Showing 60001 words to 61652 words out of 61652 words
da cewa "madallah bolaji,kai kuma hashim nasan cewa an
cutar da kai da matarka ,amma ka daure ka cije ka danne ,kayi hakuri ka yafe musu ,domin
muma muna yiwa Allah laifi kuma yana yafe mana',hashim idanu jajir yace 'Allah ya yafe mana
gaba daya',mai martaba ya dubi su jakadiya yace 'toh jakadiya ,kurtagu ,da barde inason ku
tattara ina ku ina ku ku bar min fada salin alin babu duka babu zagi,kuma ina fatan wannan
yazama na farko kuma ya zamo na karshe ',jiki a sanyaye suka tashi suka fice tare da yin
godiya da kuma neman gafara,mai martaba ya dubi Dr.ayuba yace 'kai kuma kaje in halinka ne
ka cigaba ,zakaga sakayya in kuma ba halinka bane Allah ya kare maka zuciyar ka ga aikata
aikin dana sani',Dr ayuba idanunsa na zubda hawaye yayi godia sosai tare da daukan
Alkawarin zai kasance mai yin aikinsa bisa doron gaskiya da tsoron Allah!
Mai martaba ya dubi sultan da ke kuka shabe shabe yayi masa nasiha mai ratsa jiki tare da
kuma ce masa ya fidda mata yayi aure,bamidele yatashi ya rungume bolaji bayan mai martaba
ya bashi hakuri ,tare da rokon alfamar ya yafe wa nawwara ,ita ma bolaji ta rokeshi da ya
yafewa nawwara ,bamidele ya yafe mata ita da fulani ,domin komai ya faru mukaddari ne kuma
rubbutacen al'amari ne !
☆ ☆ ☆ ☆
*GIDANSU HISHAM*
Misalin karfe 4:30pm su mai martaba suka isa gidansu hisham,da gudu su zuhra da zahra suka
rungume bolaji,haka zalika hajiya ,bayan an zazzauna ,sai mai martaba yafara da yi musu godia
,sannan ya basu labarin bolaji tun daga aurenta da hashim izuwa yau da komai ya zamto
bayyananne,hisham kwalla ce ta cika masa idanu ,shikenan ya rasa mujiba a karo na biyu,tashi
yayi ya bar falon,hashim ne yayi wa bolaji nuni da idanu da cewa ta bishi,a study room bolaji ta
iske hisham,idanunta cike da hawaye tace 'hisham ka kwantar da hankalinka ,mujiba taka ce
,baka rasa ni ba ,insha Allah zan kasance mata a gareka...',hisham ya katseta ta hanyar cewa
'mujiba ki daina yaudarar kanki ,stop getting ur hopes high,and stop giving me false hope ,kar ki
manta ke fa matar hashim ce ,u can never be mujiba ,u r bolaji ,so kawai go back to ur
husband",bolaji jikinta na rawa tace 'ni kuma bana sonshi ,ban taba sonshi ba ,kuma bana
tunanin zan so shi a rayuwata ',hisham yayi murmushi mai ciwo tare da cewa 'ki koyawa kanki
sonshi ,kuma so da yawa a rayuwa yana da kyau ka auri wanda yake sonka ba wai wanda kake
so ba,hashim yana sonki ,he deserves you ,ya cancanci zama miji a gareki ,nasan kina tunanin
cewa rayuwarki ta shiga garari saboda shi ,amma ina son ki bashi chance please yayi making
things up to u,idan har kika bari hashim ya subce miki ,wallahi kiyi asarar masoyi na gaskiya
.....',bolaji tace"wai shin meyasa ba zaka dubi halin da zuciyata take ciki ba.....",hashim ne ya
katseta ta hanyar cewa 'bolaji kar ki damu ,farin cikinki shine nawa ,bakin cikin ki shine nawa
,zanyi iya yin komai domin dawwamar da zuciyarki cikin farinciki na har abada ,kuma ni mai son
duk abinda kike so ne,don haka zan sawwake miki in har yin hakan kadai zai sa ki mallaki
hisham a matsayin mijin aurenki',hisham ya dubi hashim yace 'kar ka kuskura ka aikata wannan
mafi munin gaganci,bolaji taka ce ,you couples are meant for each other.....',hashim ya katseshi
ta hanyar cewa 'nagama magana dasu maimartaba ,na ce musu i'm willing to let bolaji free ,in
har ta bukaci hakan,domin so ba'a yi masa dole,ba a hada kiyayya da so ,she dont love me and
she will never ever love me',hisham ya dubi bolaji dake zubda hawaye yace 'bolaji i dont love
you ,i only love mujiba ,and you are not mujiba ,mujiba ta riga ta tafi ,na riga na rufe shafinta a
rayuwata,so for once ki budewa hashim zuciyarki,for once ki kalleshi a matsayin masoyinki ,for
once ki yi masa kallon mijinki ,ki bashi dama ya koya miki sonsa .... in har kika bari hashim ya
sake ki wallahi tallahi bazan taba yafewa kaina ba ,kuma ke ma bazan taba yafe miki ba ",yana
gama fadin haka ya fice daga studyroom din ya barsu !
Hishan yana fita ya tsaya passage din din da zai karasa parlour ,kuka ya kama yi kamar
karamin yaro yana mai cewa 'ya Allah ina mai mika godiyata a gareka a duk halin da na tsinci
kaina ,kai ka samin so a zuciyata ,kuma ina mai rokon ka saka min dangana , hakuri da juriyar
da zai maye gurbin so a zuciyata ",cike da tausayawa zahra da zuhra suka zo suka tsuguna
kusa dashi ,zuhra tana cewa 'yaya sham ka daina kuka haka ,kar kasa bolaji ta karaya itama
,sadaukarwa a so sai jarumi',zahra tace 'i'm very proud of you bro",ahaka suka lallashe shi
,suka tashi tare da komawa parlour ,hira ce ta barke tsakaninsu (mai
martaba,ummu,hisham,dad,hajiya,zuhra,zahra da badiyya),ana kuma jiran shigowar bolaji da
hashim!"
Hashim ya mikar da bolaji tsaye tare da goge mata hawayenta ,rungumeta yayi kamkam tare
da cewa "my better half can you feel my heartbeat ,kinji yadda soyayyarki ke wahalar da
zuciyata ,ban san da wacce kalma zanyi amfani ba wajen baki hakuri tare da gaya miki irin
dimbin son da nake miki amma i guess this will explain it better', ba shiri jikin bolaji ya mutu
murus domin kafafunta kasa daukarta sukayi ,ji tayi kamar ba 'a duniya take ba,sai da hashim
ya gaji dan kansa sannan ya dakatar da kiss din tare da cewa "my better half ....',kwantar da
kanta tayi akan kirjinsa ,ko motsin arziki ta kasa yi ,balle yasa ran zata tankashi ,murmushi yayi
tare da cewa 'OUR LOVESTORY IS SO UN-USUAL'!
Written by : ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 1:49 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~63~
Hashim Rungume da bolaji suka shigo parlour,ko ba'a fada ba daga ganinsu kowa yasan cewa
sun sasanta junansu.....!
♡♡♡♡♡KOMAI YAYI FARKO...♡♡♡♡♡
*BAYAN WATA DAYA*
Fulani tana mu'amala da kowa a fada tsakani da Allah ta watsar da duk wani makamin kiyayya
da ta dauka ta sawa zuciyarta,ta rungumi hanyar Allah,alaka tsakaninta da maimartaba ,hashim
da sultan ya ja baya ba kamar yadda suke da ba ,bolaji da ummu ne suke kokarin janta a jiki a
kullum !
Hisham da Sultan sun bawa bolaji wuka da nama game da zabin matayen da zasu aura ,babu
bata lokaci aka sanya ranar auren badiyya da hisham ,wanda kowa yayi murna da amanna da
wannan hadin da bolaji tayi, domin badiyya mace ce abar so ,batada makusa a halayya da
kuma sura,kuma su kansu hisham da badiyya sunyi na'am!
Bayan auren hisham da badiyya ,nawwara da mijinta bamidele sukayi haramar komawa
erin,inda bolaji da mijinta zasuyi masu rakiya,shima sultan ba 'a barshi a baya ba!
Ko da suka isa erin,kowa yayi mamaki da aka ce bolaji ce da fuskar mujiba,tabbas babu ta
yadda Allah baya tsarawa bawa lamarinsa!
Kwanan su uku a erin ,sultan da funmilayo soyayya mai karfi ta kankama tsakaninsu,wanda
babu bata lokaci,hashim ya shaidawa mai martaba ,mai martaba da tawagarsa sukazo suka
nemawa sultan auren funmilayo ,basu bar yankin erin ba sai da aka daura auren sultan da
funmilayo!
☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Bolaji ce zaune a gaban dressing mirror tana cire earrings dinta ,hashim ne ya fito daga
bathroom,kugunsa daure da towel ,rungumota yayi ta baya ,murmushi kawai tayi tare da cewa
'oga hitler when are getting back to work tunda yanzu everything is settled ',hashim ya cusa
kansa a wuyanta yana cewa 'what work?',bolaji ta amsa da cewa'aikin sojanka mana',hashim
yayi dariya tare da cewa 'ni da aikin soja har abada my better half,bana son abinda zai kara
nisanta ni da ke,nagama magana da mai martaba ,i will join sultan in the family business so that
we can manage it together',bolaji tace 'shikenan,Allah yasa hakanne ya fiya maka
alkhairi',hashim ya amsa da 'amin',tare da cewa "bolaji i know u r trying to force ur self to love
me by trying all the best u can to please me....',bolaji ce ta katseshi ta hanyar juyowa tare da
dora hannunta akan bakinsa tace 'ka daina fadin haka oga hitler,ni dai kawai ka cigaba da
kyautata min,ka cigaba da nuna min so da kulawa,da izinin Allah sonka zai yiwa zuciya mugun
kamu wanda kai da kanka sai kayi mamaki",sai kuma tayi murmushi tare da cewa 'wuyarta in
ganni da babynka',hashim idanunsa cike da kwalla yace 'my better half i love you with all my
heart,Allah ya nuna min ranar da zaki haifa min babies masu kama da asalin
fuskarki',kankameta yayi a jikinsa ,tare da cewa 'i will love my kids to learn the 2TRIBES from
you",bolaji ta maida masa martani da cewa "ni da kai zamu koya musu YARE BIYU"...............
"Indeed hashim and bolaji's love story was very un usual.... "
'ililee'
♡♡♡KARSHE♡♡♡
Created &written by : ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
☆☆☆☆☆☆☆
Godiya ta tabbata ga ALLAH daya bani ikon kammala labarin YARE BIYU !
ina kuma mika godiyata ga duk wanda ya karanta wannan labari (YARE BIYU),da kuma
wadanda sukayi supporting dina financially and emotionally,godiya gareku ga wadanda suka
taimaka min wajen koya min yaren (yoruba) tare da fada min duk abinda ya shafi (yoruba land),
bazan manta da ku ba! Duk wani mai sharhi,,jinjina ko kuma comment game da labarin,pls ya tuntubeni via whatsapp
:08125363328 ,ina jiran sakonninku !
Love you all
#ILILEE