Showing 6001 words to 9000 words out of 99740 words

Chapter 3 - DUK KYAN TAKALMI COMPLETE BOOK 1 BY ESHAT.pdf

Advertisement

ESHAT   

23 Mar 2025

5579

karasa makarantar primary sai
yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen
sabongari na zana jarabawar common entrance
ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa
sai naci jarabawa aka turani makarantar da na
zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya
karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden
makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya
barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo,
gashi bansan kowa ba a makarantar amma
daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai
na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a
na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi
da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son
ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na
yi suna a makarantar nan da nan malamai ma

suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya
magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga
aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu
sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min
siyayya ba da biyan kudin makaranta ba
kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba
kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na
farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar,
sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a
jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin
haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci
ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya
kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan
koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya
harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da
ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani
hakuri cewar zai mayar dani makarantar
gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na
koma makarantar shekara naci gaba da karatu,
daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin
dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a
FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa
da yaran hausawan da suka sami horon turanci
tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science
class) har Allah ya kaini aji shida aka bani
shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara
ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni
nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan
babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar
makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana
kwatance dani saboda kokarina. Da muka
gama makarantar ita da malamai sai da sukayi
takaicin rashina saboda ba'a sami madadina
ba. Bayan gama makarantata da wata uku
yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani
kudin mota da guzuri na zuwa shagamu,
saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da
'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani.
Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da
tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu
daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba.
Ina samun wasikun kanwata munauwara akai
akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai

ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar
an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3
anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai
yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu,
dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba
zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan
'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya
suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk
da rashin wadatar da muke ciki a kano sai
naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da
gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa
har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda
yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege
a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi,
gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye
da ashirin, yare kala kala kamar hausawa,
yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban.
Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara
layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan
shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita
kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin.
Saboda tausayin halinda na same ta kusan
dukka kayana na sakawa na bata kyauta,
sannan na hada mata mayafai, sarkokina,
takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk
kudaden dana samu na bata dukka kudin mota
na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha
kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na
tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan
rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake
haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu
komai duk na rabar da kyana kuma da masu
kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin,
yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na
dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan
haka na daina zuwa taron biki ko gidan
kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi
garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye
wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min
wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta
kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka
inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da
cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da

shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan
zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya
kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna
bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana
suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri
da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta
koma wajen mazansu, su kuma suka
tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai
dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar
gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da
kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a
duhune sai a zaci abida ta fara bin maza.
Sukayi ta zuba masa bayanan da dole
hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi
mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace
ya iske ni a kwance yace min in kira abida
itama ta shigo nan dakin yana da magana da
ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna
karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace
gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci
abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura
tayi masa karya akan abinda zai tambayeta,
haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana
tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu
fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da
fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai
fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha
farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a
gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi
wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai
firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan
ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh
haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta
fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada
kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na
dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane
nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na
daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana
duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe
ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka
kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai
fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada
kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi

hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra
ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga
mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai
harara koda yaushe. Sai na daina fita koina ,
koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare
da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta
ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe
shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba
ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara
yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta
bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje.
Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye
tace ka yafe mana laifukan da muka maka,
munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya
hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu,
rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka
bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe
dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce
ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu
saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin
tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai
yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen
kawayenta shine nake bata aron kayana ta
saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda
'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo
ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai
yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk
laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da
ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka
fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi
da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk
shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya
lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya
baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta
bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira
dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu.
Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta
iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas
macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya
zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi
nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo
yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5
Saurayina guda daya nake kulawa mai suna

musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan
mu tare, yana sona sosai nima haka saboda
yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire
yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai
aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa
bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu
auren gida, shi kuma ni yake so ya
aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a
hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na
daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen
kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a
shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana
sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min
leshi guda daya da atamfa ya hada min da
naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min
fada in daina boye masa sirrina saboda yadda
yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce.
Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa
ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai
in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani
hakuri akan halinda yake ciki shi da
mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu
zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da
addu'a Allah Ya karkato da zuciyar
mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren
dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire
ya fito naci credit takwas, geography ne kadai
naci pass shima dan a ranar da muka yi
jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan
ya sami kudi zai saya min form din jamb in
wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a
jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi,
bani da mai bani kudin mota da kudin sayan
handout, gashi dole sai an saka sutura masu
kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga
shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk
wadannan sabida dan abinda yake samu ba
mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan
sami ayyuka da yawa suna samun kudi a
business center yake aiki, suna typing a
computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to
zai samo min management in fara, nan ma
nace bana so nafi son inyi schl of nursing

saboda ba ruwana da neman kayan sakawa,
suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko
yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin
ra'ayin yayana. Yayana ya amince da
shawararmu kuma yaji dadi musamman da
musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi
masa sallama da yayana hussaini ya kara yi
masa bayani. Yace zai taimaka min da wata
dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince
yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka
hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake
bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya
ta malam aminu kano dake unguwar court
road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku
ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka
karatu na yi tayi haikan, ban taba samun
matsala ba cinye jarabawata nake yi koda
yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar
damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa
kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court
rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus
zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin
acabana kit da kit babu canji wata rana ko
purewater zan sha sai dai kawayena su saya
min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan
lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai
dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun
gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail
kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma
duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko
na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi
fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in
kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba
sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake
ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna
min bakin hali daga baya kuma in dinga jin
kananan maganganu cewar na cika san banza
kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina
abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a
saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon
kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan
tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta
ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a

wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin
mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija
bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari
sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk
wasu manyan littattafai na karatu (text book)
babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi
morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita
ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani
nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan
littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya
sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata
rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk
ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi
sai yace in hakura kada inje makaranatar randa
ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da
kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da
kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya
naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira
ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa
kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da
nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi
hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka
tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu
wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake,
basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai
sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli
wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake
sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga
bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su
tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan
kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate
ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin
rayuwata a wannan bangaren saboda bani da
wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan
amayar musu da radadin da zugin matsalolin
da suke addabata. Kawata guda daya, itace
aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar
yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba
dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu,
koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin
gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin
da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi
a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta

tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a
baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata,
ni burina guda daya ne shine in gama karatuna
in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan
gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna
shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron
kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga
mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida
ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu
kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan
karami mun cunkushe gashi su dukka yaran
abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba
katifar sai zarni take dan haka na hakura da
katifar na bar musu. Na koma kwana akan
tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla
akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin
wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu
kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata,
rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace,
tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi
tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar
makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan
kawa, na rike talaucina na kama kaina bana
sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai
gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina
karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida,
wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai
'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka
shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni
'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi
musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba,
tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan
Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU
Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na
rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa
lafiya muke wadanda aka kwantar dasu
sakamakon wasu kurajen da suka feso a
jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron
maryam tana nunnana mana yadda ake aiki,
domin neman karin bayani sai tace bari ta
hada mu da kwararren likita wanda ya kware a
bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga
muma muka bita a baya da alama dakin

daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla
da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda
naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun
iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu
daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya
da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan
wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai
yake yi musu cikin harshen turanci kai kace
baturen america ne, kalmomin kimiyyar
(botanical names) da yake ta ambato yana
jerowa layi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login