Showing 3001 words to 6000 words out of 68416 words

Chapter 2 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4740

da yayi akansa Ya
bada yardar sa akan Aurensu,

Da shagalin Aurenta da shagalin murnar samun aikinta Alhaji Bulama Ya haɗa mata
gagarumun biki .

Kamar yarda Hafiz yayi mata Alƙawari kuwa Haka Ya ɗauki Nameer da Nadiya matsayin nashi,

Lagos suka wuce tare duba da yarda kasuwancin sa Ya tarkata chan,inda ita kuma ta fara
aikinta cikin kwanciyar hankali.
Soyayya suke gwanin ban sha'awa a gidan Wadda tayi lasting na wata biyu kacal,

Hallayyarsa bata fara fito mata ba sai bayan dawowarsa daga wata tafiya da yayi zuwa indiya a
lokacin da karamin cikin Abdallah ,babu kalamai masu daɗi Ko zama suyi hira mai sanyaya
zuciya ballantana akai Ga mu'amala ta Auratayya,

Wasa Wasa tun abun tana ɗaukarsa wasa Har ya fara wuce tunanin ta,

Haka take dannewa tana koƙarin nuna masa kulawa amma hantara da kyara babu abunda
baya mata.

A cikin gidansa akwai ɗaki guda wanda bata taba shigansa ba hasalima bata san dashi ba sai
ranar da Yayi wata dawowa gida cikin dare a lokacin watan Abdallah biyu.

,tana jin shigowarsa ta tashi ta fito dan jin dalilin da yasa bai shigo da wuri ba,tayi mamakin
ganin yarda Ya dana wani katon photoframe dinsa ,boyewa tayi ganin bangon Ya buɗe Ya
bayyyana kofa,

Binsa tayi a baya a hankali ta shiga ɗakin itama,

Mamaki tasha sosai lokacin da ta ga wasu kayan tsubbu da pads na mata a jere a saman wani
table,ba sai an faɗa mata ba tasan ɗakine na tsubbu,

Saurin komawa tayi da baya ta koma ɗaki jikinta na faman rawa musamman da taji yana faɗin
zai kawo musu jarirai biyu kamar yarda yayi wa King manta Alƙawari.

Komawa tayi ta kwanta kamar tana bacci,

Dama bai kwana a ɗakinta a yanzu 'dan Haka ta saka key ta koma ta kwanta tana zulumi,Allah
yasa Nannyn su NAMEER na tare dasu kuma suna kulle ɗaki,fargaba da tsoro sune kawai
abunda Ke fama da ita,shekarar ta a lokacin Uku da Hafiz duk da fizge fizgensa bata taba sanin
money ritual yake ba,juyawa tayi ta kalli jaririnta Abdallah tana ayyanawa kilan ma da Abdallah
cikin jariran zai bada.

Tunanin barin da tayi farkon Aurensu tafra wanda tasha mutuƙar wahala duk da karamin cikine
amma bata kawo komai ba musamman lokacin da ta tsincesa yana waya akan cikin wanda ya
mata karya da Auntynsa ce.

Tafiyar gaggawa ta kirkira zuwa Adamawa wadda ko sanar mashi ba tayi ba,sallamar
nannysu tayi ,a ranar da suka je adamawan da dare Ya kirata yana tambayar tana Ina ,karya ta
masa tace taje kano ne karbo wasu takardu,sabida abin bai gabansa bai tambayeta abunda
yasa ta tafi bata faɗa masa ba sai cewa yayi ta ɗauke Abdallah suje south Africa zai zo Ya
samesu,

Batayi magana ba wanda dalilin hakan yasa shi buga mata wata uwar tsawa ,

To kawai tace masa ta kashe wayanta,

Bataje gidansu ba ,gidan kakanninta da Daddynta ya ƙera masu taje,



A ranar da safe ta tashi da labari Mai mutukar gigitarwa ,wai an kama Hafiz sannan ane neman
iyalansa 'dan case ɗin da aka kamasu babba ne kuma mutum ɗaya daga cikinsu da hannun
matarsa wanda Hakan yasa ake nemansu ,

Lokacin ta gane mai yake nufi da su tafi south Africa,

A ranar ta san wanda ta Aura,Ashe Hafiz babban ɗan yahoo ne wanda suke bada jinin mata da
jirirai 'dan shi kam matansa biyu Ya bada umaimah ɗince yake ma san da bazai iya bada ta ba
da ɗansa wanda dalilin hakan yasan asirinsu tonuwa,

Bai tsaya anan kaɗai ba harda safarar mutane wanda matar ɗaya daga cikinsu ke musu safara
da yawancin yara da mata,ba ma nan kadai ba har Arm Robbery sunayi,

Tasha kuka sosai sosai lokacin da tagane wanda take so jabu ne,

He was lowkey 'dan duk binciken da mahaifinta yayi akansa bai gano wani nakasu nashi ba ,

Kawai an samu labarin shi ɗin marayane mara uwa da uba wanda Ahalinsa suka banzatar daga
bisani kuma bayan wani Alhaji Ya jashi lagos yasashi kasuwancinsa wanda hakan ya
habbakasa .

Ashe akasin Haka ne money ritualist ne,

Bayan zama da akayi a kotu da binciken da akayi akan umaimah aka yanke masu hunckin kisa
ta hanyar rataya.







BAYAN SHEKARU BIYU.

CITY TEACHING HOSPITAL ADAMAWA STATE NIGERIA.

7:30 am

Cikin taƙama da kwarewa take takowa cikin harabar asibitin a yayin da wani Nurse ke riƙe da
jakarta,

Idan akace maka tana da Yara uku zaka ƙara tsayawa ne ka Kalle ta da kyau har ka ƙaryata
Mai faɗin maganar,

Asalin Umaimah irin matan nan ne wanda sukayi kyawu irin na fulani har zuwa jikinta, bata da
ƙiba amma ba Haka ke nuna bata da ƙira ba,

Kirar jikinta ita ake kira kalangu,a fuskar ta babu abunda zai fara ɗaukar maka ido kamar sexy
eyes ɗinta masu kama da tana jin bacci,

Zuwa Ga maidaidacin hancinta Mai 'dan tsayi sai cute lips ɗinta pink,

Ba tada yawaitar sakewa saboda irin abubuwan data fuskanta a rayuwarta ,kullum idan zaka
ganta serious face ɗinnan ce kawai a fuskarta ,tsakaninta da colleagues ɗinta abunda Ya shafi
aiki amma Babu alaƙa ta abota,mutane da dama akan gulmarta suke asibitin ,wasu suce girman
kai ne ke ɗawainiya da ita 'dan tana ɗiyar Mai kuɗi wadda komai take so zata samu wanda
sukance aikinma saboda shi ta samu saboda connection 'dan tana cikin manyan surgeons na
asibitin.

Abun Ɗaya da basu sani ba shine da kuɗi nasiyan komai da batayi Aure uku ba,

A rayuwarta mutum ɗaya ta taba ƙawance da itama shekarar da take harvard suka haɗu
HINDU duk da shareta da take bai hana HINDU tusa Kai rayuwar umaimah ba a yayin da ta
sake mata duba da lokacin tana da ƙaracin damuwa 'dan rashin mahaifiyarta yayi ƙaranci
saboda yarda mahaifinta ke nan nan da ita,


Kai tsaye Cabin ɗinta ta nufa 'dan Ko karyawa batayi ba,

Aje jakan nurse ɗin yayi kana yace"Dr Bulama,akan matar da za'ayiwa operation ɗin appendix
ɗinnan yan uwanta sun saka hannu and kamar yarda kika faɗa yayi severe Dr Jabir yace Ya
kamata ayi aikin da gaggawa 'dan shi yama sa hannu"



Dago Kai tayi ta kalli nurse ɗin tace"nurse farouk patient ɗina ne Ko na Dr Jabir mene Ya saka
yasa min hannu?

Kara haɗe rai tayi tana Mai jin haushin yarda Dr Jabir ke mata katsalandan a aiki,



Shiru nurse ɗin yayi bai ce komai ba 'dan yana tsoran fadar abunda zai bata mata rai Cos she's
short temper wani lokaci musamman gareshi wanda tunda tazo suke aiki tare,amma sau da
dama shi zai fadi alkhairinta saboda tana masa,

Katse masa tunani tayi ta hanyar cewa"so ka tura mun detail ɗin patient ɗin,"?

Kaɗa kai yayi Kafun yace "yes doctor"

Jawo laptop ɗinta tayi tana faɗin "and I'm hungry jezzz!"

Juyawa yayi yana faɗin bari naje na kawo miki breakfast,
Saurin tafa hannu tayi alamun ya tsaya Kafun tayi saurin tashi tana cewa wait this is serious we
Are going in for surgery now,

Yanzunnan akai ta OR yanzun nan and i need the team available ASAP.

Da sauri Nurse ɗin Ya fita ganin yarda ta fadin maganar ba Wasa.



Koda taje operation Room already team ɗin na nan,hannunta da tayi sanitizing ta miƙa aka
samata Hand Gloves Guda biyu,kana ta juya aka sa mata rigan operation then aka ɗaura mata
face mask.

Bayan gama operation ɗin cikin sa'a tana fitowa bayan tayi disposing Hand gloves ɗinta da
face mask,ta juya zata tafi taji tayi gware da mutum papers ɗin hannunsa sun zube ,
Sorry kawai tace ta wuce ba tare da ta bawa wanda tayi gwaren da ba last kallo.






CHUCHUJAY ✍
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a hospital romance)

By

CHUCHUJAY.

EPISODE 3⃣

Kallo ya bita da shi a lokacin da ta rab'a ta gefansa ta wuce baƙinta da Kalmar Sorry wanda
bayan nan Kallan Arziƙi daya bai ishe ta ba,

Tab'asa yaji anyi,

Dago wa yayi Ya kalli wanda Ya dafa shi ɗin Kafun yace "guy how far".

Murmushi guy ɗin yayi yace wa kake kallone Haka PAKI?

Yana mai tambayar nashi yana Kallan direction ɗin da yake kallo.

Dafe ƙirji PAKI yayi yace "Rayuwata nake kallo Kb,haƙarkarina da Ya bata na tsinta yanzun
nan".

Dariya KB yasa sosai kafun yace "baka da lapia gaskiya ,ka bari sameera taji labari kaga wata
kana faɗin kaga missing ribs ɗinka".

Tafiya PAKI Ya fara KB na biye dashi kafin yace"tun da nake da Kai tsakanin ka da Allah ka taba
ji nace maka ina san sammy?"

Ita kaɗai take haukan ta wanda Ya kamata iyanzu kuma ku sani,

She's not My type of girl,i mean guy she's just not the one.

Kasan irin taste ɗin PAKI da na daɗe ina zayyana maka to yau na ganta cikin asibitin nan and
insha Allahu sai ta zama ta IMAM MUKTAR PAKI.

Bai tsaya jin Abunda KB zai ce ba yayi gaba inda kb ɗin Ya bisa a bayan yana faɗin,guy hold
on ana kiran mu 'fa Cos za'ayi attaching ɗin mu da snr doctors.

"To kawai yace masa suka nufi inda sauran young doctors ɗin suke".

Zazzaune suke cikin maɗaiɗaicin hall ɗin dake asibintin a yayin da Ko wannesu ke sanye da
Farar lab coat,

Shigowarta ba karamun sa IMAM PAKI yayi ba cikin wani yanayi na shauki,

Bai taba jin irin Haka akan Ko wacce ƴa mace ba,zungurar sa KB yayi yace abokina kar kace
mun itace,

Cikin wani irin yanayin farin ciki yace"Ya kagani ta haɗu Ko?"

Ƴar karamar dariya KB yayi yace baka da lapia,bafa cikin mu take ba mutumina likitace Mai
zaman kanta,sannan ka Kalleta da kyau PAKI she's off limit,a fuska ma idan ka Kalleta kasan no
nonsense ce,Kai kilan ma wallahi matar Aure ce.

Ba tare da Paki Ya ɗauke idanun sa akanta ba yace"KB jikina Ya bani ba matar Aure bace
'dan bazan taba jin yarda nake ji yanzu Haka akan matar Aure ba and da kake maganar she's
off limit just look At me ,young and handsome ,sannan idan ita senior doctor ce nima Ai kasan

jan Kai ne tunda bana wasa da abunda Ya shafi Aiki ,beside saboda dedication ɗina first class
holder ne wanda ba sai na faɗa maka ba,not to brag amma kai ma kasan idan magana ake ta
ƴaƴan banki daga su nake,amma mutumina ba ta wannan ake ba batu ake na soyayyar ta da ta
caccakar mun zuciya ,"Kai dai kawai idan mun gama abunda zamuyi anan muyi bincike akan ta
'dan Ko sunanta ban sani ba,



Ƙasa KB yayi da murya ganin Babban surgeon na asibitin Ya fara magana,yace"tana cikin hand
book ni kam kamar naga hoton ta ,

And "..

Jan hannun sa Paki yayi yace "Kai yi shiru zata fara magana".

"Sunana Dr Umaimah Bulama ,surgeon ce da zaku yi aiki da,and ba sai na faɗa ba ,nasan
dukkan wanda yake zaune anan yasan Abunda Ya kawo sa ,ba wai har kace ta Wasa ba
saboda we are not some Artist or any sort of entertainers, we are here to save life da taimakon
Allah wanda I'm sure shine aim na duk wanda ke zaune anan gurin ,idan kuma kana da wani
otherwise aim to i will tell you that nan gun ba gurinka bane, So ba wasa just do abunda Ya
kawoka,

If im right zaku ɗauki year a nan right?"



Yes ma!wani matashin saurayi Ya faɗa daga gefen su Imam,

Cigaba tayi da magana inda take cewa well,Ina muku fatan nasara a rayuwa And ina fatan zaku
amafana da abunda zaku samu wanda za kuce gwanda da kukazo CITY HOSPITAL.

Bayan ta kai karshen maganarta gurin Ya ɗauki tafi ,a yayin da umaimah ta shiga kalbin
young interns ɗin ,

Babu abunda Imam yake baya ga kallon ta yana Mai jin ta sake burge sa dan hatta muryarta
wani abu take masa a kunne.

"Na shiga uku "Ya furta a hankali yarda KB kaɗai Ya jisa,shima ɗin maganar zuci ce ta fito fili,

Dariya karama KB yayi yace "Ai tukunna ma Alaji baka fara shiga uku ba."

Bai kula sa ba illa tasbihi da yake Ga ubangijin da Ya halliccesa Ya kuma halicci umaimah.

Bayan an gama ƙarbarsu aka rabasu ƙarkashin likitocin ,a Haka kaddara ta taka gudunmawarta
wajen jefa Paki da KB karkashin Umaimah,

Sai wata yarinya Aisha shareef wadda ba ma makarantar su ɗaya da su Paki ba .



Fita tayi dan tana da VIP patients' da zata gani bayan ta wakilta Nurse farouk kan yayi
addressing interns ɗin dake karkashin ta Kafun tazo and su tabbatar sun tsaya tazo.



Kallan KB imam yayi yace "kaji yin Allah ko?"Kai ni tunda na ganta nasan akwai wani
boyayyen al'amarin da zai faru tsakanina da ita,
Gyara zama KB yayi yace wait paki mubar maganar wasa wai dagaske kake maganar kana
santa?

Kalli 'fa ba tsararka bace,kar ka jama kan ka damuwa,



Dafa kafaɗar KB yayi yace "kwantar da hankalinka ,zaka maimaita maganar nan lokacin da
kaga na sata a ɗakina ,kar ka manta Paki ne 'fa,wanda Ko wacce mace ta mutarwa a campus "

Suna wannan surutan Aisha shareef tazo yarinyar da aka sasu tare karkashin Umaimah,

Da fara'arta tazo garesu ,zama tayi kujerar dake kallansu tace"sunana Aisha Shareef,And
zamuna aiki tare ne,

Washe mata haƙora KB yayi amma ita hankalinta yana kan Imam Paki wanda Ko inda take bai
kalla ba dan yasan karshen maganar tace tana san shi. "



Miƙamata hannu KB yayi yace sunana"KABIR ASHIR abokina nan kuma IMAM PAKI,hope we
will get along."Babu musu ta kama hannun KB tana Mai faɗan sunnan Paki a zuciyarta dan
sunan Ya dace dashi sosai.



Bayan ta saki hannun KB ta juya ga Paki wanda hankalin sa ke kan waya ,hannunta ta miƙa

masa domin handshake,

Kallan hannun yayi sheƙeƙe kafin yace"last da na tuna ni dake ba muharramai bane sannan
addinin musulunci bai yarda macen da ba maharramaka ba wani abu nata Ya ta b'a ka ,ban san
wanne addini KB Ya shiga ba a yanzu da Ya kwakumi hannunki cikin nasa ,amma ni har yanzu
ban fita ba ,bayan addini kuma I'm Allergic to handshakes cos it disgust me,"


Ganin yarda tayi da fuskarta gwanin ban tausayi sannan ta janye hannunta cikin sanyin gwiwa
yasa Imam Paki cewa"hope zamuyi aiki Mai kyau tare".



Washe masa hakoranta tayi jin abunda yace ,cikin farin cikin tace insha Allahu,.

Bai sake ce mata komai ba Ya cigaba da danna wayansa inda yake jin suna hira su biyun
kamar sun daɗe da sanin juna,



Tunda Ya duƙufa kan wayansa #tag DR Umaimah Bulama yake sawa yana san ganin duk wani
post da Ya shafe ,da Haka ya samo profile ɗinta wanda ba komai sai abun da Ya danganci Aiki,



Har zai fita Ya ƙara komawa hashtag sunanta ,wani hoton ta ya gani a baƙin harvard university
tayi murmushin daya bayyana well cleaned arranged white teeths ɗinta,



Gefe guda kuma wata kyakyawar mace ce da bazata wuce sa'arta ba ta dora hannunta kan
kafaɗarta itama tana Mai mayar da murmushin,

Kana kallansu kasan suna cikin farin cikin irin na freshers da suka samu favorite course ɗinsu
da suke ta mafarki,

Sunan Mai Account d'in da ta dora ɗin Ya shiga #HinduSD#

Scrolling Ya fara ,idanunsa ne suka sauka kan wani hoton Umaimah da yayi mutuƙar tafiya da
imanin sa ,dimples ɗinta Ya lotsa sosai gwanin sha'awa ,

Hoton matric ne ,anyi tagging ɗinta ana wishing ɗinta happy birthday ,

Caption ɗin Ya duba yana san gani Ko ansa shekarunta,

#happy 25 baby,out of sight is never out of mind ,hindu forever Love you.

Irga shekarar da akayi posting ɗin yayi da yanzu yaga shekara Ashirin da Tara!

Duba Month ɗin da akayi posting ɗin yayi yaga birthday date ɗin 9th march.



Dan leƙowa cikin wayar KB yayi yana san ganin me yakeyi bayan tashin Aisha ,karaf idanun sa
suka nuna masa hoton Umaimah,dafa sa yayi yace guy Abeg Stop this.

Tsaki Paki yayi yace "rabu dani dan Allah ,nifa wallahi a yau kawai na kamu da san ta and
guess what nigga"I'm 1 month older,wata ɗaya kawai na bata kuma bashi zai hanani cigaba da
santa ba ,"



Ƙara dafasa KB yayi yace "Paki shekara ishirin da Tara 'fa ,taya kake tunanin bata da Aure ka
rufa mana asiri,".

Tsaki yayi ya miƙe yace "sai kuma kayi tayi ai".



Sai wuraren shida na yamma umaimah ta nemesu,da rawar jiki Imam Ya ja KB sukaje cos duk
yarda KB yaso su wuce sa haɗu gobe ƙi Paki yayi dan yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login