Showing 12001 words to 15000 words out of 68416 words

Chapter 5 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4742


bakinta kamar tana ƙasar,kasancewar su achan ɗin bai hanasu bin addini ba da hanya Mai
kyau,

Su biyu ne gurin iyayen su ita da yayanta Areefullah,

A lokacin da Alhaji muntari Ya kawo maganar Aurenta Nigeria gida ba ƙaramun balli
mahaifiyarsa hajja Hanne(Nana) ta tayar ba akan sam sam bata yarda Ya Auri kafura ba ,

Ƙarfin mijinta da kuma biyayyar da take masa ce tasa wannan Aure Ya ɗauro amma 'fa habici
duk inda ta zauna,



Bayan rasuwar mijinta wani ciwo da tayi ta tattara ta koma gidan Alhaji Muktar a lokaci ummu
na da cikin imam ,babu irin zagin da bata sha gurin Nana duk da irin wahalar da tasha da ita
duk da itama jinyar da take na ciki 'danma intisar wanda imamu kebi tana 'dan kama mata,



Irin mitar Nana da halayyar ta a dole ummu ta saba tun tana sawa a ranta har ta saba
musamman da ta lura da babu abunda zatayima Nana ta burgeta 'dan tun filazal ta nuna bata
santa,

A Haka dai suka cigaba da rayuwa har Allah Ya azurta ummu da yan biyu Affan da Afnan,

Duk da halin Nana hakan bai hanata jin jikokinta a ranta ba kar ma ace imamu wanda duk
jarabarta bai cika Kulata ba ,

Duk ranar kuwa da Abbi Ya dawo daga Abuja Ya bani da korafe korafe na an mata kaza an
mata kaza kullum a haka take,



Tayi nacin san ta sakewa Abbi Aure amma abun yaci tura 'dan duk yarda tabi sai Ya bulle dan
shi baya da lokacin mata biyu,bama wannan ba shi yana san matarsa ita kadai kuma ta ishesa
haka zalika ƴaƴa biyar ɗin da ta haifa masa Ya gode Allah duk da Allah ne bai sake basu rabo
ba.


**********

Bangaren umaimah kuwa koda ta koma gida tun a parking space yaya Aliyu ya tareta,

Rabawa ta gefensa tayi zata wuce dan bata san masa rashin kunya sannan bata san ƙarar da
energy Ɗinta akansa 'dan yau da batu Ta dawo wanda dole ayisa yau 'dan ita bata da time da
safe kafun kuma ta yi Aikin kwana gwanda tayiwa tufkar hanci.



Wani mari yaya Aliyu Ya ɗauke ta dashi wanda yazo mata a bazata,

Juyowa tayi ta kallesa Idanunta Ya kawo ruwa hannunta dafe da kuncinta tace"mari 'fa Yaya
Aliyu,you slapped me".



Cike da masifa yace"na mareki ɗin Ko zaki rama ne?

Ba dai ke kinyi wuyan da zakina wa matata gorin haihuwa ba wallahi nan gaba bulala Zansa na
zaneki mara tarbiyya kawai sakariya wadda ta kasa killace kanta guri ɗaya gidan miji,menene
Amfanin ƴaƴa irin naki masu uba daban daban ke ba akuya ba".



No this can't keep on,

da gudu ta yi ciki tana faɗin Daddy?

Daddy Daddy im leaving this house.



Cike da tashi hankali Alhaji Bulama Ya miƙe ganin yarda ta shigo tana kuka tana kiran sunsa ,

Lapia?

Ya tambaya yana Mai rike hannunta,



Cikin kuka tace "Daddy gidan nan zan bari nagaji da gidannan,ace ni da gidan ubana ni da
yarana bamu huta ba ,Daddy abunda akewa su Nameer a gidannan is too much for kids there
age ,sannan ba wannan ba yanzun nan 'fa marina Ya Ali yayi."

Mari?

Daddy Ya faɗa da mutuƙar mamaki.



"Sai ki fadi Mai kika mashi Ya mareki Ai ba wai kawai kizo kice Ya mareki ba ,jiyan nan gabana
babu ko kunya kika yiwa matarsa gorin haihuwa,

Hajiya ta faɗa tana Mai kauda kai ".



Cikin rufewar ido Umaimah tace"dama Ai hajiya zakiga nawa laifin amma baza kiga nasu ba
tunda ni bake kika haifeni ba amma dake kika haife ni bazaki ƙi fadar bangren da matar Ya Ali ta
fara mun gorin zaman Aure ba ,sannan dake kika haifeni bazaki tab'a faɗawa yarana cewa
ubansu daban dabanba sannan uwarsu ta kasa zaman Aure ba,baza kuma ki taba barin yan
uwansu suna kwararsu ba ko kuma matan ƴaƴanki,

Yara kanana baza kuna wasa da mental health ɗinsu ba,

Amma yayi dama ba gidan ne baki so na zauna ba?

Zan bar miki ki zauna ke da ƴaƴanki,

Fita tayi a ɗakin, tana jin daddy yana ƙwala mata kira amma ta ƙi sauraransa 'dan marin Aliyu
Ya kaita bango,



A Sashen yaya Abubakar ta ɗauko su NAMEER ,taji daɗi yarda bata tarar da yaya Abubakar
ba,bata tsaya sauraran maman Sultan ba ta sakasu cikin mota ta ,kamar jira take gate man Ya
buɗe mata ta figi motar zuwa titi.







Wattpad:chuchujay

AREWA BOOKS

https://arewabooks.com/book?id=653305e91c06f4783fc2ef84



Facebook:https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share





CHUCHUJAY ✍

TBC.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a hospital romance)

By.

Chuchujay

EPISODE 7⃣

Umaimah!

Na'am Daddy .

Gyaran murya yayi yana mai gyara zaman sa yace "umaimah naji komai da yake faruwa
,sannan ina Mai baki Haƙuri ga dukkan abunda ya faru wanda a yanzu Ya zama past ɗin da
baza'a kuma maimaitawa ba nan gaba na miki Alƙawari,

Yanzu ki ɗauko su Abdallah kizo mu koma gida zamu zauna a yi magana wadda na tabbatar
miki babu makamancin Abunda Ya faru da zai kuma faruwa indai nine Mai gidan Bulama
sannan marin da Ali Ya miki har haƙuri zai baki .



Shiru tayi kafun tace"ni Daddy bana so Ya bani haƙuri kawai ina san Ya kiyaye Ko da Wasa kar

Ya kuma marina, 'dan Allah Daddy idan ya kuma shari'ace zata rabani dashi, tunda dai su basu
ɗauke ni yar uwar su ba,tun kuruciya ina sane da dukkan abunda suke min daga su har
hajiya,yaya Abubakar ne kawai yake nuna ni tashi ce".



Sannan ni Daddy ba zan koma gida ba, ba tare da na samu Mai kulamun dasu nadiya ba tunda
Family na duk Albarkars u babu Mai sansu.



Dafa ta yayi yace "umaiman daddy idan kina faɗan Haka har da Daddy fa".



Ɗan karamun murmushi tayi tace"ni banda Kai Daddy dan nasan da ace kai mace ne zaka kula
mun da yarana kamar Kai ka haifesu,"



Yanzu ma Dada tace zamu tafi da shatu ƴar baffa dikko ƙanin baffa da mijinta Ya rasu babu
abunda take gida ni ko biyan ta ne zan nayi duk da tace bata so,



Hankalina zai fi kwanciya idan tana tare dasu,sannan ba wai nace Aunty sadiya bata mun ba,
Daddy itama Ga ɗawainiyar yaranta ga na su nadiya abun yana mata yawa,



Dama kuma Nameer jiya yace mun yana san zai rubuta exam ɗin NTIS (Nigerian Turkish
international school)na Abuja yayi jss to sss a chan wanda dama nima na dade Ina so.



Murmushi daddy Ya faɗaɗa yace kinga shikenan sai suje tare da Ibrahim(ibi) ya samu ɗan uwa,

kicin kicin tayi da ranta tace"Daddy nifa ba wai bana san Alaƙar su nameer ne da jikokin ka na
gun su yaya usman ba kawai ni dai gwanda nameer yaje Abuja ɗin in yaso su suje na nan
Adamawa ɗin. "

Tabbas abunda zaisa umaimah ta nemi su ibi suyi nisa da nameer ba ƙaramun abu bane duba
da yarda take nunawa yaran kauna ,

Shafa kanta yayi yace shikenan yarda kike so Haka za'ayi, yanzu dai kije gurin baffa ki kira su
nameer ɗin mu koma gida tunda ai nasan Ko yanzu kikace shatun tazo zata zo Ai baza a tsaya
ma dasu Nadiya karatu ba ,ga Abdallah ma za'ayi enrolling ɗinsa ya kamata kuma ace da kaina
naje na saka shi.


Bata san cigaba da musu da Daddyn nata 'dan Haka tace "to daddy".



Sallama sukayi da Dada da baffa yayin da suka ɗauki shatu wadda a kalla umaimah zata bata
shekaru huɗu da haihuwa ,



Taron gaggawa daddy ya kira a daren ranar wanda dukkan sun tabbatar da sun hallarta har da
matan su kafin Ya buga musu zazzafan warning ɗin da Ya tabbatar suma zasu wa ƴaransu dan
bazai lamunta ba su b'ata masa gida da negativity ba.

Sanin Halinsa yasaka ko wannensu shiga taitayi.



Washe gari da sassafe ta wuce asibiti inda daddy kamar yarda Ya faɗa Ya dauki Abdallah da
kansa ya kaishi makarantar su Nadiyan domin saka shi.



Tana zaune a office kamar kullum bayan Farouk Ya gama shigar mata da duk abunda take
bukata ciki har da coffee ,bata nemi wani cookies ba 'dan yau da irish and egg sauce ɗin da
shatu tawa su nadiya ta taho ,



A hankali take kurban coffee ɗin a yayin da hankalin ta guda yake kan system ɗinta tana
studying wani method na surgery,

Kulan irish ɗin ta buɗe ta faraci a hankali bayan tayi bismillah,

Knocking taji a bakin door ɗinta,



Sai da akayi a karo na biyu Kafun ta bawa Mai kwankwasawar izinin ya shigo ,



Da sallama a bakin sa ya shigo wanda jin muryarsa kaɗai sai da yasata kwarewa ,



Da saurinsa Ya tako yana faɗin Ya salam kinyi missing ɗina har haka kenan,

Bottle Water ɗin dake gefen Kulan Ya ɗauko ya balle mirfin Ya miƙa mata ,babu musu ta ƙarba
ta kafa bakin Gorar a bakinta .



Sai da taji dai dai Kafun ta aje ruwan,kallan sa tayi tana Mai haɗe ranta tace "lapia"?



Murmushi yayi yace "lapia ,da fari dai ina san saka Ki a ido nane domin a yanzu kallan ki shine
yake kosar dani naji bana jin ko wacce irin yunwa,"



"Na biyu kuma idan kin manta ni ban manta ba kince ni dake zamuyi magana dan Haka yau da
zumuɗina nazo Asibitin nan Cos i cant wait to hear duk wani abu da zai fito a bakin ki koda zagi
nane domin ni akan ki mahaukacin masoyine,

Ya ƙarasa yana Mai saka irish ɗin da Ya ɗauka a bakinsa a yayin da idanunsa ke cikin nata
kamar zai fasa kwayar idanunta.



"Wata iri ƙaramar dariya tayi Kafun tace "imam paki Ina san ka maida hankalinka kasani ni ba
tsarar ka bace.."



Tsk yayi da baƙinsa Kafun Ya karkaɗa dan yatsansa cikin rashin amincewa kafin yace"point of

correction ni yayanki ne da wata ɗaya".



Serious face tasa tace "lallai zamu samu matsala da kai a asibitin nan saboda i wont tolerate
this,"

"Wani murmushin Ya kuma yace "nifa ba wai ina nemanki da hanyar banza bane umaimah
Auren ki zanyi ".



Nunasa tayi da ɗan yatsanta tace "DR Bulama,ba muyi kusancin da zaka kirani umaimah ba
,dafe goshinta tayi cikin rashin sanin Abunda zatace masa ta furta"get out ".



"Yunƙurawa yayi kan table har sai da ya Kai saitin fuskarta Kafun yayi wani irin arnen murmushi
ganin yarda Ya zaro idanu yace "Stop thinking silly ,im not going to kiss you Ina so naji ne idan
da gaske kike san datse Alaƙar da na kulla mana ,amma ga mamakina sai naji zuciyarki tana
luguɗe da sauri da sauri tana kiran Imam Paki,wanda Haka Ya tabbatar mun baki tsaneni ba".


"Wata irin kunyace ta kamata musamman da Ya zaman zuciyar ta sai da tayi skipping beat.



Murmushi yayi yace "abincinki zai huce zuwa anjima Zan dawo na sake duba lafiyarki dan
yanzu aiki nane."



Tashin sa keda wuya farouk Ya kwankwasa kofa,

dama ta bashi Ya shigo,

Kallan paki dake tsaye yayi Kafun Ya Kalle ta yace "Doctor kinyi baƙo and yana ta creating
scene akan dole sai Ya ganki duk da bai da Appointment dake sannan baiyyi kama da mara
lapia ba amma yace a faɗa miki Baban nameer ne "

"Cikin wata irin faɗuwar gaba tace"Habib?"Mai yake yi anan?



Ɗan kallanta Paki yayi yaga take yanayinta Ya chanza jinn ance baban nameer ,abu ɗaya Ya
sani wanda shine wannan Habib ɗin ba baƙon maraba bane,



"Baya san mata katsalandan musamman a yanzu da yake san gina Alaƙa da ita wadda yasan
zaiyyi nasara,

Juyawa yayi zai fita bayan tace da nurse farouk yace ya shigo.



"Imam paki?"

Tsaye yayi chak jin ta ambaci sunansa Kafun kuma Ya juyo yana Mai fuskantarta yace "na'am
Abar alfaharina".



Kamar bataji abunda yace yayin Amsawa ba tace zauna .



Na'am?

Ya tambaya kamar baiji Mai tace ba,

Ɗaga masa gira guda ɗaya tayi tace "ba kana san soyayya dani ba"?



Zama yayi kamar anyiwa yaro kyautar sweet yace "nace a turo ne?"



Tsintar kanta tayi da yin ƙaramar dariya duba da yarda Ya faɗi maganar kafun tace"zan biya
maka buƙatarka ne ta yanzu kacal ,bayan nan kuma ka fita hanyata ,just take it kamar im using
you for now ".

Shafa kwantaccen sajensa yayi Yace "im here use me like a tissue amma ki sani idan na
ɗanɗana sai an ƙaramun,.."



Tana koƙarin magana Habib ya turo kofar ya shigo,

Dago Kai tayi ta kallesa ,

Ya chanza sosai kamar ba shi ba,girma Ya ƙara bayyana a tattare dashi Haka zalika kasumba
da Ya tara wadda a da bashi da ita,

Sallama yayi yana mai washe mata haƙora,

Haɗe rai tayi ,jan kujera yayi Ya zauna yana Mai faɗin"umaimah ina wuni".



"Wata ƴar dariya ce ta kwace mata jin gaisuwar da yayi mata Kafun tace "Ina fatan kayi wunin
ka lafia habib sannan ina fatan abunda ya kawoka Mai amfani ne".



"Da saurinsa yace "Wallahi Mai amfani ne umaimah ,Kallan Paki yayi wanda tun da Ya shigo
yake Kallansa ,"



Mai da Kallan yayi kan umaimah yace"wannan Ya ɗan bamu Guri mana"



Kallan paki tayi kafun ta kallesa tace "duk maganar da zakayi kayita a gabansa saboda
tsakanina dashi babu wani boye boye saboda MIJIN da zan Aura ne,take gaban paki Ya yanke
Ya faɗi jin abunda ta faɗa wanda yazo masa a ba zato babu tsammani,amma a wani bangaren
kuma sai yaji dama daga zuciyarta maganar ke fita ,amma Shin wanene Wannan ɗin? "


Shine tambayarsa.

"Wata ƙaramar dariya yayi ya kalli Paki yace "haba umaimah ,wannan yaran kema Ai kinsan ba
sa'an Aurenki bane Daga gani da kyar idan baki girmesa ba ,kodan kinga kina da kyan jiki?"



Ajiyar zuciya tayi tace"Habib idan maganar kyan jikina kazo yi nima nasan yana da kyau ,zaka
iya tashi ka tafi dan Ina da abun da yafi saurarenka amfani,"



Sniffing yayi yace "kalli nan umaimah ni nasan wasa ma kikeyi,dan Allah umaimah a bar
maganar Wasa tunda kuma kince nayi gabansa zanyi yasan matsayin sa,



"nazo ne akan Auren mu ,'dan Allah umaimah,nasan saki uku Ya shiga tsakanina dake amma Ai
kinyi Aure har biyu wanda Addini a yanzu Ya ƙara hallarta mun ke,ki taimaka ki bani dama na
rufa maki asiri Ko dan Nameer dake gurinki,"



"Nayi imani da Allah yaran nan yana buƙatar uba,Mai zai hana kizo mu sasanta kan
mu?"Nasani daddy idan yaji daga gareki zai amince ,



"Umaimah look I'm a changed man wallahi duk abunda kika sanni dashi yanzu na bari."



"Lokacin imam ya fahimci wanene Habib,duk da bai san menene ya raba su ba amma tabbas
yasan abunda Ya raba su babu daɗi sannan daga jin furucin Habib bawai Ya dawo bane dan Ya
tuba ,Ya dawo ne dan wani boyayyen burin sa"



"Har a lokacin hankalin umaimah a kwance ,Kallan sa kawai take tana observing ɗinsa Kafun
tace"Na yarda baka da kunya Habib, "

"Yanzu da kazo ka ganni anan kana nufin asirina a tone kaganshi?"

Ko na taba ce maka ka kawo taimako wa Nameer mai shekara sha daya yanzu?



Kai kana tunanin idan ni kaɗai da kai muka rage a duniya zan sake zaman aure da kai?



"Bana san sunan Nameer yasake fita a bakin ka saboda idan baka manta ba a yanzu baka da
wata alaƙa dashi,"

Kalli nan'

Ta nuna masa paki ,

Kallan pakin yayi kafun tace"ka kallesa da kyau nasan ka hango qualities ɗin da baka dashi,"

Ka kallesa da kyau,He's handsome,charismatic ,hot and breathtaking,ba sai na maka wani
bayani ba kasan ta ko ina Ya fika ,to ka faɗa mun Habib ina dashi Mai zanyi da kai?

Ka kalli kanka a mudubi kafin daƙikiyar kwakwalwarka ta baka shawarar zuwa inda nake?



"Ajiyar zuciya tayi har a lokacin baza kace maganar daga bakinta take fitowa ba Kafun tace "ka
tashi ka fita sannan zan manta da wannan maganar Ko dan darajar Nameer da Ya shiga
tsakaninmu. "



"Cike da bala'i yace"kaji mun ƴar iska 'fa ,ni zaki ma lalata har kina nuna mun wani kwartan yaro
dake saka miki tayin igiyarsa da ba tayi kwari ba ,kuna kunshe a office kuna alfasha kice wai ya
fini?"



"Dan na zo maki da sauki kenan,Ko kina tunanin ban san karuwancin da kike da likitocin dake
asibitin nan ba ?"

To Ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login