Showing 51001 words to 54000 words out of 68416 words
Chapter 18 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf
da wasu yan lokuta umaimah ta tashi tana Mai jinta over hills,she just
cant help falling for Paki saboda Shi ɗin na daban ne,he's unique ta ko wanne aspect,
Bayan ta gyara ko ina na ɗakin yayi fes duk da ba datti yayi ba ta shiga wanka dan sakewa da
kuma sake gasa jikinta cos she's sore saboda paki bai mata da wasa ba,tayi reaching orgasm
kafin shi,so tabarshi yasha budirin sa dan burinta yanzu a rayuwa bai wuce ta farantawa Paki
ba,
Bayan ta fito ta shirya cikin maroon cotton lace wanda akama ɗinkin Abuja bubu,sosai tayi
kyau a cikin sa kamar ka sace ka gudu,
Ɗan touching fuskanta tayi kafun ta ɗaura kallabinta ta feshe ko wanne sashen jikinta da
sassanyan turaren da ta samo a hamam ɗin Hindu ,kana jin kamshin sa sai kaso ka ƙara ji,
Takalmi ta ɗauko brown flat ta saka ta jawo wayarta tana Mai duba lokaci,
Karfe Goma na safe ,cikinta taji yana mata ƴar kuwa ,
Murmushi tayi tana tunanin ta inda zata fara saka hayateen ta a idanunta cos bata san ɗakin sa
ba,alamun mutum da taji a ɗakin kusa da nata ya tabbatar mata da nan ne nasa,
Kai tsaye ta Murɗa handle ɗin wanda Ya buɗe kamar dama ita yake jira,
Ɗagowa yayi Ya sauke idanun sa cikin nata faɗaɗa fara'arsa yayi yace "beb kin tashi ashe.
Murmushin itama ta maida masa tana Mai ƙare masa kallo,
Daga wanka Ya fito cos ƙugunsa ɗaure da towel a yayin da hot jikinsa ke ɗigar ruwa Kaɗan ,
da takonta na ƙwalisa ta ƙarasa tana Mai masa kallon ƙauna,
Ƙaramun towel ɗin dake hannun sa ta Karb'a a hankali ta fara goge masa ruwan daga cikinsa
cikin sigar kulawa,zaunar dashi tayi a kan stool tace "give me the honour hayatee,"
Murmushi yayi a yayin da ta jawo mansa tafara shafa masa cikin wani irin salo Mai ɗaukar
hankalin wanda ake yiwa,tana shafa bayansa da man ya jawota ta faɗo kan cinyarsa,
Saƙale hannunta tayi a kan kafaɗarsa tana Mai kallan ƙwayar idanunsa tace "Good morning
again sunshine,."
Kissing goshinta yayi yace "wiffey Kin san yanzu fa bazan na iya riƙe kaina ba a kanki cos
soyayarki kamar anƙaramun ita over night,i might want you anytime and anywhere, "
Cije lips ɗinta na ƙasa tayi tace "i wont mind,we can also have some kinky hospital romance
,bazan damu ba and nasan it will be interesting ,ta ƙarasa tana Mai kashe masa ido ɗaya,
Sake Matse ta yayi a jikinsa adam Apples ɗin sa na motsi yace "how about yanzu, cant you feel
me beneath,?
Im hard for you.
Jin yarda yayi hard ne yasata saurin tashi a jikinsa tana Mai faɗin the Number you're trying to
Call is not reachable At the moment please try again later hayatee,kiss ta masa blowing tana
Mai faɗin"ina jirankaa dining Area im famish,".
Murmushi yayi yana Mai jin sa a cloud nine a hankali Ya furta"she's cute"
He cant Blv wai yau shine ke a matsayin mijin umaimah,although dama jikinsa na bashi zai
mallaketa amma He's not expecting it this soon.
Farin transparent yadin sa mai masifa kyau ya saka kafun yayi combing sajensa da kansa Ya
feshe jikinsa da turare Ya mara mata baya,
Zaune ya tarar da ita tana mai danna wayanta a hankali ,chak taji Ya ɗagata batayi aune ba,
Ɗan shagwab'e fuska tayi tace "hayatee im famish kasan baka ɗaga mun kafa ba fa,ka kwashe
dukkan wani abincin dake cikina,"Pecking lips dinta yayi yace"shiyasa Ai yanzunan zan ciyar
dake ki ƙoshi,and kinyi kyau sosai cos komai kika sa jikin ki kyau kike masa ,murmushi tayi tana
Mai lajutar hancinsa tace"nafi kowa sa'ar miji a duniya,sannan kayiwa kayan jikinka kyau."
Shafa gefen fuskarta yayi Kafun ya kaita ya aje kan kujera Kafun yaje Ya dauko abincin Ya
dawo Ya zauna,
Cikin kulawa da soyayya suka ciyar da juna kafun suka fita tare dan zuwa gaida su Ummu,
A falo suka tarar da Abbu Nana ta sashi gaba tana masa maganar da basu san ta mene
ba,suna shiga tace "yauwa gasu nan ma kilallun basu iya zuwa gaida iyaye ba sai ƙarfe sha
ɗaya na safe,ko masu bautar rana kuwa yanzu sun gama bawa rana sujjada,".
Baki ɗaya ahalin gidan suna falon banda Hamma osama,har da inteesar da new born babynta
Ummussalma yar kwana arbain,
Zama umaimah tayi dai dai ƙafar Nana wadda tayi saurin ɗauke Kafarta kamar wuta ta tab'a
ta,ƙaramun murmushi umaimah tayi cike da kunya ta gaida sirikanta inda ƙannen mijinta suka
miƙo masu tasu gaisuwa cike da girmamawa da ƙauna,
Gaida Nana sukayi a tare a karo na biyu,tura baki tayi kamar bata ji su ba,
Inteesar ce tace "nana su hamma 'fa gaidaki suke.
Fiƙifiƙi tayi da idanunta tace"ki kiyayeni inti ,nafi kashi ɗoyi idan ka tab'a ni sannan najisu Ai
ganin damar amsawa ne banyi ba ko zan daku?"
Juyawa tayi tana Mai Kallan kofar da ake bi a fito falon tace"sameera kefa nake jira."
Kamar wasa sai ga sameera da akwatinta dana Nana tana ja niƙi niƙi,
Da mamaki ummu ta Kalleta tace"sai ina?"
Murguɗa baki Nana tayi tace"sai sashen imamu,yo dama bakiji abunda nake faɗawa muntari
ba kenan,to bari na maimaita maki tunda akwai tuwo a kunnenki,to zan koma sashen imamu
tare da Sameera wadda zata na min abincin da komai dan ban yarda da cin abinda aka dafa
gidan imamu ba,amma na yarda na zauna 'dan ni da kuke gani wallahi nan gani nan bari
dumamen mayya,
Tunda na haifo muntari to sai yarda nayi da kowa a gidan nan."
Shiru ummu tayi tana Mai kallan umaimah wadda taji baki ɗaya takaicin Nana Ya sake
kamata,
Dariya Affan yasa wadda ta saka kowa a gurin kallansa ,
Wayarsa Ya ɗora kan cinyarsa yace "Nana kenan,Nana duniya ,wato ke rigimar ki 'fa kullum
ƙara yawa yake maimakon ta ragu ,ni wallahi idan kina wani abun dariya ma kike bani,".
Tasowa tayi kamar zata dakeshi tace"ma'ana dai ni mahaukaciyace Apan,a'a kafito fili ka
kirani saban kamu sai nasan ka cika zaƙaƙƙen yaro mara mutunci,
Kamota Abbu yayi yace "Nana zauna muyi magana mana ,
Zama tayi tana Mai faman hura hanci Kafun tace "ayi dai magana mai kyau 'dan ko mutuwa
nayi baku kai gawata sashen imamu ba ban yafe maku ba kuma wallahi sai nayi ta muku gizau
na hana ku zaman lapia,idan ba haka ba ban cika mace ba,tana kai ƙarshe ta saka kuka. "
Baki ɗaya Abbu babu abunda ke rikitasa irin kukan Nana,da sauri Ya dawo gabanta yace "kiyi
haƙuri Nana zaki zauna sashen imam idan ma so kike su sai su bar maki gidan ke ki koma na
saka maki Yan aiki".
Snapping yatsanta tayi tace "La bazai iyu ba,ni da ka ganni ƙafata ƙafar imam duk inda zashi
dan babu yarda za'ayi na barshi shi kaɗai da wata matar muddin ba sameera ba shi yasa duk
inda Nasa ƙafa zata saka har sai ranar da imamu Ya Aureta".
Ƙokarin tashi imam yake umaimah tayi saurin kamo hannunsa tana Mai kaɗa masa kai,
Tashi ummu tayi ta bar gurin,tab'e baki Nana tayi tace "a banza anyiwa jaka tsarki da roman
ganda, ".
"Dama Mai zataji tunda dukkanta gandar ce,indai samira ce Gaki gata dama ni tun haɗuwata
da ita nasan sheɗaniya ce amma ki bari ta maki nata sigar nan zaki gane Mai ake nufi,
Afnan ta faɗa tana Mai tashi tabar gurin gudun kar Abbu yayi magana amma jin har tabar gurin
baice uffan ba Ya tabbatar mata da shima Baiji daɗin abinda ke faruwa ba.
Shegiya jikar masu jan kunne dama Mai kika iya a hausar banda lalube.
Tsaki tayi tace "kai muntari kai nake jira nikam" .
Ƙasa Abbu yayi da murya kamar baya san maganar yace"shikenan Nana abunda kikeso shi
za'ayi,"
Tashi yayi yana kare zancen saboda baya so Ya haɗa ido da imam dan babu ɗansa da yakewa
abunda bai kamata ba kamar Imam,shiyasa babu ɗan sa da yake ƙautatawa kamar sa dan shi
kaɗai yake bawa salary Mai tsoka duk wata wanda tuntuni Ya saba musu.
Washe baki sameera tayi tana Mai kama akwatin kana tace "Paki zo taimaka mun mana
tunda guri ɗaya zamu,"
Da wani irin fitinannan kallo Ya bita Kafun yace "ki godewa Allah ban tab'a dukan mace
ba,wallahi da yau idan na fara dukanki san na ballaki kaca kaca da mutanen minna zasu kasa
gane ki,sannan idan har kina san kanki da Arziƙi ki fara shirin tattara kayanki ki koma gidan ku
dan Allah".
Dariya Nana tasa tana Mai gutsurar goro tace "yaro man kaza,Ai sameerah da kake gani
Auranta kamar kayi ka gamane shiyasa zan koma gidan ka tare da ita tunda itama ma'aikaciyar
lafiya ce babu wani ma'aikacin lafiya da zai kwazirani."
Hannun umaimah da tayi sakalo tana Mai jin zuciyarta na mata zafi ya kama yace "beb tashi
muje ,"Tashi tsaye tayi tace "ka nunawa Nana gurin su bari naje gurin ummu."
Knocking kofar ɗakin ummu tayi wadda ta bata izini ta shigo,zaune ta tarar da ita kamar Ma
kuka take,tana ganin umaimah tayi saurin goge idanunta tace "umaimah kece shigo mana".
Babu musu ta shigo ,tana ƙokarin zama ƙasa ta kamota tace"No umaimah ban yarda da zaman
ƙasan nan ba,taso kizo ki zauna kusa dani,"Babu musu umaimah ta zauna gefen gadon,
Hannunta ummu ta kama tace"ki ɗaukeni uwa umaimah saboda na ɗauke ki ne a matsayin
intee da Afnan,nasan abunda Nana take bai kyautuwa,amma We just have to handle them mu
bisu hankali mu rabu dasu lafiya,
Kin ganni nan ,rashin jin daɗin Nana yafi jin daɗi na da ita yawa ,amma na yarda tana da kirki
kawai dai rigimarta ce damuwa,sau da dama nakan ɗauke ido idan na tuna alherinta ta wani
wajen,amma a bangarenki bana jin dadin abunda take maki,kiyi haƙuri na kasa yin komai a
lokacin da ake shirin kwace maki farin cikin ki,
Kiyi hakuri sannan zanyi ƙokari naga kun koma gidan ku sannan samira zan san yarda zanyi na
sa ta tafi gida."
Murmushi umaimah tayi tace ummu"a shekaru na marasa yawa rayuwa tayi kwallo dani
yarda take so,lokacin da nake buƙatar mahaifiyata bata kusa dani,haka na rayu cikin kaɗaici da
rashin uwa duk da yarda mahaifina ke ƙokari wajen ganin ya cike mun wannan gurbin,"
Gidan Aurena dukka bani da sa'a ,banyi tunanin zanji ina san Imam ba har haka amma na
yarda da Allah Ya bani wannan kaddarar tawace ta hanyar faranta min,ummu bana so Aurena
yayi failing shiyasa Nana ko sameera babu wanda zai zaman min matsala a abunda Ya shafi
zamantakewa ta daki ko mijina,
Ummu bana san ki saka kanki kan abunan saboda Nana nada babban iko akan Abbu ,shiyasa
bana so ni nazama matsalar Aurenki na shekaru da kika gina,
Insha Allah ni nasan yarda zan zauna da Nana har da kanta zata sama Aurenmu Albarka .
Kama hannunta ummu tayi tana petting kafin ta jawota jikinta ta rungume tana Mai jin hawaye
na zubo mata dan shes very emotional ,"Allah yayi maki albarka Ya saka maki albarka cikin
gidan ki,sannan ni ki ɗaukeni mahaifiyar da baki da ,zan cike maki wannan gurbin ,kar kiyi ƙasa
a gwiwa wajen zuwa ki sanar dani damuwarki."
Bayan tabar sashen Nana kai tsaye sashensu tayi tana Mai jin kwarin gwiwa dan ta shirya
ma Nana da Sameera bazata taba bari su lalata mata Aurenta da zaman lapian taba.
Already har sun shigar da kayan su ɗakin da Paki Ya nuna masu dan bata gansu falan ba sai
buruntun su.
Kai tsaye ɗakin imam ta shiga 'dan tasan yana ciki,
Zaune ta ganshi gefen gado ya saka fuskarsa cikin tafin hannunsa ,kana kallo kasan yana cikin
damuwa mutuƙa,
Sama ɗakin key tayi ta karasa a hankali ta zauna kusa dashi,hannunta ta saka ta jawosa jikinta
wanda gladly Ya ɗora kansa kan kafaɗarta yana Mai faɗin"beb im Sorry na kasa hana Nana
dawowa nan and nasan That old woman mean trouble sannan ga sameera wadda nasan ita ce
babbar bad influence akan Nana,amma i promise you zan gyara komai,"
Shafa kansa ta fara a hankali tace"mijina bana san kana sakawa kanka damuwa akan
abunda ba damuwa bane,ni ban ɗauki wannan damuwa ba 'dan babu abunda zai tare mun
Nunawa Hayatee na soyayya yarda Ya kamata 'dan har sai ka manta da bamu kaɗai bane
gidan nan,so ka kwantar da hankalinka 'dan matarka ma rigimammiya ce kamar Nana,
Kasan 'fa babu namijin da Ya sace zuciyata farat ɗaya kamar ka and na shirya faɗa da kowa.
Murmushi yayi a yayin da Ya tsinci kansa da cewa "harda mazajen da kika Aura duka."
Knocking d'in da akeyi ne ya katse mata magana,Ya tashi 'dan zuwa Ya buɗe ta kamosa
tace"Ya kamata ace yau kasan labarin Aure na duka,da kanka zaka bawa kanka amsan
tambayarka,"
Kan gado ta mayar dashi ta kwantar ta koma kan kirjinsa ta kwanta tana Mai basa labari kamar
ba su ake ma knocking ba.
Chuchujay✍
TBC.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU
(a hospital romance )
By chuchujay
wattpad :@chuchujay
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j
Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.
Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,
Just follow and share ❤.
Episode 3⃣1⃣➡3⃣2⃣
Da sauri paki Ya tashi yana Mai kallan Nana da mamaki dan bai san lokaci da ta inda ta shigo
ba dan Ya tabbata Ya kulle ko wacce kofa da zata sadaka da cikin gidan a yayin da zai raka
abokan sa,
Shigowa tayi tana masu wani irin kallo Kafun tace "Aw mene kuke kallo na kamar kunga
fatalwa?"
Kana mamakin ta inda na shigo ko?
To Ai lokacin da aka shigo da Amarya sashen mu domin gaisawa damu na biyo danginta muka
shigo ,sai da na fahimci kowa baya kallona na shiga kitchen na buya,to kaji,wannan Shine
dalilin da yasa ka kulle dani a gidan ka,
Hannunta Suka kalla,a lokacin suka kula da plate da cup ɗin da ta ɗauko wanda ko buɗesu
umaimah bata tunanin Anyi,
Turesa tayi gefe tace "kai gyara mun nan dallah,kalle kalle ta farayi tana neman ledar da ango
ke shigowa da ita,
Aikuwa idanunta na sauka kan ledar dake kan bedroom couch tayi sauri ta ɗauko ta zauna
bakin gado tana Mai jawo extra stool ta ɗora plate ɗin ta bude ledar kazar,
Juyewa tayi a plate Kafun ta jawo gorar fresh milky yogurt ta balle mufin ta zuba a kofi tana
mai haɗe hannayenta biyu tace "yes bismillahi,
fara cin kazar tayi kamar Allah Ya aikota,zama paki yayi Ya rufe fuskarsa da Hannayen sa yana
Jin wani irin kululun baƙin ciki wanda bai taba ji ba dan gane da NANA,
Hakazalika umaimah kallanta kawai take tana raya abubuwa da dama akanta,tabbas dole ne
ta shirya ɗamarar zama Da Nana dan tunda ta Auri paki babu wanda Ya isa Ya rabata dashi sai
Allah,babu yarda za'ayi ta zubawa mutum ɗan adam ido Ya kashe mata Aure cos tana san
mijinta sannan ta shirya zama dashi na iyakacin rayuwar ta,a shirye take da cima duk wanda
yake san shiga tsakanin su koda kuwa Nana ce.
Sai da taci kazar Mai isarta kana ta kalli paki tace ",kazar amarci da daɗi ,har na tuna tawa ta
Aure,kayya Allah ka jikan maza,baku da sabon brush na wanke baki ne?"
Kamar ta zunguresa haka Ya miƙe yace"seriously Nana?
Fisabililahi menene ma'anar hakan,wacce irin rayuwa ce wannan,maine nayi maki a rayuwa,
Kifaɗa idan kina da damuwa dani ni ki faɗa mun amma ba ki ringa mun abu irin haka ba,
Ki tashi na raka ki kije ki kwanta."
Ƙaramar dariya tasa tace "Aw wai kai tunanin ka na yarda da Auren ka da wannan jairar dan
na barku ku huta? "
Lallai to Ai ni da ka ganni na dawo nan kenan da zama kuma wallahi babu mai korata.
Dawowa yayi Ya tsugunna gabanta in frustration yace "Nana Mai kike so dani,ki faɗa mun mu
wuce gurin dan Allah,"Ƙaramun murmushi tayi tace "yauwa ka biyo hanyar da Ya dace ka
biyo,"Ba komai nake so ba face ka Auri Sameera ,sannan ban yarda wata alaƙa ta Auratayya ta
shiga tsakaninka da wannan matar ba,idan ka yarda Hankalin mu Ya kwanta,dan muddin baka
Auri Sameera ba to ka shirya tarbar tsiyata,
Licking leben sa na ƙasa yayi yace"Nana menene haɗin ki da sameera wai,bana santa bana
ƙaunarta ,bazan taba iya Zama da ita ba karkashin inuwar Auratayya ,wai menene ribar ki?