Showing 24001 words to 27000 words out of 61652 words

Chapter 9 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4032


jikinsa ya rage daga shi sai boxers,sannan ya nufi gun bolaji wacce ke kwance akan darduma
,ta fara yin bacci,hannu yasa ya cicci6eta ya kaita kan gado ya kwantar ,ya rage mata kayan
jikinta,ya tofe su da addu'a tare da kankameta,ya kashe wutar bedside lamp ,a haka har bacci
ya kwashesu!

Fulani tana shiga d'aki ta d'au waya ta kira nawwara!
Nawwara ta shigo d'akin tana cewa 'umma lafiya?','ina lafiya kuwa,hashimu ya auro jinin
oduduwa da sango',fulani ta bawa nawwara amsa!
Nawwara hannun akan 'kirji ta 'kwalalo idanu tace'aure?','kwarai kuwa aure dai da kika sani'
sannan fulani ta labartawa nawwara komai kamar yadda mai martaba ya labarta mata
d'azunnan', nawwara ta jinjina kai tare da cewa 'noma!' lallai yaya hash wannan yarinya ta gama
asirceshi',fulani tace'barni da shegiya,ni fa da maimartaba yayi min zancen,kasa yin zancenki
nayi wallahi,domin nasan raina ne zai 6aci,wai ni hashim da abbansa zasu munafinta,ba laifinsu
bane,laifin matsafiyar yarinyar ce ,yar gaban goshin sango ,amma dani take zancen,zata gane
cewa shayi ruwane,a siyasance zanci ubanta,in kuma fitar da ita daga fadar nan ba tare da
kowa a cikinsu ya lura ba,kema ya zama dole ki danne zuciyarki,ki nuna murnar ga wannan
auren,domin yin haka kad'ai zaisa mu cimma burinmu akanta batare da kowa yagane
'kiyayyarmu gareta ba',nawwara tace'hakane umma,gaskiya kin kawo shawara mai kyau',fulani
tayi murmushi tace'sai na nunawa wannan tsinanniyar cewa ni ba'kar masa ce ,tuyar
iblisai,batare da na sanya boka ko malam a lamarin ba!'

created by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 12:37 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~28~

Washegari da safe bayan gaba d'ayansu sun gama karyawa,fulani ta d'auko wasu royal
abayas guda biyu ,ta 'kwan'kwasa d'akin

yarima hashim!

Hashim ya bud'e kofar ,ganin fulani ce yasa ya russuna yana cewa 'ina kwana',fulani da
fara'arta ta amsa tana cewa'my souldear ango,aure babu gayata babu labari',hashim ya fara
sosa 'keyarsa ,fulani tayi murmushi tace'ungo ka mi'kawa surukar tawa kafin anjima mu fita da
ita mu had'o mata lefe' ,hashim ya amshi kayan yana cewa'godiya muke umma,amma fa umma
tafiyar da zanyi zuwa liberia a yau da ita zan tafi,idan munje can zan had'a mata lefen'fulani ji
tayi kamar ta sha'keshi ,a zuciyarta cewa take'huh zama da marasa kunya yasa d'ana ya zama
mara kunya,ka tafi da ita can salon ka 'kunsa mata ciki ko,jiya ma ba yadda na iya ,hakan yasa
na barku kuka kwana tare',a fili sai fulani ta amshe kayan daga hannunsa tana cewa'ayya toh
shikenan, turo min ita,muje in tsuma maka ita ,yadda zakuji dad'in yin honeymoon d'in naku a
can',hashim ji yayi kamar kasa ta tsage ya shige,a kunyace ya koma d'akin yacewa bolaji taje
umma na kiranta!
Bolaji sanye da jallabiyar hashim ta fito ,ta russuna,fulani taja hannunta tana cewa'my
daughter,the beautiful damsel,stand up lets go to my room!'

Suna shiga d'akinta ,fulani ta fara janta da zancen tafiya liberia,anan bolaji ta nuna mata cewa
ita fa bata son tabi hashim!
Fulani ta murmusa tana cewa 'da kinsan abinda zai sameki da kin tattara kin bi mijinki',sannan
ta dafa bolaji tana cewa'my daughter,don't worry no one will force you to follow him,lie down and
rest for now,i will talk to him',kasancewar mai martaba ya gabatar da kowa ga bolaji,hakan yasa
bolaji ta rungume fulani tana cewa 'thank you mummy folani',fulani tace 'folanin uwarki,haka
kawai zaki gur6atamin suna da shege harshenki na yare',bolaji tace 'what?',fulani tayi ya'ke tare
da amsa mata da cewa 'i mean i love the way you pronounce my name',bolaji tayi murmushi ta
kwanta akan gadon fulani ,kamar yadda fulanin ta umarceta'
¤¤ ¤
Misalin 'karfe 11:00am hashim ya gama shirin tafiya tsaf!
fitowa yayi daga d'aki ya wuce bangaren mai martaba,anan yasamu ummansa da ummunsu
,ya russuna ya gaishesu suka amsa masa da fara'a,kanshi a sunkuye yace masu zasu
wuce,maimartaba da ummu suka masa fatan alkhairi,a kunyace hashim ya dubi fulani yana
cewa 'umma ina take,ta fito mu tafi',fulani ta murmusa tace'd'ana kenan,tana d'akina a kwance
,amma fa matar nan taka ta nuna min rashin son tafiyar nan,sai naga kawai me zai hana ka tafi
kai kad'ai ka barta damu ,tunda wata d'aya kawai zakayi kadawo,kaga kenan kafin ka dawo ta
riga ta gama sabawa da masauratar nan da kuma mutanenta,amma kana da damar tafiya da ita
fah,tunda abar ikonka ce',hashim ya 'kas'kantar da kai yace'umma duk yadda kikace daidai
ne,da ni da ita duk abun ikon ki ne,bara na wuce' ,fulani tace 'ALLAH ya kiyaye ya kuma tsare'
,a haka hashim yayi sallama dasu gabad'aya ya fice!

'Dakin fulani ya wuce ,anan ya tadda bolaji kwance akan gado,'karasawa yayi gareta ya
ran'kwafa ya kwanta akanta,bolaji ta bud'e idanunta,a sanyaye hashim ya rad'a mata a kunne
'my better half,i'm leaving',turo baki bolaji tayi tare da kawar da kanta gefe,bakinsa yasa ya
chafki bakinta,wannan karin jikinta yayi sanyi 'kalau,kwata kwata ba ta nemi ta janye bakinta
ba,sai da ya gaji da kansa,sannan ya 'kyaleta,ya mi'ke tsaye,ya gyara zaman uniform d'insa
sannan yace 'my better half take care of your self,if you need anything ask my mum',bolaji ta
tashi zaune,ta turo bakinta tare da jan tsaki

hashim yayi murmushi tare da juyawa zai fice!
A daidai kofar ya juyo ya dubeta idanunsa jajir yace'i'm going to miss you my better half,and
always remember that ,cap.t hashim love's you',bai jira amsarta ba ,ya fice tare da wucewa
mota inda royal chaffeur ke jiransa,yana shiga mota r ya mannawa idanunsa ba'kin spec,royal
chaffeur ya harba motar suka fice daga modibbo's palace,suka wuce airport,daga can hashim
zai hau jirgi ya wuce liberia!

Bolaji ta sauke numfashi,ta koma ta kwanta tana mai murnar rashin tafiyar hashim da ita !

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 12:38 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2trbes }
na ILILEE

~29~


Misalin 'karfe 2:00 na rana ,fulani ,nawwara,da bolaji suka fice tare da royal guards,bayan
fulani ta amshi ma'kudan kud'i a gun mai martaba!

Siyayya wanda ya amsa suna siyayya fulani tayiwa bolaji sosai,wanda nawwara ita ce mai kan
gaba wajen za6owa,sai da suka sha'ke akwatuna guda 24 da kaya,sannan suka dawo fada da
kaya ni'ki ni'ki!

Bolaji ta kasa cewa komai,sai murna take a yau tasamu madadin mahaifiyarta,fulani ta nuna
mata so da gata ba kad'an ba,haka zalika nawwara!

¤¤¤
A kwana a tashi yau kwanan bolaji 20 a fada,wanda zuwa yanzu ta saba da mutanen fada,a
kullum sai jakadiya mara'kisiya ta kaita gun ummu,ummu kuwa ba laifi tana jan bolaji a jiki tana
hira da ita ,tare da bata shawarwari cikin harshen turanci!

Bolaji abu d'aya ne bata saba dashi ba,shine d'aura zani ,kuma kusan duk tufafin da fulani ta
kwaso mata atamfofi ne wanda fulani tasa a din'ka mata su zannuwa!
¤¤¤
A yau sultan ya kamalla bautar 'kasar sa ,kuma a yau sauran kwana uku hashim ya dawo!

Tun safe ummu ta fara shirye shiryen tarbar sultan,itama ta nuna tata bajintar wajen sawa ayi
gyare gyare da girke girke na tarbar d'anta!

Misalin 'karfe 5:00 na yamma sultan ya iso fada,ummu tayi masa tarba mai kyau,inda ta d'inga
mamakin haske da 'kibar da yayi kamar bashi ba!

Da dare ,kasancewar ummu ke da girki,ta wuce sashin mai martaba!
Sultan ya nufi sashin fulani ,a mini parlour d'inta ya tadda fulani bolaji, da nawwara,suna hira
suna shan kayan itatuwa! Neman waje yayi ya zauna,suka gaisa da fulani da nawwara,sannan
ya 'kurawa bolaji idanu,wanda maimartaba ya riga gabatar masu da junansu d'azu a gun cin
abinci! Sultan yayi gyaran murya yace 'umma wai ita matar bros batajin hausa ne',fulani ta yatsine
fuska tana cewa 'ka ta6ajin cewa oduduwa yana jin hausa?',bolaji tayi caraf jin fulani ta ambaci
oduduwa, tace 'mummy folani,so you know oduduwa',fulani ta washe ha'kora tana cewa 'ba
dole in san oduduwa ba,tunda ga irinsa a gabana',bolaji tace 'i beg your pardon',fulani tace
'what i said is that ,back then when i was in secondary school,i love the yoruba's so much,so i
know alot about them',bolaji tayi dariya tana cewa 'excuse me',ta mi'ke tsaye ta wuce toilet d'in
d'akin fulani!

Tana fita fulani taja tsaki ,nawwara ta tayata !
Fulani tace'wallahi nagaji da nunawa wannan YAREN so,kullum nice magana cikin harshen
turanci kamar d'iyar mango park',nawwara tace 'umma ke dai bari,gwolaji tana 'konamin
rai,musamman idan ta ambaci sunayenmu' ,fulani tace 'kyale 'yar iskar mana,lokaci kawai nake
jira in gabatar kudiri na akanta, kafin souldear ya dawo', nawwara ta amsa da 'ya kamata
kam',sultan fuskarsa dauke mamaki ya dubi fulani yace 'umma me aibunta idan ta zamo
YARE,zamanta matar bros ya kamata ace kin so ta tsakani da Allah',fulani ta aika masa da
da'kuwa tana cewa 'tashi ka fice min daga d'aki,kafin yanzu in sauke maka kwandon tsinuwa
akai',sum sum sum ya mi'ke ya fice!
Fulani ta 'kara jan dogon tsa'ki tana cewa 'ya zama dole in fitar da yarinyar daga wannan
masarauta'

Sultan kuwa ya kamu da matsananciyar sha'awar bolaji,kyawunta da dirinta ne yake fisgar
tunaninsa,wanda hakan yasa ya kasa jurewa ,ya fara neman mafita ga yadda zai kashe wutar
sha'awar bolaji da ya addabi zuciyarsa!

¤¤¤
A yau maimartaba ya umarci fulani da naja'atu dasu shirya zasu fita rangadi,fulani ta tsiro da
rashin lafiya,wanda hakan yasa maimartaba ya tafi da ummu[naja'atu] tare da royal chambers
da royal guards!

Fulani taji dad'in wannan fitar tasu! Sultan shima a wannan rana ya nufi d'akin bolaji domin
gudanar da nasa 'kudirin,inda itama fulani tazo aiwatar tata kud'irin ,sai kuma ta tadda sultan [ku
duba 1,2 3,]!

CIGABAN LABARI.....

*Ya rayuwar bolaji zata kasance a wannan dajin,mutuwa ko rayuwa?
*Ya capt.hashim zai yi idan ya dawo ya tadda matarsa bata fada?
*Me fulani zatace ga maimartaba da hashim akan 6acewar bolaji daga fada?

*Shin kurtagu,barde,nawwara,sultan,da jakadiya zasu tona asirin fulani?

Muje zuwa dai tare dani ILILEE ma'kir'kirin YARE BIYU ,domin samun amsoshinku!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 12:41 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~30~

A lokacin da fulani suka dawo fada,su maimartaba basu dawo ba,hakan ba 'karamin dad'i
yayiwa fulani ba!
kud'i ta d'auko ma'kudai ta bawa su barde da duk wani wanda yasa hannu a cikin fitar bolaji
daga fada a yau ,in an d'auke nawwara da sultan,wanda su ja masu kunne tayi sosai akan kar
taji kar ta gani,sannan ta wuce d'akin bolaji ,taje ta d'auko wata doguwar riga a cikin kayan bolaji
da kuma awarwaronta guda uku na daham ,wanda maimartaba ya bawa bolaji a matsayin
sadakin aurenta da hashim!
Fulani ta wuce d'akinta ta 6oye kayan tana murnar faruwar abinda ta aikata ayau ,tana cewa a
ranta 'nan gaba zakuyi naku aikin'!

Daf da magriba mai martaba da ummu suka dawo daga rangadi,
Fulani tayi masu tarba mai kyau!

Bayan sallar isha,kowa ya hallara a gun cin abinci in an d'auke bolaji,
bayan sun gama cin abincin,suka dawo restroom,maimartaba ya dubi fulani yace'ni ko ina
yarinyar nan take,tunda muka dawo ban ganta ba',fulani ta marairaice murya tace'kasan gobe
maigidanta zai dawo,shine d'azu mukayi mata gyaran jiki da fuska ni dasu nawwara,,toh
gajiyane yasa kanta ciwo,tasha magani ta kwanta abinta,kuma dai da yake tana fashin sallah
ne,hakan yasa tayi kwanciyarta'',maimartaba yace'ayya,ALLAH ya sawwake','amin' fulani ta
amsa ,a haka suka cigaba da tattaunawa akan dawowar da hashim zai yi gobe!
Sultan wanda hankalinsa gaba d'aya yana gun bolajin da suka baro kwance a daji,tashi yayi ya
koma d'aki yana mai tunanin neman mafita ga yadda zaiyi ya ceto rayuwar bolaji!

¤¤¤

Bayan tafiyarsu fulani da awa d'aya,wasu ayarin mahauta da karnukansu suka zo wucewa ta
dajin,ganin karnukansu sun nufi gun da bolaji ke yashe a kwance a dajin,yasa mahautan suka
bi bayan karnukan nasu,ganin mace kwance fuska jina jina yasa sukayi mata chaa akai,sun
tsorata matu'ka ga yanayin da suka tsinci fuskarta! Hannu suka sa suka cicci6eta suka yo bakin titi da ita suka kwantar da ita!
'Daya daga cikin mahautan ne ya tsaya akan titin yana mai d'aga hannunsa ga duk motar da ya
gani tazo wucewa,amma fafur haka zasu wuce ba tare da sun tsaya ba!

Wata ba'kar motace 'kirar vibe tazo wucewa a guje,har motar ta wuce mahaucin,sai kuma ta
dawo da baya,sannan aka sauke gilasan motar!
Wani Matashine ma'abocin kyau dake zaune kujerar dake kusa da kujerar direba ya dubi
mahaucin yana cewa'bawan Allah lafiya kake tsaida mu',mahaucin yace 'ina lafiya kuwa
yalla6ai,gawa muka tsinta a daji,shine muka yanke shawarar neman taimako gun irinku masu
motoci,ku tafi da gawar asibitin cikin gari,ko a dace,iyalan mamacin suzo nema',matashin mai
suna HISHAM yace'gawa kuma? A daji?','eh yalla6ai,sauko ka ganta ,macece ma,inaga wani
naman daji ne ya hallaka ta,saboda fuskarta ya nuna alamun faruwan hakan',hisham ya bud'e
mota ya sauko tare da duban matashin dake zaune a mazaunin direba yana cewa 'bala sauko
muje mugani',matashin da ya amsa suna bala yaja gajeran tsaki tare da cewa'haba oga ,me
had'inmu da gawa kuma,wayasani ko kasheta sukayi,shine zasu 'ka'kaba mana ita',hisham ya
daka masa tsawa da cewa'common get out from the car my friend',jiki na rawa bala ya
fito,mahaucin yayi masu jagora suka 'karasa gun sauran mahautan dake tare da bolaji!
Ganin fuskar bolaji tamkar d'anyar naman shanu ,yasa hisham da bala suka kauda kawunnansu
bakunansu d'auke da salati!
Hisham ya umarcesu dasu d'auki bolaji su sanya ta a mota,bayan sun kwantar da bolaji a
motar,hisham ya dubesu yace yana bu'katar koda mutum d'aya ne a cikinsu ya bisu domin bada
shaida,a take mutum biyu suka amince zasu bisu!
Sauran mahautan sukayiwa hisham godiya,sannan sukayi sallama da juna suka wuce!
Police station direct suka zarce ,anan hisham ya nuna masu I.Dcard d'insa,sannan yayi
reporting cewa gawa suka tsinta a daji,suna bu'katar d'ansandar da zai rakasu asibiti sukai
gawar!
A take aka had'asu da d'ansanda guda d'aya ,bayan an tabbatar da bayanin nasa,ta hanyar
tambayar sauran mahautan guda biyu!

YABO CITY HOSPITAL suka zarce da bolaji domin mi'kata ga mortuary!

¤¤¤
Sultan kuwa ya yanke shawarar komawa dajin dasu ka baro bolaji ,a wannan dare,ba tare da
kowa yasani ba,ya d'au mota ya fice daga fada,ko da ya isa dajin ,ya iske wayam babu bolaji
babu labarinta!
Jiki a sanyaye ya dawo fada ,yana mai tir da halinsa na neman mata,gashi ya jazawa 'yar
mutane ,an salwantar da rayuwarta ta dalilinsa,a take ya d'au al'kawarin ba shi ba neman mata
har abada!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 7:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE

~31~

Da isar su hisham asibitin[YABO CITY HOSPITAL] ,suka zarce reception suka sanar da nurse
on duty abinda ke tafe dasu,da hanzari ta had'asu da DR AYUBA wanda ya kasance aboki ga
hisham!

Bayan sun gaisa da junansu,sai hisham ya korowa abokinsa jawabi akan abinda ke tafe dasu!

Dr ayuba ya jinjina namijin kokarin da sukayi wajen ganin sun kawo gawar bolaji
motuary,sannan ya koma kan bolaji wacce take kwance tamkar matacciya yana bincike domin
tabbatar da mutuwarta ,abin mamaki sai ya tsinci jijiyar hannunta[pulse] yana matsowa,wato dai
da ranta ,a take ya bawa nurses umarni da su shigar da bolaji emergency room domin abata
taimakon gaggawa!

Dr ayuba ya shaidawa su hisham cewa tana da rai bata mutu ba,su kwantar da hankalinsu,da
izinin Allah zasuyi iyaka bakin 'kokarinsu wajen ganin su ceto rayuwarta,yana gama fad'a masu
haka ya shige emergency room!

Hisham a take ya sallami mahautan da 'yansandan da suka taho tare,ya rage daga shi sai bala!

Bayan awa biyu Dr.ayuba ya fito daga emergency room ya shaidawa hisham cewa 'everthing is
going smoothly,munyi 'ko'karin daidaita numfashinta tare da treating ciwon dake kan fuskarta
da duk wani external wounds dake jikinta,yanzu haka ansaka mata drip,muna jiran farfad'aworta
domin mu 'kara bincike akanta ko tana da internal wounds',hisham ya dubi dr.ayuba yana cewa
'godiya nake ayuba,ALLAH ya saka da alkhairi',dr.ayuba yayi murmushi tare da dafa kafad'ar
hisham yace'never mind hisham,ko da ace ba kaine ka kawota ba,iyaka abinda zamu iya yi
mata kenan',sannan yace 'zaka iya tafiya dare yayi,i will handle everything,kar ka damu'!

A haka sukayi sallama da juna,hisham da bala suka fice daga asibitin!

¤¤¤

Washegari misalin 'karfe 10 na safe fulani ta nufi turaka gun maimartaba bisa jagorancin
jakadiya mara'kisiya ,hankalinta a tashe kamar dagaske ,da isar su turaka ,fulani ta shige
,bayan ta mi'ka gaisuwa ga maimartaba,sai ta d'ora da cewa' ni fa tun da asuba banga yarinyar
nan ba a d'akinta,kuma nasa an dudduba ko ina a cikin fadar nan,amma ba'a ganta
ba',maimartaba hankali a tashe yace 'tir'kashi ba'a ganta ba,toh ina taje?',fulani ta amsa da
cewa 'nima tambayar da nake wa kaina kenan,amma fa ina ganin kamar guduwa tayi fa,domin
a yadda na lura yarinyar bata son hashim ko kad'an'!

A take maimartaba ya bawa royal guards umarnin cewa su fita su nemo bolaji a duk tashoshin
dake jihar sokoto,sannan ya umarci sultan da yaje gidan sate comissioner of police,ya kai masa
hotuna da duk wani details na bolaji!
Hankalin kowa ya tashi a fada,nawwara ce taje ta binciko jakar bolaji ,ta ciro hotunanta guda
biyu daga cikin album ,ta kaiwa sultan,ya tafi dasu gidan commissioner!

Ita kuma nawwara ta wuce gidan radio da television ta bada cigiyar bolaji!

Fulani sai kuka take tana cewa 'me zatacewa souldear idan ya dawo ya tadda matarsa bata
nan!

Ko da sultan ya isa gidan Commissioner da hotunan bolaji,ya kuma shaidawa commissioner
sa'kon maimartaba ,a take commissioner ya tura yaransa da hotunan bolaji suje duk wani
checkpoints da police depot dake jihar sokoto su bada cikiyar bolaji!

Har 'karfe 2:00pm na rana,babu labarin bolaji,hankalin maimartaba duk ya gama tashi!
Fulani duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login