Showing 27001 words to 30000 words out of 68416 words

Chapter 10 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4752

za'a samu
mai faɗawa Nameer abun da yake faruwa ,

Sai kuma maine zai faru?

Kuka sosai ta fashe dashi.

Kukan da take haka paki yake jinsa har cikin ransa ,

Idanunsa ne suka fara kawo ruwa dan akan umaimah da damuwarta ya manta da Mai ake kira
Dakiya da jarumta,

Zuciyarsa ce ta ƙara karyewa da Ya fahimci a gidan mahaifinta ma ita da yaranta bawai zamane
ake dasu na soyayya ba.



Juyawa yayi ya fita dan idan Ya cigaba da tsayuwa bai san maine zai faru ba.



Rungume ta Hindu tayi bayan fitar paki tana Mai lallashin ta,

Zumbur Ta miƙe tace"sai naje italy' na kamo habib nasa an wulaƙanta mun shi a kasar nan,".



"Baza kije italy' ba."



Ɗaga kai tayi 'dan ganin Mai maganar,

Da gudunta ta ruga gareshi ta faɗa jikinsa tana Mai faɗin"Daddy".cikin kuka,



Shafa ƙanta yayi a hankali kana ya raba ta da jikin sa ya kamo hannunta Ya zaunar da ita kan
kujera Ya zauna a ƙasa hannunsa cikin nata .

shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa idan yana ganin umaimah ciki hali irin
wannan.

gefen ta yaya Abubakar yazo Ya zauna shima yana jin dama zai iya ɗauke mata kuncin dake
damunta Ya maida kansa.



Daddy ne yace "umaimahn daddy,"Ni kaɗai nasan abunda nake ji idan ina ganin

hawayenki,jikina yana bani Nana surbajo bata farin ciki dani a duk inda take saboda i failed her,



"Nine na ja miki komai sabida ni na haɗa Aurenki da Habib a karo na farko sannan na haɗa a
Karo na biyu,"

Ki yafe mun umaimah ,soyayyarki ce ta rufe mun ido nayi tunanin gata ne na miki.



Saurin goge hawayenta tayi tace"daddy mana,ni baka mun komai ba ,hasalima dalilin Auren na
samu ƴaƴanda wasu ma da kuɗi suke nema amma sun rasa,"Ni'ima ce Allah yayi mun a lullube
kuma ina gode masa a kullum daddy,



"Idan ka cigaba da ɗorawa kanka laifi ni Bazan iya yafe wa kaina ba,"Ƙaddara tace da babu
wayau ko dabarar da za'isa na tsallake ,

Mene kuma abun daɗin daddy?



Ina da rayuwa kuma ina da lafiya shine yafi komai .



Murmushi yayi ɗan yana san yaga da kanta ta lallashi kanta wanda a Yanzu tayi sannan Ya
gamsu da ƴar ɗiyar sa Ta girma .



Goge mata ƴar karamar kwallarta yayi yace "nan da awanni 48 za'a kawo mun Habib har gida
ba sai Kin wahalar da kanki binshi italy' ba,"

Ba italy' ba ko ina ya buya a cikin duniyar nan ina da yarda zanyi a ɗukafar dashi gabanki
sannan ban shirya sassauta masa ba ,tunda bayan shekara goma sha ɗaya bai ƙasa a gwiwa
ba yazo dan bata miki,

Nikuma na shirya yaƙi da duk wani Mai saki kuka yarinyar daddy.

"Murmushi maganar da yayi ta karshe tayi ,"



Daddy ya kamata ka gane yarinyar nan ta girma fa yaranta uku fa amma Bazaka ɗaina
shagwab'a taba .

Yaya Abubakar Ya fada.



Murmushi daddy yayi yace "ai ko duniya umaimah ta tara tana nan a yarinyar daddy."



A haka suka gama lallashinta Kafun suka tafi,

Bayan Ya rage daga ita dai Hindu a ɗakin ne ta kalleta tana tunanin ta inda zata fara tambayarta
ina Paki,



Ɗan shiru tayi Kafun tace "ke dawa kika dawo"im sorry na barki ke ɗaya."



Ƙaramun murmushi Hindu tayi tace"kawai kice mun ina Imam paki,"To Inajin Ya wuce.



"Ya wuce kuma?"



Kallanta hindu tayi tana mai san gintse dariyarta tace "kina da matsala da hakan ne?



Ɗan haɗe rai tayi tace "ina tambayane kawai ɗan Ya shigo har falo ba ba tare da izini na ba."

Dariya Hindu tasa aranta tace "munafuka kina so kina yanga".



*********

Kwance take kan Gadonta da dare tana Mai tariyo abubuwan da suka faru a yau,

Tunanin Paki Shine abinda yafi damun kwakwalwarta dan duk yadda taso ta cire sa ta kasa.



"Yau yazo sannan yaga wani bangare nata da ba kowa Ya sani ba,

A lokacin tsintar kanta tayi da kasa yin shiru na abinda yake damunta 'dan Nameer Ya riga da
Ya gama tabo mata damuwarta,



Tsakanin ta da habib kiyayya ce amma bazata taba bari tsakanin sa da Nameer Ya zama
kiyayya ba duk girman lefin da zai mata.



Gyarawa Abdallah kwanciyarsa tayi daga kan cikinta dan yanzu baya yarda yayi bacci idai ba a
gurinta ba a gurinta ɗin ma a jikinta,

Murmushi tayi tana Mai kissing goshinta a zuciyarta tana Mai faɗin"ko me kaikuma Zan faɗa
maka akan naka mahaifin idan ka girma?"



Ta dai san baza ta tab'a faɗawa Abdallah mahaifinsa ɗan blood money bane komai
rintsi,sannan Zatayi duk yarda Zatayi taga abun bai bibiyesa ba Tayi Wannan alwashin.



Addua tayi masa tayiwa kanta ,

Tana rufe idanunta paki Ya cigaba da dawo mata,

Jin tunaninsa zai addabeta yasata jawo wayanta ta shiga numbernsa da tayi saving da INTERN
I'P .

"Murmushi tayi a yayin da zuciyarta ke ingizata akan ta kirasa,"

Har ta danna zata ƙirasa Tayi saurin fita kamar an tsikare ta.



"Karshe ta tsinci kanta da tura masa message "thank you for everything'."



Tafi karfin minti nawa tana duba wayarta taga ko ya maida mata amma shiru,a haka har bacci
b'arawo Ya kamata.



Bangaren Paki kuwa.

Yana fita a sashen umaimah ya fita a gidan baki ɗaya,motar sa Yashiga ,kai tsaye gida Ya
nufa yana Mai jin zuciyarsa na Tafasa,



"Yana ƙokarin haurawa sama yaji muryar nana na faɗin"an dawo daga kokerar ne?"

Shine kake fama sanɗa kamar b'arawo?



Ba tare a Ya Kalleta ba yace "Alhamdulillah ba'a Sino's biggest super market aka kamani ba da
hannuna maƙale a baya ina zazzare ido kamar an ƙaɗa bera a buta ba".

Ki barni yar da kika ganni nana dan Allah.



Har Ya haura saman yana jin banbaminta da bala'inta na yau da kullum.



Kai tsaye ɗakin ummu Ya nufa,

Yana knocking sau ɗaya ta bashi izinin Ya shigo,

Zaune Ya tarar da ita tana duba wani file,

Zama yayi kan stool Ya gaida ta,.



"Amsashi tayi tana Kallansa kafin tace lafiya dai ko?"

Naga ka dawo da wuri.



Saukowa yayi daga kan stool ɗin Ya zo kusa da ita ya zauna yana Mai ɗora kansa a kafaɗarta
Kafun yace"Ummu zuciyata zafi take mun".



Cikin rikidewa tace "wanne irin zuciya kuma muna zaune kalau Imam?"

Hawayen dake maƙale a idanun sa ta hango,cikin tashin Hankali tace"tashi muje asibiti imam
ba abun Wasa bane wannan harda kuka?"



"Ƙaramun murmushi yayi yace dama akwai likita da zai mun magani ummu,".



Dafa sa tayi tace Imam kasan dai baka da wanda zaka faɗawa damuwarka sama dani ko?

"Just tell me ni da kai zamu gyara komai ,"i promise,akan clip ɗin chan ne,hope baka da hannu
ciki?



"Dan ajiyar zuciya yayi yace an kama waɗanda suka dora ma".



Ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah "Wallahi yarinyar jiki na raina ,na ji tausayinta Sosai".

Tsintar kansa yayi da murmushi dan yasan mahaifiyarsa ce zata fara ƙarb'ar umaimah.



Haka nan Ya barta ba tare da Ya faɗa mata komai ba yana Mai jiran lokaci.



Yana tsaka da tunaninta da halin da Ya barota yaga saƙonta,

Kamar an sashi a aljanna musamman da Ya tabbatar tayi saving layinsa kennan.



"Har zai replying huɗubar Hindu ta dawo masa, "

Haka Ya dane zuciyarsa ba tare da Ya mayar mata saƙon ba duk yada yaso kuwa.





Chuchujay ✍

T

B

C.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️:
https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqKDgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AURE UKU

(a hospital romance)

By

Chuchujay ✍

Episode 1⃣5⃣➡1⃣6⃣

BAYAN SATI BIYU.

"Mami ina ta cewa kiyi haƙuri amma mami kina ta ignoring ɗina gashi zan tafi".



"Banza ta masa a karo na ba iyaka Kafun tace"zo nan Nameer,"



Babu musu Ya ƙarasa gare ta Ya zauna a gefen ta fuskar sa gwanin ban tausayi,

"Kallan sa tayi na ɗan wani lokaci tana Mai jin soyayyar sa da tausayin sa kafin ta jawo sa jikinta
ta rungume sa tsam,"



"Raba jikin ta tayi da nasa tace"Nameer ina san ka sosai nasan ka san wannan,and yanzu
Abuja da zaka wuce ,kasa ma ranka karatu kaje ,"

Study hard Nameer ,i want to be proud of you ,kar kasawa ranka wai baka da kowa achan gurin
,kaje ne dan kayi karatu,



Sannan ina so Nameer kasan irin abokan da zakayi hulɗa da saboda rayuwa ce zaka je kayi
sabuwa and i hope you wont disappoint me ,



And last abunda nake san faɗa maka ,Abunda ka faɗa last time bana san Ya Maimaita kan sa
dan Allah Nameer ,you're hurting me with your words,sannan duk wanda kaga Ya kashe mutum
a duniya to karshen sa baya kyau Kafun akai ga lahira,



Na tabbata baza kaso mamin ka ta shiga wani hali ba saboda i will die without you,

I need you ,Nadiya and Abdallah also needs you,

So please Nameer bana san wannan zuciyar da kake yawanyi.

Rumgume ta Ya kuma yi yana Mai shesheƙar kuka Kafun yace "mami baza kizo muje tare
ba,?"Its a flight 'fa minti kaɗan zaki dawo,



Shafa kansa tayi tace"Nameer i promise you first visiting ni zaka fara gani,".



Murmushi yayi wanda Ya bayyana side dimples ɗin sa yace "mami i will make you proud i
promise".



Kissing forehead din sa tayi tace "Allah yayi maka Albarka".



Da gudu nadiya ta shigo tana Mai faɗin"Hamma Nameer daddy fa yana chan yana jiran ka,and
yace tare zamu tafi,. "



Kallan ta umaimah tayi tace dake?



Kaɗa kai tayi tace"Eh,daddy yace muje tare Cos i was crying ,mami muje da Abdallah?"



Kaɗa mata kai tayi tace "A'a Abdallah bazashi ba amma ke ɗin kije ."



To mami"ta faɗa da dauki Kafun ta fita a falon tana murna zata raka Nameer abuja. "



Tare dukkan su suka je Airport dan raka Nameer,

A dawowa ne ta bawa shatu Abdallah suka bi motan da su daddy suka zo wanda Aunty sadiya
ke tuƙawa a yanzun suka koma gida,ita kuma tayi CITY HOSPITAL.

SATI BIYUN DA SUKA GABATA.



Kamar yarda daddyn umaimah yayi mata alƙawari within 48 Hours aka kamo Habib daga
wani ɗan ƙaramin ƙauye Mai suna Cosò cikin garin italy ,

Last garin da bai tab'a tunanin za'ayi tracing ɗinsa a gurin ba.



"Lokacin da aka dawo dashi nigeria da fari sai da yayi gardama akan bashi da hannu akan abun
da Ya faru,amma da yasha matsa babu shiri yayi confessing ."



Babu irin roƙon da baiyyiwa umaimah ba akan ta yafe masa ko dan darajar Nameer amma
tace "Ai da yasan da darajar Nameer bazai ƙokarin zubar mata da daraja ba."



Sosai Ya daku,Kafun aka kaisu court ,zaman ƙwana daya aka kaisu gidan maza.



"Ta bangaren daddy kuwa Ya yanke Alaƙa da mahaifinsa dan a cewar sa Ya kasa saka Habib a
hanya tunda tun fari Ai Ya musu Kashedi".



"Bangaren asibiti kuwa ,bayan Abun da Ya faru ta samu ƙwaƙwaran kira daga board,"Kamar
bazataje ba amma Hindu ta lallashe ta Akan taje.



Haka nan ta shirya taje,baki ɗaya board ɗin asibiti ne suka hallara dan tattauna abunda Ya faru ,

Zaune ta tarar already Paki har yaje,

Murmushi tayi masa lokacin da ta haɗa ido dashi,

Ɗauke nasa yayi kamar ma bai san da ita a gurin ba,

Tunani ta fara ko sun faɗa masa wani abu da bai dace ba .

Ta rasa dalilin da zaisa ana kiran board meeting dashi,

Ita likitan asibitin ce shi kuma Intern ne its okay ma idan ance yayi abune da za'aiya reporting
ma school ɗin sa ,amma Ai case ɗin is close tunda an gane menene gaskiyar Al'amarin ,Shin
mene dalilin kiran nasu?

Board President ne yazo cos dama shi kaɗai ake jira.

Sake maimaita abunda Ya faru yayi Kafun yace "Dr Bulama i heard zaki aje aiki" .



Ƙaramun murmushi tayi tace"with All due respect sir,

Im offended a yarda kayi Narrating whole situation ɗin nan,

But its okay what's done is done i Just hope lesson ɗin yaje ,

And yes im resigning from HERE.



Ɗaure fuska tayi cos tasan halin su dukkan su yan rainin hankali ne sannan meeting ɗinnan
akwai wani motive ,



"Dr Bulama im pleading on case ɗin Jabir dan Allah kiyi haƙuri ki janye case ɗin da kika ƙara
akan sa na harassment Abun yayi masa yawa imagine kece a shoe ɗin sa ya za kiyi.



"Wata irin dariya tayi tace "Mr director ,bazan taba zama a shoe ɗin Nephew ɗinka ba ,shi
munafiki ne ni kuma ba munafuka bace,bazan taba yin abunda yayi min ba ga wani,"



"Sannan idan baka manta a lokacin da na yafe masa case ɗin harassment da defamation of

character na yi tunani ba ɗan iska bane wanda ba a bawa isashen guidance ba,

Nayi tunanin kuskure ne ,ashe wautace ,so bana tunanin yanzu 'dan na kara da case ɗin
akan sa wani abu ne."



And yes idan na janye masa wannan case ɗin kaga za'a iya bashi licence ɗinsa na aiki
wanda ni bana san hakan,



"Amma yanzu kaga an kwace masa lisisi aikin likitanci na shekara goma sha biyu,mene yafi
wannan dadi?"



Im Happy that's All that matters ,i don't Care about him .

I didn't spare My baby daddy ,wanene Jabir.



Dukan table ɗin tsakiya ɗaya daga cikin board members ɗin tayi tace"watch it Dr Bulama,you're
the youngest here,Mai kika sani?"

Mai kike taƙama dashi da kike fama da wannan arrogant and rude attitude ɗin,

You're just 29 act your Age.



"Cikin sanyin rai umaimah ta kalli matar da Akalla zata yi arbain ,tace"im the youngest ,im the
fastest,i'm intellectual,

Na ɗauki ciki guda Uku a womb ɗina ,na haifa ,ina kan raina,less time, but teaching them the
best ethics ,and yea Less i Forget kar kice ban faɗa Maki ba,

I Am a single mom. "

Duk wannan yayi girma ga ƴar shekara Ishirin da tara,so Mai yasa Zan Acting Age ɗin when
abunda yake kaina yafi karfin age ɗin?

" Snr Dr Halisa ,cikin mutuntawa ina san na faɗa miki cikin shekarunki Arbain da wani abu
na tabbata bakiyi experiencing abunda nayi experiencing a rayuwa ba,this is not the first time da
kike poking hancin ki cikin abunda Ya shafe ni,

Kin zata lokacin da kike faɗawa Director ina sleeping da board members ban sani ba?



"Kar mu fara allura ta tono garma,"

Sannan abu na ƙarshe ,im no hypocrite .

Da shi nake taƙama.



"Gyaran murya president ɗin yayi yace"ba shi Ya kawo mu ba please".



Kallan Dr halisa wadda tayi gum umaimah tayi tace"nima nasan haka Dr halisa ce kamar bata
san da hakan ba."



"Dr Bulama your resignation is rejected tun kafin ki kawo cos i have talked with the
management this hospital need you,

Dan Haka on behalf of All the board muna tura miki Apology na abunda Ya faru ,hope You will
accept this Apology".



Shiru tayi na wani lokaci idanun ta akan Paki wanda yaci mur kafin tace "ina fatan kuna sane da
bani kaɗai akayiwa laifin ba,"Har da Imam paki.



"Hannun sa Ya dunƙule yana feeling less a gurin ,"Murmushi Director yayi yace "we Are very
sorry Imam Paki,"

President Ya Karb'a ta hanyar faɗin ,shima yana bin mu cos abinda ma'aikacin mu yayi Ya kusa
lalata masa career ɗin sa and babban Abunda dama muka gama yanke shawara Shine,za'a cire
sa daga ƙarkashinki dan gujewa jita jita irin haka,musamman wadda ake cewa kuna soyayya.



"Tana kokarin magana paki Ya katseta ta hanyar faɗin,"Dr Bulama i can talk for My self,

Gyara zaman sa yayi a karo na farko yace "with all due respect Inajin daɗin aiki da Dr Bulama i
refused to be switched saboda ba Wasa nazo yi ba ,likita anan yayi koƙarin bata mun suna and i
know the law i can sue this hospital for All i care,

So banzo na zauna anan ba dan ana mun Kallan kaɗan.



"And yes Ba soyayya muke ba ni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login