Showing 9001 words to 12000 words out of 99740 words
Chapter 4 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf
layi da ka ba tare da yana duba
littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan
don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada
take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka
kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai
muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta
cushe muna shiga don muna da yawa, ga
dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun
gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido
hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa
kawai na fara hangowa daga nesa sai na
tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban
hango jan kunne ba da farin gashi irin na
turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu
na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye
da bakaken kaya riga da wando (suit), farar
riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure
wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana
matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa,
wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai
dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da
take tsada a duniya wato hasken duhu
(chocolate color). Ko dana sake samun daman
na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar
ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa,
sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba
ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda
ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin
irin wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido
mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu
gashin ido da gashin gira masu yawa da
tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau
suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar
fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba
duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a
ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce.
'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a
ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi.
Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban
hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka
kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa
kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun
sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da
rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan
da ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da
'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka
hadu suka same shi bakar fata da farar fata.
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna
musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan
mu tare, yana sona sosai nima haka saboda
yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire
yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai
aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa
bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu
auren gida, shi kuma ni yake so ya
aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a
hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na
daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen
kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a
shekara. Musbahu ma yaji labarin duka dana
sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min
leshi guda daya da atamfa ya hada min da
naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min
fada in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce.
Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa
ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai
in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani
hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu
zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da
addu'a Allah Ya karkato da zuciyar
mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren
dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire
ya fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan
ya sami kudi zai saya min form din jamb in
wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a
jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi,
bani da mai bani kudin mota da kudin sayan
handout, gashi dole sai an saka sutura masu
kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga
shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk
wadannan sabida dan abinda yake samu ba
mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan
sami ayyuka da yawa suna samun kudi a
business center yake aiki, suna typing a
computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to
zai samo min management in fara, nan ma
nace bana so nafi son inyi schl of nursing
saboda ba ruwana da neman kayan sakawa,
suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin
ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi
masa sallama da yayana hussaini ya kara yi
masa bayani. Yace zai taimaka min da wata
dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince
yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka
hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake
bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya
ta malam aminu kano dake unguwar court
road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku
ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court
rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus
zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin
acabana kit da kit babu canji wata rana ko
purewater zan sha sai dai kawayena su saya
min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan
lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai
dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun
gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail
kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma
duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko
na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi
fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in
kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba
sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna
min bakin hali daga baya kuma in dinga jin
kananan maganganu cewar na cika san banza
kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina
abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a
saya min. Rashin sani yafi dare duhu, KALLON
KITSE sukeyi wa ROGO. Hakika ni mai yawan
tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta
ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a
wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin
mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija
bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari
sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text book)
babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi
morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita
ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya
sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata
rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk
ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi
sai yace in hakura kada inje makaranatar randa
ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da
kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da
kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya
naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira
ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa
kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da
nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi
hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka
tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu
wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake,
basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai
sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake
sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga
bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su
tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan
kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abakin
gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin
rayuwata a wannan bangaren saboda bani da
wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin matsalolin
da suke addabata. Kawata guda daya, itace
aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar
yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba
dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu,
koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin
gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin
da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi
a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta
tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata,
ni burina guda daya ne shine in gama karatuna
in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan
gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna
shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron
kazanta da cinkoso, babban burina ba wuce
inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja
gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke
mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan
karami mun cunkushe gashi su dukka yaran
abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin
wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu
kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata,
rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace,
tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi
tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar
makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan
kawa, na rike talaucina na kama kaina bana
sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai
gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida,
wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai
'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka
shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni
'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi
musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba,
tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan
Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU
Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na
rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa
lafiya muke wadanda aka kwantar dasu
sakamakon wasu kurajen da suka feso a
jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron
maryam tana nunnana mana yadda ake aiki,
domin neman karin bayani sai tace bari ta
hada mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin
daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla
da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda
naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun
iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu
daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya
da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan
wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai
yake yi musu cikin harshen turanci kai kace
baturen america ne, kalmomin kimiyyar
(botanical names) da yake ta ambato yana
jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba
littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan
don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin
ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada
take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka
kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai
muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta
cushe muna shiga don muna da yawa, ga
dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun
gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido
hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa
kawai na fara hangowa daga nesa sai na
tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban
hango jan kunne ba da farin gashi irin na
turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu
na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana
shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa
karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye
da bakaken kaya riga da wando (suit), farar
riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure
wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana
matso ciki sai na fara hango gefen fuskarsa,
wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai
dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da
take tsada a duniya wato hasken duhu
(chocolate color). Ko dana sake samun daman
na matso kusa dashi sai ga gefen fuskarsa tar
ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa,
sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba
ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda
ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya
danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin
irin wadannan dara daran idanuwan ba masu
tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido
mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu
gashin ido da gashin gira masu yawa da
tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau
suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar
fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba
duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a
ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce.
'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a
ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi.
Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban
hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka
kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa
kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun
sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da
rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan
da ake kira african American, hukuncin da na
yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da
'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka
hadu suka same shi bakar fata da farar fata.
Duk da tashin hankalin da na shiga da naji
bayananta sai nayi murmushin karfin hali nace
subhanallah! Bai kamata kice zaki bi kowacce
hanya ba gara ma kice zaki bishi da addua in
da alkhairi Allah ya yi. Khadija tace bawai ina
nufin zan fita daga musulunci ba akansa ba,
amma fa dole saina saka malamaina sunyi min
addua. Na fahimci maryam ahmed da mansura
mahmud suna sonsa kin san su da bin
malamai, in ban dage ba sai sun janye
hankalinsa. Gaskiya tunda nake a duniya ban
taba ganin Kyakkyawan bakar fata irinsa ba, ko
kin taba gani? Na girgiza kai nace ban taba
gani ba, amma shima yana ji da kansa dan
yasan ya hadu kuma mata suna nuna masa
haka. Ba kya ganin 'yan matan nan medical
student suna ta kawo hare harens garshi?
Khadija tace tabbas na gani, shiyasa nace sai
nayi da gaske fa. Ai mu uku ne kadai muka
amayar da maitarmu a waje, nasan mata da
yawa sun dasa a ajin fada ne kawai basu yi ba.
Kin burge ni aisha umar, sai naga kwata kwata
ba ya gabanki, ko a bayan idonki muna yabonki
don kina kama kanki bakya shiga rigimar da
tafi karfinki. Sai kawai nayi murmushi nace a
raina kallon kitse kike yiwa rogo, aini zuciyata
tuni ta kunsa min abinda zuciyoyinku basu
kunsa muku ba. Tabbas nasan burina da fatana
akan dr shurain yafi nasu. Aisha umar kalli
motar can, inji khadija yayin da ta matse 'yan
yatsunna don gigicewa. Na juya da sauri, sai
naga wata dankareriyar mota baka mai farin
gilashi. A cikin motar kuma zankadeden mutum
ne, sanye da farar riga da bakin gilashi a
fuskarsa. Ya kalle mu, muma kallonsa mukayi
sai ya kawar da kai ya fisgi motarsa da gudu
ya nufi gate din fita. Na dubi motar har da
waiwaye sannan na juyo na dubi khadija nace
motar nan ta hadu, haka mutumin da yake
cikin motar ma ya hadu. Wanene shi? Tace au
baki gane shi bane? Dr shuraim ne likitan da
muke zancensa yanzu. Dan halak yaki ambato.
Sai nace kai bashi bane, ai shi bakar suit ya
saka. Tace bakar ta saman ya cire, ya bar
farar ta ciki. Baki shaida jan neck tie din bane?
Sai nayi shiru saboda haduwarsa tafi karfin
tunanina, sama ta yiwa yaro nusa ba zai iya
tabawa ba sai dai ya daga ido ya hango. Sai
na tuna ai Allah ne ya halicce shi wanda ya
halicce ni, babu wanda yafi wani a wajensa sai
wanda yafi bauta masa don haka na daina
raina kaina. Na kudira a raina zan sake rikar
addinina yadda zan sami babban rabo a lahira,
koda kuwa ban sami wanda nake so a duniya
ba. Zuciya ta fara warwarewa daga kuncin
daya damke ta na son maso wani. Tun ina
sauraron surutun da khadija takeyi har na
daina ganewa, burina kawai in ganni a gida na
shige lungun dakina. Ina hau yamutsattsiyar
tabarmata in kudindina inyi ta aiyano ni tare da
abin kauna ta shuraim. Ina daukar jakata sai
nayi musu sallama na nufi gate din fita a
sanyaye ina tafe ina tunani. Na fita waje na
tsayar da acaba kamar kullum na haye ya kai
ni kofar gidanmu. Tun daga zauren gidanmu
nake cin karo da matan gidan suna ta
hidindimunsu na saye da sayarwa da surutin da
suke yini suna yi, ayi gulmar wannan, a zagi
waccan, yau sai suka ganni ba kamar kullum
ba. Da bayan na gaishe su sai in dan zauna ayi
barkwanci sannan in wuce cikin gida, yau babu
kanta da kyar nake magana, sauri kawai nake
yi in shige ciki. Sunyi zaton yunwa nakeji, har
suke zolayata da cewa abida ba ta nan, ba'ayi
abinci ba. Na wuce abu na, na iske abida tana
dafa a binci a risho. Tana ganina tayi kasake
tana kallona, ta san akwai damuwa tunda bata
jiyo muryata ba, bata gano murmushina ba
saboda ina da yawan dariya. Ta dube ni tace
aisha farida kalau kuwa, ko allura zakiyi