Showing 24001 words to 27000 words out of 68416 words

Chapter 9 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

Advertisement

14 Apr 2025

4806

amma
kasancewar Fuskar ki ciki ba ƙaramun soya mun zuciya yake ba,"

"Dafa saitin zuciyar sa yayi yace "wani irin ƙuna haka nake jin zuciya ta ,"

Ƴar ƙwallar dake shirin zubowa a gefen idanun sa Ya goge yace "wallahi tallahi Umaimah ina
mutuwar sanki ,wallahi ina miki san da bana yiwa kaina.



"Ƴar da kike nuna kamar zamana cikin soyayyar ki abune mara dacewa, da ace da yarda zanyi
na cire soyayyar ki da na yi Ɗan na faranta miki rai ,



Wallahi umaimah ina sanki da yawa babu abunda Ya dameni da past ɗin ki ni present ɗin ki ne
a gaba na,

Kiyi haƙuri idan soyayyata tana b'ata miki rai .



Tashi tsaye yayi ya juya yana Mai goge idanun sa,

Ba tare da Ya juyo ba yace"And na manta ban faɗa miki ba ,guy ɗin da yayi editing Clip ɗin
yana ciki shi muka fara kamawa Kafun Ya sanar mana da Dr Jabir Ya bashi kuɗi masu yawa
yayi editing amma bashi yayi uploading ba ,sannan an cire clip ɗin daga dukkan websites,".



"Juyawa yayi Ya taka Ɗan shiga ciki,"

Baki ɗaya taji kamar an cire mata wata laka a jikin ta,

Kalaman sa ne kawai ke mata yawo a kwakwalwa ,haka nan ta tsinci jin zafi a zuciyarta ta
dalilin hawayen sa da ta gani,



"Tafi minti goma zaune a motan Kafun ta tashi tabi bayan sa ,

Tun kafin ta shiga take jin ihun Dr Jabir yana ƙarb'ar warb'a hannun sojojin.

"Zaune ta tarar da Hindu gefe guda tana Mai juya wayarta ,gefe guda kuma KB ne shima zaune
sai Paki dake chan gefen Wanda yayi editing Clip ɗin wanda yasha Ɗan banzan duka ,daga
gani sai da yasha luguɗen tsiya Kafun ya faɗi sunan Dr Jabir.



"Kallan matashin yaran tayi tace "nawa suka biyaka?"

Bakin sa kamar ansa goruba saboda kumburi kafin yayi mata alamu da hannu.



"Ƙaramun tsaki KB yayi yace 500k fa,just 500k Ɗan kawai Ya b'ata sunan wasu ba tare da
yasan Mai zai biyo baya ba,"Guy you messed with the wrong people.



"Zama tayi akan kujerar dake facing Paki wanda koda wasa yaƙi bari su haɗa ido,"

Kallanta ta mayar kan Dr Jabir tace "ku tsaya da dukansa haka",



"Matsawa tayi daf dashi tace "you're a very good doctor ,ina tuna lokacin farko da na fara aiki da
kai,it was amazing saboda yarda mukayi aiki hand in hand,"



"I have been dreaming naga na samu likita da yasan abunda yake a kusa dani,"I wanted to work
with you again and again saboda kasan Mai kake.



"Ban sani ba ,a lokacin da kazo kace kana sona da wane motive kazo but i told you i wasn't
interested da mutunci nayi rejecting offer ɗin ka idan zan tuna ,amma ka dauke sa something
else,ban san mane Ya maida soyayyar da kace kana mun ba ta koma kiyyayya ,"

"Ko 'dan tun farko wani abu ne dama ka shirya?"

"I wasn't understanding sudden diss ɗin ka akaina , "Bani da wani riƙo da nake dashi akan ka,

I don't hate you,

Nasan kilan you're just jealous of me And kana tunanin connection Ya kawoni nan,but i told you
ranar a office ɗin Director ,ina matsayin da nake, da gumina,da hawayena ,da jinina .

Da kasan gwagwarmayar da nasha Kafun nazo nan Bazaka ma fara tunanin kaini ƙasa ba.



"But you decided to,ba tare da kayi tunani sau biyu ba kwakwalwarka ta baka wani banzan
shawara na ɗora edited clip ɗin nan da Intern ɗina ."



"Kasan kuwa abunda ka aikata?"

Kasan girmansa kuwa ?



Ƙaramun murmushi tayi tace "trust me anan gurin zan nuna maka ƙarfin izzar kuɗi ,'dan bayan
sun gama chasa mun kai,za'a kaimin kai Asibitin kaje gaban board members ɗin da kasa suke
nuna mun dan yatsa ka wanke ni".



"Ɗagowa tayi ta kalli Paki wanda yayi saurin ɗauke idanun sa akan ta tace "shima ka wanke
sa,then i will Call the press ka tabbata ka b'ude kazamin bakin ka kai da wanchan abun then i
will decide your fate ɗan ban shirya yafe maka ba nan kusa.



"Tashi tayi tace ina waje ku chasa munshi kamar yarda ake chasa shinkafa amma ku tabbatar
baku taba bakin sa ba dan dashi nake san yayi magana,".



Wayar tace ta hau ruri,Director ne ke kiran ta,tana ƙokarin ɗauka ta tsinci muryar Dr Jabir yana
faɗin"bani na kawo idea ɗin ba wallahi".

"Juyowa tayi tana Mai ƴar ƙaramar dariya tace"kana nufin kace mun ba kai da wancan abun
bane kawai a cikin wannan haɗakar?"



"Takowa tayi tace"its getting more interesting ,faɗa mun wanne shegen ɗan iska ne ɗayan,



Wayartace ta sake ƙara,

Daga masa hannu tayi tace "ɗan tsaya".



"Dagawa tayi tasa a handsfree tace "director ina ji,barka da rana ,ina fatan ƙalau.



"Cikin sassauta murya yace"Dr bulama ina kika kai Dr Jabir?"

Don't do anything illegal with him,kar ki saka kanki ciki matsala,you will answer to the board.



"Gyara zama tayi kamar yana kallanta tace"mr Director sir,ina fatan wanda Ya faɗa maka bai
faɗa maka da hukuma nazo ba,Hukuma suka tafi da Jabir dikko har iri biyu,"



"Akwai Dodanni da malaikun duniya a ciki,sannan ni zakanyyar da zan cinye duk wanda yayi
ƙokarin Wasa da jelata,".



"Bana tsoran kowa a board ,i told you zan miƙa resignation letter na,kar ka manta sunana
UMAIMAH USMAN BULAMA, diya guda ɗaya tilo a gurin attajirin Mai kuɗi nan,USMAN
BULAMA"Idan kaga na tab'o nice naso na tab'u,nasan zakace nayi taƙama ko?



"Ƙaramar dariya tayi tace wani lokacin sai da haka"

Na faɗa maka zan kawo maka wanda yayi editing wannan clip ,sannan Next time dear Mr
Director kar ka fara yanka huƙunci ba tare da ka san gaskiyar abin ba,



"Gaskiyar kuma gata nan gaba na,muna nan tare da Dr Jabir muna wasan chess and two men
down,

Ina fatan ka iya chess kuma kasan me ake kira da two men down,

So na zubar da biyu guda ɗayane nake ƙokarin saurare ka Katseni ta hanyar kira.



"Kallan Dr Jabir tayi tace "maza gaisa da Dr mr director sir sai ka sanar damu wannan Strong
opponent ɗin mu sai mu shirya Cos nasan kilan black horse ne ".



"Cikin sheƙewar muryar Dr Jabir yace Hello sir"



Murmushi ta kumayi tace Dr Director kaji Nephew ɗinka ko?



Na'am?

Yafaɗa ta ɗaya bangaren wayan.



Ƙaramar dariya tayi tace "aw Sorry na manta ashe ba baka san nasan Nephew ɗinka bane ba
Dr Jabir,"

Well a ranar da ka nema masa yafiya a gurina ranar nasan wanene shi a gurin ka,

Ina fatan ba kaine Black horse ɗin mu ba,?

"Well muna sauraranka Dr Jabir ,sweet uncle ɗinka ne Ya saka ka ko kuma wani mastermind
ɗin ne da yafi kawun ka zarra da yayi tsautsayin taka ɗiyar BULAMA?"

Duƙan desk ɗin dake tsakiya tayi cikin wani irin tsananin fushi dan taje maƙura.



"Jin yayi shiru ne yasata nuna sojan da yafi ko wannen su girma da murɗewa tace"

Mr hot soldier, daga gani a training ɗin da ka samu kana haɗawa da Gym ba,Cos you look build
i must say.



"Murmushi soldier ɗin yayi yace 'i work out twice a day".



"Tsaki paki yayi yace "And who asked you sau nawa kake working out ?"

Ba wannan Ya kawo ka nan ba.



"Ƙasa yayi da kansa cikin girmama Yace Sorry young master . "



"Dan karamun murmushi Hindu tayi lokacin da ta hango kishi karara a idanun Imam paki,"



"DR Bulama don't do anything you'll regret, "Muryan director ta wayar Ya karade store room ɗin,



Murmushi tayi tace "naso na manta kana speaker fa,"Well idan Nephew ɗinka Ya buɗe baki yayi
magana bazai samu ƙarin duka ba akan wanda yasha ,Amma idan Ya zab'i yayi shiru ni kaina
Ban san Mai sojojin nan da suka gino ba zasuyi masa ,

And bana tunanin akwai abunda zan dana sani,amma jabir kuwa yana kan yi.



Daga ɗayan bangaren Director yace "Jabir kayi magana mana wenene yasa ka" .



Fashewa da kuka yayi yace"na yarda ina mutukar kishin yarda Allah yayiwa Dr bulama ƙokari
da sanin kan Aiki,idanuna sun rufe har na kasa gane menene dai dai."



"Idan ina ganinta ji nake kamar na hadiye zuciya na mutu ,i Am a second best a asibitin nan and
i cant lose to a woman,i wanted to be the first best amma Dr bulama ta shiga mun gaba ta tsole
mun ido, "



"Da gaske lokacin da na nemi yafiyarta i mean it amma kwatsam tsohon mijinta HABIB ya kawo
mun offer ɗin kaita ƙasa And da haka ma Ya bani 3million sabida da fari naƙi amince wa ".



Dukkan wannan idea ɗin sa ne and tun ranar yabar Nigeria ,ji tayi baki ɗaya jikinta Ya hau
karkarwar bacin rai Cos bata taba sanin Habib zai mata abu har haka ba,Cos a tunanin ta ita
uwar dansa ce ko dan ɗansu baya Kai wannan limit ɗinba.



"Cin Kwalarsa Paki da Ya tako gurin jin Ya ambaci Habib yayi yace"idan kayi ƙarya ka yarda
dani zan cire girmanka na babbalaka na bawa kare kai.



"Cike da tsoro yace "wallahi tallahi ba ƙarya neke masa ba Ai akwai transaction ɗinsa da wayan
da mukai."



Yanzu yana ina"paki ya tambaya,"

Kafaɗa mana Jabir"director Ya faɗa".



Yana itally ,

Ya faɗa yana Mai fashewa da kuka.



Cikin wata irin sassanyar muryar broken heart tace "ko birnin sin yaje sai na kamasa na saka an
hukuntasa ".



Mikewa tayi ta fita a store room ɗin tana Mai ignoring kiranta da suke.



Da gudu paki ya bita da gudu,

Da ƙar ya kamo hannunta ,

Chak ta tsaya ,

A hankali ta juyo idanunta ciki da hawaye tana Kallan idanun paki wanda Ya Marairaice mata da
ido yace ,you cant drive a wannan yanayin sanann ina zaki.



Itally,

Ta bashi amsa tana Mai ƙokarin shanye kukanta Kafun tace "let go of me".



Saurin sakar mata hannu yayi kamar shocking Ya kamasa,

Tana ganin haka ta ruga motanta.

Ko takan Hindu dake ihun ta tsaya batayi ba tayi wani mugun reverse ta fita.





*

Mun tai itally kamo habibu



Chuchujay ✍

TBC.
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK
AURE UKU

(a hospital romance)

By

Chuchujay



Ga masu san a tallata musu hajarsu

09058191213.



Episode 1⃣4⃣

A yarda umaimah ta figi motarta Allah ne kawai Ya kaita gida,

A lokacin da ta tafi rasa abunyi paki yayi amma yana bukatar wanda zai hana umaimah zuwa
italy,



Kallan Hindu yayi yace"babu wanda zaki kira ki faɗa masa cos she cant go to italy, zan ji da

komai ."



"Ƙaramun murmushi tayi tace "do you love her that much"?



"Shafa kansa yayi yace "with My life".

"Murmushi tayi tace"tana da soft heart and im sure a zuciyarta kana da wani soft guri kawai ka
bata maganin attitudes ɗinta "

Ka fahimceni?



Murmushi yayi yace "zai gwada ."

Wayanta ta ciro ya kira Yaya Abubakar dan kaf gidan shine take da numbern sa shima ɗan
umaimah ta tab'a ƙiran sa a wayanta ne.



Ringing ɗaya Ya ɗauka,

Bata b'ata lokaci ba wajen sanar masa abunda Ya faru tiryan tiryan,

Godia yayi mata yace yanzu zai kira daddy sannan Umaimah baza taje italy' ba.



"Tana gama wayan Paki yace "bari na bita, Yana ƙorakin shiga motar sa tayi folding hannun ta
tace "dan saurayi idan ka tafi ni wanene xai maidani gida?"



Sosa kai yayi yace "im Sorry dan Allah,"KB Zan barka nan ina nan dawowa.

Shi da Hindu suka nufi gidan su umaimah .

A bakin gate ɗin tamfatsetsan gidan Paki yayi parking motar sa ,

Kallan sa hindu tayi tace bari na maka iso a maimakon Umaimah i know she wont mind.



A tare suka shiga ,kai tsaye part ɗin umaimah suka nufa ,dama ita ba gwanar kula maƙiyan
umaimah bace a gidan ,

Sannan bata damu da shiga ta main gidan ba ,kofar da zata sadata da sashenta kawai take
nufa.



Tsayawa Paki yayi a bakin kofa,

Juyowa tayi ta kallesa tace "yadai?"

Dan Sosa kai yayi yace "i think ba dai dai bane na shigar mata guri kai tsaye bata san da zuwa
na ba".



"Karamun murmushi Hindu tayi tace "kar ka damu You're not going to find her naked i promise".



Ƙasa yayi da kan sa cikin jin kunya,

Gaba tayi yana biye da ita a baya,

A cikin wani tamfatsetsan falo suka tsaya,

Babu alamun ta dan haka hindu tace 'bari na ƙarasa inda idan kaje you might actually find her
naked dan nasan yanzu haka tana chan tana shirin tafiya italy' cikin rashin sanin masu hanata
na hanya.



Zama yayi yana Mai Jin nauyin maganar Hindu wadda ya kula ita ko a jikin ta,

Yana wannan zaman Nameer Ya shigo duba da shi yanzu ba zuwa makaranta yake ba ,yana
shirin wucewa Abuja.

"Turus Nameer yayi lokacin da yaga Paki,"

Da murmushi Paki Ya kalle sa yace"Big boy ."



"Haɗe Nameer yayi yace"im not a boy,i Am a man Cos a sashen mu nine babba kuma protector
ɗin mami , "Mai kake yi anan.



Faɗaɗa murmushi Paki yayi cos fushin Nameer a gurin umaimah Ya kwaso shi,



Yana Mai kokarin magana muryar umaimah ta katsesa a yayin da take fitowa daga sashen da
Hindu tayi hannunta dauke da jaka tana faɗin"Hindu kima daina koƙarin tsayar dani 'fa,wallahi
Habib sai Ya kwashe kashin sa a hannu tunda dai shi bai gaji mutunci ba,"Wallahi sai yaga kalar
wulakanci na da bai tab'a gani ba.


'Mami Habib?

Mai yayi miki,

Mai Habib ɗin yayi miki.

Muryar Nameer ta ziyarce ta cikin wani irin fushi ba kamar na yaro ba.



"Turus tayi Kafun ta tako gareshi tace"Nameer yaushe kuka dawo kai da daddy"?



"Yanzun nan ya bata amsa Kafun Ya sake cewa "mami Mai Habib yayi miki".

Durƙusawa tayi dai dai tsayin sa tace "Nameer na faɗa maka ba sau ɗaya ba ka daina kiran sa
Habib He's your father for God sake. "



Ture hannunta da ta dafa kafaɗarsa yayi yace"mami he's not My father ,na faɗa miki ba sau
ɗaya ba shi ba daddy na bane ,i might be using his name amma mami we are not related."



"He lost that right mami a long time ago, ki faɗa mun abunda BASTARD ɗin nan yayi miki and i
swear i will kill him.



"Babu wanda yayi tsammanin Abinda Ya biyo baya,sosai umaimah ta ɗauke Nameer da mari
Mai zafi idanunta cike da kwalla tace "who taught you that"?



"Uban wanene Ya koya maka wannan?"You're calling your father a bastard har kana cewa
zaka kashe shi.



"Ni na koya maka wannan?"

Tana kokarin sake marin sa hindu tayi saurin shiga tana cewa 'a'a Bulama.



Sai a lokacinne ta kula da paki wanda ya janye Nameer daga gurin.



"Sake nuna Nameer tayi da yatsa tace "i raised you to be better than that,"ko mene ke tsakani
na da mahaifinka tsakanina da shi ne amma baka da right ɗin zagin sa har kana ikirarin zaka
kashe sa.



Kwace wa yayi daga hannun Paki Ya nufi hanyar da zata sadasa da inda ɗakinsa yake Kafun
yace "amma mami ina da right ɗin tsanar sa and you can not do anything about that, i hate him

and idan na girma na tsincin Ya miki abunda ban sani ba yanzu i will kill him,saboda you're My
World .



Da gudu ya shige,



Zaman ɗirshen tayi a kasa tana Mai cewa "shekarun sa sha ɗaya kawai fa,"He's just 11,and ina
Kallan tsanar mahaifin sa akan idanun sa,why me?



Mai yasa kaddarata zata zo da haka?

Yaro ƙarami amma a cikin kwayar idanun sa akwai kiyayya.



"Habib shine wanda ya fara ja mun komai saboda duk da ba dan 'ina san shi na aure sa ba
Atleast da yana da decent life i will get to adjust,amma yayi ruining komai ,sannan bai tsaya
anan ba After 11 years yake san b'ata mun rayuwa".



"Mene laifina Hindu?"

What's My fault?

"Yarda nameer yake yanzu Ya kike tunanin zai kasance idan nan gaba yaji labarin abun da yake
faruwa a yanzu?"



Nasan da ace daddy bai jama ƴan gidan nan kunne ba akan abunda suke yi ba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login