Showing 12001 words to 15000 words out of 99740 words

Chapter 5 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf

Advertisement

ESHAT   

23 Mar 2025

5581

wata
mara lafiya ta kwace ta tsira miki? Nayi dariya
nace haba dai ayi haka kuwa? Bana jin dadi
dai. Tace Allah ya sawake, shiga daki kihuta
kafin abinci ya dahu ki ci zaki murmure. Ina
shiga daki na cire uniform dina sai na daura
tawul na dauki kwandon wanka zan je in watsa
ruwa dan inji dan sanyi a jikina saboda na
kwaso rana.sai na ga abida ta shigo tana

dariya tace da ni "af ashe wanka zaki yi da
labari zan baki mai dadi kuma marar dadi." Na
ajiye kwandon wanka na jawo hannunta muka
zauna.Na ce bani in sha ai na fasa wanakan,me
ya faru? Ta yi dariya tace labarin musbahu
tsohon saurayinki da matarsa lubabatu zan
baki daman,aure dai yaki dadi har ya yi mata
saki daya dazun nan aka yi rigimar. Lungun
nan ya cika da mutane mahaifiyarsa dai sai a
taya ta da addua don ta cika naci,ce masa tayi
idan ya sake furta kalmar saki sai ta tsine
masa dole sai ya zauna da lubabatu tasan
akan aisha farida yake yi mata wulaqanci kala-
kala. Tayi rantsuwa tace ko bayan ranta idan
ya saki lubabtu ya aure ki Allah ya isa. Kin ji
wata kiyayya sabuwa ko? Na yi murmushin
karfin hali nace,Allah ya kyauta,ta ma daina
kokarin tsinewa danta a kaina tuntuni na yi
masa sallama nace ya bi mahaifiyarsa don ya
sami rahama. Ya na aiko min da kudi tun ina
karba sai na daina karba daga baya idan ya
aiko sai in mayar da dan aiken in ce bana so
don zaman lafiya. Abida tace haka ya fi,ai gara
da kika yi. Masa haka kin taimake shi. Ni na
dauka ma zancen kika ji tun daga zaure da na
ga kin shigo ranki a bace. Amma fa ki godewa
Allah AF saboda kin samu kyakkyawon yabo a
ung nan. Ba kiji. Yadda kowa yake yabonki
ba,ake ta tsine mata ita kuma. Kowa ya dinga
cewa me ye laifin AF har da bata so danta ya
aura? Yarinya mai nutsuwa da hankali mai ilimi
da fara'a tana gaishe da mutane. Ta zo ta
tauyewa yaro rayuwarsa ta cusa masa
dakalkalalliyar macen da ba ta da tsari. Nace
au daman an sanni da yawa a ung nan haka?
Abida tace "ji ki da Allah da neman magana
waye bai sanki ba,musamman da kika shiga
skul of nursing kina karbar haihuwa kina allura
a cikin ung sai ki ji kowacce mata tana cewa
wajen aisha likita zan je ta rubuta min magani.
A nan dai muka tashi muka rufe hirar nan
zuciyata cike da tausayin musbahu ba don
mahaifiyarsa ba ta sona ba da na aure shi mun

zauna mun rufawa juna asiri,in huta fadawa
cikin hatsarin da nake shirin jefa kaina. Bayan
na yi wanka na ci abinci sai na wartsake na
shiga cikin matan gidan muna ta hira har ma
na ji na fara mantawa da abunda yake damuna
a zuciyata. Sai da kowa ya shiga barci dare ya
fara nisawa sai tunanin Dr shureim imran yace
da wa Allah ya hada ni in ba da ke ba,sai na ji
gaba daya daya zuciyata ta kasa sukuni. Da
zarar na rufe ido sai in ganshi tamkar a zahiri.
Sai na yi ta yaki da zuciyata ina ture shi daga
tunanina.kai in takaice maka a cikin satin nan
ban gane kaina da kaina saboda tsananin
tunaninsa. Idan na je asibiti bana walwala haka
idan na dawo gida ba na jin dadin zuciyata
kada ma dare ya ji labari sai ka ga idona ya
wartsake garau na burma tunanin DR shureim
imran. Da gaske sonsa nake,so ba da wasa
ba.tun ranar kuma ban sake ganinsa ba sai dai
kullum sai khadija ta yi min labarinsa.Albishir
din da ta yi min shi ne ta sami lambar wayarsa
amma tana tsoron kira don tana ganin zai yi
mata wulaqanci. Ta shaida min ta rabawa
malamai kudi ana ta ragargaza mata addu'a ta
koina,a kalla ta raba musu zunzurutun kudi ya
kai N25,000 so take sai an gama addua tas
sannan ta kira shi dolensa ya amince. Sai na
sake jin jikina ya yi sanyi na sake yi wa
zuciyata fada da ta yi ta- ka tsan- tsan ta
daina cusa abunda zai iya kasheta.idan da
khadija. Zata lura duk sanda ta fara yi min
zancen Dr shureim sai jikin yayi sanyi kuma na
kan rasa amsar da zan bata ko shwara.
Kallonta kawai nake tsayawa ina yi yayin da
zata iya ganin hawaye yana cika min ido sai
inyi sauri in mayar da shi ina tauisayinta na fi
tausayin kaina domin na san zuciyata ta fi tata
shiha hatsari kuma ta fini sanin yadda zata yi
da kanta. Ni ko wayar ma bani da ita babu
kudin saka kati balle in saka rai ko zan karbi
lambar in kira inji dadi. Na zama na rasa
walwala ta ko abincin kirki bana iya ci na
dukufa da adduar Allah ya yaye min don sonsa

ya zame min ciwo.naji duk na tsani kaina karfi
da yaji nake fisge tunaninsa daga cikin
zuciyata.amma abu ya ci tura sai ma karuwa
yake yi. Idan naki tunaninsa karfi da yaji a ido
biyu da zarar na kwanta sai nayi mafarkinsa,
sai gani cikin dare ina kuka wiwi ina sallah da
adduar Allah Ya yaye min, Allah Ya kawo abin
da zai sa inji na tsane shi ma. Duk satittikan
nan da nayi ina jinyar sonsa ko a hanya ban
hadu dashi ba balle ma in ji dan sanyi a raina,
ina so ina kara ganin suffarsa don in kawata
tunanina domin kamanninsa suna kokarin
disashe min. Ranar talata da sassafe ina
dirowa daga kan acaba a kofar shiga gate din
asibitin aminu kano sai na yi kicibus dashi a
cikin wannan tsaleliyar motar tasa. Na
waiwaya da sauri na dube shi yayin da shi ma
yake dubana har da rage tafiya amma fa duban
da yake yi min bana kauna bane, hararata yake
yi game da nuna tsana mai yawa a bayyane.
Sai yayi tsaki ya girgiza kai ya kada sitiyarin
motarsa yayi wucewarsa. Sai na dankare a
tsaye ni ban ciro kudin mai acaba na biya shi
ba, ni banyi gaba ba balle ace mantuwa nayi.
Bani kudin mana, inji zalamamman dan acba.
Na ciro kudin na mika masa ya karba yana
shirin ya miko min canjina naira ashirin sai na
girgiza kai nace kayi min sadaka, ku taya ni
addua don bani da lafiya. Sai ya tsaya yana
kallona cike da tausayi yace to ko gida za a
mayar dake idan ba zaki iya aikin ba? Ai komai
sai da lafiya akeyi. Nayi murmushin karfin hali
nace ciwona addua yake bukata ba hutu ba, ko
shan magani. Sannan maganin ciwon yana
cikin asibitin nan, idan na koma gida ai babu
maganin a can. Yace gaskiya ne duk wani
magani yana asibiti. Allah Ya yaye miki
kowanne irin ciwo ne wannan. Na amsa da
amin nagode. Na juya a sanyaye ina tafiya
kamar kwai ya fashe min a ciki. Ina mai
matukar mamaki da takaicin kallon wulakancin
da yayi min. Na kasa tantance ni kuwa laifin
me nayi masa a rayuwata da ya tsane ni,

yaushe ma ya taba ganina banda sau daya
shima a rubibi, yaushe zai ganeni? Aisha farida
umar, karaf naji an kira sunana daga gefena.
Nayi firgigit na juyo da sauri. Khadija sani
ismail na gani ta tsaya da motarta hience 2008
ta sauke gilashin wundonta kasa, na tsallako
inda take na bude gaban motar na shiga. Ina
kokarin gaishe ta sai ta katse ni cikin murna
take magana tace albishirinki? Na kira Dr
shuraim imran jiya ya dauka, sai dai mun fara
magana yace in bashi bane wanda nake newa
wrong number ce, ya katse wayar. Sai na tura
masa sako nace ni dalibarsa ce , na kira in
gaishe shi. Kinga amsar daya bani. Sai ta miko
min wayarta, sai hannuna ya hau kakkarwa,
har sai da ta tsaya tana kallona saboda gaba
daya jikina bari yake yi. Na duba na karanta
sai naga ya runuta "thanks". Sai na lumshe ido
don dadin ganin rubutunsa da lambarsa, naji
dama nice nake yi masa waya da tura sako da
ko amsar da ya bawa khadija na samu ya bani
kadai na gama jin dadin rayuwata, ta isheni
abin farin ciki. Na bude baki nayi magana da
kyar, nace lallai kinji dadi. Tace dadi ka-n jiya
ai jar da barci da munshari don samun
kwanciyar hankalin dana ji. Dole in karawa
malamaina kudi su sake dagewa da addua
sosai. Nayi ajiyar zuciya nace ya san sunanki?
Tace bai tambaye niba, ki kyale shi sai a
hankali, dan wulakanci ne fa wannan da kike
gani. Muka isa bangaren da muke,mun bar
bangaren masu kuraje mun koma bangaren
yara. Muna shiga ciki muka iske 'yan ajinmu a
tsaitsaye kowannensu da dan littafinsa a hannu
da biro, da alama matron ta fara bayani akan
wannan yaro mai ciwon amai da gudawa. A
tsaye nake ina kallon bakin yaron a hannun
mahaifiyarsa yana tsala kuka, amma ban
fahimci bayanan matron ba, ko kadan ban san
me take cewa ba. Tunanina kawai daman ace
dana ne wannan jaririn muka haifa tare da Dr
shureim imran. Sai da ta gama bayani ta juya,
naga an bi ta duuu a baya zuwa gadon wani

yaron marar lafiya, shi kuma mai ciwon
pneumonia ne, sai na ja birki na tsaya cak na
ki bin su saboda kafafuwana da kwakwalwata
sun gaji ba zasu iya daukar abubuwa guda biyu
ba, tunanin dr shuraim imran shi yafi matsa
min, gara in yi shi shi kadai, shi yafi
muhimmanci a gareni don haka na juya na nufi
ofishinmu inda muke zama mu huta da ajiye
jakunkunan mu. Ina shiga sai naga maryam
ahmad tayi kasake a zaune akan kujera tana
matsa wayarta, fuskarta babu walwala. Nayi
mata magana sai naji da kyar take amsa min.
Na tambaya cikin damuwa maryam lafiya? Me
ke damunki? Baki da lafiya ne. Ta girgiza kai
tace lafiya kalau. Ni dai na dame ta da
tambaya lallai sai ta fada min abin dake
damunta. Ko a mafarki ban zata amsar da zata
bani ba kenan. Budar bakin ta ke da wuya tace
waye inba dr shureim ba? Sai naji gabana ya
fadi daf! Na fada a gigice me yayi miki? Sai ta
dube ni kwalla ta cika mata ido tace aisha
farida na yarda dake shi yasa zan fada miki
sirrina, na san kina da rike sirrin jama'a ba
ataba fada miki magana kin yada ba, na san
zaki bani shawarar da ta dace. Ina matukar
son dr shureim imran, har zuciyata sai naga da
in tsaya labe labe shi ma mutum ne kamar ni,
me zai hana in tunkare shi in fada maas tunda
ni bazawara ce, kunyar me zanji? Duk inda
mace ta kai na kai, ina da kyauna da ilimina da
arzikina, gani 'yar asali karewa ma 'yar
sarauta. Dazun nan na tare shi a bakin ofis
dinsa yana ganina ya bata rai na gaishe shi ya
amsa da kyar, ya bude kofar ofis dinsa ya shiga
sai na bi bayansa. Muna shiga sai ya daka min
tsawa yace lafiya? Nace nazo in gaishe shi ne.
Ya fada a fusace yace to naji sai anjima. Nace
kuma ina da magana da nake tafe da ita. Sai
yace fadi maganarki ki fita. Nace so nake mu
saba in karbi lambarka, ka karbi tawa. Ko rufe
bakina banyi ba yace bana bukatar in saba da
ke, haka bana son lambarki, sai anjima. Sai ta
fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na

dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah
Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki
tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara
zancen nace ai da kika fada min abin da yayi
miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu,
shine nace Allah yaji kaina. Tace meye
shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita
nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu
dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata
sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi.
Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi
ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da
dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata.
Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa
ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake
magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin
da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a
wahalar min da abin kaunata. Daga nan na
kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran
a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar
ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min
maganin ciwon nan. DUK KYAN TAKALMI 7 Sai
ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda
na dora hannu aka ba nace mun shiga uku,
Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da
mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri
na gyara zancen nace ai da kika fada min abin
da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in
mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye
shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita
nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu
dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata
sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi.
Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi
ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da
dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata.
Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa
ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake
magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin
da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a
wahalar min da abin kaunata. Daga nan na
kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran
a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar

ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min
maganin ciwon nan. Abida ta lura bana cikin
walwata kullum ina cikin damuwa, ta
tambayeni har ta gaji na kasa fada mata
wannan badakalar cutar da zuciyata ke fama
da ita, babu abinda nake boyewa abida amma
wannan dai ba zai fadu ba. Na gwammace a
dauki gawata a dinga tunanin fuju'an na mutu
babu ciwo ni da Ubangijina munsan abinda ya
kashe ni. Sai na shiga tunanin ko shi yasa ya
dinga hararata saboda masu irin uniform dina
ne suke damunsa ya zata nice? Haka ne ma
babu tantama ya dauka khadija da maryam ce
ni. Bansan takamaiman ofis dinsa ba, don haka
kaina tsaye na tunkari ofishin dr lukman likitan
kwakwalwa dauke da file din matron maryam
ta umurce ni da in kai masa. Ofis na uku tace
min daga hannun dama, don haka kaina tsaye
nan na kwankwasa na shiga tun kafin a bani
izini, saboda saurin da nake yi don inyi in koma
wajen daukan darasi. Abin da nagani a cikin
ofishin shi ya firgita ni har sai da kowa ya gane
na tsorata, dr shureim imran na gani a zaune a
kan kujera da laptop dinsa akan table yana
danne danne, maimakon mai ofis din dr
lukman. Wace wannan? Ya kika koma da sauri?
Wa kike nema? Tambayoyin da na jiyo ana yi
min kenan daga cikin ofishin ni kuwa tuni nayi
waje. Na rufo kofar a hankali na fara sanda zan
juya, jikina yana rawa ina gudun wulakancinsa.
Wata murya naji an kira ni, har na kai kan
barandar waje. Ina juyawa naga mai gadi ce
(security). Tace inje inji doctor. Hankalina ya
tashi kan kace kwabo na fara gumi tamkar ana
gasa ni a garwashi. Ofishin dr lukman kuwa ta
nuna amma ban ga kowa a bakin kofar ba,
kuma har yanzu kofar a rufe. Ni kaina ban san
ayoyin da nake karantawa ba har na isa bakin
kofar, na tura kofar na shiga ina mai jan dan
gajeren hijabina ina rufe rabin fuskata. Ina
sauraron yadda Allahi Zaiyi dani kuma. Nayi
sallama na shiga amma na kasa daga ido in
dube shi. Yaya kika leko kika koma? Wannan

karon kuma wata sabuwar murya naji daban ba
irin ta dazu ba, sai na dago ido da sauro na
dube shi. Dr lukman na gani zaune yana danna
laptop dinsa ba dr shureim imran bane. Sai
mamaki ya rufe ni a zahiti har ya fahimci haka,
na tabbatar son dr shureim yayi min yawa da
har ya fara yi min gizau. Nayi murmushi na
dauka ba ofishin na shigo ba shiyasa na juya.
Na matso na mika masa file din yana dubawa
ya girgiza kai yace me yasa matron zatayi min
haka, ni ba wannan nace ta aiko min ba. To
iyakacin kalmar da na fahinta kenan daga nan
na daina sauraronsa saboda dr shureim imran
na gani ya fito daga bandaki da alama alwala
yayi don jikinsa daruwa. Kallo daya nayi masa
na zazzare ido sai na sunkuyar da kai kasa
yayin da jikina ya hau rawa, zuciyata ta hau
tsalle tana oyoyo ga abincin da na dade ina
yunwarsa. Shine ma dai yayi min kallo sau biyu
ya watsar ya shige lungu ya shimfida abin
sallah. Kafin ya tayar da sallah dr lukman ya
tsokano shi da ci gaba da hirar da suke yi.
Yace wato dr shureim ka tsani ka ga 'yan
acaba kenan? Yayi dariya yace yadda naki
mutuwata haka naki inga mutum ya hau acaba
musamman mace ina takaicin wannan abu, sai
inga ba gara mutum yaje ya kwanta a sibiti ba
yace a zuke jininsa gaba daya a rabawa
marasa lafiya saboda ya mutu, gara yace a
yayyanki duk sassan jikinsa a raba sadakatul
jariya. Dr lukman ya kwashe da dariya har da
buga kafa a kasa. Yace haba dai doctor har
abin ya kai haka? Yace haka ne mana, saboda
yadda zaka ga suna kutsawa a jikin tirela. Na
fada maka fa acaba ne ya kashe san uwa na
uwa daya uba daya, kuma ina tsaye ina kallo
ya kutsa dashi karkashin tirela. Daha cewa dan
acaba kai ni can in siyo batir motarmu ta mutu
a hanya, shikenan ya warce shi sai karkashin
tirela sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login