Showing 48001 words to 51000 words out of 99740 words

Chapter 17 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf

Advertisement

ESHAT   

23 Mar 2025

5571


da kanta kasa ba ta dago ba har ya wuce
waje, iyakacinsa kan baranda yaje ya dawo
har yanzu wayar yake yi, da alama da
kanwarsa farida suke magana tana wajen
likita. Bata dago ba, sai da ta tabbatar ya
shige babban dakin kwanciya na mata. Sai
mamaki ya rufe aisha farida matukar
mamaki kuwa. Wato ashe rububin nan da
mata sukeyi a kansa da kallonsa, da
shishige masa dadi yake ji kenan? Da
gangan yake basarwa yasan ana sonsa
kenan, ai ga shi yanzu bai ji dadi da ta share
shi ba, tabbas ya bata satar amsa ya hadu
da shariya sai ta rama duk abubuwan da
yayi mata, inyaso ta rabu dashi daman ta
fitar da ran samunsa. Bata gama tunanin da
takeyi bi sai ta tsinkayo shi ya fito shi da
matron maryam suna tafe suna magana har
da kyakyata dariya. Dariyarsa tana tayarwa

da aisha farida hankali, saboda sai yayi
dariya kyawunsa yake kara bayyana.
Aisha farida ta mike tsaye a nutse tana
duban Matron maryam ita kadai, yayin da
suka tunkaro inda take tsaye. Bai kalle ta
ba, haka itama. Matron maryam ta dafa
kafadarta tace Allah sarki 'ya ta yi hakuri na
zaunar dake ko? Ina so in fito aka tsayar
dani ai munyi waya da ita tace ba ta baki
sakon ma yana nan waje shima yazo tun
dazu, gezawa zai kai. Wannan shiriirta tawa
dai Allah Ya shirya na barku ku biyu kuna
jira, ke baki sanshi ba shi bai sanki ba balle
ince ki bashi. Gashi baki da waya da na baki
lambarsa, dole dai sai nazo.
aisha farida tayi murmushi tace babu komai
matron. Ta duka cikin ladabi ta mika mata
'yar karamar ambulan din. Matron maryam
ta karba tayi godiya fuskarta cike da fara'a.
Dr shuraim na tsaue a gefe hannayensa
dukka biyi na cikin aljihun wandonsa kansa
a sunkye a kasa bai cika kallonsu ba, yayin
da aisha farida take gaggawar barin wajen,
matron kuwa sai tsayar da ita take tana
damunta da surutai barkatai. Dr shuraim ya
dubi agogon dake hannunsa ya huya ya
dubi matron yace sister maryam zan koma
ciki, zamu hadu anjima, kinsan ina duba
patient. Tsaya tsaya kanina, gara mu gama
magana don idan ka zille min bansan sanda
zan sake nemo ka ba, da gaske nake ni da
mijina muna neman visa london ya za'ayi
kenan? Aisha faroda ta samu ta sulale ta
barsu nan a tsaye suna magana. Tana tafe
tana mamakin wannan kyauta da Allah yayi
mata a yau, Ya jeho mata sahibinta ta
ganshi har ta gaji sabanin da, da sai ta yini
tana zagaye bata ganshi ba.
Tabbas abida tayi gaskiya, babu abinda yafi
irin ka daga hannu ka roki Allah abinda kake
so, zai biya maka bukatunka cikin gaggawa.
Ta kudiri niyyar zagewa ta lullunka yin
addua fiye da yadda take yi a baya. Ta isa

wajen 'yan ajinsu sunyi aiki yadda ya
kamata, har zuwa lokacin tashinsu, kowa ya
lura yau aisha farida tana cikin walwala har
ma wasu na tambayarta meyasa take
murna yau. Da ta isa gida tun daga tsakar
gida abida ta lura da yawan fara'arta don
haka sai tabi ta cikin daki tana tambayarta.
Lafiya meya faru yau naga kina ta fara'a? Ko
aisha farida bata fada ba, abida ta canki
daidai cewa tayi nasan dr shuraim ne ya
saka ki walwala yau. Aisha farida ta kwashe
da dariya ta gyara zama ta zayyane mata
duk abubuwan da suka faru a yau.
Tambayar da farida ta furta itace anty
meye abunyi a nan gaba? Abida har kamar
tafi farida farin ciki, sai tayi dariya tace ki
zuba min ido gobe ni nasan abin da zanyi
masa. Mamaki mara iyaka zaka iya gani
daga idanuwan farida, zatayi tambaya abida
ta katse ta, tace kada ki tambayeni, ki saka
min ido kawai. Allah Ya kaimu gobe. Asuba
ta gari AISHA SHURAIM!!!
Washe gari da asuba kiran farko aisha farida
ta bude ido, abin mamaki sai ta dinga jin
motsi a kofar dakinta. Ta kame a kwance
sannnan dai ta tabbatar ba aljanu bane,
haka ba bakin dare bane wato barayi.
Motsin abida ne don ta jiyo tarinta. Aisha
farida ta cika da mamaki me ya fito da
abida ne daidai wannan lokaci? Shine me
takeyi a waje ta dade haka? Aisha farida ta
mike a hankali tana sanda taje ta tura
window ta leka duhu kirin tsakar gida,
amma da hasken fitilar kwai a gaba abida,
tana gaban murhu tana dahuwa. Sai
mamaki ya sake lullube zuciyar aisha farida.
Ta ambaci sunan abida atsorace a hankali
cikin rada. Nan da nan abida ta dago ido ta
dubi window tayi murmushi tace farida
tsoro kika ji? Kada ki firgita nice dahuwa
nakeyi. Aisha farida ta maimata dahuwa?
Me kike dafawa da tsakar daren nan? Abida
tayi dariya tace asuba ce ai yanzu, idan ya

dahu zaki gani. Tayi wuf ta bude kofa ta fito
tana kokarin bude tukunyar don taga abin
da ake dafawa. Abida ta rike mata hannun.
Tace idan ya dahu da safe zaki gani, abincin
mijina ne. Aisha farida tace bulaguro zaiyi?
Abida tace eh. Aisha farida tace ina zaije?
Abida tace lagos. Aisha farida tace zai bi ta
shagamu? Abida tace ba lallai bane don
daga ofis zasu tafi. Aisha farida tace zai
dade ne? Abida tace zai kwana biyu, kina da
sako ne a fada masa? Aisha farida tace a'a
zan so muyi sallamai dai kafin ya tafi
saboda halin tafiya. Abida tace kada ki
damu zan masa magana kafin ya fita sai
kuyi sallama. Aisha farida tayi murmushi
tace anti bari nayi alwala inyi nafilfili kafin a
kira assalatu, sai inzo inci dadi, ina jin dai
kaje ne ake rababbaka mana. Abida tayi
dariya ba tare da ta bata amsa ba. Doguwar
sujjada aisha darida keyi tana ta addua tana
kai kukanta wajen Ubangijinta Ya bata abin
da take so wato dr shureim idan har shine
mafi alkhairi a gare ta. Idan kuwa babu
alkhairi tana rokon Allah Ya yaye maata
sonsa Ya bata wanda ya fishi alkhairi. Sai
taji hawaye yana surnanowa daga
idanuwanta, don tana tausayawa kanta da
kanta, halin da ta tsunduma na soyayya.
Ba ta bar kan tabarmar sallarta ba sai bayan
datayi raka'atanil fijr da kuma sallar asuba,
ta tofa adduoi a tafin hannunta ta shafa a
fuska sannan ta mike zuciyarta cike da farin
ciki tana da tabbacin Allah Ya amshi
adduointa. Don shi kadai ne mai bayarwa
wahidul kahharu. Daga nan sai ta shiga cuku
cukun yin wanka da shiryawa saboda tafiya
asibiti. Kafin ta kammala gari ya waye
wasai, sai ga abida dauke da dan faranta da
cokali a ciki ta mikawa farida. Aisha farida
ta karba da sauri cike da mamaki, sai ta
duba taga ai dambun shinkafa ne ya sha
zogale da gyada, ya tiraru kuwa sai kamshi
yake yana hayaki, da zafinsa kau. Ta koma

ta zauna ta dandana, sai taji zakwai ya sha
maggi da gishiri, ga dan yaji yaji sabida
attaruhu da albasar da aka yayyanka yiri yiri
a ciki, aka turara dasu sai kamshi yake
tashi, hade da kamshin man gyada ziryan.
Aisha farida ta girgiza kai ta sosa kunne
tace tunda Allah Ya halicce ni ban taba cin
dambu mai dadi irim wannan dambun ba.
Lallai yaya yana cabawa irin wannan
haduwa haka? Abida dai na tsaye a kanta
murmushi kawai take yi bata ce komai ba
har yanzu yayin da aisha farida ke faman
turawa a cikinta tana ta santi.
Aisha farida ta dagi ido ta dubi abida tace
abin mamaki kuma dambu da aka sanshi da
shakewa mutum makogoro sai gashi
wannan dambun baya shake mutum silif
silif yake wucewa. Wai, yaushe rabon in
karya kumallo a gida, lallai yau zanfi jin
dadin aiki don cikina yayi nauyi. Allah dai ya
saka da alkhairi, Yaya hussani yayi sa'ar
mata. Da dambun zai tafi a cikin food flask
su dinga ci a hanya? Abida ta fita bakin
kofa, sai ga tata shigo riki riki dauke da dan
kwandon roba mai marika, irin wanda ake
saka flask din abinci. Aisha farida tace lallai
haduwa irin wannan sabon food flask haka?
Yau aka bude shi daga leda duk saboda
yayana tabbas babu mu babu kara aure.
Abida tayi dariya tace bude ma kiga yadda
aka shirya ciki. Aisha farida ta jawo
kwandon ta daga wani babban hankici sakin
ulu, wanda dashi aka lullube saman. Ta zaro
wani dallelan flask mai madaidaicin girma,
tsaka tsaki karkashinsa kuwa farantai biyu
ne na tangaran da babban cokalin diba
wato serving spoon da cokula biyu
dukkansu sababbi ne filfil a wanke tas tas.
Aisha farida ta gyada kai tace lallai wannan
kwandon abin sha'awa ne tun kafin na
bude ma abinda yake ciki. Abida tace bude
mana ki gani. Aisha farida tayi bismillah ta
bude, tana budewa sai wani kamshi ya daki

hancinansu. Aisha farida tace humm lallai
abin ma son kaine ko anty, ashe har da
hanta da koda aka yayyanka a ciki shine ba
a sako min bako daya sai maigida aka
tulawa gasu nan burjik a ciki.
DUK KYAN TAKALMI 2* 7
Abida tace me kika yi masa haka a rayuwa
da zai tsane ki? Ba zai tsane ki ba, saboda
kin riga kin kai kararsa wajen mahaliccinsa,
zan sake baki wasu adduoi masu zafi
wadanda suke kara soyayya da tausasa
zuciyar wanda kake so. Idan kina karanta su
hakika dole yaji yana sonki sosai. Adduar
itace "Allahumma ya mukallibul kulubi
wamusarrafuha kaifa ya sha'u usaibarul
muhabbati fi kalbi (ambaton suna) bi hakki
ismikal wadudu Ya wadudu. Ya wadudu sai
dubu daya da dari daya da goma sha daya.
Kiyi tayi kullum har zuwa lokacin da zai
sanke kece mai dambu sai ya hadu da
kaunar dambun da aikin wanna adduar su
fara aiki. Ni kuma a lokacin zan fada miki
abu na hudu da zaki rike nan gaba, kinsan
yanzu uku na fada miki shine ADDUA,
HAKURI da RIKE MUTUNCI. Bazan fadi na
hudun ba, sai a lokacin da kika tabbatar min
ya gama saninki. Idan ya ganki a ko ina zai
shaidaki, zai kira sunanki, zaiyi miki
murmushi, zaki gaishe shi ya amsa cikin
farin ciki, to sai na jeho miki makami na
hudu wato taryo soyayyarsa. Aisha farida ta
lumshe ido don dadi tace kamar a mafarki
nake jina. Sai nake jin bayaninki kamar na
samu shuraim na gama. Abida tace shi yasa
ake so mutum ya rike Allah, Shi zai biya
masa bukatunsa banda bin boka ba ko 'yan
bori. Shiyasa mata muka fi yawa a wuta,
saboda karamin tunaninsu da gaggawa.
Gaggawa kuma daga shaidan take, yanzu da
kika riki Allah zaki ga yadda Allah zai
taimake ki, ko baki samu shuraim ba zai
musanya miki da wanda ya fishi, kuma zai
tanadar miki babban rabo a lahira. Aisha

farida ta gyada kai tace haka ne. Allah Ya sa
mu dace, wadanda suka bata irin su Ummi
Allah Ya ganar dasu gaskiya. Abida tace
amin. Ci abinci ki fita kije ki cefano min
kayan dambu. Asuba ta gari AISHA
SHURAIM!!
Washe gari aisha farida tayi sammakon
zuwa ofishin dr lukman tayi sa'a kuwa tana
isowa kamar tare suka zo, shima yazo yana
bude ofis dinsa, don haka sai suka dunguma
suka shiga tare. Ta gaishe shi ta ajiye katon
kwandon mai dauke da katon food flask din
abinci, babban na jiya ne da farantai hudu
da cokula hudu. Dr lukman yayi murna da
ganin dambu kuma yayi godiya. Yau ma yayi
kokarin bata kudin taki karba, tayi gaggawar
fita daga ofishin ta rufo masa kofa. Misalin
karfe uku da rabi ta koma ofishin ta iske
ofishin a kulle baya nan, amma ta jiyo
muryarsa a ofishin dr shuraim, don haka sai
ta sadada ta bar wajen. Ta dade a labe tana
hango kofar ofishin ko zai fito bai fito ba,
sai ta hakura ta tafi gida. Yau dai bata
walwala sosai, don bata jiyo sakamakon
jarabwar dahuwar dambu ba. Shin gogan
nata yaci koma bai ci ba? Ya yaba ko ma bai
yaba ba? Data fadawa abida sai tayi dariya
tace ai ya ci ma kawai tunda kika jiyo
muryar dr lukman a ofishinsa suna tare,
babu yadda za'ayi yaga dambun yaki ci.
Aisha farida tace ya za'ayi kuma gobe?
Abida tace dan wake zanyi musu ki kai
musu tunda shuraim yana son dan wake.
Aisha farida tace a'a kada ayi, ki bari dai a
kwana biyu kada lukman din ya zargi wani
abu, ko yaji tsoro. Abida tayi darriya tace
tsoron me? Idan kika kai musu dan waken
kika dauko duka food flask dinn sai muyi
shiru muji abinda zasu ce, kuma muji
wanne suka fiso, suka fi jin dadinsa. Sai mu
dinga yi musu shi. Aisha farida tace ni sai
nake ganin kamar duk ba zai damu da sai
yasan waye yake dahowa ba, balle ya

sanni. Abida tayi murmushi tace kin manta
abinda nake fada miki, ki zama mai hakuri
duk mahakurci shi yake cin riba.
Aisha farida ta jinjina kai tace haka ne,
shikenan zanci gaba da hakuri. Abida tace
yawwa tashi muje mu daka yaji mai dadin
gaske yadda zasuji dadin danwaken sosai.
Sai ki siyo tumatur, albasa, kokunba duk a
yayyanka musu a ciki. Aisha farida tayi
dariya tace har naji yawuna ya tsinke,
gaskiya danwaken nan zaiyi dadi, zaiso shi.
Rana ta uku ranar alhamis kenan kamar
kullum da sassafe aisha farida ke fitowa
daga gida tana fin kowa sammako. Tayi jira
fiye da awa biyu sannan dr lukman ya iso.
Sai da ya jima da shiga sannan tabi
bayansa. Yayi farin ciki da ganinta, sai dai
yayi matukar mamaki da jin dadi da ya ga
ta sake dire masa wani kwandon abinci a
gabansa. Yace lafiya, meye wannan kuma?
Dama kin dauki kwandon jiya? Ta girgiza kai
tace nazo baka nan sai na wuce gida kawai.
Wannan wani ne na kawo muku, wannan
karon ba dambu bane, wani launin abincin
gargajiyar ne. Dr lukman yace a'a 'yar
shagamu kinaso muyi fada ko? Yaya zaki
tayi mana wahala, kartai muna taruwa
muna cinyewa babu ko sinsinmu? To
gaskiya bazan karbi wannan ba, ki koma
dashi gida, ko ajiyar ma bazan yi ba. Aisha
farida tayi dariya tace yi hakuri yayana,
daga yau shikenan. Yace kwanukan jiya
suna ofishin dr shuraim, kuma bana jin yazo
yanzu, don bai cika zuwa da wuri ba. Ina da
mukullin ofishinsa bari in bude in dauko
miki kwandon da farantai da cokulan,
amma ainahin food flask din ta tafi dashi
gida, dambun jiya yayi dadi sosai, har yafi
na shekaran jiya. Sai yace dole ya kai wa
babansa yaci yaji irinsa, donshi ya koya
masa cin dambu. To wallahi kinji yadda
akayi, sai anjima zai zo zan ma sake yi masa
waya kada ya mance dashi a gida, lallai lallai

ya taho dashi. Tuni farin ciki ya cika zuciyar
aisha farida, taji tamkar ta daka tsalle don
murna. Tayi dariya tace ba koma dr ai ko
food flask dinnan ba yanzu zan dauka ba,
sai da yamma. Yanzu aji zan tafi. Sukayi
sallama aisha farida ta tafi, kowannensu na
farin ciki.
La'asar sakaliya Aisha ta tunkaro ofishin dr
lukman saita hango gogan nata yana shige
da fice tsakanin wannan ofishin zuwa
wancan dauke da wasu fayil don haka saita
diro daga kan barandar ta shige lungu ta
samu waje ta zauna har saida ta ga fitarsa
ya shiga motarsa ya tafi gida bata bari ya
ganta ba.ta tashi cimak ta nufi ofishin dr
lukman hankalinta a kwance baby wata
fargaba dr lukman ta iske shi kadai da
alama shima ya miqe yana shirin tafia gida
yana ganinta yayi dariya yace yar shagamu
gaskia kin iya girki kice daman tun farko a
shagamu na nemi mace ba'a yobe ba
kinsan yadda mukayi santin dan waken nan
dr shuraim har cewa yayi week end zaizo in
kaishi ya gaida kakata mai dambu da dan
wake da yake nace musu itace take daho
min Aisha ta tuntsire da daria tace lallai
kuwa daka zo shagamu an baka mata daka
sha girki mai dadi ya miqo mata
kwandunanta guda 2 yana godia tana godia
suka yi sallama ta tafi tana fitowa bakin get
ta dane acaba sai gida tana mai farin cikin
zuwa sanrwa da abida labari.Abida na
ganinta sai tabi ta daki suka rungume juna
suna murna tun ma kafin abidar taji labarin
abunda ya faru. Aisha tace zauna in baki ki
sha suka zauna Aisha ta zayyana mata suk
abubuwan da suka faru yau tsakaninta da
dr lukman da abunda dr shuraim ya
fada.Abida tayi murna sai ta shiga bubbude
food flask din ta bude na farko saiga kudi
yan 500 sabbi har guda 4 tayi sauri ta bude
daya food falsk saiga yan 1k har guda 3
suma sabbi sai su duka suka bude baki suna

mamakin wannan kudi da suka gani Aisha
tasa hannu a hankali ta debo yan dari biyar
din ta shinshina saita a jiye a gefe ta sake
yan 1k ta shinshina saita lumshe ido tayi
murmushi ta dubi abida tace wadannan
kudin daga dr shuraim suka fito shinshina
kiji qamshin turarensa Abida ta karba da
sauri ta shinshina tace ehmm qamshi farida
har a jikin kudi kike gane qamshin turaren
masoyinki?lallai kin laqanci qamshin
turarensa to shine ya zuba wadannan kudi
kenan dr lukman ya zuba yar dari 500
dinnan daya ga kinki karba?Aisha tayi fari
da ido tace Allah sarki mai karbar addu'a
kalli daki-daki yana koro mana hanyar
haduwa da shuraim a cikin ruwan sanyi
yanzu ga kudinsa ya shigo hannu cikin
hikimar ubangiji sai ta fara kuka Abida tace
kada kiyi kuka kici gaba da dagewa da
addu'a to yanzu kin ga kudin dr
shuraimkinyi kuka ina ga ranar da kika
ganshi kacokan a qofar gidanku yazo zaance
balle ranar da zaki ganshi a dakinki a
matsayin mijinki?sumewa zakiyi kenan don
dadi?Aisha tayi daria tace gobe jumu'a yaya
za'ayi a sake musu ko a bari?abida tace aa
tsahirta gobe jumu'a sai kije ofishin dr
lukman kice doctor ranar litinin me kuke so
a dafo mukudambu ko dan wake kiji
abunda zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login