Showing 45001 words to 48000 words out of 62027 words

Chapter 16 - MAI SONA COMPLETE Book Writing By Reefat Yahya .pdf

16 May 2025

3554

yawa ga kyau da
tsada. Ruhaimat ma akwati set1 baba ya cika mata da kayan arxiki yace na fitan biki, shirye2*
sukayi Yau saura kwana 4 a fara programs gidan ya cika makil da dangin baba da na mami sai
kuma abokan arxiki.duk inda Ruhaimat ta gifta sai kallonta akeyi Shiyasa bata rabuwa da
hijabinta, sadeeq ya sauko jirgi tare da sadiya tana tura katon ckinta na 6monts.se raba ido take
don bata taba xuwan ABJ bah..driver ne ya daukesu xuwa gida, a nan ta San lallai mahaifin
sadeeq ba karamin attajiri bane gidan ya hadu sosai fiye da yanda take tsammani.hannayensu
sarke da na juna suka karasa ckn gidan ana ta musu barka da xuwa falon mami suka shiga
jama'a ne a cike makil kai tsaye bedroom nata suka wuce tare da sallama.. Ruhaimat ce ke
xuba shagwaba wai ita baxata ci abinci bah, mami na faman lallabata tana bata a baki..turuss
sadiya ta ja ta tsaya ckn mamaki tace "Ruhaimat!"

*Reefat ce*
[11:00AM, 13/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*58*
BY *Reefat yahya*

~a short n imaginary Lov story~

Ruhaimat ta juya ckn halin rashin kulawa tace "naam ya kike" daga nan ta haura saman gadon
mami tayi kwanciyar ta mami tace "Dota kin gaji koh..kwanta ki huta kiyi bacci zuwa anjuma sai
Ku shirya xuwan Fulani day koh" ta kwantar da kanta bisa cinyar mami tana mai lumshe ido
sadeeq Wanda ya shagala da kallonta gani yake tamkar ba Ruhaimat dinsa bah don tsabar
kyau da tayi a sannan ne suka xauna ckn girmamawa suka gaisa da mami, ta amsa ckn fara'a
da sakin fuska har tana tambayar sadiya ya take fama da nauyi ta amsa cike da jin kunya.waya
mami tayi aka kawo musu abinci da snacks da drinks kala2* a hnkli ta kwantar da kan Ruhaimat
bisa gado don ta fara bacci daga nan mami ta fice ta bar musu dakin.sadiya ta kasa boye

mamakinta na ganin Ruhaimat ta juya gun sadeeq "mai sona..dama Ruhaimat er uwarku ce?"
murmushi yayi baice komai bah yana cin abincinsa sai faman lumshe ido yake yana kallon
kyakkyawar fuskar Ruhaimat yana jin wani farin ciki Mara misaltuwa, bayan sun kammala cin
abincin yace ta tashi su tafi can bangaren sa suka nufa nan ma sun tarar da amarya tare da
kawayenta domin an sauke baki a can dakin meenah. Kawayen meenah sai yaba kyaun
sadeeq suke shi kuwa ko sannu babu Wanda ya tanka wa yayi shigewarsa daki sadiya na biye
dashi a baya.."ke xaki xauna a nan ni xan tafi can gidan da ake sauke maza don gskiya baxan
iya xama ckn gayyan mata bah kingane ai" ta shagwabe fuska "haba mai sona kasan fah babu
Wanda na Sani don Allah mu tafi tare , kana ganin nan babu mai kula wani yaushe xan sake
dasu" idanunsa ya juya ckn yanga yace "no...baxaki tafi dani bah don masaukin na maza ne
xalla" ta hada rai ta xauna bisa gado murmushi yayi yace "ok xanyi magana da Ruhaimat xata
kula dake ok..sorry yi xamanki a nan duk abunda kike bukata ki nemeta ok" "me dangartakarku
da ita" "just do wat I asked bana son gardama" "shikenan naji" nan ya juya xai fita tayi saurin
cewa "ina amaryar ka take batazo mun gaisa bah , ina son ganinta" wani lallausan murmushi
yayi tare da cewa "jama'a sunyi yawa ki bari idan an gama biki sai ki nemi ganinta" "ok takkia"
yasa kai ya fice yana tunanin dramar da xasuyi idan sadiya taji labarin cewa Ruhaimat ce
amaryar tasa.
Da yamma sun caba ado ckn kayan Fulani ba karamin kyau suka yi bah musamman meenah
da Ruhaimat sun fita daban ckn sauran matayen da suke wajen, sun gama shiryawa ana jiran
motocin da xasu xo daukar su xuwa *silver bird* a can zaayi program din.imran ne tare da
Ibrahim da sadeeq da kuma sauran abokansu suna tsaye a harabar gidan suna dan
tattaunawa, sanye suke da fararen kaya sunyi kyau sosai maigadi ne yaxo wucewa rike da
akwati Ameena na biye dashi a baya dai2* nan Ruhaimat ta fito daga ckn gida ckn shigar Fulani
da gudu ta fada jikin Ameena suka kankame juna sai murna suke, gaba daya ta dauke
hankulan abokan angon imran yayi saurin kauda kansa gefe Ibrahim ko ya sunkuyar da kai
yana kallon kasa.wani kishine ya turnuke xuciyar sadeeq idanunsa a rufe yayi fuu..ya wuce inda
suke , fisgota yayi yana rike da hannunta sai kallonsu ake can bQ ya wuce da ita falon ba kowa
nan ya jefata bisa kujera yana sauke numfashi sai faman haki yake idanunsa sun kada sunyi ja
"ya isheki haka kina jina...wai meke damunki ne? Da auren naki xaki yi wannan Dan iskan shiga
baki da hankali ne?" Harara ta galla masa tare da cewa "me laifina? Ni banyi banxan dressing
bah da har xaka wani.." Bata karasa ba taji saukan mari Tass a kumatu ya nunata da yatsa "ki
nutsu kisan abunda kike yi don naga kanki na rawa kamar akwalar keke, bana daukan wargi
kuma so ba hauka bane" yana kawo nan ya juya ya fice , nan ta fashe da kuka tayi rub da ciki
bisa kujera ta fara rera kuka babu mai rarrashinta.sadeeq kuwa yana fita ya wuce gun motarsa
ya shiga ya figeta ya bar gidan, a can kasan layinsu yaje yayi parking ya hada kai da siteri kuka
yake kamar wani karamin yaro yana jin haushin kansa akan Marin da ya mata. A can ckn gida
kuwa sai Neman Ruhaimat ake sama da kasa babu labarinta, Ameena taja bakinta tayi shiru
tunda tare suke da mijinta kila shi ya hanata xuwa.haka aka shirya xuwa wajen program ba da
son raayin meenah bah, Ruhaimat tana can kwance ckn bacin rai taki fita a yayinda sadeeq ke
xaune ckn motarsa sadiya ko bacci take harda minshari program din da basu halarta ba
kenan.bayan Magrib Ruhaimat ta koma ckn gida dakin mami ta shiga ta babu kowa a ciki don
haka ta shiga bayi tayi alwala ta fito tayi salla , tana nan xaune har aka kira isha ta gabatar
sannan ta fada gado ta kudundune ckn bargo nan da nan jikinta ya dau xafi haka ta cigaba da

kukan ta.
9pm sadeeq ya shigo bangaren mami yana son sanin halin da take ciki, a hnkli ya murda kofar
dakin tare da sallama sheshekar kukanta yaji da rawar jiki ya karasa kusa da ita.jikinta xafi rau
nan ya jawota ya rungumeta ta cigaba da kuka gaba daya hankalinsa ya tashi "am so sorry
pretty ki yafemin pls "
*Reefat ce*
[11:07AM, 13/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*59*
BY *Reefat yahya*

*an imaginary Lov story*


Kuka take babu kakkautawa dama Ruhaimat akwai shagwaba *goyon kaka* ce( na sisy nah
umma yahya) habarsa na bisa kanta yana bubbuga mata baya a hnkli ta sagaita kukan sai
ajiyar xuciya take daga bisani yasa hannu ya daga kanta yana share mata hawaye idanunta sun
kumbura ta bashi tausayi sosai yace "pretty I din min to hurt u wllhi ina matukar kishin ki pls am
very sorry " bata yi masa magana ba ta xare jikinta daga nasa ta koma ta kwanta, dai2* mami ta
tura kofa ta shigo tare da sallama tana ganin Ruhaimat tayi saurin karasawa "dota Nah are u
ok" nan ta yaye bargon jiknta xafi kamar garwashin wuta nan mami ta daga kanta tana kallon
sadeeq yayi saurin sunkuyar da kai ta hada rai tace "burinka ya cika ka hanata xuwa ka sata
kuka ynxu gashi LA haddasa mata xaxxabi me kuma ya ajiyeka a nan" ya marairaice kamar
xaiyi kuka "mami kiyi hakuri wllhi ba.." "Get out now..bana son na kara ganinka kusa da ita"
hawayene ya cika masa ido haka ya tashi ya fice daga gidan gaba daya ko ta kan sadiya baibi
bah.tea mami ta hada mata dakyar tasha tare da hadiye magani sannan ta koma ta kwanta aka
rufa mata bargo, jama'a na ta shiga suna mata sannu ..hmm Ruhaimat dai *'yar gatace* ( na
daso Lov..miemie b).
Da safe ta wartsake sosai ana ta tambayar ta ya jiki tana amsa wa daga nan bangarensu ta
wuce dakinta ta shiga meenah ce tare da Ameena suna ganinta suka fara mata shakiyanci
Ameena tace "oh..daga shigan bQ sai muka ji shiru" duka ta kai mata ckn wasa meenah tace
"ni nabi na daga hankali na ina faman nemanta bansan cewa suna can suna ta lovin" "ehh..din"
dariya suke nan Ruhaimat ta fada wanka bayan ta fito tana shirya wa meenah tace "ke namanta
ban gaya miki bah jiya kishiyarki taxo nemanki" "mtsww..bani da lokacinsu" "ke inaga fa bata
San kece amaryar tata bah" "umm...I tink so don gskiya na Santa da kishin hauka da baxata
sauraramin bah" haka dai suka cigaba da tattaunawar su.har yamma sadeeq bai shigo gidan
bah wai a dole fushi yake sadiya kuwa tana samun kulawa gun mami don haka bata kara
Neman Ruhaimat bah, itama ko ta kanta bata bi bah sai harkokinta take dangin mijin na rawar
kafa a kanta sai yabonta suke.sun gama shirinsu ckn lace milk color n purple su 6ne kawayen
amarya ciki kuwa har da Ruhaimat ba karamin kyau sukayi bah sun wuce wajen da xa'ayi
*kamu* amarya tayi kyau sosai Ruhaimat ce chief best.motocin nasu a jere suke tafiya ga wani
cool music na tashi, nida kishiyata manshart muna xaune ckn wata Benz mai kyawun
gaske..manshart ta hango wata Ferrari tace "kai Reefat dama wancan arniyar motar muka

shiga" nace "ke..wancan motar amarya da chief best ne fah, don ma kin samu kin shiga wannan
Benz din..I knw dis ur first tym don mijin mu motar 1980model yake hawa"��lol..taro
yayi taro wuri ya kacame da kida jama'a da dama suka halarci taron sadeeq yana can xaune da
sadee ya kurawa Ruhaimat ido duk inda tabi idanunsa na kanta, imran ko yaki haduwa da ita
sai dodging yake sadiya kam mamaki ne karara a fuskar ta sai kallon Ruhaimat take tamkar
wata sabuwar halitta tana son sanin dangantakar dake tsakaninta da mutanen gidan don ganin
yadda ake rawar jiki akanta har mamaki abun yake bata.a haka aka gama taro lfy kowa ya tashi
ya kama gabansa a nan muka hadu da miss xoxo tare da *naufal* nata sunyi kyau sosai
motarsu muka shiga nida manshart da xhany bukar da billy Ibrahim ( wai itama taxo auren
takwaran baban ta..wannan kwakwaf din har ina) muna fitowa na hango asy khaleel da
rabia SK tare da ummu jafar�� chabb..son jin gulma kenan hmmm.washe gari aka
hada walima a ckn gidan nasu akayi decoration yayi kyau sosai amarya tayi kyau masha Allah,
ranar Saturday 10am aka daura auren Ibrahim tare da masoyiyarsa meenah daga suka shiga
flight xuwa yola a nan xa'ayi fansa.da yamma misalin 4:30pm akayi fansar ido daga nan aka
wuce da amarya xuwa gidan mijinta.


*Reefat ce*
[3:02PM, 15/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*60*
BY *Reefat yahya*

*an imaginary Lov story*

_godiya mai dumbin yawa masoyana Lov u all_❤❤❤

An gama biki lfy yan uwan Ruhaimat ma sun halarci fansa , bayan an watse ta koma gidan
baba dake yola a daga ita sai masu aiki tayi kewar mami da meenah ba kadan bah.an bude
skul da sati 2 don haka ta shirya ta koma kunsan final year tinx is not easy��...sadeeq ko
yana can yana dawainiya da sonta a ckn zuciyarsa har Yau bai gayawa sadee cewa Ruhaimat
ce kishiyar ta bah.
Xaune take bisa lallausan kujerun falon nata ga uwar tumbi da ta tura a gaba tana cin pizza
dayan hannunta rike da wayarta tana dialling din wata num na leka naga an rubuta "besti
Fa'iza" ta kara a kunne "hello besti Lov ya kke..lfy ina fama ya shirin komawa skul , ehh..wllhi
last 2weeks na dawo ai.kadai bari kawata Abuja ya hadu..ke kinga gidan baban sadeeq hmmm
gskiya suna da naira ..ehh..hmm ai na gaya miki a can na hadu da Ruhaimat kinga kyaun da
tayi wllhi baxaki ganeta bah, ehh..ah haba ..hmm wllhi yaki ya gayamin "... Oho can ta matse
musu ni ina ruwana tunda nasan bai damu da ita ba ai shikenan, kadai bari gskiya aikin malam
yayi dole na kara masa kudi "..ehh jibi xan tura miki kudin sai ki kai masa don ni gobe xan wuce
skul"..toh shikenan nagode"..lahh ina xai Sani, ai har Yau naki fada masa gskiya ..ehh ya dauka
nice Ruhaimat dinsa"..hmm bar wawa mana,ai ce masa nayi asalin sunana sadiya Amma ana
kirana Ruhaimat"..hhhh ni din wasa neh, hmm ynxu hnklina ya kwanta ai tunda shaidaniyar tayi
aure"..haba tun yaushe mun raba gari da ita, ai ni ban taba ganin wawiya irinta bah a duniya.. In

banda hauka da wautanci ya xaayi mutum ya sadaukar da soyayyarsa"..ehh mana ita ta
hadamu ..hmm Ruhaimat kenan ni tausayi take bani don nasan har abada baxata daina son
sadeeq bah, ..ehh hmm toh shikenan ki gaishemin da swt hrt dina kice masa I miss him yayi
sauri ya koma don nikam gobe ina hanya ..yawwa sai kin ji ni bye" ta kashe wayar tana
murmushi, sadeeq dake tsaye a bakin kofa yayi saurin komawa da baya dama xai shigo falon
kenan jin ta ambaci sunan Ruhaimat ne yasa ya dakata da shiga.ckn mota ya xauna yama rasa
gane halin da yake ciki "alhmdllh" kadai yake furtawa "I just can't bliv dis.. Ruhaimat itace
maini? For all dis while meyasa bai gane hakan bah? Ya Allah nagode maka da ka dawor min
da farin ckin rayuwata a lokacin da nake bukata.. Allah nagode maka, oh my Ruhaimat I can't
wait to c u" kyakkyawar fuskarta ya fara gani ya hangota ranar kamu last din haduwarsu kenan ,
lumshe ido yayi yana ta murmushi ji yake tamkar ya xama tsuntsu yaje ya sameta..toh skul take
ko ABJ? Yes..meenah xai kira ita xata sanar dashi komai.ya tuna ranar da akayi ruwan sama ta
taimaka masa, da kuma zoben hannunta da tace masa zoben Nada matukar muhimmanci a
rayuwartA.sai kuma ranar da take fadawa Ibrahim an mata miji inda take cewa shikenan an
rabani da mai sona" tabbas Ruhaimat itace asalin wacce yake nema ba sadiya bah.Amma waye
kuma sadiya take kira da swt hrt? Kodai saurayin da ya gansu tare ne? ba komai a sannu
zai bincika.haka sadeeq ya kasance ckn farin ciki da walwala bayan ya kira meenah ta gaya
masa Ruhaimat ta koma tana skul , murna yake yi har sadiya ta fuskanci halin da yake ciki ta
tambayesa yace mata riba suka samu company Shiyasa yake wannan murna. Da yamma ya
dauketa ya kaita shopping ya kashe mata kudi sosai sannan suka koma gida, baiyi bacci ba a
wannan daren ya kwana yana nafilfilu har asuba ya kwanta.misalin 9am suka gama shirinsu
daga nan suka dau hanya ckn motar sadeeq shiyake tuki sadee na xaune a gefe, karfe 1 suka
shiga mubi garin gwamna ( Amana state) gida suka wuce bayan sunyi salla sun huta sadeeq ya
fada wanka yayi kyau sosai kamar vijay singhania�� ya fito kenan sadiya ta bude baki tana
kallonsa "mai sona wannan wanka kuma fah ina xaka?" "Wani friend dina mun Dade bamu
hadu bah wurinsa zani" "shine kayi kwalliya haka ga kuma qamshin turare mai rikitarwa"
murmushi yayi sannan ya sumbaceta a goshi daga nan ya juya xai fita tayi saurin cewa" tunda
mukayi aure ban taba ganinka ckn farin ciki da walwala irin Yau bah y?" Murmushi yayi daga
nan yayi ficewarsa.
Kai tsaye adsu ( adamw st uni) ya nufa duk inda ya wuce sai an kurawa motar ido ga tint
glass baki wuluk bai tsaya ko ina ba sai bakin girls hostel( ba fa gidan anty sis bah...lols)
ya gyara parking ya fito �� yan matan dake wajen saura kiris su sume daga inda suke..chaii
guy din ya hadu���.."hello sis taimako nake so pls" cutee da hamee ne tsaye sun kura
masa ido, hamee tayi saurin cewa "ba damuwa fadi bukatar ka" ta bashi amsa tana wani fari da
ido.."pls ki shiga room 4 a nan Aisha hall kice ana Neman Ruhaimat mami ce ta tura mata
sako" nan suka wuce ckn hostel din. _15 mints leta_...ta fito sanye da hijabi batayi aune bah
kawai taga mutum ya rungumeta, ckn tsananin tsoro ta daga kanta idanunta suka fada ckn na
sadeeq wani lallausan murmushi ya sakar mata tare da cewa "I Lov u Mera Dil..n I rily miss u
maini" ido ta kura masa tana ganinsa kamar a mafarki "maini meyasa kika min haka..meyasa
xaki sadaukar da soyayya ta y??" Sai ynxu ta tuna cewa ana kallonsu nan ta raba jikinta da
nasa, murmushi yake daga nan ya rike hannunta suka wuce ckn motarsa bayan ya bude musu
gidan baya suka xauna.duk abunda yake faruwa kan idon wata aMiniyar sadee ne don haka ta
xare waya tana Neman Layin sadee��

*Reefat ce*
[3:14PM, 15/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*61*
BY *Reefat yahya*

A ckn mota ya jawota ya kankameta a jikinsa tamkar wani zai kwace masa ita hawaye ne ke
fitowa daga ckn idanunta harshensa yasa yana lashewa ya dan sassauta rungumar
suna mai fuskantar juna ya hada goshinsa da nata hancinsu na gogan juna yace "meyasa kika
min haka my Dil..am not happy serious" a hnkli tace "am sorry kismat bada son raina na aikata
hakan bah" daga nan ta kwashe labarin komai ta xayyana masa, murmushi yayi tare da Jan
kumatunta yace "u'l Neva change maini..kina nan da halayen nan naki" idanunta ta rufe tana
murmushi ya cire fuskarsa bisa nata sannan ya daga habarta yana kare mata kallo.idanunta a
rufe ya kura mata ido yace "daz my ril Ruhaimat wancan jabun ce..u r so cute my Dil" hannu
tasa ta rufe fuska ckn jin kunya tace "tnk u kismat" murmushi ya bayyana a fuskar tasa ya
cigaba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login