Showing 30001 words to 33000 words out of 68416 words
Chapter 11 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf
Dr Bulama nine nake soyyaya da ita, rumours ɗin kusan
gaskiya ne amma Zan muku ƙarin haske ,
"Ni nake san Dr Bulama amma its a one sided love,im confessing a nan saboda babu wani
protocol da ya haramta mun san Dr Bulama,
And ina faɗa ne to clear duk wani confusion,
Cos i know im not in the wrong,so im begging With the board and All the staff akan kowa Ya fita
issues ɗina ,its gonna take me a year here, then im out.
Sannan ni Aiki nazo yi ba wani abu ba,sannan soyayyar da nakewa Dr Bulama bazata tab'a
shiga tsakanin Aikina ba.
Haɗe hannayen sa yayi biyu Kafun Ya tashi ya fita ba tare da Ya damu da abunda zai biyo baya
ba.
"Shiru gurin ya ɗauka kowa na ciki shock ɗin confession ɗin Paki,karma ace Dr bulama
wadda tafi kowa shiga 'dan bata taba tunanin Paki zai yi hakan ba,sannan tana Mai jiyo fushi a
maganar sa.
"Haɗe rai tayi cos bata shirya amsa abunda zasu faɗa ba musamman yarda kowa yake kallanta
tasan akwai masu magana. "
"Cikin haɗe ran ta miƙe tace ,Apology accepted and i will put paki in the right place,pardon his
attitudes ".
"Da haka ta fice a board room ɗin inda ta bar su da maimaita Ya akayi."
"Kai tsaye neman Paki ta fara,
"Good morning Dr bulama,Aisha shareef ta gaisheta a yayin da take hangen imam,
"Ɗan tsayawa tayi ta kalleta Kafun tace"morning and yes ki kiramun Paki kice masa ina
nemansa a cabin ɗina.
A cabin ɗinki?
Aisha ta tambaya da wani irin tone.
"Har umaimah tafara takawa ta tsaya ta juyo ta kalleta musamman jin da yayin da Aisha tayi
maganar".
"Dan daga girar ta guda ɗaya tayi tace "Kina da matsala da hakanne?"
"Saurin kaɗa kai Aisha tayi 'dan ita kanta bata san ma maganar ta kwace mata ba".
"Juyawa umaimah tayi ta bar gurin tana Mai jin wani irin yanayi Akan Aisha wanda ta kasa
fassarawa,"Tafi mai dashi a jinin su bai haɗu ba .
"Tafi minti nawa a zaune tana jiran Paki amma yaki zuwa,"Sai da ta fara tunanin ko Aisha bata
faɗa masa tana kiran sa ba ,
Tana kokarin tashi taje ta samesa Knocking ɗIn sa da ta haddace ya mata sallama.
"Bayan Ya shigo ya tsaya a tsaye yace"Dr Bulama Kin kirani and Na tsaya stitching ma wani
patient ciwo ne as per Nurse Farouk instruction".
"Kallan sa tayi da kyau jin yarda yake mata magana kamar bashi ba, "
Alamu ta masa da hannu tace "zauna"
Cike da kafewa yace"im okay Dr and Dr Kaseem yana nemana idan babu damuwa ina san ki
faɗa da sauri,idan ba urgent bane kuma naje na dawo".
"Cikin sosowar rai tace Imam paki have a seat bana san na sake repeating kaina, "
Kamar bazai zauna ba amma sai Ya zauna ɗin yana Mai Kallan gefe.
Ji tayi wani irin yanayi na rashin dadi Ya ziyarceta,
Cikin kulawar da bata san tana da ita ba tace "akwai abinda ke damunka ne,"Zan ma Farouk
magana Ya dubaka.
Murmushi yayi kafin yace "a makarantar mu nine must brightest student,sannan na fita da First
class, bangaren medicine kenan kama ai kinsan ba abun Wasa bane,so ina da capability ɗin
ganewa idan bani da lapia ko a'a bana buƙatar kowa. "
"Haka nan taji yayi mata wani irin kwarjini a karo na farko,"
Dan har tana hada in ina a maganarta musamman yarda taga Ya kuramata ido da wani irin
yanayi,
Sauke idanun ta tayi saboda yarda taji Idanunsa na mata a cikin nata.
"Wani irin murmushi yayi yace"Dr Bulama Stop making me feel less,i can fight for me,ni
namijine da yasan right ɗin sa,im not some coward ,and yes im not scared 'dan nace ina sanki
cikin gurin Chan mai cike da mutanen banza ".
Ai ba laifi nayi ba ko sab'awa mahalicci ,ina sanki kuma har gobe ina sanki, and nasan kinajin
wani abu a zuciyarki a tatare dani,
Musamman idan ina tare dake ,idan kikaji muryata nasan zuciyarki na bugawa da sauri,
Sannan idan baki jini ba nasan kina kewata.
Amma Zan ɗaga miki kafa tunda kamar ina zaƙewa da yawa,duk lokacin da kika gama tattara
shawararki akaina ni a kullum ina tare dake ,sannan maganata da nafaɗa na barin field ɗin nan
idan har bakiji wani abu na soyayyata a tatare dake ba nan da shekarar da Zan bar nan then na
maki Alƙawari zan aje mafarkin zama surgeon .
"Yana gama maganar sa Ya tashi yakama Hanyar fita ,yana ji tana masifar Ya dawo bata gama
dashi ba and how dare he zaina Wasa da mafarkin sa akan soyayya."
Banza Yayi mata,tun ranar Ya chanza Mata baki ɗaya ,tun tana wa kanta excuse akan baya
damunta har zuciyarta ta yi ƙarfi wajen karyata ta 'dan sosai take jin abun har ranta ,musamman
a yanzu da taga wani kusanci da Ya shiga tsakanin sa da Aisha shareef musamman idan tana
musu lecture.
*
Cikin sati biyun nan halayyar paki ba karamin damunta take ba,cos a yanzu tunanin sa yana
ɗaya daga cikin abunda yake hanata sukuni,
Kafun Hindu ta wuce tasha faɗa mata tana san paki ne wanda take shan mur tace Ai karyane
ita ba sanshi take ba amma a yanzu tana neman ta ƙaryata kanta.
"Kai tsaye bayan Ta raka su Nameer Airport tayo asibitin,
Tunda ta shiga take san ta sa idanunta akan Paki amma bashi babu alamun sa,
A ranar koda taga babu shi bata tsaya basu wani lecture ɗin kirki ba,
Bayan ta gama suna fita,tace "Kabir ashir."
Juyowa yayi yayin da ta masa alamu da hannu akan yazo,
Babu musu yaje yana Mai boye karamin murmushi a zuciyar sa yana faɗin "shege paki yasan
Mai yataka.
"Kamar kuwa yarda yayi expecting yana zuwa tace paki 'fa".
"Dan Sosa kai yayi yana san tuno yarda Paki Ya shirya masa kafin yace"Ai Dr Paki yana gida
bashi da lapia sosai,"
"Cikin reaction ɗin da bata san tayi ba tace "bashi da lapia kuma?"
Mene yake damunsa?
And idan baya da lapia mai yake a gida?
Boye dariyar sa yayi yace"Ai yana Chan kuma rashin lafiyar sosai yake amma ko ummu bata
sani ba 'dan yana part ɗinsa a kunshe".
Cikin damuwa tace "and kake nan Kana faɗa mun when Kana abokinsa,idan shi baya san
lafiyansa Ai akwai masu so".
"Na'am ?"KB ya tambaya bayan sarai yaji abunda tace,
Wani irin kallo ta bashi musamman da ta fahimci abunda tace,
Tashi tsaye tayi tace ,
"Kaini Gidansu."
*********
So jiya baku samu update ba cos banji daɗi ba ,
But im Good.
To munje gidan Muntari ɗan Nana Mai abun mamaki,
Team# pakiumaimah
Kuna kusa?
Chuchujay ✍
To be continued .
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AURE UKU
(a hospital romance)
By
Chuchujay✍
Episode 1⃣7⃣➡1⃣8⃣
Tsaye taki bakin katafaren mansion ɗin su Paki tana tunanin abun da ya kawo ta ba tare da
tayi tunani na biyu ba,
"Wata zuciyar na faɗa mata ta koma saboda bata san abunda zata ce ba idan ta shiga,tunda
dole tasan yana tare da iyayen sa,"
"Wata zuciyar kuma tace mata "taje a matsayin Caring doctor ɗin da yake ƙarkashin ta After all
babu wanda yasan baya da lafia ɗin,"
Kallan Kb dake kallan ta tayi tace lapia?
Murmushi yayi yace "lapia kalau Dr ,ina so ne kawai na faɗa miki,Paki yana mutuwar san
ki,sannan saboda Allah yake sanki,tunda nake dashi babu ɗiya macen da Ya tab'a nuna
soyayyar ta ƙarara kamar taki,".
"Kallan sa tayi Kafun ta ɗauke idanun ta kamar abin bai affecting ɗin ta ba tace "zaka mana
jagora ne ko kuma na shiga da tambaya".
Faɗaɗa fara'arsa yayi a lokacin da Ya jiyo humour cikin maganar ta,
Baisan tana da wannan side ɗin ba.
Kafun yace "cikin da tafiya yi horn sai mu shiga."
Gate biyu ne a gidan wanda tsakanin gate na farko dana biyu akwai yar tazara,tun daga gate
ɗin farko tasan Paki yaran Soldier ne ,taso tayi sensing a case ɗin su Dr Jabir ganin yarda
sojojin ke basa ladabi.
"Sojoji ke gadin su dan sune gate ɗin farko dana biyun,"
Ganin KB ne yasa basu tsare su ba suka basu damar shiga,
Ba tare da ta kalli KB ba tace "dad ɗin paki hala soja ne?"
Kaɗa kai yayi yace admiral ne ,yaso sosai paki yayi aikin amma yaki wanda nafi maidashi ga
kaddarar haɗuwa dake takaisa Likitanci.
Tsintar kanta tayi da yin murmushi wanda bai kub'ucewa KB ba,at least yanzu hankalin sa Ya
kwanta daya gane Abokin sa ba haukan banza kawai yake ba.
"A gefen expensive motocin gidan ta faka tata,"
KB ne Ya fara fitowa Kafun ita,
Haka nan taji gabanta na faɗuwa,
Kallan Kb tayi tace "is it okay.
Kaɗa mata kai yayi Kafun Ya fara tafiya tana binsa a gefe,
A bakin wata wide kofa dake rufe suka tsaya inda Kb Ya danna door bell,
Minti ƙalilan aka buɗe kofar,
Sameer ce tsaye "idanun ta na sauka umaimah ta haɗe rai kamar an aiko mata da saƙon
mutuwa tace"uban me Ya kawoki nan?
Kin biyo sa gida ne a cigaba daga inda aka tsaya tunda ke roban pants ɗinki ya sake baya
Kama miki ƙugu. "
KB na koƙarin magana muryan ummu da ta Aiko ta ta buɗe ta katse ta a yayin da take
cewa""Ke Sameer wa kike faɗawa maganar rashin ɗa'a haka.
Faɗada murmushi umaimah tayi Nervously a lokacin da Ummu ta bayyana wadda ke mutuƙar
Kama da Iman paki,kana kallanta kasan mahaifiyar sa ce,
"Matsa mun bakin hanya nan,Au kabir kune ma ,Kallan umaimah tayi Kafun tace "da ita
kike,"Baiwar Allah kiyi hakuri dan Allah ku shigo daga ciki,
Kiyi hakuri.
Murmushi umaimah tayi ba dan maganar sameera bata mata zafi ba,ita bama tasan sameera
gidan take zaune ba da ba lallai tazo ba dan ta fahimci yarinyar notinan kanta a kunce suke.
"ƙara gyara fara'arta tayi tace "babu komai Ummu,
Shiga ciki tayi ga jagorancin Ummu wadda ke daɗa bawa umaimah haƙuri tana maiwa Sameera
Faɗan abunda tace mata .
Zama tayi cikin ladabi ta gaidata kafun tace "sunana Dr Umaimah Bulama ,sannan nazo ne dan
duba imam paki ,muna tare ne a asibiti so naga yau bai zo ba Shine kabir ke sanar dani bashi
da Lafiya and its severe sannan bai sanar da kowa ba.
So nazo ne naga Ya jikin nasa".
Daga gefe sameera tace "da bashi da lafiya Ai mu zamu fara sani ba ke ba ,kawai dai kice da
abunda ya kawo ki".
"Wai nikam sameera zaman Mai kike anan?"Bana san shashanci da iya shege 'fa,maza tashi
kibar nan,
Ummu ta fada cikin jin sameerah na sake sire mata,
Da zumbura baki ta tashi tayi sashen Paki dan san gano gaskiyar Umaimah.
Dan kallanta ummu tayi tace "Umaimah,kece wadda wannan abu mara daɗin Ya faru tsakaninki
da Imamu na ko"?
Ɗan kasa da kai umaimah tayi tana Mai jin kunyar Ummu kafun tace nice".
"Allahu Akbar ,Allah sarki,abun baiyyi daɗi ba,and naji daɗi da aka kamo waɗanda sukayi cos
tunda abun nan Ya faru da Imamu na dai ,amma zuciya ta tana gare ki,
Sannu ko."
Murmushi umaimah tayi tana Mai jin kaunar ummu kafin tace "ai ummu dama mutum baya cika
idan baya samun jarabawa".
Kaɗa kai ummu tayi tana Mai faɗaɗa fara'arta tace "hakane ƴata,Allah Ya bamu ikon cinye
dukkan jarabawar rayuwar mu,"
"Kai kuma Kabir kace Imam bashi da lafiya?
Inace gidan nan ka kwana Ya akayi baka sanar dani ba tun ɗazu yana ɗaki akwance idan da
karar kwana kuma 'fa.
Ɗan Sosa kansa yayi yana Jin nauyin yiwa ummu karya kafin yace"Ai ummu da na fita na
barshi yasha magani ma Shine yace kar na faɗa miki cos zuwa jimawa ma zaije asibiti so daga
baya kuma ya kirani,"Zan taho gida ne Dr Umaimah ke tambayata shi ,Shine na sanar mata.
Kaɗa kai ummu tayi tace Amma dai kun cika shiririta,
Bari naje na gani ,
Tashi tayi ta nufi hanyar sashen Su pakin,
Bakin kofar ta tarar da sameera tana ta aikin kwankwasa masa kofa tana cewa yazo Ya buɗe
mata,
"Lapia dai ko?"
Cikin kiɗimewa tace ummu Ai ya mutu a ciki ,inata bugawa ko alamar sa banaji.
Tsaki ummu tayi tace "matsa mun dan Allah,ke kike shiga kika kashe shi ai"
Knocking tayi tace "imam open this door ,"
Yana jin muryar ummu Ya taso Ya buɗe kamar mara lafiyan gaske yace ummu?
Da gudu sameera ta shiga gaban ummu tana Mai kamo hannun sa cikin wata irin murya tace
"wallahi na zata ka mutu a ɗakin nan har hankalina Ya ɗugunzuma Ya tashi sosai ".
Jawota ummu tayi ta mayar gefe kana ta kallesa daga sama zuwa ƙasa ,hannun ta tasa gefen
fuskar sa ,cike da kulawa tace "Imam lafiyarka ,"
"Mini Mini yayi da idanu yace"Ummu im sick,"
Cikin kulawa ta Kama hannun sa ta shiga dashi kerarren ɗakin sa ta zaunar dashi kan kingsized
bed ɗin sa dake yane da ash bedding ɗin da ba'a gyara ba tace "amma imam mai yasa baka
kirani ba ? "
"Nima Ummu da Ya kirani zanzo ba sai Ya ƙira wacchan balagazar matar ba."
"Dan rintse ido ummu tayi kafun tace"sameera kije ko,"Zan magana da imam ne,
"Tsayawa tayi tace amma ummu.."
Kafun ta ƙara cewa wani abun ummu tace "nace kije ."
Da turo baki ta fita a ɗakin.
"Sarai yasan wa sameera ke nufi amma gudun kar ummu ta rafkosa yasa shi langwabewa yace
"ummu wacece tazo?"
Murmushi tayi tace"Dr Umaimah ce tazo duba jikin ka,ban san tana da kirki haka ba, naji daɗin
zuwan nata,
Tana da ladabi sosai,ina santa".
Wani irin daɗi yaji aran sa kafun yace,"yauwa ,ummu tazo ta dubani ,dan ko asibitin naje gurin
ta zanje cos ita kaɗai tasan abinda yake damuna.
Cikin rashin Fahintar inda Ya dosa ummu tace"to ka zo muje babban falo tana Chan sai taga
jikin naka ,"Ko tazo nan?.
Kara langwabewa yayi yace ummu tazo nan kafafuna ji nake kamar bazasu ɗauke ni ba.
Tashi tayi tana cewa "shikenan bari naje na kawota ,amma imam baka da hali ace wai har
ƙafafunka su kasa ɗaukar ka amma ka gagara faɗa mun baka da lafia,."
"Tare suka dawo su uku,da ummu da KB da umaimah,"
Idan tace hankalinta bai tashi ba jin ummu tace wai kafafun sa sun kasa ɗaukar sa to ƙarya
take.
"Zaune suka tarar dashi yana rirriƙe kai,da dan hanzarinta ta karasa tana Mai faɗin" Paki maine
yake damun ka,and a matsayin ka na mai duba wasu Mai Ya saka Wasa da lafiyarka haka for
God sake.
"Ki faɗa masa dai kila yaji naki Baiji nawa ba cos imam halin sa sai shi,
Kalan ummu yayi cikin shagwab'e murya wadda tasa umaimah mayar da hankalinta gareshi
yace"ummu dan Allah zanci chips ban breakfast bafa."
Cikin kulawa tace bari naje nasa Emmanuel ya soya maka,
Cikin wata shagwab'ar yace "ummu please ni naki nake so bana cook ba,".
Murmushi tayi tace" naji ,bari naje nayi maka ,daɗina da ciwan ka dan banzan demanding,
Dr Umaimah ki duba munshi dan Allah ,kin gansa dai nan akwai raki da ragwanci.
Murmushi umaimah tayi cikin jin kunyar Ummu wanda ta rasa dalilin jinta .
Bayan fitar ummu Paki Ya kalli KB yayi masa alamu da ido akan Ya basu guri,
Babu musu KB Ya juya yana Mai smirking aransa yana faɗin"paki shegene".
Jawo stool umaimah tayi ta zauna tana Mai facing ɗinsa"tace mene yake damunka paki,?"
Kaifa ba yaro bane da zaka zauna a gida bayan kasan baka da lafiya and of course zaka iya
bawa kanka kulawa why this.
Zuba mata ido yayi kafin yace"ke kike damuna,sannan ke ce kawai Mai bani maganin ciwo na
sabida ciwan sanki ne Ya dameni Ya hanani fita ko ina,amma ganin ki ɗin nan da nayi Ya yaye
mun duk abunda yake damuna ".
"I miss you ,ina san sakaki cikin idona ,ina san nuna miki kulawa ta da