Showing 57001 words to 60000 words out of 62027 words
Chapter 20 - MAI SONA COMPLETE Book Writing By Reefat Yahya .pdf
*MAI SONA*
*71*
BY *Reefat yahya*
~an imaginary Lov story~
❤❤❤ _Reefat tana sonku_
Sun shigo falon tare da sallama, imran ya fito zai wuce masallaci kenan ya daga kansa suka
hada ido da Ruhaimat yayi saurin dauke kai yace "mami barka da xuwa Ku karasa suna ciki"
yayi wucewarsa Ruhaimat de tana mamakin sauyin da yayi bahaka ta sanshi bah..Momi tayi
farin ckn ganinsu a nan sukayi magrib sannan suka koma falo suna hira yasmeen ta shigo tare
da sallama tana cewa "wash..Momi na gaji wllhi nayi rawa Yau ba kadan bah" tsaki Momi ta ja
tare da cewa " Allah ya shirya.. Ki jira mijin naki don ya shigo yana tambayar ki, dama karya
kika min da kika ce shiya baki izinin xuwa gidan bikin" dariya tayi sai ynxu ta kula da su mami
tace "lah..Momi baki mukayi" "Mara kunya..wannan mahaifiyar sadeeq ce tare da matarsa"
murmushi tayi "ina yinin Ku" mami ta amsa ckn sakin fuska , Ruhaimat ta juya kenan suka hada
ido yasmeen ta bude baki cke da mamaki tace "ahh..wannan ce matar sadeeq?, amma ai ba ita
bace wacce na Sani" "amaryar sa kenan sunanta Ruhaimat" tabbas yasmeen tasha ganin
hotunan Ruhaimat ckn wayar imran kuma ta San cewa imran yana matukar kaunar Ruhaimat..
Amma mamakinta shine yanda ta canza ta kara kyau ga kuma dressing nata mai daukar hnkli
..sabanin da ta Santa da hijabi tana mata kallon bagidajiya, da wannan tunanin ta wuce dakin
Momi "hajiya mami kina ganinta ai..haka nake fama kullum gani nan sai raba fada, wllhi nagaji
abun nasu baya karewa" mami tace "meya kawota nan gidan bayan ga gidan mijinta" "wllhi bata
da hankali ko kadan iyayenta sun sangartata..ni tausayin imran nake ji hakuri kawai yake ya
xuba mata ido" "gskiya kiyi kokari ki wayar mata da kai don na lura tNa ckn duhu batasan ya
ake rayuwar aure bah..kina cutar da danki a banxa ga mata nan birjik meyasa kuka xaba masa
wannan fisararriyar" "uhmm kedai bari kawai..xanyi bakin kokarina" "Allah yasa mu dace" wayar
Ruhaimat ya sake vibrating a karo na 5 murmushi mami tayi tace " chewing gum naki
koh..nasan yana can yana jira tashi mu tafi" Momi tayi jugum tana kallon Ruhaimat.. Allah sarki
imran da Ibrahim sunyi rashin mace ta gari .."toh Momi imran mun tafi" "nagode kawata Allah ya
bar xumunci..dota nagode koh" daki ta wuce ta fito dauke da wata bakar Leda ta mikawa
Ruhaimat dakyar ta karba tare da yin godiya daga nan suka wuce gida.
Sati 1 su mami sukayi daga nan suka koma Abuja tare da Mimi Ruhaimat tayi kewar yarinyar
sosai don ita take kipin nata busy...wata sabuwar rayuwar soyayya suka shimfida tamkar xasu
hadiye juna tare suke yin komai idan yana office ma suna makale da juna a waya haka Rayuwa
ta cigaba suna rokon Allah akan samun haihuwa don har ynxu shiru kake ji kamar an shuka
dusa.xaune yake bisa carpet grass a yayinda Ruhaimat tayi matashi da cinyarsa a garden din
gidan suke suna shan iska tana karanta masa littafin *kissoshin annabawa* yana jin dadin
tarihin annabi Yusuf da take karanta masa sai faman lumshe ido yake, Momi ce tare da
yasmeen suka shigo masu gadi suka shaida musu inda masu gidan suke kai tsaye wajen
garden suka nufa yasmeen na raba ido tana mamakin girma da kyawun gidan saboda bata taba
xuwa bah gidan da sadee ta xauna ne taje sau 1.sadeeq ne ya hangosu yace "maini munyi
baki tashi ki xauna" ckn sauri ta tashi ta sanya hijabinta don kananan kayane a jikinta
"lah..Momi Yau kece a gidan namu..barka da xuwa" ckn tsananin kunya Ruhaimat ta musu
maraba , sadeeq yace "mu je ciki koh" daga nan suka koma ckn gida a falo suka xauna
Ruhaimat ta jera musu kayan motsa baki bayan sun gaisa sadeeq ya tashi ya fita Ruhaimat tabi
bayansa a bakin motarsa ya tsaya nan suka rungumi juna ya manna mata peck a kumatu
yace"ki kula kanki idan sun tafi ki kirani ok.." "Ok..u too takkia" "Lov u" "Lov u more..banda
kallon mata" murmushi yayi tare da cewa "ni me xan kalla a jikin wata mace..I have u I have
everything" murmushin jin dadi take daga nan ta daga masa hannu yaja motarsa ya tafi.duk
abunda sukayi akan idon yasmeen mamaki ne karara a fuskarta..dama haka Ruhaimat ta iya
soyayya? Yaushe ta waye haka? Xama tayi bisa kujera tana bin falon da ido har taji ta raina
kanta..ikon Allah kenan wai Ruhaimat ce ckn wannan katafaren gida haka?, koda Ruhaimat ta
shigo yasmeen bata daina kallonta bah..minti 50 sukayi a gidan sannan suka mata sallama..
Cake doughnut da kunun Aya ta xuba musu ckn bakar Leda sai kayan makeup da turarukan
humra masu kamshi ta rakasu har bakin mota ta ajiye ledojin a gidan baya godiya sukayi
yasmeen ta ja motar sika koma gida. Momi ta kula da halin da take ciki tun bayan dawowarsu
daga gidan Ruhaimat "yasmeen meke damunki na ga kin xama wani iri" "Momi magana
zamuyi" "ok go ahead"......
*Reefat ce*
[9:26PM, 20/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*73*
BY *Reefat yahya*
~an imaginary Lov story~
Baba ya kira ya sanar dasu akan cewa visa dinsu ya fito daga nan Ruhaimat ta xaga danginta
na ckn yola da jimeta sannan suka wuce jada a nan tayi kwana 3 tayo sallama da iyaye da en
uwanta suka dawo yola washe gari jirginsu ya daga xuwa Abuja, mami tayi murna kwarai da
gaske meenah tana can ta koma sai bayan ta haihu xata dawo gidan minjinta.mimi ta girma tayi
wayo ga jiki bulbul gwanin sha'awa tana ganin Ruhaimat ta fara dariya Ruhaimat ta dauketa
tana mata wasa, bayan kwana 2 da xuwansu suka cigaba da shirin tafiya don saura kwana 3
tafiyar tasu.Ruhaimat dauke da Mimi tana mata wasa sai dariya take kyalkyalewa a falon mami
suke mamin na xaune a gefe tana kallonsu a can kasar xuciyarta kuwa tausayin Ruhaimat ne
ya kamata ..tana mata adua Allah ya bata haihuwa Allah ya axurtata da ya'ya masu albarka,
sadeeq ya shigo da sallama ckn shigar kananan kaya yayi kyau sosai Ruhaimat na satar
kallonsa.kusa da ita ya xauna yasa hannu xai dauki Mimi yarinyar taki amincewa ta kara
makalewa Ruhaimat, dariya mami da Ruhaimat sukayi sadeeq ya marairaice yace "mami kina
ganin yarinyar nan..tun shekaran jiya fah taki amincewa na daga ta" "toh ba sai ka hakura bah
malam" ya bata fuska kamar xeyi kuka Ruhaimat ta fakaici idon mami ta masa gwalo nan ya
kara harzuka "mami kina gani tana min gwalo" "wa kenan?" Haushi yasa ya bar musu falon
suna masa dariya. Ruhaimat tace " Allah mami kin shagwaba ya sadeeq dayawa" murmushi
mami tayi tace "wato kin koma team din su meenah koh" dariya tayi tace "aa mami's team nake"
meenah ta shigo rike da pancakes a plate murmushi Ruhaimat tayi tare da cewa "acici's" tsaki
meenah taja tace "sanin kanki wllhi larura ce don da bahaka nake bah" dariya mami take musu
"haba mami dariya kke xaki min " " meenah me xan miki" ta bata fuska tace "dama ai anty
Ruhaimat bata laifi" mami ta tashi tsaye tace "kinga tafiyata don nasan wasu abubuwan kuna
yine don ganin idona" daga nan ta fice tana dariya, Ruhaimat ta matso kusa da ita tace "haba
mutuniyar kinsan nida ke mutu ka raba..wasa nake miki my meenah" murmushi meenah tayi
tare da cewa "lokacine yarinya.. Ai naki na nan tafe" hira suke sosai meenah na jajanta batun
sadee , sadeeq ya shigo yace " lallai maini..kina ganin mijinki yayi fushi ya tafi Amma kin kasa
xuwa ki bashi hakuri kin xauna kina biyewa wannan mai surutun tsiya koh" "hmm..su miji
manya" meenah ta fada tana dariya nan Ruhaimat ta sauke Mimi bisa cinyar meenah tace
"xauna a nan my bby kinsan baban naki Dan rigima ne" murmushi yayi ya jawota suka jera suna
shirin barin falon meenah tace "oh..antyna babu ko kunya" "babu harkar kunya yarinya..ke waya
San me kike yi a gidan naki" dariya sukayi gaba dayansu nan suka wuce bangaren su. Da
yamma suka shirya sadeeq ya daukesu a mota suka fita yawo tare da Mimi da kuma meenah
basu dawo gida bah sai xuwa dare, haka suka kasance ckn kwanciyar hnkli har xuwa ranar da
xasu tafi gaba daya familyn suka dugunxuma xuwa airport dakyar aka raba Mimi da Ruhaimat
ta makalkale a jikinta da aka rabasu kuwa ta fara kuka nan hawaye suka cika idanun Ruhaimat
a haka suka shiga jirgi tana xubda hawaye, sadeeq ne ya daura mata belt ya kwantar da kanta
a kafadarsa yana faman rarrashinta dakyar ya samu ta daina kukan daga nan jirginsu ya
daga✈✈✈✈don xuwa Saudi arabia d most wonderful country.
******* sun sauka lfy hotel ya kama musu kafin ya nema musu inda xasu xauna permanent,
bayan sunyi sallah sun huta ne ya kira iyayensu ya sanar dasu sun iso lfy daga nan suka fada
wanka.tare suka shirya nan suka hau gado kanta na bisa kirjinsa haka sukayi bacci mai dadi.
Haka Rayuwa ta kasance Ruhaimat ta fara xuwan makaranta fannin addini take karantawa
haka nan sadeeq ya fara xuwa PhD classes nasa a garin jeddah, rayuwar so da kula tare da
mutunta juna sukayi duk Wanda ya kallesu dole yaji sun burgeshi kowannensu ya maida hankali
sosai gun karatun da suke..a kwana a tashi ba wuya gun Allah Yau sun share shekara 2 a kasar
saudiya nan suka fara shirin xuwa ganin gida.Ruhaimat tayi kyau tamkar a saceta a gudu har
Yau babu labarin ciki kuma daga shi sadeeq har iyayensa babu Wanda yasa damuwa a ransa
basu fidda tsammani bah a ganinsu komai lokaci ne Mimi ta girma sai shegen surutu,yaran
meenah 2 duk mata haka nan yasmeen ta haifi danta namiji Ameena Aliyu na da yara 2mace
da namiji.sati 2 Ruhaimat tayi a jada tayi mamakin ganin sabon ginin da aka musu Hajja Dada
tsohuwa mai ran karfe ita ta fada mata cewa baba ne ya bada kwangilar gidan tsakaninta da
surukan nata sai godiya taje xiyara a can yola yasmeen ta karbeta da hannu biyu, haka nan taje
gidansu sadee Allah sarki Rayuwa tana kwance sai abunda aka mata ta xama abar
tausayi..duniya kenan ( mohulai Allah semti).
*3 years leta* xaune take bisa gadonta mai alfarma a can madinatul munawwara katon ciki ne
da ita sai marairaice cewa take sadeeq yana xaune yana faman ririta ta "haba maini ina xaa
samo saki a nan garin" kamar xatayi kuka tace "ni nasan bara'a rasa bah kawai ni faten saki
xanci " ta karashe maganar tana kuka gaba daya ya rikice haka yake fama da ita tunda ta
samo ckn bata son yayi nisa da ita ga kuma kwadayin tsiya..ynxu ckn Nada wata 6 .ya gama
PhD dinsa ita kuma tana final year nata tana hada masters don tayi degree ta gama ynxu tana
kan masters, tayi xurfi ckn karatu sosai addini ya shigeta ba kadan bah don tana da kwazo
sosai ynxu haka ana inviting nata conference ko seminar a garuruwa daban2* ckn fadin
kasar.haka sadeeq yake fama da shagwaba sai lallabata yake kamar kwai har Allah yasa ta
sauka lfy ta haifi danta kamar Dan larabawa, baba mami umma Abba Hajja Dada meenah
Ibrahim imran yasmeen da kuma momin imran su suka zo suna yaro yaci sunan Abba wato
Abubakar.. Abubakar Dan Abubakar jikan Abubakar bayan suna sukayi aikin hajji
gaba dayansu sannan suka dawo 9ja..
*Reefat ce*
[9:27PM, 20/12/2016] +234 703 007 7024: *MAI SONA*
*72*
By *Reefat yahya*
~an imaginary Lov story~
A hnkli yasmeen ta fara magana da cewa "Momi ina son komawa gidan ya imran Amma baya
sona bansan ya zanyi bah..don Allah ki taimakeni wllhi ina matukar son ya imran , baya sona
har ynxu yana bakin ckn rabuwa da Ruhaimat Shiyasa bana gabansa" "kiyi hakuri yasmeen..
Shi namiji tamkar jariri yake ke xaki koya masa komai tun da farko , amma rashin ilimin
xamantakewar aure shiya jawo miki wannan matsalar...is not too late zaki iya gyarawa" ta gyara
xama tace "Momi ya xanyi? Wllhi a shirye nake zan iya aikata komai don jawo hankalinsa"
murmushi Momi tayi tace "Abu daya zaki yi" "menene wannan abun " "gidan Ruhaimat xaki
koma ita xata koya miki duk abunda ya dace na tabbata xata wayar miki da kai" "Allah Momi
kunyarta nake ji don naci xarafinta a da can baya " "kada ki samu damuwa..Ruhaimat yarinya
ce mai hankali na tabbata xata taimaka miki" "shikenan Momi hakan xaayi " "kwantar da
hankalinki gobe xan kirata a waya xan sanar da ita komai" "nagode Momi..wllhi baki ji yanda
suka birgeni bah Yau da muka je gidan, gskiya Ruhaimat tayi dace a duniya " haka dai yasmeen
ta cigaba da xancen Ruhaimat. Kamar yanda suka tsara hakan ta kasance da safe Momi ta kira
Ruhaimat sun Dade suna magana daga karshe sukayi sallama nan ta kira driver ya sauke
yasmeen gidan Ruhaimat don xata fita da motar saboda yasmeen bata taho da tata motar bah.
Sadeeq ya tafi office don haka Ruhaimat ta gyara gidan ko ina fes tayi wanka ta fito ckn ado
na alfarma tamkar mai shirin xuwa gidan biki, yasmeen ta shigo tare da sallama cike da kunya
Ruhaimat ta karbeta hannu bibbiyu bayan sun gaisa ta kawo mata kayan marmari bata ci bah
nan Ruhaimat ta gane cewa yasmeen na jin kunyarta bisa abubuwan da suka faru tsakaninsu,
murmushi tayi tace "haba yasmeen ki daina jin kunyata ki daukeni tamkar kanwarki uwa daya
uba daya sannan kuma aminiyarki mai fatan ganin farin cknki, ina so ki mance da duk
abubuwan da suka faru a da can baya" yasmeen ta sunkuyar da kai tace " kiyi hakuri nayi
hakan ne bisa kuskure da zafin kishi saboda ina matukar kaunar imran Amma har Yau na kasa
samun soyayyarsa, xuciyarsa na can wani waje yana dawainiya da son wacce bata San yana yi
bah" "kina nufin ya imran wata yake so ba ke bah" cike da mamaki yasmeen ta daga kanta tana
kallon Ruhaimat tace "tabbas..imran baya kaunata imran yana fama da ciwon sonki Wanda har
abada baxai iya cirewa a ckn xuciyarsa" shiru sukayi suna kallon juna..rayuwar da sukayi tare
da imran ya fara dawo mata a kwakwalwa..tabbas imran mai kaunarta ne Amma meyasa bai
taba furta mata bah?? Take taji tausayinsa ya kama ta..Allah sarki dosti..Ashe haka yake fama
da ciwon so kamar yanda ta fama lokacin da ta rasa sadeeq, lallai dole ta fidda shi ckn wannan
halin ..hawayene suka cika idanunta tace "yasmeen ki min alkawari xaki dasa kaunar ki a ckn
xuciyarsa xaki mantar dashi sunana a ckn rayuwarsa..xaki sa ya manta da duk wata alakar da
ta taba faruwa tsakanina dashi, idan kinyi alkawari ni kuma a shirye nake da taimaka miki" "na
miki alkawari insha Allah xan saye xuciyarsa ya fara sona Amma baxan miki alkawarin cewa
imran xai manta dake a ckn xuciyarsa bah..don nasan hakan baxai taba faruwa bah" numfashi
ta ja sannan ta fara magana " yasmeen ina son ki Sani cewa xuciyar Dan Adam kamar miyace
wadda akayi mata shiri na musamman don tayi dadi ko abarta haka taki yin dadi, kamar yadda
tsiro yake nuna abunda aka shuka shi xaa girba..haka rayuwa take don haka ya xama dole mu
kula da addininmu da lafiyarmu da kuma mazajen mu..idan har kina Neman soyayyar mijinki
dole ne ki San wadannan abubuwan: da farko ki kasance mai tsafta... mai gaskiya..ladabi da
biyayya..iya kwalliya..iya girki ..girmama iyayensa da karrama danginsa...iya magana..ki
kasance mai hakuri..kibi umarninsa..iya tafiya, murmushi, shagwaba da sauransu" a takaice dai
yasmeen ta yini a gidan Ruhaimat har yamma sannan driver yaxo ya dauketa suka koma gida.
Ta gama tsara kwalliya tana jiran dawowarsa bayan wasu yan dakika taji tsayuwar motarsa
nan ta tashi xata fita sukayi arba a bakin kofa ya dagata sama tamkar baby yana juyata dakinsa
ya wuce da ita bai direta ko ina bah sai saman gado sannan ya fada gefe "washh..nagaji my Dil
" sumbatar goshinsa tayi tare da cewa "sorry mai sona..muje kayi wanka ka ci abinci ka huta
sannan na maka tausa" ya tashi xaune yace "da gaske ??..oh my pretty kinsan I Lov ur
massage ai" gira ya daga mata murmushi take ta gane meyake nufi daga nan ta bude fridge ta
dauko masa exotic mai sanyi ya karba yayi sipping kadan ya mika mata ta ajiye yace "Allah ya
miki albarka maini..I Lov u so much" "Lov u more my Dil" ya jawota ta fada jikinsa yace "akwai
albishir da xan miki Amma sai kin min wanka xan gaya miki" dariya tayi tace "toh muje
mana...wannan dai baxai hada fada bah" daga nan suka wuce toilet tare.
_40mins leta_...yana kwance rub da ciki tana masa tausa " pretty kinsa nayi overfeeding gashi
ynxu kasala nake ji" murmushi tayi "shine mai kyau kenan.. Kullum haka xaka yi dama baka son
cin abinci ynxu dura xan maka every day" dariya yake sosai "aw..wayo koh! Ban manta ba ai
..albishir da kace xaka min" "ohh..hakane har na manta wllhi, sorry dawo nan kusa dani" babu
gardama ta kwanta dab dashi tare da kura masa ido "ihmm..ki shirya goron da zaki bani" "a
shirye nake sir!" Dariya ta basa , hannu yakai yana shafa Dan karamin bakinta yace "na fadawa
baba dream naki na xama international scholar , dazu ina office ya kirani yace ya sama miki
admission a garin madina tare xamu tafi ni xanyi PhD Nah a king Abdullahi university of science
n technology jeddah" wani irin ihun da Ruhaimat tayi ta kankame shi tamkar xata shiga ckn
jikinsa.dariya kawai yake mata "nagode..nagode..nagode *mai sona* Allah yabar kauna Allah ya
kara budi da bunkasar arxiki, tnx I Lov u so much" godiya take masa