Showing 39001 words to 42000 words out of 68416 words

Chapter 14 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4746

tana da yara guda uku,and Im just a month
older,amma hamma abun da za'a duba anan Shine wallahi idan na rasa ta Bansan Ya zanyi
ba,trust me wani ciwan zai iya kamani na mutu."

Dan shiru usama yayi na wani lokaci kafin Ya faɗaɗa murmushin sa Ya dafa kafaɗar paki
yace "brother as far as you love her just go for her,live your life ,babu fa wanda zai maka
rayuwa,kai zakayiwa kanka,so chase it and have it and na baka dukkan wani suport ɗina,ina
Tare da kai a duk wani step da zaka ɗauka a rayuwar ka,kawai ka tabbatar you're sure about it.
"

Nima ina Tare da kai Hamma imam ,i will support you and we will beat Nana to it,

Muryan Afnan yayi echoing cikin ɗakin a yayin da yake shigowa ciki,

Kallansa imam yayi yace "lab'e ka koma kai kuma?"

Takowa ciki yayi yace"Ba lab'e ba nake bafa ,i Just got to overheard something and yau
Brother's night ne shiyasa nima nazo a yi dani,

Sai a lokacin suka kula da pillow ɗin dake hannun sa,dariya suka sa a yayin da Ya shigo cikin
yana Mai darawar shima,a haka sukayi ta hirar yaushe gamo har bacci Ya daukesu ".

******

Washe gari kamar yarda Iyalan Paki suke karin kumallo a yau ɗin ma haka ne,sai dai a wannan

karan baki ɗayan su ne suka hallarta ciki kuwa har da sameera yar karo wadda ke ta faman
shishigin ganin yan uwan Imam sun karb'eta dan yarda Nana ta saka mata Auran imam gani
take kamar ta Aure sa an gama,

Hatta Abbu da bai gari sai da Ya amsa shamacin Nana,

Bayan addua babu abunda kakeji na surutu face karar cin abinci,bayan sun gama Nana ta
miƙe tana Mai faɗin"kowa Ya sameni a babban falo ".

Babu musu kowa Ya hallarta duk da kuwa sun san sarai rigimace,

Zama tayi ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya Kafun ta kalli Afnan tace "ke tashi kije ki kira sameera Ya
Ana zama na ahali zata ware kanta?.

Wani irin kallo Afnan ta mata kafun tace "bana tuna lokacin da kika haifi Daddynta ko
mummynta,"

Tsawar da Abbu ya daka mata ne yasata tashi zuwa kiran Sameera tana Mai jin haushi,

Gyara zama usama yayi yace "Amma Abbu banga inda maganar Afnan tayi rashin dai dai
ba,Nana fa taso mu tayi ta katse mana dukkan wani aikin da muke Mai amfani ta kawo mu nan
dan yin magana mai muhimmanci,mene na sako wata sameerah?

Wacece wata sameerah ma?"



Cikin fushi Nana tace"uwarka Habiba mara ɗa'a ɗinchan ce Sameera usama,"Nace maka
uwarka habiba.

Duk yaran gidan babu Mai fushin usama dan muddin Nana ta zagi Ummu gabansa baya
b'ata lokaci wajen nuna fushinsa,cikin fushi Ya tashi yana Mai faɗin"Nana nazata komai Ya
chanza shekara talatin da shida kenan fa!

Yakamata ki gane a yanzu da baya ba ɗaya Bane ,a da muna yara bamu fahimta,yanzu kuwa
Ummu na da yaro Mai shekara talatin da shida idan baki ɗaga mata ƙafa dan komai ba kya
ɗaga mata dan yaranta,babu yarda za'ayi muji daɗi muna zaune kina aibata mana uwa.

Baki tab'a kaunar ummu ba kamar ta kashe miki wani,Mai tayi miki?

Babu 'fa abinda ta tab'a miki illa zuri'a da ta bawa yaran ki,menene laifinta?

Gaskiya bana jin daɗin irin abunda kike yiwa Ummu Nana .

Kallan Abbu wanda yayi shiru yayi yace "kayi mun afuwa Abbu akan abunda na faɗa sannan
ni Zan wuce dan na bar aiki sosai a company na dan Kafun nazo nan ma meeting biyu na
ɗaga."

Ya juya zai bar falon Ya jiyo muryar Nana tana Mai faɗin"ɗan kundun uba Mai shegiyar baƙar
zuciya Ya ta kakan sa,Ai sai kayi hakuri ka dawo muyi abinda ya kawo mu sannan indai Habiba
ce Zan yi ƙokari naga ban faɗi abu mara daɗi ba akan ta har ka juya kuntacce."

Usama ka dawo ba!.

Muryar Ummu wadda taji daɗin tsaya matan da yayi ta Katsesa,

Dawowa yayi Ya zauna yana Mai faɗin "Allah yasa shima zaman ba wani rigimarki bace".

Yana ƙare maganar Sameera ta biyo Afnan,gefe Nana ta nunawa Sameera tace"zo zauna
yarinyar Arziƙi,"

Babu musu kuwa ta dawo ta zauna.

Gyaran murya Nana tayi tace"Muntari maganar nan ce dole na yita, Maganace kuma da ta
danganci imamu,matsar kwalla ta fara tace "muntari Nidai nasan ni na haifeka sannan kai yaro
ne Mai biyayya,"Bawai ina san haɗa ka da iyalin ka bane amma da kaga abunda Ya faru dani
jiya sai kayi kuka,
Wannan karuwar yarinya diyar Bulama jiya Bakaga rashin mutunci da tayi mun ba,kuma habiba
na gurun haka zalika imamu, apan wa Apnan ,wallahi baka ji ɗiban Albarka ba har da cewa
babu wanda Ya isa Ya hanata Auran imam ta maidashi waina sai yarda ta juyasa,

Shi yasa nikuma tunda na san wadda imam yake so tun jimawa wato Sameera shi yasa na
kiraku gaku ga ita nan ayi magana a saka iyayenta a ciki ayi Auren su nan da ƙarshen wata
guje ma shaiɗancin ɗiyar bulama .

Cikin bacin rai Abbu yace"habiba maine ke faruwa."

Affan ne dake gefe yace"haba Abbu kai kasan babu wanda zai zo har gidan,nan Ya zagi Nana
bamu ci,masa ba,and Wallahi Abbu ba wai ina karyata Nana bane amma wallahi Adda
umaimah bata zagi Nana ba ".

Cikin harzuƙa Nana tace"uwar Adda ba dai Adda ba,kaga muntari ni ba wannan ba ,muddin
imamu yana san nayi shiru da maganar nan sai Ya Auri Sameera dan ba zamu saka ido ba Ya
Auri zawarar da tayi Aure uku har da ƴaƴa uku,

Wallahi bazai sab'u ba,idan Ya sab'u kuma mutuwa nayi.

Allah Ya kiyaye,yarinya ƙwara yar shekara talatin bazawara?

Badai a zuri'a paki ba.



A Karo na farko ummu tace"idan yana santa kuma 'fa Nana?"Mene aibun dan Ya Auri Mai
yara uku,bafa zunibi bane,abu ɗaya zamu duba shine suna san juna to mene Ya rage kuma?

Cikin fitina Nana tace "ke dallah rabu dani da tunanin ku na yahudanci,imamu bazai taba Auren
ɗiyar Bulama ba,sameerah zai Aura".

A karo na farko intisar dake fama da kanta tace "amma Nana babu Ya hudanci 'dan hamma
imam Ya Auri bazawara indai har yana santa sannan indai har ta ɗebo raban sa sai fa ta
saukeshi,idan kika matsawa yin Allah sai kiga kamar yarda kika faɗa sai ki mutu ayi , Haba
Nana kefa musulmace ,ko Kin fi san su samu rabansu ta hanyar banza?
To su samu Mana inti,ke nifa da Ya Auri yarinyar nan gwara Ya je Chan su watse su da
Allahn su sannan babu mai kawo mana ɗan zina mu ƙarba,kilan ma sauran ƴaƴan duk a haka
aka same su,sannan kiji da kyau Intii tunda na kai yanzu mutuwata ba yanzu ba nayi imani da
Allah ,'dan jikina na bani habiba ma sai ta rigani tafiya!
Nana ta Faɗa tana Mai faman hura hanci kafin tace"muntari ,usama ku nake jira kuyi magana
'fa."

Ƙaramin dariya usama yayi yace"Nana wannan yasa kika kiramu dama"?

Ni dai babu abunda zance illa Abar imam Ya Auri wadda yake so,After all imam ne zai zauna da
matar sa ba kowa ba Ko me kace Abbu?

Ni ganina abun nan Ai ba Mai wahala bane.

Idanun Abbu akan paki yake wanda ke goge kwallarsa gudun kar a gani amma hakan bai
hanasa gani ba.

Gyaran murya yayi yace "yanzu Nana Ya kike so ayi,"?

Kaɗa kai tayi tace"yauwa yanzu kayi magana,so nake imamu Ya Auri Sameera nan ba da
daɗewa ba.

Cikin Siririyar murya Abbu yace "shikenan Nana abunda kike so shi za'ayi".

Washe baki tayi ta dafa Sameera dake ji kamar An sata a Aljanna tace "kinji ko sameerah dama
na faɗa miki ki kwantar da hankalin ki muntari ya haifu a cikina".



"Wallahi tallahi bazan Auri Sameera ba,dana Auri Sameera gwara na mutu banyi Aure
ba,wallahi bazan Aureta ba ,'dan wallahi kuka ce sai na Aureta zaku rasani, 'dan Zan mutu ne,

Wallahi Abbu bazan Auri Sameera ba sabida a yanzu maganar da ake babu macen da nakejin
a duniya bana ƙauna sama da ita saboda tana neman shiga tsakanina da rayuwata da farin
cikina wanda Nana ke tayata wajen ganin sun kashe ni,

Wallahi bana santa na tsaneta,

Da kuka imam Ya ƙare maganan sa Kafun Ya tashi Ya bar gurin da saurin sa ba Tare da Ya
saurari kiran da suke masa ba,

Ɗakin sa Ya nufa Ya kulle dan yasan dole wani zai biyosa ,ille kuwa Ya tsinkayi muryar Usama
yana Mai faɗin Ya buɗe masa .



Kallan Nana ummu tayi idanun ta a cike da kwalla Tace "ban tab'a tankawa hukuncin ki ba
Nana tsawan shekara talatin da shida kenan ina Auran muktar amma ban tab'a jin daɗinki
ba,Bansan menene na miki a rayuwata da kika ɗora mun karan tsana ba,ban sani ba Nana
,Allah Ya sani zuciya ɗaya nake zaune dake sannan Kallan uwa nake miki ba uwar miji
ba,amma Bansan dalilin da yasa ke kike ɗaukata kamar maƙiyiyarki ba,amma duk bama
wannan ba,imam mene yayi miki da kike san tsangwamawa rayuwar sa?"

Yace baya san sameerah umaimah yake so,menene aibun haka fisabililahi?

Zan yarda da komai amma bazan lamunta ba muddin wannan abun yayi sanadiyar da na
rasa imam,Abbun usama ka rubuta ka aje idan wani abu Ya samu imam na gama zama da kai .

Tashi tayi ta bar gurin tana riƙe kukan da ke ƙokarin kwace mata .

Tsaki Nana tayi tace"shirman banza,dama wanene ke sanki da Muntari,Allah Ya kiyaye hanya
kuma Aure ne sai anyi,

Kallan Sameera tayi tace ke tashi muje ki matsa mun ƙafata ,kai kuma muntari kaji dai abinda
nace 'dan haka afara shirin biki "

Bayan tafiya Nana Affan Ya kalli Abbu wanda Ya kasa cewa komai,yace "Abbu kayi haƙuri
amma kaima kasani Nana bata kyautawa ƙwataƙwata,ai baka tab'a jin ummu ta tanka mata ba
sai yau,ya kamata an'a yiwa Ummu adalci ,"

Tashi yayi yabar gurin yayin da Afnan ta taimakawa intisar ta tashi suka bar gurin.



Tashi Abbu yayi ya nufi ɗakin Ummu,a buɗe Ya tarar dashi 'dan haka Ya murɗa handle ɗin Ya
shiga,

Zaune Ya tarar da ita tana kuka,zama yayi gefenta Ya jawo ta jikinsa yana Mai shafa mata kanta
a hankali,gudun kukanta ta kara Har da shesheƙa,

A hankali cikin kwantar da murya ta sigar lallashi yace "idan kika rabu dani nayi yaya nikuma?"

Bana san na kuma ji kince zaki rabu dani 'dan idan na rasaki Zan shiga cikin wani halin,

Raba jikinta tayi da nasa tace"Abbu haka imam zaiji idan Aka rabashi da Umaimah,yana santa
da dukkan rayuwarsa,ka taba ganin soyayya haka a idanun imam? "

A wannan karan imam ya ga wadda yake so sannan bai damu da past ɗinta ba so mene
damuwarmu?

Kamo hannunsa tayi tace "ɗan Allah Abbu kar ka bari Nana ta tarwatsawa Imam rayuwarsa
,Zan iya shanye komai na Nana kayi haƙuri amma banda wannan."



Murmushi yayi yace"bana san ganin hawayenki abar ƙaunata ,hawayenki nasani cikin
damuwa,sannan na miki Alƙawari zan san duk yarda zanyi imam Ya samu abunda yake
so."Hannu yasa yana Mai goge mata hawayen inda cikin yarda da maganar sa tace "nasan
kana cika mun Alƙwari 'dan Allah ka cika min wannan,ni nasani umaimah ba yarinyar banza
bace ita tata ƙaddarar ta haka tazo mata kilan Auran imam Shine cinyewar jarabawarta,idan
akan Intisar ko Afnan Ya faru na tabbata bazaku tab'a cewa wane baiyyi su Auresa ba,".

Hannu yasa akan lips ɗinta yace "shhhh,ki bar magana da kukan nan honey imam zai Auri
umaimah,Bansan taya Zan fara da Nana ba amma koma menene Zan shawo kanta sannan
Auren imam da umaimah kamar anyine insha Allah,!

Cike da murna ta faɗa jikin sa tana Mai faɗin nagode mijina Allah Ya barmu tare Ya raya mana
zuri'ar mu.

Kissing kanta yayi yace"ameen masoyiyar muntarin Nana".

Ƙaramar dariya tasa tana Mai jin san mijinta har ranta.



****************************

Washe gari Umaima tayi ta zuba idanu tana Mai san ganin zuwan paki amma shiru,sukuku
haka take abubuwa cos a yanzu ganin sa ya zamar mata cima,

Da kyar ta iya maida hankali wajen ganin patients' a consulting room,

Har lokacin lunch paki bai zo ba and babu KB ballantana ta tambayeshi gashi bata da
numbernsa,sannan koda ta kira wayarsa a kashe take,

Message ta tura masa akan idan yaga saƙon ta Ya ƙirata,

Tana zaune bayan ta idar da sallah taji ana mata Knocking,

Izini ta bayar da a shigo,

KB ne ,cikin danne damuwarta tace "yes and hope abokinka lafiya baizo aikiba,.

Ɗan karamun murmushi yayi yace kinyi baƙone ma,

Baƙo?

Ta tambaya tana mai juya wanene zai zo gurinta yau?

Izini ta bashi akan yaje Ya shigo dashi.



A fizge ta kalle sa tana Mai mayar da wasu files cikin locker tace"sai yanzu kaga daman zuwa
kenan i thought Ai day one of us being official har ka manta dani paki".

Zama yayi kan kujerar da yake facing ɗinta yace "Paki ne ,amma usama paki ba imam paki
ba,"

Da sauri ta ɗago jin ba miryansa ba amma Mai Kama da tasa sannan mamallakin muryar Mai
mutuƙar kama dashi sai dai wannan yafishi shekaru wanda hakan Ya tabbatar mata yayan sa
ne!

Da sauri tace"im sorry nazata imam ne,sannu da zuwa,ina wuni".



Murmushi yayi wanda Ya sake fito da kamarsa da imam yace"sunana usama Paki sannan ni
yayan imam ne,ni yake bi a gidan mu,tabbas yanzu na gane dalilin da yasa imam haukacewa
akan mace ashe dai macen ta kai har ta kai da saboda ita Ya gudu daga gida.

Cikin tsantsar damuwa tace"Ya gudu daga gida?"Saboda mene?

Murmushinsa Ya kuma faɗaɗawa ganin yarda lokaci ɗaya ta ruɗe yace"ki kwantar da hankalin
ki yana yiwa soyayyar ku yaƙine and na tabbata shike da nasara,Nana ce tasashi gaba,Sorry
kilan baki waye ta ba ƙaƙarmu ce".

Yar ƙaramar dariya umaimah tayi ta nuna masa hannunta inda Nana ta Cije ta tace "kaga
shaidar Nana a jikina ,she bite me".

Buɗe baki yayi kafun yasa dariya yace "Nana and her wahala God mai Ya haɗa ku,labari ta fara
bashi abun yana Mai dawo mata sabo yana sata dariya cos tsohuwar nan sai Allah".

Kamar sun saba da juna idan ka gansu,

Ban ko sa an kawo maka coffee ko tea ba ko wani drinks.

Saurin ɗaga mata hannu yayi yace "no"kafun Ya kalli agogon Hannun sa yace "zan wuce lagos
yau ne nace bari nazo na ganki muyi magana,"

Nasan kina da past amma past ɗinki ba zai tab'a lalata soyayyarki da imam ba sabida nasan
yana mutuwar sanki and a idanunki Kema nasan haka,

A yarda imam ke sanki ina roƙanki ki riƙemun kanina amana ,nasan kinfisa sanin rayuwa cos
you've been through alot,and ina tare daku a koda yaushe,.



Cikin jin nauyin sa tace "ina yaje hamma"

Cikin jin daɗin girmamasan da tayi yace"kar ki faɗawa kowa ,yana Airport' yana jirana zamu bi
jirgin yamma mu gudu lagos na ɗan boyesa yayi kwana biyu Kafun Ya dawo ,kiyi masa cover ,"

Murmushi tayi tace"Allah Ya tsare hanya Hamma."

Sallama yayi mata Ya tafi a yayin da take shirya fushi da paki muddin bai nemeta ba.









A/N

Wane ke jin kamar Ya zane Nana bayan ni?



Chuchujay ✍

Tbc



https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j



Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.



Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share i want audience domin baku,



Share it make it go viral
[11/25, 9:42 PM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a hospital romance)

By

Chuchujay

Episode 1⃣2⃣

Nana Mai kike faɗa haka ne ?

Kin 'fa san wannan maganar babbar magana ce!



Kallan sa tayi tana Mai gyatso baki tace "yo muntari kace na masa sharri mana kawai!"

Riyal Aini na kalli bidiyan sa da wannan shegiyar guzumar likitar suna Alfasha,



"'dan ma ina tsoran idona kar Ya lalace shi Ya hanani cigaba da kallo amma wallahi imamu ne,"



"Ina faɗa maku neman mata Ya hana yaran nan Aure ko rashin lapia to ashe kalau mazantakar
sa take zina yasa a gaba Ai wallahi imamu yaji haushin rayuwar sa Ya bata wayansa"



"Kallanta ta mayar kan ummu wadda tayi jugun tana Kallan Nana ,cikin haushin ta tace "Ai
habiba baki gama tagumi ba sai Yar iskar ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login