Showing 15001 words to 18000 words out of 68416 words

Chapter 6 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4768

wanne baya na yake sabida ni na fara farƙe ki na fara sanar dake menene wahala da
zaƙin sex,ina fatan baki manta ba a yarda na ƙarbi budurcinki a wulaƙance a daren da a ka

kawo ki gida na.

Ina nan a Habib ɗin da kika sani kuma wallahi sai an ban ɗana tunda bake kika yiwa kanki ciki
ba kika haifesa reproduction ne daga sperm ɗin.



"Karshe ma Kin Auri ɗan kungiyar asiri masu tsafi da mutane gwara ni giya kawai nake sha
banyi abunda za'a rataye ni har mutuwa ba,"Wama Ya sani shi wannan ɗin wanne kalar lalatace
ne....



"Kai karshen zancensa yana dai dai da ƙaimasa naushi da paki wanda keta tafarfasa yayi a baki
yana faman huci."









CHUCHUJAY ✍

TBC
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a hospital romance)

By

CHUCHUJAY



EPISODE 8⃣

Wani irin tafarfasa paki yake Kafun yace "wallahi idan baka tashi ka fita ba zan karyaka na
karya banza 'dan wallahi babu abunda zai faru".

"Idan kana ganin kuma kuri nake kar ka tashi ka fita,"



Ganin irin tafarfasar da Paki yake yasa Habib tashi Yana faɗin"wallahi sai kasan ka nausheni
dan wallahi Asirinku Ya gama tonuwa Kai da ita ,"



"Sannan Ai ba karya bane nine nan nafara daga daga da ita ,kai ni koda zan karbi budurcinta ka
tambayeta ta fada maka a banza na karbeshi da wulaƙanci,a buge kuma yarda zaka gane a
banza na ɗauki abunda kake bibiya,sannan maza biyu bayan ni suka bi gurin sai kuma
waɗanda baka sani ba Kai kanka,ni nasan a yanzu Ya zama tafki"


"Ba karamu ɗaci da takaici maganganun Habib suka bawa Umaimah ba musamman da Ya
kasance a gaban Paki wanda ita ta jawowa kanta da tace Ya tsaya,she shouldn't have involved
him,



"Bata damu da mutane su san Aurenta ba amma abinda Habib ke faɗa sirrinta ne,rabon da
amata wulaƙanci irin wannan har ta manta,



"Naushi Paki yake Kai masa ta ko ina ta yarda Habib ɗin bashi da halin ramawa,"



"Security Landline ta kira wanda babu bata lokaci mutum uku suka shigo ,sakin sa paki yayi
yace da Security ɗin su tafi dashi"



"Har lokacin bakin Habib bai mutu ba ,babu abinda yake faɗi sai "wallahi sai kun san dani
kukayi ,sannan kisa a ranki kamar na ɗauki Nameer ne,kuma sai na tona muku asirin iskancin
da kuke"

Har suka fitar dashi yana surutai,



"Cije baki paki yayi yana kallan kofar da aka fita da Habib ,debating yake da zuciyarsa na ya
juya ko kar ya juya."



"Juyawa yayi inda idanunsu suka haɗu cikin na juna yayin da nata ke cike da kwallar dake san
fitowa".



"Cije bakinsa yayi yace"well im Sorry akan abunda Ya faru,He's a psychopath bai kamata ace
kin saka maganar sa ba a zuciya ta dame ki "

"Hannayen sa Ya dora akan kunnuwa sa da sigar toshewa yace "maganganun da Ya faɗa ,na
toshe kunnuwa na ,kisa aranki banji ko ɗaya ba,sannan ki sani babu Abunda wani zai fada
akanki naji soyayyarki tayi rauni a zuciyata,"Hasalima karamun sanki naji kamar anyi"



"Dariya tasa cikin hawayen da yanzu suke reto a kuncinta kafun tace"Stop pretending kamar
kasan ni wacece saboda wasu abubuwan da kaji a kaina,ka ɗaina tunani kai wani knight 'in a
shining amour ne you are all scums duk hallayyar ku ɗaya ".



"Zama yayi kan kujera yana Mai faɗin wallahi.."



"Bai Kai ga ƙarasawa ba tayi watsi da kaya dake kan table ɗinta tace "GET OUT FROM HERE
BEFORE I lOOSE IT".



"Tashi yayi in surrending manner yana Mai ɗaga hannunsa sama yace "yi hakuri zan fita,".



Babu musu ya juya Ya bar office ɗin.

"Riƙe bakin ta tayi ta saka wani kuka Mai cin rai tace "oh GOD this is embarrassing ".



Koda Ya fita Kai tsaye changing room Ya wuce yana Mai jin zuciyarsa na masa zafi,ga wata
zazzafar soyayyar umaimah da tausayinsa da Ya kuma Shigarsa,kamar yarda ta faɗa baisan
wace ita ba ,sannan shi a yanzu soyayyarta yake nema in yaso duk lokacin da taji Ya kamata
zata bashi labarinta,


"Tsoran da ya gani a idanun ta a yau dangane da maza shine yake kara bashi tsoro,dan ciwan
da Habib Ya famo mata ba ƙarami bane ".



Yana tsaka da wannan tunanin yaji an dafa shi"

Ɗagowa yayi dan ganin wanene ne"



"Cike da kulawa Kb yace "Paki naga fitowar wannan baƙon na DR Bulama da maganganun da
yake faɗa sannan kaima naga fitowarka wanda Ya tabbatar mun akwai abunda ya faru
,"Wanene mutumin and Mai yasa ka zauma nan kana wannan tunanin,

Hope ba abunda nake tunani bane?



"Ganin yanayin fuskar Paki yasa KB cewa "No No No paki No dont tell me maganar da mukayi
da Kai baka dauka ba?"



"Cike da damuwa yace"wanda Ya fita office ɗinta Habib ne ,shine mijinta na farko .



Kuresa da ido Kb yayi yace uhum"menene Abun damuwa a gurinka da tsohon mijinta Cos naji

ance har dukan sa kayi"

Ko zan ji dalilinka.



"Kallan Kb yayi na wani lokaci kafin yace"Kb gayen nan ɗan iskane da kaddara kawai yasa
umaimah Aurensa tun fari sannan maganganun da yazo yana faɗa akanta bakaji ba babu daɗi
wanda na kasa jurewa!



Shine ka dake sa?

Da fari ma Mai kake a ciki a yayin da take zantawa da tsohon mijinta ,



Ba tare da Ya kallesa ba yace "ita tace na tsaya Cos ta ce masa we are in a relationship' wanda
yayi pissing ɗinsa off "



"Wani irin takaici ne Ya ziyarci Kb Kafun yace"yanzu ka yarda amfani da kaine kawai Zatayi Cos
na tabbata gobe baza ta ganka tace maka honey ba ,"



"Paki wai ina tunanin ka Ya tafi,nida da zarar na sake sanin wani labarinta nake kara tabbatar
da she's not the one,"Haba paki akwai mata da yawa da suke bibiyarka a waje maine zakayi da
bazawara Mai issues akanta da yawa?



"Sosai maganar KB ta Sosa masa Zuciya wanda tabbas da ace ba shine ba da babu abunda
zai hanasa chasa sa yayi masa shegen dukan da bakinsa bazai kuma faɗar aibunta ba,"

"A zahiri kuwa sai cewa yayi"KB i Love her and thats All that matters sannan bazan boye maka
ba maganganun da kake faɗa a kanta suna Sosa mun rai wallahi bana jin daɗi dan kawai
kaine".

"Marairaice fuska yayi yace"na faɗa maka ina santa ba da Wasa kuma nake ba ,shin haramun
ne idan naso mace irinta,bafa wai mazinaciya bace ,Aure ne kawai tayi guda uku wanda batayi
sa'arsu ba wannan ta samu ƴaƴa uku Shin menene laifinta a ciki,"?



"Na yarda bansan Mai Ya fito da ita daga gidan mazajen ba amma tabbas wannan ɗan iskan da
yazo a ido ma kasan ba mijin da zakawa ƙanwarka ko ƴarka, Sha'awa bane"



"Juyowa yayi yana facing ɗinsa yace "KB dan Allah idan baza ka tayani san Umaimah ba ka
daina zaginta a gabana ina jin ciwo,"

Wallahi ina mata san da idan na rasa ta zan shiga hali Mai wuya.



"Karantarsa KB Ya nutsu yanayi,tabbas Tunda yake da paki daga yarintarsu har girmansu bai
taba ganin irin wannan soyayyar a idanun imam ba"



"Ya yarda yana santa amma yana ji masa ahalin gidan su ne wanda da wuya su karbi batun
Umaimah kar ma ace nana"



"Ajiyar zuciya yayi yace "naji Paki,idan kana san Dr Bulama bazan hana ka ba sannan bazan
sake fadan abu mara kyau akan ta ba ,amma ni zan maka bincike akanta ,"amma 'fa wani
hanzari ba gudu ba ,kasan babu yarda za'ayi ta so ka a yarda take"

Sannan bama wannan ba,babu yarda za'ayi su Nana su amince da wannan maganar kaima
kasan ba sai na faɗa maka ba,



"Murmushi yayi a karo na farko yace "KB ni na yarda da kaina kuma nasan da yardar Allah
umaimah zata soni ,sannan maganar yan gidan mu ,kabarni na fara samun soyayyar tukunna
nasan yarda zan bullo masu".

"Murmushi KB yayi yace shikenan abokina Allah Ya zama abunda yafi Alheri yanzu ka shere
hawayen zamu shiga labor room dukkanmu da Dr Maryam ,sannan around 5 muna da lecture
da masoyiyarka".



"Tsaki paki yayi yace uwar hawaye zan share tunda Ai ka cika bokiti dashi,"

And anya Dr Bulama zata iya koyar da mu wani abu yau ɗinnan!



"Ɗaga kafaɗa Kb yayi yace"well a yarda na lura bata Wasa da Aiki kila wannan abun bazai
hanata ba".



A tare suka fita inda suka shiga daƙin haihuwa dan ganin karban haihuwan practically duk da
bashine ganinsu na farko ba.



***

Zazzaune suke a karamun lecture hall ɗin dake cikin asbiitin suna Mai tsumayin Dr bulama,

"Wani Sanyi imam yaji a zuciyarsa lokacin da yaga shigowarta,"

Fuskarta babu annuri amma hakan bashi ne Ya boye kyawnun fuskarta ba.



Ƙaramun white board ta matso dashi a yayin da ta kunna system ɗinta yarda zai Kai ga
projector ɗin da already akayi connecting ,

Cike da kwarewa ta fara koyar dasu wanda dukkansu suka bada hankalinsu akanta,



Kamar ance ta ɗaga Kai ta hango Aisha shareef gefen Paki tana Mai kananan surutu inda
shikuma hankalinsa baki ɗaya yana kanta,

Buga maker ɗin tayi da ƙarfi yace "shareef you're get up from that seat sannan ina fatan kinsan
nan ba filin soyayya bane,why Are you disturbing the guy bayan shi hankalinsa yana kan
karatu"



"Baki ɗayansu suka maida hankalinsu kan Aisha shareef wadda kunya ta kamata kamar ta
nutse,

Kasa tayi da kanta tace "sorry Dr .



"This should be the last time da zan ganki zaune kusa da imam paki tunda naga Alama yana
distracting ɗinki now dawo first roll".



Babu musu ta sauko first roll d'in ta zauna tana mai jin haushin abunda umaimah tayi mata.



Bayan lecture d'in Ya kare kowa Ya fita ,saura paki,

Dago kai tayi ta kallesa ganin bai tashi ba,tace"Mr im done with your class zaka iya fita Next set
zasu shigo,"



"Saukowa yayi yana Mai faɗaɗa murmushinsa ,har sai da yazo gabanta Kafun yace "were you
jealous ?"



Excuse me?



Murmushi yayi yace "nevermind I LOVE YOU too,"Kafun tace wani Abu yayi saurin ficewa a hall
ɗin ,

Binsa kawai tayi da kallo yayinda ta tsinci kanta da murmusawa.





CHUCHUJAY ✍

TBC
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK



AURE UKU

(a hospital romance)

By

Chuchujay.

EPISODE 9⃣

Washe gari bata shiga Asibitin ba saboda weekend ne kuma musamman saturday ,sunday ne
takan shiga , Tana tsaka da bacci taji ana ja mata ƙafa,



"Yi tayi kamar bata san anayi ba ,"Cigaba da jan ƙafar yasata farkawa ,

Dariya nadiya tasa tace "hamma nameer i won dole ka bani Tab din ka na sati nayi game,"Ɗan
bata rai yayi yace"mami why do You wake up We bet ne 'fa.



"Tashi tace tace "akan me kuka yi betting ɗin tell mami"



"Haurowa gadan da take Nadiya tayi tana Mai washe hakora tace "mami betting mukayi nace
masa yau saturday mami na bacci amma nasan idan naja miki kafa zaki tashi ,shine hamma
nameer yace Ai bazaki tashi ba Cos kina da gajiyan weekday ,amma idan kin tashi yasa mun

tab ɗin sa na sati ɗaya".



"Ƴar karamar dariya umaimah tayi Kafun ta kalli nameer dake faman haɗe rai zai bawa nadiya
Tab ɗin sa tace"okay ku saurare ni,"Anything betting is haram,ko menene shi koda da wasa
ne,a musulunci babu kyau 'dan Haka Banda Wasan betting,



"Idan nameer zai baki tab ɗin sa aro ne to Ya baki amma ba wai ɗan Kin cinyesa a bet ba
,okay".



"Kaɗa kai sukayi a tare inda Nameer yace dama mami banyi niya ba"cos duk ranar da na
arama nadiya Tab ɗina sai ta cinye chaji tas take dawo mun dashi .



"Mami nima Tab ina san na kalli johnny johnny hamma Nameer kuma baya bani,



"Dariya Umaimah tasa ga maganar da Abdallah wanda yake shigowa da gudu shatu na binsa a
baya yayi".



"Ɗannowa yayi kan gadon yana Mai hawa jikinta yayin da ta rungumesa ,"



Zama shatu tayi bakin gadon tace"Adda ina kwana ?"Kin tashi kenan.



"Murmushi tayi tace "wallahi shatu sun tashe ni zan ce ma ,ina fatan baku jira ni ba kun karya ."



"Kaɗa kai tayi tace "ai Adda kema kin san rigimar Abdallah da rashin haƙurin sa ga yunwa ba
zai bar mu shan ruwa ba musamman ace mun kai sha ɗaya ."

"'Ɗan buɗe ido tayi tace "har sha daya ,kace na sha bacci,".



"Mami mene plan ɗin yau ko za mu Roly park ne it have been a While,nameer Ya faɗa yana Mai
Marairaice murya..



A tare suka haɗa baki wajen faɗin"roly park,suna chanting tare,".

Zata yi magana taga wayanta na ringing da baƙuwar Number,

Ɗauka tayi ta kara a kunnenta tana Mai faɗin hello a yayin da yaran nata suka cigaba da faɗin
Roly park ,Roly park,.



Daga ɗaya bangaren taji an kashe wayan 'dan Haka tace naji roly park kuje Auntyn ku ta shirya
ku bari na yi wanka na ci abinci,



"Ihu suka fara cike da murna ,kana suka fita nadiya na faɗin Yau zan ridding real horse".



"Kallan shatu umaimah tayi bayan fitar nameer da nadiya tace"Auntyn yara shiryawa zakiyi
muje fa".



"Murmushi tayi tace "Adda kuje dai ku dawo kinsan ni ba ma'abociyar san fita bace,ina nan gida
ina jiran ku,ga wankin su Abdallah chan ma nasa cikin washing machine ga gugan su kinsan ni
da aiki muna haɗe amma wani zuwan zan biku.



"Kallan ta Umaimah tayi cike da kulawa tace "shatu nasan halin ki fa kilan ki zauna kina aikin
tunanin da kika saba ,in dai Aikine idan mun dawo ni da kaina zan taya ki".

"Faɗaɗa murmushin nata tayi tace "Allah Adda kar ki damu ,ba wani tunani da zan tsaya dama
akwai wani series film da nake kalo ,ina gama aiki zan cigaba har ku dawo,"



"Shikenan tunda kince Haka ,shafa kan Abdallah da yayi makale a jikinta tayi tace "malam
Abdallah maza tashi kaje Aunty ta saka maka sweater a saman rigan nan Cos da sanyi,".



******

"Kai tsaye Roly park suka je ,park ne wanda aka tanada domin yara dan kuwa duk wani abu da
yaro zaiso na dan Wasa akwai a gurin .



"Kallo ɗaya zaka yiwa su nameer kasan suna cikin farin ciki,"Motan wasan dake ta juyawa da
yara nadiya tayi da gudu tana cewa"mami this".



"Murmushi umaimah tayi tace "okay lets go ,da gudun su sukaje gurin ,inda ita kuma taje siyan
coin.



"Sun jima a wurin motan ,dan coins ma sai da ta b'ata a lissafin siya,.



Bayan sun bar gurin suka nufi gurin doku nan Wasa,

"Nameer ne yace"mami ina nadiya tayi"?



"Da mamaki ta juyo tace "nadiya ? Ina tayi"?

Cikin lokaci ƙankani hankalin umaimah Ya tashi da ta fahimci Nadiya bata biyosu ba tun daga
baya,

Daukar Abdallah tayi ta riƙe hannun Nameer tana Mai san assuring kanta a gun suka barta
,tace"Nameer nasan tana chan gurin Cars ɗin chan ,muje zamu ganta"



Kula da ɗan ruɗewar da tayi nameer yayi yace "mami nasan ma tana chan nadiya kuma da san
mota ,ko sch mukaje sai mun shiga aji zaki ganta ta shigo,"



"Wata kwallane ya zubowa umaimah lokacin da sukaje gurin motar bata ga nadiya ba ,"Gogewa
tayi tana Mai tambayar mutumin da suka siya coin a gurinsa ko ya ganta.



"Kafun Ya bata amsa ta tsinci muryar nadiya tana mai faɗin"mami!!"



Da saurinta ta juya,turus tayi ganin nadiyan da Paki ?



Da gudu nadiya ta zo gurinta tana faɗin "mami meet My new friend ,"



"Wani kallan banza ta bata Kafun tace "ina kikaje when kin san i warned You ba sau ɗaya ba
akan strangers kina so na fara dukanki ko?".



" A yarda tayi maganan da harshness Ya tabbatarwa da Paki tayi fushine dan koda ta joyu sai
da ya tsinci tashin hankalin da take shirrin boyewa, ".

Boye nadiya yayi a bayan sa yace"calm down mummy And ni Ai kinsan ba stranger bane".

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login