Showing 9001 words to 12000 words out of 68416 words

Chapter 4 - AURE UKU Part Compelet Book Writing by chuchu.pdf

14 Apr 2025

4736

Doctor Bulama's Cabin Nasan atleast ka
iya karatu zuwa nan,

Secondly we Are not that close beside ban san ka ba,ina so ka riƙe wannan Alaƙar ta
supervisor da dalibi itace tsakanina da kai dan naga alama kana san wuce gona da iri,kasan
limit ɗinka,

Thirdly ina san ka sani,i dont mix duk wani abu da Ya shafi Aikina da wani abun duk girmansa
so don't mistake what happened as My weakness

Now get out."



Gyara tsayuwar sa yayi yana Mai folding hannunsa a kirjinsa cikin blue kayan likitoci, a bangare
ɗaya kuma yana mata wani irin kallo Mai kashe jiki,



Coffee ɗin da ya kawo mata Ya aje kan table Ɗinta har lokacin idanun sa na kan idanunta Kafun
yace"cold coffee ne 'dan nasan ba lallai kin karya ba,a lokutan da kika ware na Aikin da za'ayi
kinci minti goma a waje ,komai yayi ready ke ake jira ,so take the coffee and ina san ki sani Ko
Auren ki goma a duniya da yara kimanin faɗin duniya akwai wanda hakan bai dame sa ba da

duk wani Abu da za'a faɗa akan ki.

Juyawa yayi Ya fita a cabin Ɗin.

Bin kofar tayi da kallo a yayin da taji cikin ta yayi wani ƙugin yunwa,

Daga cup Ɗin coffee ɗin tayi ta shanye Cos bata san shiga O'R ba tare da tasa komai a cikinta
ba,

Amma tabbas za suyi magana dole tasa gayen nan a inda ya dace dashi.



****

Kamar kullum yau ma bayan tayi sanitizing hannunta ta shiga operation room ɗin da hannunta a
ware tana tsoran kar wani infected abun Ya tab'a ,dukkan team ɗinta sun hallara tare da IT
student Ɗinta guda uku,

Bayan ta zama set ta koma kan mara lafiyan da batama san duniyar da take ciki ba tace "hour
nawa aikin nan zai dauka Dr Fatima?"

1 hours doctor "Dr fatima jnr ɗin umaimah ta faɗa professionally,"

Timer ɗin da akayi setting ta maida minti 40 wanda Ya bawa interns ɗinta mamaki karma ace
Paki,

Daga gefen su Aisha shareef tayi murmushi a hankali tace"i admired her naji ance she's the
most fastest doctor here".



Cike da kwarewa tace"zamu gama cikin 30 min And kamar yarda kowa yayi reading its not
just hematoma But subdural Hematoma And the patient have 2% chance so Ya 'dan ganta da
luck dinta But we would do our very best,

A hankali ta fara neman larger access to blood clot ɗin,wanda shine (craniotomy),

Inda ta cire section na ƙashin dake tare mata hanyar gudan jinin,

Bayan ta kammala,ta replacing section na ƙashin kafun ta rufe soft tissues ɗin ta hanyar amfani
da sutures .

Maida hankalinta tayi kansu Paki tace "warkewar mara lafiyan kuma zamu barwa Allah ne but
the operation is done and its a success ,And since nayi undergoing craniotomy warkewar zata
dauki lokaci ,so yanzu za akai patient ɗin recovery room Kafun a kaita ICU once situation ɗin is
stable she would be moved to the regular room har a sallameta,duk Mai tambaya Ya bini office,
so nayi highlighting ɗinsa "Alamu tayiwa sauran doctors da nurses ɗin kan su dauka daga inda
ta tsaya Kafun ta fita,

Idanun Paki ne Ya sauka kan timer wanda sai yanzu ma yayi clicking 50 min,

Faɗa yayi da bakinsa,

Murmushi Dr Fatima tayi tace "she's the most fastest doctor da zaku gani a asibitin nan ,idan
kuka maida hankali zaku karu da ita sosai.



Kallansa Kb yayi bayan sun fita yace mutumina zo muje mu zanta mana.

Babu musu Ya bishi duk da yana san zuwa gurin umaimah da excuse ɗin yana da tambaya,

Kallan KB yayi bayan sun zauna yace"Paki kasan dai ni da Kai mun wuce abokai sai dai yan
uwa ko?

Ni da kai tare muka girma mun damu da damuwar juna da duk wani abu da zai zamar mana
Mai kyau,

Kalli nan Paki sameera yarinyace Mai kirki duk da nasan wani lokacin tana da rawar kai amma
na yarda da san da take maka kuma zaka iya juyata duk yarda kake so amma mutumina kai
kanka kasan maganar Dr umaimah ba abune Mai iyuwa ba ,kai kasani Ko kowa Ya amince
Nana bazata taba yarda ba,
Kai babu ma wanda zai taba Amince maka da maganar ta kaima ka sani,

My guy Auren ta uku 'fa har da yara Uku,kasan maine Ya fito da ita daga gidan mijinta?

Baka taba Aure bafa tayaya kake san duniya ta fara ɗaukar maganar nan?

Bro ni nafi tunanin ma harda attitudes Ɗinta ya fito da ita gidan mazajen 'dan tana jin babanta
Attajirine ,i mean guy she's rude with words,

Na yarda rumours ɗin dake yawo akanta jitajita ne amma kasan gaskiyar ne?.

Dan Allah imam ka sake wani tunanin amma hanyar nan da ka ɗauko mana ba mai bullewa

bace kwata kwata ,

Ka rufa mana asiri kamar yada Allah Ya rufa mana ka ɗauke idanunka kan matar nan,idan kuma
bakaji ba ni da kaina zanje na sanarwa da Abbi Abunda ke faruwa in yaso Ko asibitine mu
chanza ,gwanda fa mu daki karfen nan da zafi.



Shiru Paki yayi yana kallan kb wanda shima da idanun Ya bisa yana san jin amsar Paki ,

Dafa shi Paki yayi yace "kar ka damu ".

Murmushi yayi masa shima Ya mayar masa kafin Ya tashi Ya nufi office ɗin Umaimah ,

Knocking yayi har sau biyu Kafun tace Ya shigo,

Shiga yayi bakinsa ɗauke da sallama,

Kallo ɗaya ta masa ta mayar da kanta kan abinda take,

Politely Ya kalli kujerar dake gefenta yace "zan iya zama Dr"?



Cire glasses ɗin idanunta tayi tace "zaka iya zama idan ka tabbata ba wani shirmen Ya kawo ka
ba,".

Zama yayi kan kujerar yace "Dr aikin ki na yau was amazing ,sai naji kin sake burgeni ta Ko
ina".

Wani banzan kallo ta bashi kafin tace"kana da wata tambayane regarding it?"

Gyara zaman sa yayi Yace "nazo ki duba ni ne Dr bani da lafia,"

Dafa kirjinsa yayi dai dai saitin zuciyarsa yace "nan gun ke mun wani irin bugu muddin idan na
saka idanuna akan mace ɗaya,"Baki daya tunani na tsayawa yake, ita ka dai nake gani,bana
ganin Ko wacce mace bayanta sannan abunda Ya wuce dangane da ita baya gaba na sannan
baya tunanina ita kaɗai ce ke ciki,


Aje pen ɗin dake hannunta tayi tace"

Well"kafi kowa sanin ni ba cardiologist bace sannan ni ba therapist bace da zan zauna sauraran
damuwarka, babu wani abu da Ya shafeni a ciki so please Imam Paki idan kana san cigaba da
Aiki a karkashina ina so ka sani Aiki shine abunda Ya dameni a cikin Asibitin nan,so please idan
babu wani abu da zaka faɗa mun da Ya shafi Aikin da Ya haɗa ni da kai zaka iya bani guri ina
Aikine.



Wani irin murmushi yayi yace"amma Dr bulama abunda yake damuna Ya shafeki,nasan zaki
ga magana ta kamar Shirme amma ina san ki sani wadda take hana mun wannan walwalar
Sunanta DR UMAIMAH BULAMA, a kwana biyun da nayi da saninki soyayyarki ta shigeni
wadda itace ake kira da Love at first sight .
Ina Sanki,sannan zuciyata tace na sanar miki 'dan da zafi zafi ake dukan karfe sannan a bari Ya
huce shine yake kawo rabon wani.



Cikin kwanakin tasan Paki na da ido akanta wanda take ɗauka kamar admiration ne amma
batayi tunanin izzarsa ta kai har Ya shigo cikin office ɗinta ba yace wai yana santa.

Yar karamar dariya tayi tace"shekararka nawa?"



Murmushin nan nasa da yasan yana ɗaukar hankali yan mata yayi yace"shekarata ashirin da
tara amma a cikin shekarar tawa za'a ɗauke wata ɗaya wanda na baki,ma'ana na girmeki da
shekara ɗaya tunda nasan Kema shekarun ki kenan,"

Sannan nasan kin yi Aure har sau uku sannan a kowanne Aure kina rabo,

Ma'ana kinyiwa ƴaƴana yayyi, mene yafi wannan daɗi?

Tun kafin na haihu yarana na da manyan su,sannan ina san ki sani idan na Aureki insha Allahu
in dai ta gurinane bazan taba sakin ki ba da yardar Allah,ni na yarda a kaddarar Aurenki nawa
ne na har Abada ,ki rufeni Ko na rufeki wanda jikina yana bani sai munga jikokin mu.



She was speechless ,lallai fukafukansa sunyi girman da tashi Ya rage musu,ba ƙaramun
tafarfasa ta tsinci ranta yanayi ba ,lallai Paki bai ga bangarenta mara kyau ba sannan Ya rainata
irin rainin da babu wanda Ya taba mata,zatayi magana taji wayarta na ƙara,

Director ne ke kiran ta ,ɗagawa tayi bakinta da salllama kafin tace "Yes sir im coming in a jiffy".

Kashe wayan tayi ta tashi ta kalli Paki ta Nunasa da wayarta tace "maganar nan bata ƙare ba,i
will look for you".



Ta kai bakin kofa zata fita ta tsinci muyarsa yana Mai faɗin"shekara guda babu kwana biyu,"

A cikin shekara guda da zanyi a asibitin nan sai na sa miki soyayyata ,idan kuma a shekarar
baki fara sona ba koda kaɗan ne nayi Alƙawari zan bar field din nan na har Abada ,zan chanza
career ta nayi Alƙwari.



Cije lebenta tayi na Ƙasa tasa kai ta fice a yayin da yayi wani murmushi yana Mai jin santa ta
Ko ina,

Yayi shirin da bazai ja da baya ba....





*************

Da salllama ta shiga office din ,batayi mamakin ganin Dr Jabir ba 'dan tafi tunanin abunda Ya
haɗasu dazune yaje kunnensa,



Zama tayi tana mai cewa"good day sir"

Murmushi dattijon yayi yace Dr Bulama .

Bayan Sun gama gaisawane yace "Dr bulama nasan ke likitace wadda tasan Mai takeyi na
yarda dake da aikinki,"Duk da yarda kika yi appearing tough nasan deep zuciyarki akwai soft
guri ,

Nan ga Dr Jabir akan abunda Ya faru dazun ,nasan kina da dukkan right ɗin da zakiyi suing
dinsa amma Yazo takanas ya Sameni akan na kiraki na baki hakuri ,kinsan shi harshe..

Kallan Dr jabir tayi wanda yayi narai narai ido Tace "director ,ni kawai inasan Ya faɗa mun lokaci
da yataba ganina ina rabawa mata jikina,director he's accusing me of something big 'fa,
lesbianism 'fa,"

Yes kuɗin babana baisa na zauna gidan miji ba sannan nayi Aure sau uku na haihu sau uku
bafa wai shine yake nufin Allah baya sona ba ko kaddarata bata da kyau,

Amma 'dan me wani mutum ɗan Adam zai judging ɗina?

Ina sane da duk ƙazafin da ake mun a cikin asibitin nan a,im arrogant ,rude,im here because of
My father,we Are money ritualist,i Am a lesbian duk inaji 'fa jira kawai nake na samu mai
fuskantata wanda yau na samu sannan a shirye nake na nuna masa karfin dukiyar da muke da
ita,
Im sick and tired sir,nazo gurin nan from scratch ,babu wanda yasan ta yaya na kawo nan gurin,

Im here with My blood ,sweat and tears,ina matsayinane saboda dagewa,

I wanted it from the start saboda yarda na rasa mahafiyata wa brain tumor And nayi Alƙawarin
cetan mutane da dama,

Ba fa wai ni na bawa kaina talent ba Allah ne,

Ba ni nace Allah Ya bani fast hannu ba shi Ya bani 'dan yasan zai amfani al'umma so Mai yasa
DR jabir keda damuwa da hakan 'dan nafi tunanin diss ne,

Dafe fuskarta tayi tana Mai danne hawayen dake san zubo mata.



Baki daya jikinsu yayi sanyi karma ace Dr Jabir,ture kujerar da yake zaune yayi Ya tsugunna
kasa yana Mai faɗin"Dr bulama i was wrong na yarda har da baƙin cikin ma ,'dan Allah ki yafe
mun".



Kallansa tayi Kafun ta tashi tace "Forget about it "Kafun ta fita a office din.

CHUCHUJAY✍

To be continued .
[11/25, 12:19 AM] CHUCHUJAY✍️: AURE UKU

(a hospital romance)

by

Chuchujay

Episode 6⃣.

Wai ni kam imamu yaushe zaka kawo mana mata ne gidan nan ,mun gaji da wannan gafara
san banga ƙaho ba ,gaka dai geme geme kana shirin bawa talatin duka amma kamar an maka
ƙwari Ko budurwar Arziƙi baka da ita,

Muntari ?

Ko ni ƙadai abun yake damu ne ,ga dai nan usama matarsa ciki na biyu ne da ita,nan ga
inteesar cikin fari gare ta ,kanwar ka ma kenan ,idan kuma ba so yake na mutu banga jininka ba
,ko kuwa baka da lafiyar mazantaka ne.



"Tari Paki Ya fara saboda kwarewar da yayi,ummu(mahaifiyarsa)ce ta miƙa masa ruwan da ta
zuba zata sha tana Mai shafa masa baya".



Tsaki Nana tayi tace "karyar soyayya kike nuna masa Habiba,idan da soyayya ki sa shi yayi
Aure itace karshen kauna idan kuma ba maganar da na faɗa ta rashin lafiyar mazantakan bace
Ko kuma leƙeleƙe.



Affan ne Ya aje spoon ɗinsa Ya tashi a gun yana mai jin takaicin Nana"Ai kamar jira take ta
koma kansa tana cewa" yo kaji mun shegen yaro,dan inawa Yayanka faɗa shine abun yayi
maka ciwo?"To dake ni,

Kaima ai yaci ace ka fara maganar Aure shekara ashirin da ɗaya kaida wannan Mai ido a loƙon"

Haɗe rai Afnan tayi tace"nifa nana tunda nazo gurin nan ban miki magana ba,ke shikenan baki
san a zauna lapia daga wannan sai wannnan".



Wani salati Nana ta rafta ta kalli mahaifinnasu tace muntari kana ji Ko?

Dama ai ance yarinya idan ta balaga ta fara nono da jini shikenan sai tana ganin dai dai take da
kowa ,

Yanzu 'dan Allah muntari sabida tsabar ta'ada ta kafurai da kuka daura ma kanku Shine ke
hanaku killace ƴaƴanku ,to wallahi muddin ni na haifeka kuma na isa da gidan nan da mutanen
dake cikinsa to dole a aurar da yaran nan uku ,sun isheni ,ga rashin ɗa'a ga rashin kunya da
rashin girmama na gaba dasu wanda suka koya gun uwarsu,


Fuu Affan Ya bar gurin a yayin da Afnan tace "Ai sai kizo ki mun Auren tunda akan ki nake
zaune a Gidan nan ,in dai fitina ne kin iyata saƙo saƙo, kece ba ga Ummu ba baga mu ba
,mene muka tsare miki ne ?

Kuma ai Abbi kika haifa ba mu ba,



Tsawar da mahaifinta ya daka mata yayi dai dai da kukan da Nana tasa tana Mai faɗin"Ai
shikenan muntari tsakanina da ƴaƴanka kuma sai duka ,kwana kaɗan Ya rage su fara mun duka
,dama waccan figaggen yaran Apan Mai zubin jijiya yafi kowa haye mun sai kuma ita Apinan ɗin
'dan idan ban ƙaryaba har bangazata ta kusa yi jiya"


Duk da sanin halinta da Abbi yayi bai hanasa cewa da Afnan ta bata haƙuri ba,sanin mahaifin
nasu baya wasa da abunda Ya shafi nana yasa tace"kiyi haƙuri Nana ,sannan Ai Allah yana
kallon,mu kuma shaidane ban bangaje ki ba kikace na kusa bangaje ki amma kije na yafe miki
ladan haihuwar Abbi da kikayi,sannan ni ba sunana Apinan ba ,ba kuma sunan Affan Apan ba
idan baki iya ba kice Hassan da usaina tunda su nasan bazai maki wahala ba".



Kafun taji wata masifar ta Nana ta bar dining Area ɗin ,

Kallanta ta mayar kan Imam tana Mai binsa da idanu a yayin da ya maida hankalinsa yana Mai
cin Abincinsa cikin nutsuwa,

Cike da fitina tace "tuzuru ba magana ne,"

Still bai Kulata ba Ya ɗauki cup d'in chapman ɗin da ummu ta zuba masa Ya shanye yayi
hamdala,

Kafun Ya kalli mahaifiyarsa yace "ummu gaskiya sai an tara mata dubu tukunna za'a samu
mace mai irin girkinki,gaskiya Abbi Ya iya zabe ,kalar hannunki kalar abincinki".



Ai kamar Nana na jira tace"inji ubanka,ina dadi a abincinnan duk an cika kafu zabo duk da
ansan likita ya hanani ci dole sai an kasheni kuma wallahi nan gani nan bari kabewar kan
kabari,a hakan kuma zaka ƙare Kana santin abincin uwarka bana matarka ba,"Ai kuma ka shiga
uku dani yanzu tunda Auranka Ya zungureni sai anyi zaka samu sauƙina.


Tashi imam yayi yace Ummu ,Abbi sai da safenku,Nana ke kuma zan kawo maki wani magani
Uku,safe ,uku rana, uku dare.



Har ya kai hanyar da zata sadashi da bangarensa yanajin ƙananun kuka da masifar Nana wai
Ya kirata tab'abbiya ,dole yasa ummu tashi sabida ruwan diban Albarkar da Nana ke mata wai
ta haifa masu yara irin yaren ta marasa kunya kafurai.



Mahaifin Imam Alhaji Muktar Paki mutum Paki ne dake cikin kaduna ,ta wani bangaren kuma
mutanen Adamawa,a Adamawa Ya tashi 'dan nan Ya tarar da iyayen sa amma hakan bai hana
sunansu na PAKI tasiri ba,su Biyar iyayensu suka haifa maza huɗu mace ɗaya inda maza biyu
suka rasu Ya rage saura su uku,
Sai Ya zamana shine babban gidan.

Naval Officer ne wanda yake da matsayin admiral ,

A wani Zuwa da yayi America birnin New york Ya hadu da Habiba wadda take half Nigerian Half

NewYorker ,mahaifinta ne ɗan nigeria mahaifiyarta kuma yar newyork,'dan Haka yaren hausa a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login