Showing 33001 words to 36000 words out of 61652 words
kula dashi a halin da yake ciki a yanzu sai
matarsa,kinga kenan yanzu ne zaki nuna masa so ta hanyar aurensa,ki bashi kulawa ,ki
tsarkake shi da kuma sauran abubuwa,nagaji da ganin hadimai suna masa wannan aiki'
,nawwara ta tsaya cak tana duban fulani galala,sannan tayi murmushi tace 'ni kuyanga
nawwara ce ta dace da wannan aikin ko?' sannan ta cigaba da cewa' soyayya da aure
manya,kinga umma nifa banta6a son yaya hash ba,kawai na amince zan aureshi saboda kinyi
min tayin aurensa a lokacin da bani da wani tsayayye,kuma ko da ace a yanzu zan auri yaya
hash,toh wallahi bazan aureshi ba,mutumin dake kwance tamkar gawa,in aureshi in ce na auri
wa ? Matacce?' ,fulani a fusace ta mi'ke tsaye tana cewa 'uwarki zaki aura,kaga yar iskar
yarinya,ni zakiyi wa halin 'yan duniya?' ,nawwara ta amsa da cewa 'menayi miki?,dan na fad'a
miki ra'ayina sai kiga ba'ki na,aure ne dai bazan auri yaya hash ba,kuma babu uban da zai
tursasani in aure shi,ko da kuwa iyayena ne,kuma nasan cewa baza su ta6a tursasa ni akan in
aikata abinda zuciyata bata so',nawwara ta zuge zip d'in akwatinta tana cewa 'in dai yaya hash
ne, akai kasuwa ,ni dai nawwara bana so',fulani sauran 'kiris ta saki fitsari amma haka ta daure
ta cije ,murya a sanyaye tace'nawwara kar ki min haka mana,kin san cewa fa duk abinda na
aikata ,na aikata ne saboda cikar burinki na mallakar hashim...' ,nawwara tana yafa mayafi ta
katseta ta hanyar cewa 'cikar burina ko kuma cikar burinki,kinga nifa dan Allah kar ki cika da
surutu ,wai ana dolene,indai yaya hash ne bana so ,akai kasuwa,ko kuma ki aura masa
kwarkwarori tunda ga kunyagai nan birjik a fada',fulani ta dafe kanta tana cewa 'na shiga
uku','baki shiga komai ba tukun ,sai ranar da asirinki ya tonu,a ranar zaki shiga miliyan uku ,ba
uku ba',fulani ta dubi nawwara tana nuna kanta da yatsa ,tace'ni kike jifa da irin wad'annan
kalaman,nawwara ni?' ,nawwara ta kya6e baki tana gyara zaman hand bag d'inta a hannunta
tace 'ke wacece? Ba kowa bace ke face makira,muguwa,mara imani da
tausayi,shed'aniya,kuma insha Allahu sai Allah yayi mana katanga da kaidinki' ,fulani a fusace
ranta a 6ace ta d'aga hannu zata kwashe fuskar nawwara da mari,nawwara tayi caraf ta ri'ke
hannunta,tana mai girgiza kanta tace 'kar ki kuskura hannunki ya ta6ani da sunan duka,domin
zan manta duk wata ala'ka dake tsakanin mu,in zage damtse in narka miki na jaki,dan haka ki
kiyaye',sannan ta watsar da hannun fulanin,ta kuma nunata da yatsa tace 'kuma ina son in
sanar dake cewa ,nan ba da jimawa ba insha Allahu , zan zamo mata ga bamidele' ,fulani
murya na rawa tace 'ba....mu....ge...le?' ,nawwara ta amsa mata da cewa 'bamidele! yayan
bolaji' ,fulani tana kifkifta idanuwa tace 'nawwara YARE zaki aura? Jinin oduduwa? Masu kashi
a leda' ,nawwara ta amsa mata da cewa 'ke kika san wannan',fulani tace 'wallahi tallahi sai kinyi
danasanin butulcin da kike shirin yi a gareni,sai na... ' ,nawwara ta katseta ta hanyar d'aga mata
hannu tana cewa 'dakata! Butulci na nawa kuma,wallahi tallahi a shirye nake in tona asirinki ,in
har kikayi 'yun'kurin 'bata lamarin aurena da bamidele,kuma ni zan nuna miki cewa ni 'yar
zamani ce mai tarin sababbin kaidi,so inason ki iya takunki kawai ,ki 'kyaleni in auri za6in
raina,ke kuma ki cigiba da rayuwarki a fada asirinki a rufe ,kafin ranar da za'ayi wal'kiya'
,nawwara taja akwatinta tayi hanyar fita daga d'akin,saida ta takai bakin 'kofa ta juyo tace
'wallahi nayi danasanin biye maki wajen aikata abinda muka aikata ga 'kanwar masoyina,kuma
fa kar ki d'auka cewa bazan iya fasa 'kwai ba,kawai rashin sanin inda take ne a halin a yanzu
zai hanani aikata hakan,kuma fasa 'kwan yana nufin kawo nakasu ga ala'kar mu da funmilayo
da kuma masoyina' ,nawwara tayi dariya tace 'umma,amma ki rubuta ki ajje ,in har bolaji tana
raye,kuma tana numfashi,toh ki sani cewa zata dawo da izinin Allah,kuma sai kin gama girban
abinda kika shuka,duk da a yanzu ga d'an naki da kike balo'ko'ko akansa a kwance tamkar
matacce,wannan kad'ai ya isheki ba'kinciki ayanzu,bisallam,sai kuma na kawo miki katin
gayyatar aurena da muradin raina' ,nawwara bata jira amsarta ba ta fice janye da akwati,ba tare
da tayiwa kowa sallama ba,ta fice daga fada,tayi shatar taxin da zai kaita gidan iyayenta!
Fulani kuwa sulalewa tayi 'kasa wanwar akan mazaunanta,ta d'ora hannu aka tana cewa 'chai!
Nawwara kin kasheni,kin gama dani!'
¤¤¤
Written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:28 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~38~
Misalin 'karfe 10:00am na safe ,Zahra ri'ke da 'karamar jakar matafiya tana mai zubawa
Hisham shagwa6a tana cewa 'yaya sham zamuyi missing d'inka wallahi,hope bazaka jima ba
zaka dawo' ,hisham yayi murmushi yace 'zahra kenan,insha Allahu da zarar na kamalla abinda
naje yi a can zan dawo' ,zuhra tace 'toh yaya Allah ubangiji ya taimaka,ya kuma tsare mana
kai',zahra da hisham suka amsa da 'amin',a haka suka 'karasa main parlour inda Dad da hajiya
ke zaune!
Dad ya dubi hisham yana cewa 'har ka fito zaka wuce' ,hisham ya russuna yana cewa 'yes Dad
,12:00o'clock flight ne',hajiya ta dubeshi tace 'shine zaka tafi tun yanzu ,ka bari sai sha d'aya
mana',hisham yana murmushi yace'hajiya zan biya office ne inyi clearing wasu files,daga can
zan wuce',hajiya tace 'toh shikenan hisham Allah ya tsare ya kuma kiyaye,ALLAH kuma ya
bada sa'a',Dad ya amshe da cewa'ALLAH kuma ya nuna mana ranar aurenka musha biki',hajiya
dasu zuhra suka amsa da 'amin' suna dariya,hisham kuma sai sosa 'keya yake ,sai kuma jikinsu
yayi sanyi dan tunowa da marigayiya mujiba,hakan yasa dariyar dake kan fuskarsu ya
gushe,suka taru suka mata addu'a,sannan hisham yayi sallama dasu ya tashi ya fice harabar
gidan, inda bala direba ke jiransa,zuhra da zahra suka masa rakiya zuwa bakin mota,bayan
hisham ya shiga motar,bala ya tada mota ya fice bayan maigadi ya bud'e masu gate!
[YABO CITY HOSPITAL] suka zarce bisa umarnin hisham!
¤¤¤
Dr ayuba ya mi'kawa hisham hannu sukayi musabaha sannan yace 'har zaku wuce ne?',hisham
yace 'eh ina patient din taka take, ta fito mu tafi kar muyi missing flight',Dr.ayuba yace'na tura
nurse taje ta taho da ita' sannan ya cigaba da cewa'a gaskiya hisham kayi namijin 'kokari sosai
akan yarinyar nan wand Allah kad'ai ne zai biyaka' ,hisham yayi murmushi kawai,Dr.ayuba ya
cigaba da cewa 'ALLAH ubangiji yasa ayi surgery d'in sucessfully,ba tare da an samu wani
matsala ba',hisham ya amsa da 'amin' sannan yayi 'kwafa,fuskarsa d'auke da alamun tausayi
yace 'ayuba nifa matsalata itace ,idan anyi surgery d'in mun dawo yaya zanyi da ita? ,ina zan
kaita?' ,Dr ayuba ya dafa kafad'ar hisham yace'why not ka kaita gidanku kawai,in yaso sai ka
yiwa su hajiya bayani kawai,nasan cewa bazasu 'ki ba,they will understand,tunda taimako ne
they won't mind,kuma zamanta tare daku na d'an lokacine da zarar tayi regaining memory
d'inta,shikenan fa' ,hisham ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa 'amma baka ganin cewa za'a
samu....'
shigowar Bolaji sanye da farar doguwar riga,kanta rufe da 'karamin hijab,tare da nurse ne ya
katsewa hisham zancensa!
Dr ayuba ya dubi bolaji wacce kanta ke sunkuye ,fuskarsa d'auke da murmushi yace'my
patient,your flight is 12oclock,so you will be leaving by now,i wish you sucess',bolaji ta amsa da
cewa 'thank you doctor,may Allah reward you!,sannan ta kai dubanta ga hisham tana cewa'
likewise brother hisham i really appreciate your effort for giving me the chance to live
again,although i don't really know who i am or know anything about my past,i have no words to
express my gratitude towards you ',Dr.ayuba yayi murmushi ya katseta ta hanyar cewa 'the
pleasure is mine,and my job is to save lives,so don't mind' ',hisham ya tashi ya amshi jakar
kayanta[shine ya siya mata su] dake hannun nurse d'in da suka shigo tare,sannan ya dubi bolaji
yace ' enough of the pleasantries ,shall we' yana mai nuna mata 'kofa!
A haka bolaji tayi sallama da ma'aikatan asibitin,suna masu mata fatan alkhairi a rayuwa tare da
mata fatan samun lafiya!
Hisham yayi clearing duk wani bill ,sannan suka fice daga asibitin!
¤¤¤
Misalin 'karfe 12:05 jirgi ya d'aga dasu bolaji da hisham izuwa 'kasar america!
Ko da jirgi ya sauka a filin AMERICAN AIRPORT,motar da aka turo daga N.G.O na Bieng
human ne ,ya wuce da su 'GREENFIELD HOSPITAL ' dake Los angeles!
¤¤¤
Note: ga masu min comment da 'tnx' 'cgb' and 'nyc' please ku daina, bana bu'kata. ,all i want is
for us 2 discuss about each chapter i posted,like what do u expct 2 happen next and what do u
tink abt the chapter and so on,hakan zaisa in samu courage da zeal wajen ganin na 'kara 'kaimi
gun posting a kai akai!
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:29 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~39~
Suna isa asibitin[GREENFIELD HOSPITAL] , guest reception suka nufa,anan suka gabatar da
salloli ,suka ci abinci ,sannan suka shiga cikin asibitin don ganin likitan da zai yiwa bolaji
surgery!
Dr.Nassif albert shine surgeon d'in da zai yiwa bolaji surgery,d'an asalin nigeria ne,haifaffen
garin jos,ba musulmi bane,amma bahaushen jos ne,karatu ne ya kawoshi 'kasar america,bayan
ya kamalla karatunsa,sai yayi housemanship d'insa a asibitin greenfield,daga nan sai suka
ri'keshi saboda 'kwazonsa da haza'karsa,a yanzu haka shine 'kwararren plastic surgeon da
asibitin ke ji da ta'kama!
Kasancewar Dr.nassif yasan da zuwansu hisham da bolaji ,hakan yasa basu sha wahalar
ganinsa ba,saboda duk wani info da details akansu, N.G.O [bieng human] sun riga sun turo
asibitin,hatta kud'in aikin da za'ayi mata sun riga sun biya!
Bayan Sun shiga wawakeken office d'in dr.nassif,sai Hisham ya mi'kawa Dr nassif hannu suka
gaisa,dr.nassif fuskarsa d'auke da fara'a ya dubesu yace'you may sit down please' yana mai
nuna musu kujera ,bayan sun zauna ,sai dr.nassif ya dubi bolaji wacce fuskarta ta malkwad'e
yace 'maam! can we go over there so that i can examine your face' ,yana mai nuna mata wani
gadon marasa lafiya dake cikin ofis d'in,bolaji ta mi'ke a sanyaye ta nufi gun gadon ta
zauna,Dr.nassif ya sanya plastic gloves a hannunsa ,ya 'karasa gunta ya fara dube dubensa da
gwaje gwaje akan mal'kwad'ad'd'iyar fuskarta da fulani tayiwa aika aika ,har na tsawon minti 30!
Bayan dr.nassif ya gama wasu rubuce rubuce akan wani takarda,sai ya d'ago ya dubi bolaji
sannan ya sauke idanunsa akan hisham yana mai cewa 'the surgery will take place by 8:00am
tommorow morning and i hope you bring along the picture of the face we will be using for her
surgery' ,hisham cike da mamaki yace 'picture? What picture?',Dr nassif ya cire spec d'insa
yana cewa 'hisham ko?' ,hisham ya amsa da 'eh' ,dr.nassif ya jinjina kansa sannan ya cigaba da
magana cikin harshen hausa wacce ke fita daga bakinsa tamkar turanci yana mai cewa'hisham
ya zama dole ayiwa fuskarta total change over,cause her face is totally ruined and disfigured,ba
ta yadda za'a iya gyara wani 'bangaren abar wani 'bangaren,saboda haka ya kamata muyi
amfani da hoton fuskarta na asali yayin da zamuyi mata aikin!'
bolaji ta 'kurawa bakin dr.nassif idanu kasancewar batajin me yake fad'a!
Hisham ya goge gumin da ya feso masa akan goshi yana mai furzar da huci ,yace 'tir'kashi,likita
akwai matsala fa,ita kanta bata san fuskarta ta asali ba,ballantana ni d'an rakiya',cike da
mamaki dr nassif yace 'how comes?' ,a take hisham ya labarta masa lalurar bolaji na memory
loss!' cike da tausayawa Dr nassif yace 'what a pity!' ,sannan ya cigaba da cewa 'toh babu
matsala,za'a iya using wani face d'in for the surgery,in har kun amince' ,a take Dr.nassif ya
bud'e drawer ya ciro wani 'katon album mai d'auke da hotuna ya mi'kawa hisham yana cewa 'ga
album nan,kuje ku duba kuyi shawara ku za6i hoton fuskar da za muyi amfani dashi for her
surgery',sannan ya dubi bolaji yace 'kar ki damu....' ,bolaji ta katseshi ta hanyar cewa 'i beg your
pardon',hisham yayi murmushi yace 'doctor bata jin ko wani YARE a yanzu sai turanci',Dr nassif
yace'oh sorry' cikin harshen turanci yayi mata bayani dalla dalla,bolaji tayi jim sannan tace 'no
problem,i don't mind doctor,i will be okay with any face you use,all i want is to look good,i don't
want to look scary anymore!
A haka sukayi sallama,suka tafi!
Masaukin da N.G.O ta tanadar masu aka kaisu!
Bayan sun idar da sallar isha,sai hisham ya d'auko album suka fara dubawa shi da
bolaji,yawanci hotunan arnan y'an matan black america ne da south africa,babu hoton musulma
ko d'aya,a haka dai bolaji ta yanke hukunci ta za6i hoton wata black america! hisham ya dubeta
yace 'are you okay with it' ,'yes i'm okay with it' ta bashi amsa ,hisham ya kwa6e baki yace
'alright then,since you are ok with it,no qualms',bolaji a sanyaye tace 'what about you?',hisham
ya amsa da cewa 'i have no option,it's your face not mine,i only pray that the surgery would be
done sucessfully!'
Kasancewar suite[masauki] d'in yana d'auke da room and parlour da kuma toilet,hakan yasa
hisham yayi kwanciyarsa akan kujerar falo,ita kuma bolaji tayi masa sai da safe ta wuce d'aki ta
kwanta,tana mai yiwa hisham addu'a a ranta ,wanda tayiwa la'kabi da 'MY LIFE!'
¤¤¤
Washegari misalin 'karfe 8:30am Dr.nassif da sauran surgeons suka shigar da bolaji theatre!
Hisham yana zaune akan restchairs dake jere a harabar gaban theatre d'in,yana mai cewa a
zuciyarsa 'ta ya za'a sanyawa yarinyar nan fuskar arniya bayan kuma tana musulma ,gaskiya da
sake','kana da hoton fuskar musulmar da za'a sanya mata in har ba internet zaka hau ka nemo
ba',zuciyarsa ta bashi amsa! Wayarsa ya ciro daga gaban aljihunsa wanda hakan yayi sanadiyar fad'owar wallet
d'insa,hannu yasa zai d'au wallet d'in,sai idanunsa suka masa tozali da hoton dake jikin wallet
d'in!
Written by :ABDULAZIZ iLILEE ISMA'IL
[10/17, 8:29 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~40~
Murmushi ne ya su6cewa hisham,ya d'au wallet d'in,ya zare hoton yana mai cewa
'ALHAMDULILLAH ,bazan ta6a danasanin bada hoton fuskarki a sanya mata ba',zuciyarsa ce
ta tunatar da shi cewa 'taya zaka bada hoton nan,bayan an riga an shigar da ita theatre,wata
'kila ma sun fara surgery.....',fitowar Dr.nassif daga theatre yana sauri ne ya katsewa hisham
zancen zucin da yake,cike da hanzari hisham ya tareshi yana mai cewa 'doctor any problem?'
,Dr.nassif yayi murmushi yace 'no prolem at all,zanje office in d'auko hoton da zamuyi using for
the surgery,i forget to pick it',hisham da sauri ya mi'kawa Dr.nassif hoton dake hannunsa yana
mai cewa 'doctor ga wannan,ayi amfani da fuskar dake kan hoton please',Dr nassif ya amshi
hoton ya duba yana cewa 'kana ganin babu matsala,kar ka manta cewa ta riga ta za6i hoton
fuskar da za'a saka mata' ,hisham yace 'babu matsal doctor,i will explain everything to her after
the surgery',Dr.nassif yace 'alright then,dafatan kuma wacce ke jikin hoton nan bata raye,domin
ko hotunan fuskokin matan dana baku ku za6a,duk matattu ne' ,'eh wallahi bata raye,'yar uwata
ce' hisham ya bashi amsa,Dr.nassif ya sauke ajiyar zuciya sannan yace 'alright it's ok,we will try
our maximum best to make her face look exactly like this!',ko da dr.nassif ya gama fad'in
haka,sai ya juyo ya koma theatre hannunsa ri'ke da hoton da hisham ya bashi! ¤¤¤
A 'bangaren Fulani tun bayan tafiyar nawwara, duniya tayi mata zafi,rashin farfad'owar hashim
yana matu'kar d'aga mata hankali,musamman idan ta kalleshi taga yadda hadimai ke juyashi
suna masa hidima tamkar matacce,a kullum Dr.ayuba yazo ya dubashi,amsa d'aya yake basu
''ku cigiba da addu'a,kar ku gajiya,at any time zai iya farfad'owa if Allah permits' ,maimartaba ya
sa an tara malamai sunyi saukar al qur'ani mai girma,amma jikin hashim sai godiya,yana
kwance tamkar gawa,zuciyarsa kad'ai ke bugawa a jikinsa,idanunsa bud'e kamar kayi masa
magana ya amsa!
A kullum fulani zama take a d'akinta tana risgar kuka tana mai cewa'danasani na barka da
matarka ban raba ku ba,gashi nayi sanadiyar shigarka wannan mawuyacin hali,wanda da wuya
ka sami macen da zata aureka,ta kuma yi d'awainiya da kai tsakani da Allah,wallahi na tabbata
da bolaji tana fadar nan,babu abinda zai hanata d'awainiya da kai,duk da bata sonka,amma
zata tausaya maka ,kuma kaci arzikina a gunta,ko kasancewarka mijinta zai sa taji tausayinka
tayi d'awainiya da kai,ba tare da ta gajiya ba',wani lokacin kuma sai ta zabga uban tagumi tana
zancen zuci kamar haka 'ina zan ganki bolaji,tayaya zan fara nemanki,baùan na tabbatarwa da
duniya mutuwarki,kaicona ! Kaicona! Tir da mugun hali irin nawa,meye aibun bolaji?'
'zamantowarta YARE shine aibunta' zuciyarta ta bata amsa!
Sultan kuwa ya fawallawa Allah lamuransa gaba d'aùa,yayi watsi da mugun d'abi'arsa na
neman mata,a yanzu haka yana aiki a [MODIBBO PETROLEUM] dake jihar sokoto a matsayin
Managing director!
A kullum idan yayi sallah sai ya nemi gafarar ubangiji,kuma sai yayi addu'a kamar haka'ya Allah
,idan har bolaji tana raye,ya Allah ka kareta da dukkan kariyarka,ya Allah ka bayyana mana ita
a raùe ko a mace,ya Allah ka tashi kafad'ar mijinta ka bashi lafiya,ya Allah ka tona asirin
mahaifiyata!'
A 'bangaren nawwara kuwa,soyayyarta da bamidele tayi 'karfi sosai,wanda a yanzu haka
iyayenta sun san da zamansa,kuma sun bashi izinin ya turo magabatansa!
Ko da Dr.ayuba ya tuntu6i nawwara akan zancen aurenta da hashim,sai ta nuna masa cewa 'ita
daman ba son sa take ba,fulani ce kawai ke kid'anta kuma take taka rawarta!'
¤¤¤
*BAYAN WATA 'DAYA DA SATI BIYU*
A yau Dr.nassif zai warwarewa bolaji bandejin dake d'aure akan fuskarta!
Wata Nurse ce ta mi'kawa bolaji madubi a yayin da dr.nassif ya gama warware mata
bandejin,ko da bolaji ta amshi madubin ta kalla,sai tasa hannu tana shafa fuskarta tana cewa
'wow! This face is beautiful',who's face is this? 'bolaji ta tambaya,hisham dake tsaye daga
gefenta fuskarsa d'auke da murmushin jin dad'i,ya amsa mata da cewa 'it's MUJIBA'S