Showing 1 words to 3000 words out of 68416 words
Chapter 1 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
[10/21, 2:54 PM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU.
By
CHUCHUJAY ✍
EPISODE 1⃣
KIRIKIRI MAXIMUM PRISON LAGOS STATE NIGERIA.
A kullum zaryarta zuwa prison ɗin yana mutuƙar bata mata rai ,
Bata jin wani tausayi ko rashin jin daɗin abunda yake faruwa da shi duk da irin ɗinbin san da
tayi masa a baya,
Ta sa a ranta akan cewa kaddarar sa ce,duk wani wanda zai nuna mata rashin dace wa akan
bibiyar sa Ya bata takardar sakin ta Kallansa kawai take sannan bata sawa a ranta domin ta
gama yarda da yarda ɗan Adam yake da hallayyarsa,
Cikin handcuff Dukkan hannayen sa biyu Haka aka rako sa ,kallan sa kaɗai yakan sa mata
faɗuwar gaba ,hakazalika a yanzu haɗa ido kawai da tayi dashi sai da Taji mumunar faɗuwar
gaba Ta kawo mata ziyara,
Abubuwan da suka faru tsakaninta dashi take suka fara tariyo mata ,danne su tayi dan tafiyar
su babu abinda ya haifar mata sai tashin hankali da dana sani,
Kallanta ta mayar gareshi dan ta gama yarda a yau sai tabar kirikiri da sakinsa akanta,
Glass Mai Kauri ne tsakaninsu Wanda yake ɗauke da bulloli Shida,telephone ɗin dake sakale a
gefenta ta ɗauka ta kara a kunne yayin da shima yayi halkan,
Magana ta fara "Hafiz nazo ka bani takarda ta dan Allah mu daina bata lokacin juna kodan
zaman mu na farko kan ka chanja Mai ɗan dadi duk da yaudara ne, ka sakeni dan koda ace
huƙuncin ka ba kisa bane ta hanyar rataya ,koda kuwa ace za'a cire duk wani charges akan
ka,Hafiz bazan taba sake zama da Kai ba. Kukan da yasa shine abunda yayi mutuƙar bata mamaki,tasan wanene hafiz mutum ne Mai
mutuƙar juriya da jarumta ,amma a yau yana mata kuka dan kawai tana masa maganar Ya sake
ta,
Shiru tayi tana Mai jin kukan nasa ta cikin telephone ɗin a yayin da yake ratsa dukkan wani
sasshe na jikinta,
Ina ma hafiz bai zabi tarwatsa rayuwarsu ba ,ina ma ba'a kamasa da laifuka mafi munin wanda
aka kamashi dashi ba,
Ina ma!
Tana kokarin cire telephone ɗin dan bazata iya cigaba da jin kukansa ba ta tsince muryarsa
yana cewa"UMAIMAH dan Allah dan Annabi kar ki takura mun na sake ki,ni mutum ne Mai
laifuka da dama a wajen ubangiji, kila yamun Rahma sakamakon mutuwa da zanyi a matsayin
mutum mai Aure,"Ke mutuniyar kirkice UMAIMA ,a dukkan rayuwata ban taba Auren mace Mai
kamala da haƙuri ba kamar ki,ke maratussalaha ce ,ke macece yar Aljanna,Mai tausayi da jin
kai,dan Allah UMAIMAH kimun wannan Alfarmar guda ɗaya duk da kuwa ni Azzalumine a
wajenki.
Bata san lokacin da ta kwace da wani irin kuka ba Mai mutuƙar cin rai,
Take duk ikirarin da take na rashin jin tausayinsa Ya kau dan ta tabbata koda a ce babu
soyayyar sa a tattare da ita tasan tabbas yana da soft spot a wani gurbi na zuciyarta,
Tana kokarin cire telephone ɗin yace"UMAIMAH bana so na mutu,Ina mutukar tsoran zuwa na
haɗu da mahaliccina,bana so umaimah ,Ina san na rayu na dai dai ta tsakanina da ubangijina
na rayu da ɗana wanda shi kaɗai Allah Ya bani,sannan babban farin cikina ta tsatsanki Ya
fito,"Amma kash kaico na ,bani da wata damar ,nayi wasa da wadda Allah Ya bani ,nayi fatali da
kyautar ni'imar da yayi mun saboda san zuciya da kwaɗayin duniya wanda a yanzu Ya kaini Ga
dana sani,
UMAIMA gobe za'a rataye ni ,gobe zan mutu,babban tsorona kenan,a razane nake da Ya
zamana nasan ranar mutuwa ta.
Shiru tayi tana Mai kallan sa ta glass d'in da Ya rabasu,hannunta tasa ta dafa glass ɗin a dai
dai inda Ya ɗora hannunsa ,
A hankali ta shafa tana Mai tuna yarda ya nuna mata soyayya kamar zai cinyeta a wata biyu na
Auren su,
Lumshe idanunsa yayi wanda suka faɗa saboda tsantsar masifa yace"kar ki bawa
ABDALLAH labarina idan Ya girma,bana san yasan babansa failure' ne a rayuwa sannan na
yarda da zaki bashi tarbiyya Mai kyau,kar ki barshi Ya rabi dangina dan na bar miki shi halak
malak,dangina ba mutanen da zanyi Alfahari dasu bane Kema kin sani sune mafarin jefani cikin
wannan masifar,ina so idan da dama ki raini ABDALLAH Ya zama cikakken Mahaddacin Qur'ani
,Ya zama malami akasin mahaifinsa,"
Idan Kinje gida a side drawer dake gefen gadona na aje cheque na milliyan goma ,ki ɗauka ki
juya ma ABDALLAH ,wallahi tallahi ba ta hanyar banza na samesu ba,kuɗi ne masu tsafta babu
gurbaci a cikinsu,
Kisa Abdallah yana mun Addua ,Kema idan har da dama zan samu a gurinki bazan ki ba, duk
da nasan abun zaiyyi wuya duba da yarda na cutar dake a rayuwa.
Ina mai mutuƙar baki hakuri akan ki yafe mun,Allah Ya baki miji Umaimah wanda yake salihi,
Ina Mai miki addua ki Auri miji nagari ba irin mazajen da kika AURA GUDA UKU BA.
Allah Ya haɗa fuskokinmu da Alheri.
Nagode Allah yayi miki Albarka.
A Yarda ma'aikatan suka kawo sa haka suka ƙara tasa keyarsa dan komawa da shi kurkukun
da suka dauko shi,
Buga glass ɗin tayi wanda hakan yasa shi tsayawa,ma'aikatan basu ja ba dan sukan bawa
wanda yayi expire dama duba da duniyar ma barinta zaiyyi baki Ɗaya,
Roban take away ta ɗauko daga jakarta wanda bata san dalilin da yasa ta zo dashi ba,ɗaya
daga cikin ma'aikatan ne Ya zagayo Ya karba,Ya juya zai tafi tace masa"ka faɗa masa Na kawo
masa favorite dambun naman kazan da yake so sannan ni na soya,sannan insha Allahu indai
na dena masa Addua to numfashina ne Ya yanke daga jikina,sannan zai Alfaharin abunda zai
tafi Ya bari."
Wani irin kuka ta fashe dashi a yayin da taga yana mata murmushi lokacin da aka aika masa da
Saƙonta,da sarsarfa ta tashi tabar gurin tana Mai Kallan yarda aka maidashi har a lokacin
murmushin na akan fuskarsa,
Kuka take sosai a motarta tana Mai jin wani irin zafi a cikin kirjinta,tabbas rayuwar Hafiz babbar
Aya ce ga mutane .
WACECE UMAIMAH ?
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,
Ƴa ɗaya tilo a gurin Amaryar Alhaji usman bulama,
Alhaji usman bulama mutumin Zaria ne wanda zama Ya kaishi garin ADAMAWA YOLA garin
FULANI tushen kunya,
Alhaji Bulama sharraren mai kuɗine wanda ake lissafawa a cikin dumbin masu kuɗin duniya ba
kasa kawai ba,
Architecture ne wanda Allah ya habaka a hanyar domin irin tsabagen basirarsa,
A irin buɗin da Allah yayi masa har Construction company (BULAMA CONSTRUCTION
COMPANY) ne dashi wanda suke samun kwangiloli masu dama wadda sai da rabanka ma suke
karba.
Matan Alhaji bulama biyu,hajiya zuwaira itace uwar gida wadda ta haifa masa yara huɗu dukka
maza babu mace ko daya.
Mutane kance soyayya da sa rai da yayi ga ɗiya mace ne ya sashi ƙarin mata amma a zahiri
kuwa ba haka bane,
Soyayyar Bafulatana Nana Surbajo dake yawan kawo nono Companin sa ita tayi masa mugun
kamu duk da kuwa yanayi kamar bai taba kula da ita ba a yayin da ita bama tasan yanayi ba
duba da shi ɗin mutum ne da ganinsa sai ka cike Paper.
Da yake Allah Ya kaɗara matarsa ce bai kasa a gwiwa ba wajen bincike akanta inda Ya gano
daga rigar da take yaje ma iyayenta da maganar Aure tun kan Ya furta mata soyayya.
Iyayenta ba masu tsaurin ra'ayi bane dan haka suka bashi dama Ya nemi soyayyar nana
surbajo duk da yarda danginsu suka masu Cha akan zasu bama dan yankan Kai diyarsu tilo.
Ba wani wahala Ya sha ba Ya samu Auren surbajo wanda kwata kwata baiwa uwargida zuwaira
daɗi ba amma babu yarda zatayi da yin Allah dan haka abun ya kullu yarda Allah yaso.
A shakara Allah Ya Azurtasu ɗiya mace wadda taci suna UMAIMAH,sosai Alhaji bulama yayi
mutuƙar murna wadda tasa shi fitar da zakka Mai mutuƙar tsoka,
A duniyarsu ta shahararrun masu kuɗin babu wanda bai san da samuwar UMAIMA ba da kuma
irin Adadin ƙaunar da yake mata dan baya iya boyewa,
Wannan ƙaunar da yakewa UMAIMAH ba karamun damun hajiya zuwaira take ba da
yayanta uku, cikin yaranta Abubakar,usman,umar,Aliyu,Abubakar babban danta ne Kawai yake
jin Umaimah a cikin zuciyarsa kamar uwa daya suka fito amma sauran kuwa ba karamun saka
masu kiyayyar umaimah da uwarta tayi ba.
A haka umaimah tayi ta girma cikin soyayya da kulawa duk da kuwa irin tsangwamar da take
sha gurin uwar gidan Alhaji bulama da yaranta uku,
Tun kafun tasan menene kiyayyar har ta fara ganewa tasan mema kiyayyar ke nufi.
A lokacin da ta shiga shekara goma sha biyar Allah yayi ma mahaifiyarta rasuwa sakamakon
brain cancer da ya sameta,babu irin kudin da Alhaji bulama bai kashe ba dan kawai Nana
surbajo ta warke amma abun yaci tura,
Tun rasuwar Nana surbajo Umaimah ta ci buri kuma ta sawa ranta sai ta zama surgeon,
Da wuri ta fara makaranta sabida irin kaifin kanta,tana da shekaru goma sha biyar ta kammala
karatun secondary school ɗinta ,
A shekarar da ta zagayo ya kai ta harvard university inda ta fara karatunta na liktanci,
Babu irin kauɗin da hajiya zuwaira batayi ba akan Kai umaimah Harvard da akayi amma yayi
kunnen uwar Shegu da ita, umaimah na shekara ta uku a Harvard mahaifinta yaje Ya ɗaukota,
Bata tambayesa dalili ba d'an tasani idan da wanda yake san cigaban ta bai wuce shi ɗin ba
sannan ta yarda duk wani decision da zai yanke akanta mai kyau ne.
Bayan dawowarta Nigeria tayi mutuƙar mamaki da taji wai ansaka ranar Aurenta da Habib
Aliko yaran Aminin Daddynta,
Koda Daddynata yayi mata magana akan Aurenta da Habib nuna wa tayi duk abunda Ya yanke
akanta dai dai ne muddin karatunta bazai tsaya ba,
Tasani Daddynta Ya chanza amma bata saka wa ranta komai ba,baƙaramar rawa Hajiya
zuwaira ta taka na wajen Auren Umaimah da Habib d'an ita ta haɗa komai.
Yaya Abubakar kaɗai ke bata baki yana Mai nuna mata Auren ma ba matsala bane sannan
bazai shiga rayuwar karatunta ba tunda Daddy Ya jaddada ma Habib d'a mahaifinsa kan zata
cigaba da karatun ta and baya buƙutar su ɗauki nauyi zaiyyi komai,
Haka nan ya Auri Habib inda Ya ɗaukota daga garin adamawa ya kawota kano,
DE ta samu a TURKISH MEDICAL SCHOOL inda ta dora daga inda ta tsaya.
Tun ranar da aka kaita gidan HabIb tasan ba mijin Arziƙi bane 'dan a buge ya shigo ,bai tsaya
anan ba kuma a ganawarsu ta farko raping ɗinta yayi wanda yaji mata ciwo sosai,tashin
hankalinta bai fara ba sai da tasan Habib manemin mata ne sannan kuma ɗan giya ,bata sanar
da kowa ba take zaune dashi a Haka musamman da taga yarda Daddynta ke mutuƙar yaba
hankalinsa 'dan munafukine na masifa saboda baya taba nuna shi 'dan iskane gaban iyayenta,a
Haka har rabo Ya shiga tsakaninsu ta haifa masa yaro na miji wanda yaci suna NAMEER,
NAMEER na da shekara ɗaya Habib ya saketa sakamakon dawowa da yayi gida a buge suna
zaune da NAMEER a falo 'dan kawai tayi faɗa da mita akan Ya daina shigo musu gida muddin
giya bata sake sa ba,
Cikin maye Ya mata saki uku wanda a musulunci ma ta saku,
Daga baya Ya dawo yayi ta naci akan shi bai saketa ba amma Daddynta yayi masa koran
kare sannan Ya ƙwaci NAMEER ɗin da Ya kwallafa rai akai wanda mahaifin Habib bai jaba 'dan
baya san alaƙarsa ta baci da Alhaji Bulama.
Kamar wasa bayan iddarta Daddy ya sake introducing mata BILAL shima dai yaran
Abokinsa,
Abun ne Ya dameta duba da Ko Auren ta na fari bata gama Alhini akai ba amma wai Daddyn Ya
kawo maganar Auren ta da wani,wanda shima kamar Habib ba sanshi take ba,
Kuka ta ɗingawa Abubakar Akan ita bata san Auren Bilal 'dan Auren ma bata so baki daya
,she's just 21 amma ace wai har Zatayi Aure na biyu,
Baki abubakar yayi ta bata akan zai je ya samu mahaifinsu yayi masa magana,
Koda yawa Daddyn nata magana sai cewa yayi Ai hajiya zuwaira taje wajen malaminta dake
mata Addu'a Ya tabbatar mata muddin Umaimah ta zauna babu Aure zata lalace kuma babu
wata nasara da zata tabayi a rayuwa shi kuma bazaya taba barin ɗiyarsa tilo guda ɗaya ta
tagayyara ba, Ƙara yarda yayi da Lallai daddy yana san umaimah to extent that yama rasa inda zaisa
Alƙibilar tunaninsa,'dan ko shi da yake ɗan Umma yasan maganar ta ba dai dai bane duba da
kalar tsanar da take wa UMAIMAH ɗin ,kawai dai tace tana so ta bar mata gida,
Kara bawa umaimah hakuri yayi a karo na biyu inda ta yarda da Auren BILAL wanda yake da
mace ɗaya,shima kuma mazauninin garin kano 'dan Haka Ta dora karatunta inda ta tsaya.
Duk da tarin kuɗin mahaifinta hakan bai hana kishiya da miji da uwarsa galaza mata ba,gida
ɗaya suke baƙi dayansu,
Karatun ta ne basu so amma kuma babu yarda zasuyi dan basu suke ɗaukan nauyin Karatunta
ba sannan yarjejeniya ce akayi Mai zaman kanta,a Haka tana wannan rayuwar ta sake samun
ciki cikin shekarar su ta biyu da Aure duk da bata so ba amma Haka nan Ta ɗauki dangana,
Duk wani wulakanci da take gani gidan Bilal dannesa tayi Ko yaya Abubakar bata faɗawa ba
'dan faɗan ma is pointless 'dan tasan babu mai duba mata kar ma ace Daddy zaice kawai
Zaman Auren ne bata so.
Hankalinta ta mayar kan karatunta wanda take samun nasarori sosai a ciki,gefe guda kuma
tana kula da NADIYA yarinyar da ta shiga tsakaninta da BILAL Yar shekara,
Saukinta kawai NAMEER YARO DAN SHEKERA UKU a lokacin yana gurin Matar Yaya
Abubakar "Sadiya" wadda ke nan cikin mansion d'in Bulama 'dan bai yarda Ko wanne ɗan sa
Ya fita da iyalinsa daga gidan ba ,duba da gidane duniya guda.
CHUCHUJAY ✍
To Be continued.
[10/21, 8:53 PM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU
BY
CHUCHUJAY✍
EPISODE 2⃣.
Idan kana bibiyar labarin Rayuwar Umaimah zakace Shin dama masu kuɗi ma suna samun
kalubale a rayuwarsu duk da kuɗinsu?
Zaka na tunanin tayaya Umaimah zata jure dukkan wannan Abun bayan mahaifinta sharararen
Mai kuɗi ne!
Abun ba Haka yake ba,sau da dama kana da kuɗin da komai amma muddin Allah bai so ba
baza ka ji daɗi ba tawani bangaren ,Ya 'dan ganta da kaddarar ka,
Auren dake tsakanin umaimah da bilal bai wani lasting ba saboda irin sharrin da suka haɗu
suka haɗa mata,
Tana kwance kan Gadonta tana bacci ta tsinkayi hayaniyar mutane akanta,koda ta farka mijinta
da mahaifiyarsa da matarsa ta gani a gefenta sai gefe guda wani ƙato da bata taba gani ba a
rayuwarta kwance kan gadanta!
A ranar suka mata wulakancin da ta kasa mantawa a rayuwarta wato kazafun zina wanda ya
Kai har bilal Ya ke tantamar kasancewar Nadiya yarsa ,duka bilal yayi mata sosai da belt wanda
sai da Ya farfasa mata jiki kana ya sake ta saki biyu,
Abu na farko kenan da yaje kunnen Alhaji Bulama wanda yayi mutukar harzuƙashi,
Kuka sosai umaimah Take masa tana Mai masa rantsuwa akan bata taba Aikata zina ba
hasalima ita bata san mutumin da ta farka ta gani a gefenta ba,
Mahaifin bilal Ya kira wanda baida masaniyar Mai ke faruwa saboda Ya rabu da mahaifiyar
bilal,
Kwata kwata Alhaji bulama bai tsaya yi masa da sauƙi ba saboda yarda ranshi Ya baci,hakuri
Alhaji muntari Ya bawa Daddy saboda shi bai masan wainar da ake toya wa ba,
Gudun kar zumuncinsu ya lalace yasa Alhaji Bulama yace masa zai bincike sannan yana so Ya
fitar da hannunsa akan duk abinda zai biyo baya dan muddin Ya gane bilal ne baida gaskiya sai
Ya ɗauresa.
DNA Ya fara sawa akayi conducting akan Nadiya da bilal wanda Ya fito 99% positive,
Da bincike yayi bincke aka gano haɗine na matar bilal da mahaifiyarsa ,baki ɗayansu Alhaji
Bulama Ya daure a yayinda yasa a bawa bilal mugun kashi ladan dukan da yayi wa yarsa
sannan yamasa haramiyya da NADIYA.
Haka nan ta cigaba da zama a kano 'dan karasa karatunta wanda a lokacin tafi yinsa cikin
kwanciyar hankali ,
A shekarar da ta gama karatunta ta haɗu da Hafiz matashin Mai arziki wanda haduwar farko Ya
nuna mata soyayya ,ita macece da bata taba soyayyar ɗa namiji ba sai akan Hafiz ,
A hankali soyayya Ya kullo tsakaninsu inda baki daya bata ganin aibunsa musamman da yasan
tana da yara biyu Ya amince da daukan su idan sukayi Aure ,
Da kalamai masu daɗi Hafiz yasa umaimah ta saki jiki dashi sosai,
Bayan ta gama karatunta ta samu licence na fara Aiki takai Hafiz gidansu a matsayin mijin da
Take san Aure,
Kiranta Daddynta yayi Ya zaunar da ita Ya tambayeta akan gamsuwarta da Hafiz sannan Ya
jaddada mata shi bazai sake ce mata ta Auri kowa ba idan tana so ma zata iya cewa bata so
baki ɗaya bazai ce mata dan me ba,
Nuna masa tayi ta gamsu da hafiz wanda shima a hankali bayan binciken