nifa har da goyo,
na zama bazawarar karfi da yaji. Haka dai
muka tafi muna ta fada a hanya kamar zamu
cinye kanmu a cikin bus. Tana jin haushina ni
har nafi jin haushinta fiye da malamin ma.
Muka iske shi a zaure yana ganawa da wasu
guda biyu da alama hamshakan masu kudi ne,
daga ganin motar da suka zo da ita da kuma
kayan da yake jikinsu. Malam yana ganinmu
sai ya bata rai, bai amsa gaisuwarmu bai sai
bakinsa ne suka amsa. Muka wuce jikinmu a
sanyaye zuwa cikin gidan, da kyar daya daga
cikin matansa ta bamu tabarma muka zauna
sai wani irin kallon banza suke yi mana dan
suna suyar dakwalen kajin da aka karba daga
wajen mutane na sadaka amma suke juyewa a
cikinsu babu wata sadaka. Shi da iyalansa sun
zama tika tika saboda da cin kaji da raguna da
suke karba da sunan za'a rabawa almajirai. Na
zunguri ummi na nuna mata kajin da ido, ta
gyada kai ta fada a hankali tace eh kudinmu

ne, ai yau sai na masa rashin mutunci. Can
malam ya shigo ko kallonmu baiyi ba ya wuce
dakinsa, yayin da matarsa daya ta dinga
wucewa da abinci kala kala tana kai masa,
kamar shayi, kaji soyayyu, wainar kwai da
biredi. Mu dai muna zaune muna kallon ikon
Allah. Su kayi kasonsu a faranti yara da manya
suka dauka kowa yana ci babu ko sala daya da
suka bamu. Malam yaci ya gyatse, yazo ya
wuce ya shige wanka. Ya fito ya shiga daki ya
fesa kwalliya da farar shadda mai kyau sannan
yazo ya wuce ciki daki in da yake ganawa da
baki. Sannan ya aiko matarsa yace ta kiramu.
Muka shiga muka iske shi a tsaye a tsakiyar
dakin, muka sake gaishe shi ya amsa a
gaggauce. Yace daman yau mu kayi daku zaku
dawo? Haushi ya kama mu, sai ummi ta kalle
ni, nima na kalle ta sai ta murguda baki tace
yau ne laraba ko? Kuma yau kace mu dawo. Ya
kalli agogo yace kuma ce muku nayi kuyi
sammako? Ummi ta fada a fusace, kamawa
tayi ka ganmu yanzu kasan ba lafiya ba. Ni dai
ina zaune a lungu nayi kuri ina kallon irin
wannan damfara kiri kiri, a lokacin da zai karbi
kudinmy yana fara'a yanzun da muka zo karbar
aiki rai ya baci. Ummi tana durkushe tana
kokarin sakko da goyonta. Sai yace ba sai kin
sauke goyonki ba yanzu zan sallame ku akwai
inda zanje don sauri nake yi. Ummi tace ko
yanzu zaka sallame mu ai na sakko da 'yata
tasha nono ko? Tunda ta farka tana kuka. Yace
meye ma yake tafe daku? Ummi ta waigo ta
sake dubana tace kinji ya manta ma. Saina
sankare a zaune na tabbatar mun fada hannun
mayaudati kamar yadda kawayena khadija da
maryam suka fada. Ummi ta sake cewa malam
gaskiya komai ya kwabe tsakanina da mijina,
har ya sake ni. Ga kawata ma taji shiru bai zo
ba. Yace kuje zan bincika naga abinda yake
faruwa, amma aiki dai na gama. Ummi tace
wanne bncike kuma, kai da ka mance abinda
muka fada maka. Ya zazzare mata ido yace ke
ba'ayi mana tsiwa ana kibi a hankali. Ummi ma

ta zare masa ido tace tsiwwa ko zance
gaskiya? Ni dai ba zan gidan nan ba sai an san
abin da za'ayi, kudin da muka biya a banza
kenan, bashi muka ciyo muka kawo maka.
Aisha farida kiyi magana kyayi shiru. Na fada a
sanyaye mai zance ummi? Ya jawo wata jakar
leda a fusace sai ga daurin rubutu kashi kashi,
ya miko min daya ya mikawa ummi daya, ya
sake kwance wata ledar ya miko min laya daya,
ya mika mata daya. Duk iri daya ce. Yace kuje
kusha rubutun nan a tsaye, sannan ku kasance
layan nan a jikinku sai kuyi kokari ku hadu da
mazan da kuke so, ku tambayesu duk abinda
kuke so daga gare su zasu yi muku. Ummi ta
karba ta tabe baki tace mu fa ba wani abu
muke nema a wajen mazan ba illa soyayyarsu.
Yace to ai haka nake nufi ko soyayya ko kudi
duk zasu baku. Na zuba abubuwan daya bani a
cikin jakata na mike tsaye nace da ummi taso
mu tafi. Ta mike a fusace tace zamu tafi
malam, sai dai gaskiya idan bamu ga canji ba
zamu dawo, asan abinyi dan bangane irin
wannan aikin ba. Muka fice yayin da ya bimu
da harara, muka fito tsakar gida dukkanin mu
rai a bace. Matansa sunyi carko carko suna
kallonmu domin suna jiyo duk abubuwan da
ummi take fada. Ta harare su tace Allah Ya isa
kudinmu da ake damfarar mu ana cin kaji, ko
wacce shegiya tayi bul- bul da abincin haram.
Ni dai nayi wuf na fice kada a biyo mu da duka,
har zaure suka rako ummi suna zaginta tana
zaginsu. Naja hannunta muka tafi, a hanya ta
fashe da kuka don takaici, ni kukan ma na kasa
yi sabida tsananin tashin hankali. Tace dani
aisha kinga macutan malamai ko? Wallahi ni
ban taba kula da cutar da wannan dattijon yake
min ba sai yau. Duba kiga yadda komai ya
dagule mana. Nayi ajiyar zuciya nace yanzu
ummi meye abinyi? Tace kije wajensa ki gwada
ki gani bayan kin sha rubutun kin daura layar.
Nima yanzu gidan yassar zanje in gani ko zai
kula ni, idan abinda ya bani bai yi aiki ba
wallahi sai na dawo na tarawa malamin nan

mutane. Nace kina ganin wannan rubutun da
layar daya bamu ta gaskiya ce? Ta wa da naki
fa iri daya ne, babu wani suna daya tambaya
balle ace kowa daban, rubutun ma daga gani
ba namu bane saboda baiyi niyyar bamu komai
ba sai da yaji kince babu inda zakije idan baiyi
wani abu ba sannan ya bamu. Tace ke dai
muje mu gwada mu gani. Mukayi sallama na
hau acaba zuwa asibitin malam ummi kuwa ta
hau bus zuwa unguwar zango gidan yassar. Ina
sauka na bude jakata na zaro kullin runutu na
tashi tsaye kamar yadda ya umurce ni na
shanye, yayin da na ciro layar nan na damke a
hannuna na nufi ofishin sahibina. Ina mai
karanto adduoi don neman dacewa. Zuciyata
cike da fargaba. Na tura kofar ofishin a
sanyaye gami da yin sallama, zazzakar
muryarsa ce ta amsa sannan na tura kai na
shiga. Kallo daya yayi min ya dukar da kansa
kasa bai sake dagowa ba yaci gaba da rubuce
rubucensa. Na gaishe shi ya amsa a shelake
yayin da fuskarsa babu annuri. Na dade a tsaye
bai ce dani komai ba kuma yaki dagowa ma ya
kalle ni. Nayi ajiyar zuciya na tambaye shi a
tsorace dr lukman ya zo kuwa? Da yazo da
baki ganshi ba. Amsar da ya bani kenan. Nace
likita ina da tambaya game da kurajen fuska.
Sai yace dani ke fita ki bani wuri, nan ba
ofishin dr lukman bane, ya koma ofishinsa a
room 8 an gama masa gyaran, kada ki sake
shigowa nan nemansa. Nayi sadan sadan na
fice, na dade a tsaye a bakin kofar daga waje
ina takaici tamkar in rusa ihu. Sai wata zuciyar
ta raya min ko in saka layar a bki in tauna zata
fi aiki. Sai na zura ta a baki ina taunawa na
sake tura kofar na zura kaina ciki. A tsaye a
tsakiyar ofishin na iske shi yana duba wani
littafi a jikin durowar littattafan dake kusa da
bakin kofar. Nace dan Allah likita zan iya bar
ma sako ka bawa dr lukman? Naje ofishinsa
baya nan..... Ban rufe bakina ba naji ya banko
kofar ya rufe booom saura kada ya bame da
fuskata, ba dan na daka tsalle nayi baya ba,

daya illata ni. Tunda na kalli kofar waje
bansake waiwayr ofishinsa ba, na saka a raina
ni dashi har abada koda kuwa zan mutu banyi
aure ba a duniya dan wannan wulakancin ya
isa. Naji na tsane shi na tsani kaina. Na tsani
ummi da ta saka ni a hanyar halaka kuma na
tsani malamin daya cuce ni ya tagayyara ni. Na
toho da layar daga bakina na farke ta saiga
takadda a ciki babu abinda yake ciki sai zanen
wani hatimi mai gida gida an rubuta alifun,
ba'un, ta'un kawai aciki. Na fusata na yayyaga
kuci kuci na watsar yayin da kuka ya turnuke
ni. DUK KYAN TAKALMI 14 Kawata ummi
wacce na taba baki labari tana son wani
malamin mu a sakandirw abdulyasar shi kuma
baya son ta amma daga baya ya fara sonta har
ya aure ta, ita na tuntuba don ta bani shawara.
Sai tace dani malamai ne suka yi mata aiki,
dole akayi masa yazo ya aure ba a hayyacinsa
ba. Don haka sai ta jani wajen malaminta ya ce
in kawo masa naira dubu ashirn da biyar zaiyi
min asirin da dr shureim zai zo har inda nake
da kansa, ya aure ni. Dogon salati abida ta
dauka ta dafe kirji tace farida boka? Me ya
kaiki bin bokaye akan wannan 'yar karamar
matsalar? Sai na daga ido da sauri na dube ta,
ina mamakin yadda ta ambaci matsalata 'yar
karamar matsala. Nace a raina lallai abida bata
san yadda dr shureim take ba da yadda
halayensa suke ba shiyasa take ambaton haka.
Abida ta dora hannu aka tace innalillahi wa
inna ilaihir rajiun. Aisha farida kinyi kuskure.
Wai shin ina wayon nan naki? Ina dubarunki?
Ina iya zama da jama'ar da kika koya daga
wajen magabatanki? Ai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login