Showing 33001 words to 36000 words out of 68416 words

Chapter 12 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

Advertisement

14 Apr 2025

4808

soyayya ta ,na gaji da
punishing kaina da ƙin nuna miki soyayyata shi yasa nayi creating ciwo na,

Naga Kin damu dani kuma zaki zo ki bani magani?



Sai gashi kuwa kin zo,har gidan mu,har ɗakina ,Kin kawo mun maganin ciwona.



"Kallan sa tayi da mamaki tace "so dama lafiyarka ƙalau ka tadawa mutane hankali must
especially ummu,"

This is childish Paki,and nazo nan as a doctor don't get it twisted .



"Dariya yasa yana Mai faɗin"Ai wata ƙaryar ba haramun bace tunda gashi Kin zo ganina ,wanda
Ya tabbatar mun da Kin damu dani,shi kaɗai Ya isheni,bakiji yarda zuciyata tayi sanyi ba ""



"Addua kawai nake na mallakeki,kamar yarda kika shigo ɗakin nan as My doctor and lifesaver
na shigo dake a matsayin matata .tunanin hakan kawai yana sani farin ciki".



Dan Allah umaimah,ki buɗe mun kofar zuciyarki na shiga na b'ata ki da soyayyata ,wallahi
bazaki tab'a Allah wadai da hakan ba,

Zan baki dukkan soyayyar da kike mafarki a rayuwarki har da ƙari.



Ɗ'an Marairaice mata yayi da idanun sa kamar zaiyyi kuka yace "kinji umaimah na".



Saurin ɗauke idanun ta tayi jin yarda Abun Ya saka mata goosebump nan take,

Cikin rashin sanin abunda zata fada tace"na tabbata ba kaine na fari ba ko na karshe Stop
acting like one".



Shafa gefen gyararren sajen sa yayi yace"im the 3rd born and kar kiyi using wannan topic ɗin
as an excuse ki b'atar da maganan da nake".



"Ajiyar zuciya tayi tace"Paki zamu iya yin maganar nan a office ba sai kayi faking rashin
lafiyarka ba kasa kowa a damuwa, kasa nazo gidan ku, wani idan ya shigo ya ganka haka ka
sani gaba kuma yaji maganan da muke kasan we are in trouble ko?

"Za'a fara bawa clip din chan second thought,"



"Har a lokacin idanun sa akan nata Kafun yace"Umaimah,muna zaune ni dake a ɗaki ɗaya mu
kaɗai trust me babu wani abu mara kyau a tattare dake a zuciyata,"Ina sanki ,ina girmmaki,ina
ganin mutuncinki to the extent that bazan taba tunanin banza akan ki ba.



"Ya kamata kuma ace Kin sani,duk wani abu da wani zaice baya damuna ,sannan muddin kika
ƙarbi tayi soyayyata bana tsoran kowa a duniya yasan ke tawace,"



Kin tuna ?

I even confessed to the board ,im not scared.



"Kamata yayi ace tayi mutuƙar jin haushin abunda yayi mata na sakata zuwa da ƙarayar
ciwo,amma sai ta tsinci kanta da jin daɗin zuwan nata,

Lips Ɗinta na ƙasa ta mayar bakinta tace"im scared".



"So yaka Ya Kama hannun ta yayi assuring Ɗinta amma yana tsoran kar ta fara wani tunanin,"

Daga inda yake zaune yana facing Ɗinta yace"tsoran me?"

Tsoran kar na yaudareki?

Ko kuma tsoran abunda society zasu ce?

Ko kuma tsoran kar ayi ta maganarki ace kinyi Aure uku amma Kin wa saurayi wayau Kin
Auresa?

Ɗaga girar sa guda ɗaya yayi cikin sigar tsokana lokacin da yayi maganar ƙarshen.

Murmushi tayi tana Mai saurin kai idanun ta ƙasa dan wata irin kunya Ya bata,Kafun tace "duka"

Ɗago idanunta tayi ta kalesa tace"look paki,im 29 kaima kuma you're 29 kamata yayi ace ka
Auri macen da bata kaini a shekaru ba,

Paki kana ji da jini a jiki ,bai kamata ka ja rayuwarka baya ba ta hanyar shiga cikin tawa
alaƙarba,

Kasan ni ne kawai as Dr Bulama amma Bakasan labari na ba,



Trust me ,im not the type da zakayi getting involved da,last mijina ɗan Blood money ne and har
takaba nayi masa ,Family ɗin ka ma would never Approve of us. "



Saurin Mikewa tayi saboda zuciyarta ta fara melting wa Paki sannan cikin san kanta taji
zuciyartata tana faɗa mata ta bashi dama ta jawosa rayuwarta amma baza tayi hakan ba .



"I think mu bar abun nan a nan ,yes na yarda im attracted to you ,i mean who wouldn't,amma im
not that selfish ,so please paki mu yanke wannan alaƙar da baza ta haifar mana da ɗa Mai ido
ba.



Hanyar fita ta nufa,da sauri yasha gaban ta yace "Im not perfect umaimah nasani i would never
be perfect ,im not perfect amma na maki alƙwari zan baki dukkan soyayyar da nake da ita,



Nasan bazan taba impressing ɗinki da kuɗi ba amma i will spoil you with love,

Zan ɗauki su Nadiya kamar nawan Zan basu uba ,na miki wannan Alkawarin insha Allah."



Ban san labarin ki ba ke na sani sannan bazan takura akan dole sai Kin faɗa mun labarinki ba
,Zan jiraki duk ranar da kika shirya faɗan mun Zan saurareki sannan ki sani duk munin past
ɗinki bazai dameni ba ,

"Society kuwa ,Forget about it ,ni Zan zauna dake basu ba,sannan maganar iyayena they are
mine kuma nasan yarda zanbi dasu,"

Clip kuwa ,wanda Ya fasa bashi second thought, ni dake da ahalin mu Ai munsan dai dai.

.And yes Kafun na manta kar ki manta na baki wata ɗaya



Ki Amince dani dan Allah.





Yar ƙaramar dariya tayi tace "wata daya kamar shekara biyar yarda ka ke wani juyata,"



"Matsa na wuce and Zan kijiraka a asibiti da safe i will be expecting you.



Dan shiru yayi yana san gano abunda take nufi zai magana ya tsinkayi muryar Nana na faɗin
Au har ƙurya suka shiga ?

Ke wacce irin uwace Habiba?

Zaki bar ɗanki da baligar mace.



Bari naje naci uban yar iskar yarinyar.



Da sauri Paki Ya matsa bakin kofar jin yarda Nana ke neman balle kasa kofa....

Chuchujay✍

T

B

C.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a Hospital romance)

By

Chuchujay ✍

Episode 1⃣9⃣➡2⃣0⃣

Kamar guguwa haka Nana ta faɗo cikin ɗakin ,

Tsaye Paki yake gefen Umaimah dan tana turo kofar Ya matsa ,

Wani irin kallo yake bata ran sa a mutukar bace

Daga bayan ta ummu dake biye da ita tace "Nana yanzu Kin yarda imam baya da lafiya shine
abunda Ya kawo umaimah nan ,amma ba abunda kike tunani ba".

Kallan ummu dake maganar Nana tayi kafun ta matsa gurin Umaimah wadda ta fara ja da
baya dan bata manta cizan da Ummu tayi mata ba saboda yarda Ya bar mata tabo,

Shinshina ta Nana ta fara kamar wata kare Kafun tace "kwarankwatsa Habiba yarinyar nan
kanshin turaren imamu take ,hakan kuma abu ɗaya yake nufi wanda Shine daga jikin sa take."



Cikin bacin rai imam yace "subhanallah ,Nana menene haka wai?"

Wacce irin magana ce daga jikina take?

Duka ta kai masa wanda yayi saurin kaucewa tace "dan ubanka babu abunda ban sani ba

musamman wanda Ya dan danganci mata irinta ,idan ba kinibibi ba uban menene Ya kawota
duba imamu cikin gidan nan?

Ko ance mata bamu da likitan da yake zuwa duba mune ,

Wanda ma yasha gwagwarmaya a filin daga ,Ya samu horo na sojoji mazan fama masu jini a
jika .

Kallan umaimah tayi wadda take ji a ranta da ace nana ba kakar paki bace ta daɗe da
maganinta,

Cikin yin fiki fiki da ido tace sameera zo ki gane mun bakinta kamar sumba suka sha dan naga
Ya kumbura ko ido nane?.



Da sauri sameera da ta biyo bayan su tace"zancen ki dutse Nana wallahi gashi nan da tazo
bakin ta ba a haka yake ba ,ni dama tunda naga Ummu ta fito ,KB ma Ya fita nasan Akwai
magana,amma nasan ummu bazata saurareni ba,ke kuma gashi baki gida,shi yasa kina
shigowa naga Ya kamata na faɗa maki wannan zance kiyiwa tufkar hanci.
Wani irin kallo Ummu ta bawa sameera kafin tace"anya sameera za'a tafi haka kuwa ?,

Mene yake damunki,duka duka yaushe na bar su a dakin sannan menene laifi idan har likita da
mara lafiya suka keb'e a ɗaki tare ?

Haba dan Allah muna yiwa mutane zato Mai kyau mana.



"Ba shakka habiba,ba shakka ƴar masu jan kunne har tasan wai ayiwa mutum zato Mai kyau,

Gaskiya Muntari nikam Ya cuce ni da Ya Auro ki,

Duk yan matan Fulani dake garin nan kyawawa Ya rasa wadda zai Aura sai wadda addinin ta
ma yake da rauni,

Ke da baki da tarbiyya ina zaki samu damar bawa wani,?

Kan umaimah ta kuma yi wadda ta kai maƙura ,ta ɗaga hannu zata mareta tayi saurin rikewa.

Wani karamin murmushi tayi a yayin da Nana ta saki baki tana Mai rafka salati,

Sauke hannun nata Umaimah tayi da nutsuwa tace"Nana ke babba ce ,sannan ke kaka
ce,kuma a matsayin ki na Nana'n imam na ɗauke ki kamar tawa,dan Allah ki bari sannan duk
abunda kike tunani bashi ne Ya shiga tsakanina da Imam ba,ni ina da abunyi a asibiti ,

Kallanta ta mayar kan ummu tace "ummu imam is okay yanzu sannan Zan bawa KB
magunguna Ya kawo masa ,stress ne kawai yake damun sa."



Murmushi ummu tayi tana Mai jin umaimah a ranta kafin tace"na gode My daughter,Allah yayi
miki albarka.

Wani irin daɗi umaimah taji a lokacin da ta saka mata Albarkar dan rabonta da jin Kalmar nan
gurin uwa har ta manta,

Jakarta ta ɗauka tana mai mayar da kallanta kan imam Kafun tace Allah Ya ƙara sauki ,sai na
ganka a asibiti, "

Cikin zaƙuwa yace "insha Allahu gobe zaki ganni,ai tunda kika zo na warke ."

Murmushi tayi masa ta ɗauki hanyar fita a ɗakin ,

Tana isa falon da suka zauna da ummu taji muryar Nana na faɗin"hylloooooo,ɗiyar Yan marasa
kunya ni zakiyiwa fitsara cikin gidan ɗana ki fita Hankalinki a kwance bansa an karya mun ke
ba."

Appan ,Appan maza zo nan ,zo zo yau akwai bala'i an zagi uwar ubanka,

Affan da suka dawo daga unguwa da Nana wanda baisan wainar da ake Toyawa bane Ya fito
da saurinsa jin tana kwala kiran Appan kuma tana faɗin ana zagin ta Ya fito da saurinsa yana
faɗin"Nana wanene wannan yake zaginki na miki maganinsa?"

Turus Yayi ganin umaimah ,kallo ɗaya Ya gane fuskarta dan shi ba ma a case ɗinsu Ya santa
ba dama tun tuni shi A wani hira da ka tab'a yi da Alhaji Bulama Along side da ita take burgesa
musamman da ake faɗan nasarorinta As a young female surgeon Mai ƙarancin shekaru.

Dr Umaimah Bulama a gidan mu?

Wow wow,dafa Paki da Ya biyo Nana tare da kowa yayi yace "hamma ita ce dama Dr Bulaman,
da kuke aiki tare,God wallahi kina burgeni,

Takawa yayi zaije gurin ta Nana tasa hannu ta kamo masa hular sweater ɗin dake jikin sa tayo
baya dashi kiiiiii tace"Ubanka muntari,

Ni zakayiwa ɗiban albarka da rana tsaka,to sai in gani idan ni ko ita,nan a ɗakin imam Babu irin
wankin babban bargon da batayi mun ba,sannan har gida ta biyo Yayan ka ta lalatashi.

Saƙalo dukkan su sukayi suna mamakin yarda Nana bata kunyar gandara ƙarya.

Har Umaimah ta juya zata tafi dan bata iyawa Nana da harigidonta taji an sake fincikota,

Imam ne yayi yunƙuri yana Mai faɗin "wai Nana menene hakan?

Nuna sa tayi da yatsa tace "kul ka kiyayeni,wallahi naci maka mutunci yanzu ,tunda dukkan
ku kuna ganin kun kai akan karuwa zaku juyawa uwar uban ku baya,To wallahi ni nasan
maganin ta ,sai taji dama bata kawo kanta iskanci gidan nan ba ,dan sai nasaka TEGA Ya cizar
mata ƙaffafun 'da suka kawota.
Finciƙar Umaimah ta farayi har sai da ta kaita Harabar gidan,a karo na farko umaimah tasa
hannu ta bige na Nana wadda reaction ɗin Ya kuma zaubarata,

Cikin jin zafin kiranta karuwa da tayi tace"Nana ni ba karuwa bace ,ki tambayi jikanki,

Murmushi tayi da wani abu Ya ɗarsu a zuciyarta ,Ya kamata ta bawa tsohuwar nan maganin
larurarta,

Kamo hannun Nana tayi guda biyu tace "ina ta gujewa amma Nana kinƙi bari kinsa dole sai na
faɗa miki gaskiyar abinda yake faruwa tsakani na da Imamun ki ,"

Petting hannun Nana tayi tace "nasan rashin sani yake saki yi mun komai,bari na sake gabatar
miki da kaina,".

Sunana Dr Umaimah Bulama ,ina harka ne ta farka mutane da ɗinke su a babban asibiti dake
cikin garin nan na Adamawa,

Ni bazawarace ,sannan nayi Aure ɗaya ɗaya har uku,

Ɗan karamin murmushi tayi ganin yarda Nana ke mata wani irin kallo tana mai san kwace
hannunta a nata ta kasa duba da yarda ta damke hannun sosai tace "A'h bari kiji Nanan mu,a
kowanne Aure da nayi sai da na haihu,

Na samu Nameer ,Nadiya da Abdallah,sannan a duk mazan da na Aura akwai tarihinsu ɗan
daya ma yana cikin kungiyar tsafi,

Kwalalo ido Nana tayi jin maganar tsafi ga kuma yarda Umaimah ta damƙe mata hannu inda
ummu da Paki da Affan suke gefe suna kunshe dariyar su,

Sameera kuma na kusa da Nana tana zazzaro ido kamar an kaɗa jab'a buta.

Wani murmushin gefen Baki umaimah tayi ta ƙara matsowa kusa da Nana tace "wani abu da
zai miki daɗi Nana Shine ni da Paki muna soyayyane sannan ina san na Aure miki shi na mayar
dashi mijina na sunna kinga da haka zaki yarda ni ba karuwa bace tunda komai zai faru
tsakanin mu sunnah ne,"
Ki yarda Nana'mu Ina san jikan nan naki sosai ,sakar hannun Nana tayi guda tace "zan mutu
idan ban zama matar shi ba,"

Nasan da kikaji daga baki na zaki amince da Auran Imam da Umaimah dan na ƙosa nayi maki
tausa.

Sake matsa hannun Nana tayi kafin ta jawoshi saitin bakin ta ta sumbata,



Fincike hannun Nana tayi tace "uban ubaki dan kan uwaki,kina kallo ko habiba,ba nace miki
yarinyar nan yar iska bace ,kuna kallo kuna kuma jin abunda ta mun sannan ta faɗa ko,

To wallahi sai dai kiyi bunga ,kiyi funfuna ki rub'e babu Aure akan mu baki ɗan mu,wanene Ya
faɗa maki mu shashashune da basu da tunani,

Dan ubanki ina kika taba jin wannan gambizar,duk kinyi kwararo a hakan kike so ki Auri yaran
da yake sabo fes a leda,wanda nayi imani da Allah yana kaffa kaffa da kansa baya iskanci.

Wallahi sai dai ki mutu sau ɗari 'dan muddin in ni nayi cikin muntari kuma na haifesa a cikina
nayi rainan sa wallahi bazaki Auri imamu ba. "



Wani murmushi umaimah tayi tace "yanzu da kanki Nana kinga kin gyara maganar da kikayi
na muna iskanci nida Imam a ɗaki ,tunda Kin yarda shi sabo fes ne a leda kuma yana kaffa
kaffa da mata ,kinga kuwa lafiyar sa kawai na duba a ɗakin chan sai kalaman soyayya da muka
faɗawa juna,
Ba komai Nana,ni na yafe miki tunda dai kinga inda daf da shigowa zuri'ar ki dole na maki
ladabi na soki na kyaunace ki,

Ni umaimah ina sanki har raina Kaka ta gari".

Ai kamar ta kuma chinno Nana cikin Balai tace "wallahi karyarki yarinya ,imamu da kike gani
jelar raƙumi tayi nesa da ƙasa sai yarinya irin sa,"Jawo sameera tayi gabanta tace"kinga
wannan to irinsu ne ake faɗawa tubus tubus ba irinki marau marau ba,iyhe,"Kuma ki gaggauta
barin gidan nan Kafun wallahi na sa a sako mun karen Chan TEGA Ya ciccinye mun yar banza.


Juyawa umaimah tayi ga ummu wadda ke ta faman guntse dariyar ta ganin Yarda Nana ke
hakikancewa tana maidawa umaimah magana,

Zata so ace maganar da Umaimah ke faɗa gaske ne ,ita kanta ta gaji da Nana da halinta,tasan
Umaimah ne zasu gwara tare amma ita kam Nana tafi karfin ta.

Murmushi umaimah tayi tace "ummu ni Zan wuce".

Murmushin ummu ta mayar mata tace "Allah yayi maki Albarka."



"Ai kamar Ta sake hasala Nana ta Kalle ta tace "idan ke zaki sashi yayi mata Albarkar habiba
'dan Allah saka shi,Ai Albarka tayi gabas wannan fitsarariyar yarinyar tayi yamma ,"



Murmushi umaimah ta kumayi tana jin daɗin shaƙar da Nana wadda takai maƙurar shaƙuwa,

"Ina sanki Nana,Sosai ,Kema ki samun Albarka na bar gidan nan da soyayyar mutane da
dama,nasan kaima Affan ka karb'e ni ko?"

Tamayar da tambayar ta ga Affan.

Dafe saitin zuciyar sa Yayi yace "In a heart beat,Adda Umaimah".



Kamar Nana zata haukace haka ta juya tana Mai zagin Affan Kafun ta jawo hannun Paki Ya
dawo yana Mai facing Ɗin umaimah tace "maza faɗawa wannan fitsarariyar guzumar baka
santa sannan kajata kamar shara ka fitar mun a gidan nan".

Kallan Umaimah yayi cikin ido yace"Ina Sanki sosai Umaimah na ,idan na rasaki na tabbata
Nana zata rasa ni 'dan mutuwa zanyi,gobe da safe insha Allahu da fuskata zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login