Showing 42001 words to 45000 words out of 61652 words

Chapter 15 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4060

zuba godiya ba,ummu cewa take 'kar ka damu d'a na kowa
ne',ita kuwa bolaji mamaki ne yayi mata dirar mikiya bata taba tsammanin cewa komai zai zo da
sauki haka ba,jin muryar hisham yana cewa 'toh ranki ya dade bara ni na tafi ,godiya nake sosai
,Allah ya saka da alkhairi',tsam bolaji ta mi'ke tana cewa 'muje in raka ka yaya' ,fulani tayi murmushi tare da cewa 'sannu mai yaya',sannan ta dubi hisham tace'ka gaida
gida',sai kuma hisham ya kara yin kasa da kai yana cewa 'insha Allah gobe zan kawo mata

kaya da sauran abubuwan da....',da sauri fulani ta katseshi tare da cewa 'haba kai kuwa meye
zata nema a fadar nan ta rasa ,kai dai kawai je ka abunka',hisham ya kara yin godiya sannan ya
fice ,bolaji tana biye dashi,suna isa gun mota ,bolaji ta fara tafa hannayenta tare da cewa 'bravo
my love!',sannan ta cigaba da cewa 'kana ganin cewa babu matsala kuwa domin ni ina shakkar
wannan amincewar gaggawa matar nan tayi na zamana a gidannan',hisham yayi murmushi tare
da cewa'mujiba kar ki damu ,be optimistic mana,ni nan na yarda dasu kuma sanin kanki ne
cewa bazan barki a gun da za'a cutar dake ba ,kuma ko ma menene ki sa a ranki cewa muna yi
komai ne domin cikar burin mu na mallakar junanmu a matsayin ma'aurata',bolaji ta ja numfashi
tare da cewa 'toh shikenan Allah ya shige mana gaba ,amma fa idan naga babu wani cigaba
game da regaining memory dina ,toh a gaskiya kazo ka dauke ni',hisham yace 'kar ki damu ,i
will be coming to see u time to time,so u dont have to worry,insha Allah zamu dace ',bolaji tace
'toh yanzu in ka koma gida me zaka cewa su hajiya idan sun tambayeka ina nake',hisham ya
amsa da cewa 'kar ki damu ,i will deal with that',sannan ya bude mota yasa hannu ya dauko
wani kwali daga backseat ya mikawa bolaji yana cewa 'ga waya nan ,na hada komai,zamu
dinga communating,sannan kuma pls ki kula min da kanki ,ki kuma rike min amanar zuciyarki
',bolaji ta amshi kwalin tana cewa 'thanks dear,kuma insha Allah zan rike maka amanar
zuciyata ,ka cire shakku da waswasi a zuciyarka domin zuciyata taka ce kai kadai,ni taka ce ',a
haka sukayi sallama ya shiga mota ya tayar ,royal guards suke bude masa gate ya fice,bolaji ta
juya ta koma ciki zuciyarta dauke da kewar su zahra da zuhra!

A ranar Fulani da kanta takai bolaji gun mai martaba tare da yi masa bayani game da
ita,kasancewar mai martaba yasan wanene hisham tunda yana zuwa duba hashim lokaci lokaci
,kuma ya yaba da nutsuwarsa ,shiyasa ya amince tare da yin amanna da zamanta a gidan!
Fulani kuwa dakin da nawwara ta zauna tasa aka gyarawa bolaji,sannan ta umarci jakadiya
mara'kisiya da suje dakin hashim su kwaso kayan(lefen) bolaji daga wardrobe ,su zo su jera a
wardrobe din dakin mujiba(bolaji) domin tayi amfani dasu!
Sultan kuwa bai san wainar da ake toyawa ba a wannan ranar kasancewar tun safe ya fita
neman matar aurensa wato mujiba(bolaji),sai yamma ya dawo a gajiye likis ,dakinsa ya wuce ya
watsa ruwa sannan yabsakaya marasa nauyi,a lokacin kuwa bolaji tana sabon dakinta ,tana
warwara da sa'ka game da yadda zata fara tunkarar abubuwan da zasu sa tayi regaining
memory dinta ,daga karshe ta yanke shawarar shiga cikin hadimai da kuyangu,hakan yasa ta
yanke shawarar shiga cikinsu a wannan rana sukayi girki tare ,fulani tayi kokarin hanata amma
hakan ya gagara domin ta nuna mata cewa she loves what she's doing!

Bayan sallar isha gaba dayansu in an dauke hashim dake kwance a daki sai kuma sultan
wanda bai karaso ba
suka hadu akan dinning domin cin abincin dare ,jakadiya marakisiya tare da bolaji sukayi
serving ,sannan bolaji ta zauna kusa da kujerar fulani ,suka fara cin abinci,a lokacin sultan ya
karaso ya zauna ,bayan jakadiya tayi serving dinsa ya fara cin abinci ba tare da ya lura da
bolaji ba kasancewar yunwar da ya kwaso ,ita kuwa bolaji tun shigowarsa ta gane fuskarsa
,kuma sai da gabanta ya yanke ya fadi ! ,sultan kuwa sai da ya fara koshi sannan ya lura da
mujiba (bolaji),sauran kiris ya saki kofin juice din da yake kwankwada saboda rikicewa,mamaki
da dimuwa ,amma a take ya tattaro nutsuwarsa yaùi watsi da rikicewar da yayi ,amma ya kasa

dauke idanunsa akan ta ,gani ya ke tamkar in ya dauke idanunsa zata bacewa ganinsa ,ji yake
tamkar a mafarki yake ganinta, ganin ta tashi tana taya su jakadiya kwashe plates yasa ya
dawo hayyacinsa ,a lokacin ya lura ashe su mai martaba sun bar wajen ,ita ma bolaji juyawa
tayi hannunta dauke da cups ta wuce kitchen,cike da zafin nama ya bi bayanta,a kitchen ya
isketa ,a take ya bawa royal maids umarni da su fice daga kitchem din,sum sum suka fuce ya
rage daga shi sai bolaji ,ganin kowa ya fice yasa bolaji ita ma tayi hanyar fita,cike da zafin nama
sultan ya ri'ke mata hannu,cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba,hakan yasa shi ya juya ya
fuskanceta,hannunta ta fisge daga hannunsa ,ta fara ja da baya zuciyarta na dukan tara tara
,shi kuwa bin ta ya dinga yi yana mai jifanta da kallon so,har sai da bayanta ya hadu da bangon
kitchen din,hakan ya bashi daman sa hannunsa ya kewayeta ta hanyar dora hannunsa akan
bangon,bolaji kuwa duk tagama tsorata domin babu ta yadda zata iya guduwa,goshinsa ya
daura akan goshinta bakinsa na furta kalmara 'kin bani wahala!'


Written by;ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:21 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~50~

Bolaji ta rintse idanunta tare da kauda fuskarta tana cewa 'please ka bani hanya in wuce',sultan
yayi murmushi yace'in matsa kije ina?,bazan bari wannan karin ki subuce min ba ,ba tare da kin
gaya min sunanki ba',shiru bolaji tayi ba tare da tanka masa ba,hakan yasa sultan yace'zamu
kwana a haka kenan',kallonsa tayi da idanunta da suka canza launi suka koma jajawur ,murya a
raunane tace'mujiba',murmushi yayi tare da cewa'ina sonki mujiba,
Ban taba son wata diya mace ba a rayuwata sai ke,mujiba i love you,loving you was the best
thing that has ever happen to me,mujiba i love u! mujiba i love u !!! mujiba i love u !!! ,yana
gama fadin haka ,ya yi murmushi tare da bata hanya ta wuce,da sauri ta fice daga kitchen d'in
,sultan yabi bayanta ,murna fal cikin zuciyarsa yau gashi ga mujiba a gida daya,d'akin ummu
yaje,itace ta labarta masa batun zaman mujiba(bolaji) a fada ,shima anan yake shaidamata
itace matar aurensa dayake basu labarin ya gani kwanaki,ummu ta tayashi murna sannan tayi
masa alkawarin nema masa aurenta idan har tana sonshi kuma zata amince ta aureshi,kuma
a yanzu ya kamata ya nemi soyayyarta kafin ta koma gaban iyayenta,cike da murna ya wuce
dakinsa, a ranar yayi bacci har da munshari !

* * *
A bangaren hisham kuwa ,ko da ya iso gida ,hajiya ta nemi dalilin rashin dawowar
mujiba(bolaji),sai cewa yayi" muna zuwa asibitin,bayan ta shaidawa doctor ayuba abun dake
damunta ,sai ya bada umarnin sai dai a wuce da ita abuja gun wani kwararren doctor din
kwakwaluwa domin ciwon kanta ya shafi brain dinta ne ,shine kawai sai nayi waya office ,aka
turo officers daga can NGO , daman sune suka dauki nauyin duk wani health issue dinta,yanzu
haka sun wuce da ita abuja',hajiya ta kama baki tace 'yanzu daga zuwa asibiti sai tafiya abuja
,kuma kai baka rakata ba, kuma baka biyo ta gida ku tafi damu ba?',hisham ya marairaice tare

da cewa 'haba hajiya naga fa lokacin dana tsinto ta ni da officers din ne muka keta hazo da ita
muka je har kasar waje domin neman lafiyarta....',hajiya ta katseshi ta hanyar cewa 'naga
lokacin she was'nt part of the family ,and she was'nt our responsibility,but a yanzu she
is...',hisham yace'alright naji please ki kwantar da hankalinki mujiba is safe ,zata dawo ',hajiya ta
amsa da cewa 'shikenan daman kai ka kawota ,idan ma maidata kayi in da ka
daukota,matsalarka ce ',a lokacin dad ya tsoma baki ta hanyar cewa 'daman abinda ya kamata
kisa a ranki kenan tun ranar da ya kawo ta ,shi ke da iko da ita,amanarsa ce,mu yan taya riko
ne,Allah ya bata lafia ,yasa kuma sa ayi komai a sa'a',hajiya ta amsa da 'amin',zuhra da zahra
kewar mujiba(bolaji) duk yayi musu katutu a zuciya,ji suke tamkar ta tafi kenan,bazata kuma
dawo wa ba,kamar yadda mujibar asali ta tafi ta barsu! A haka zancen mujiba ya mutu a
gidan,washegari hisham ya shaida musu cewa an wuce da mujiba(bolaji) u.s.a domin further
treatment,ci kanka babu wanda yace masa,shi kansa bai ji dadi ba,amma ya zama tilas hakan
ya faru domin cikar burinsu shi da bolaji na muradin mallakar junansu a matsayin
ma'aurata,kuma duk ranar da mujiba (bolaji)tayi regaining memory dinta ,ranar zai shaida musu
gaskiyar inda mujiba taje ,amma for now he has to keep this as a secret !

* * *
Washegari da safe bayan an gama yin breakfast ,fulani taja hannun bolaji ta kai ta dakin da
hashim yake kwance ,suna shiga dakin gaban bolaji ya tsinke ya fadi domin tabbas in bata
manta ba wannan shine dakin da tagani a mafarkinta,fulani ce ta katse mata tunaninta ta
hanyar cewa 'mujiba zan baki wani gajeran labari ,wanda nake fatan zaki share min
hawayena,ki kuma cika min burina na ganin cewa souldear yayi aure',sannan ta cigaba da cewa
'wannan da kika gani a kwance sunansa hashim,d'ana ne kuma ina kaunarsa fiye da kowa a
duniyar nan ,rayuwarsa ta lalace ne a lokacin da ya auro YARE wato BAYARABIYA a matsayin
matarsa ,duk yadda na kai da tsanar YARE haka na hakura ya aureta domin naga yana mata
wani irin mahaukacin so wanda daga alamu, asiri tayi masa ,haka muka zauna da ita cikin
aminci da yarda ,amma duk da haka sai tayi mana butulci ta gudu ,sai daga baya aka tsinto
gawarta wanda sanadiyar ganin gawarta hashim ya zama haka ya shiga wannan halin na
matacce a raye ,naso aura masa diyar yayata amma fafur ta ki amincewa saboda taganshi a
haka',fulani ta goge hawayen idanunta tare da dafa kafadar bolaji tace 'ina son ki share min
hawayena ,ki auri d'ana ,domin a jiya ina dora idanuna a kanki jikina ya bani cewa kaddara ce ta
kawo min ke ,kuma ke ce zaki share min hawayena,bazan miki tilas ba,amma kije kiyi
tunani,kuma ina son ki dinga shigowa kina kula dashi ,a haka sha'kuwa zai shiga
tsakaninku,domin ina son aje a nema masa auren ki a ranar da kika koma gidanku',fulani tana
gama fadin haka ,ta fice ta bar bolaji a tsaye tana warwara da sa'ka ,ita a yanzu danasanin
zuwanta take yi,wannan wani irin azal ne ,ga abbas(sultan) da yace yana sonta,ga kuma
wannan hashim din da uwarsa take son kakaba mata shi,ga kuma masoyinta hisham da tayi wa
alkawari,shin menene mafita ? Ta tambayi kanta tare da cewa 'ya Allah ka dawo min da memory
dina domin sanin ko ni wacece? '!


A daki ummu ta iske fulani ,bayan sun dan taba hira ,sai ummu tayi gyaran murya tare da cewa
'maganar d'ana nazo yi miki,ashe mujiba ce matar aurensa da ya gani rannan yake bamu

labari,shine nace yanzu me zai hana idan mujiba ta koma gidansu aje anema masa aurenta
,domin a gaskiya yarinyar ta kwanta min',Fulani tayi kasake tana kallon ummu ,sannan tayi
kwafa tace 'kin ga rabu da shashashan yaron nan,ni na riga nayiwa d'ana kamun mujiba
,sanadiyar da yasa na amshi amanarta kenan a jiya ,domin mujiba da my souldear ta
dace',ummu da mamaki ya cikata tace 'haba fulani wani irin magana ne haka ?,ya zaayi a hana
mai lafiya auren mujiba sannan abawa mara lafiyan da ba'a san ranar da zai warke ba
aurenta...',fulani ta katseta ta hanyar cewa 'hashim dina zai warke ,ni nasan zai warke ,kuma shi
zai auri mujiba,kuma shi sultan din zai zo ya sameni,idan ma shine ya turoki zanyi maganinsa
,ya zama dole ya hakura da mujiba idan har ni dinnan ina da iko dashi' ummu idan ranta yayi
dubu ya baci domin lamarin fulani ya fara bata mamaki ,hakan yasa ta mike tsaye a fusace tare
da cewa 'fulani ya isa haka,ke a kullum kin fi son ki yanke hukunci ba tare da kinyi la'akari da
abin da zaije ya dawo ba,toh tunda abin yazama iko da tutiya,naga nima hashim d'ana ne
ko,kuma nice na dau cikinsa na kuma haife,toh ki ji da kyau idan har ina da iko akan hashim to
wallahi bazai auri mujiba ba,sultan ne zai aureta',ita ma fulani ta mike tsaye tare da cewa 'haka
zalika shi ma sultan bazai aureta ba idan har ni ce uwarsa kuma idan har zan gaya masa ya
bi,toh bazai auri mujiba ba,my souldear ne zai aureta,ki rubuta ki ajje!'

Written by: ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/18, 7:18 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~51~

Fulani na gama fadin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin!
Jiki a sanyaye Bolaji ta dubi hashim dake kwance idanunsa a bude tamkar kayi masa magana
ya amsa ,fes fes dashi ,sai taji kawai ya bata tausayi,ta kuma kare godewa Allah da ya barta da
lafiyarta har take iya sarrafa gangar jikinta,a cikin wannan yanayi kuyanga badiyya ta shigo
dakin ta sameta ,murya a sanyaye ta dubi bolaji tare da cewa 'ranki shi dade,yarima sultan ne
yake bukatar ganinki a lambu','me zanyi masa ?',bolaji ta tambaùeta ,'ban sani ba,yace dai in
taho da ke','bazataje ba',fulani ta bada amsa ,sannan ta bawa badiyya umarnin fita daga dakin!
Fulani ta dubi bolaji tare da cewa 'menene tsakaninki da sultan?,'babu!' Bolaji ta bata amsa
,fulani ta cigaba da cewa'toh ina son hakan ya cigaba da kasancewa tsakaninku,domin bana
bukatar soyayya tayi tasiri a tsakaninku ,kamar yadda na gaya miki dazu hashim zan nemawa
aurenki da zarar yayanki ya maida ki gida',bolaji kasa tankawa tayi hakan yasa ta fice ,tana isa
dakinta ,wayar da hisham ya bata ya fara ringing ,jikinta na rawa ta dauki wayar ta amsa tare da
yi masa sallama,bayan ya amsa sai ya jefeta da tambayar'yanaji muryarki haka',ta budi baki da
niyyar labarta masa abinda ya faru ,sai wata zuciyarta ta kwa'beta da cewa'kar ki dagawa
bawan Allah hankali,tunda ke kanki kinsan cewa ta shi ce ke,da zarar yazo ya daukeki kun
koma gida shikenan',sai kawai tace 'daga bacci na tashi,yasu hajiya da zuhra"',hisham ya amsa
da 'duk suna lafia ,sai dai fa duk sunyi fushi dani,gani suke tamkar na rabaki dasu',bolaji
tace'ayya nima nan i'm already missing them,but soon zan dawo garesu',sannan suka cigaba
da hirar so, daga karshe sukayi sallama !
Sultan ne yayi sallama ya shigo dakin,bolaji ta amsa tare da janyo hijab ta sa,idanu ya watsa

mata yana mai jifanta da wani irin shu'umin murmushi,sannan yayi gyaran murya tare da cewa
'mujiba kenan,meyesa kike son wahalar da zuciyata ne ,ni mai kaunarki ne,ki bani dama',bolaji
ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa!
Fulani ce ta shigo dakin dalilin tasa jakadiya tazo ta sanar da ita a duk lokacin da taga
shigowar sultan dakin mujiba(bolaji)!
Murya a kausashe fulani ta kira sunansa tare da cewa 'kai sultan ka fita idanuna in rufe
,ummunka bata fada maka sakona ba ,toh hashim zan aurawa mujiba,domin kai baka dace da
ita ba,kuma in kace zaka yi jayayya ga hukuncin dana yanke ,wallahi zan tsine maka albarka ka
bi duniya',bolaji ce ta mike a razane tare da cewa'hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya zama dole
in bar muku gida,haka kawai daga jiya zuwa yanzu zuwana ya fara haifar da fitina',fulani ta
dubeta tace 'ki kwantar da hankalinki mujiba,babu in da zakije ,kiyi zamanki har izuwa ranar da
yayanki zai zo ya tafi dake ',sannan ta maida dubanta ga sultan tace 'kai kuma dafatan zaka
daina takura mata,ka fita daga harkarta ,ita ma ba sonka take ba',a fusace sultan ya bar dakin
ba tare da yace uffan ba,hakan ya bawa fulani daman rarrashin bolaji,amma fafur bolaji taki
amincewa da zaman fadan,daga karshe sai tace zata koma bangarensu kuyangu da
zama,fulani ta amince!
A kwana a tashi yau satin bolaji daya a fada ,ita da kuyanga badiyya sun zama kawayen juna
,tare suke zama suyi hira kasancewar dakinsu daya,fulani bata daina jan bolaji a jiki ba ,domin a
kullum sai ta aika an kira mata ita,haka zalika ummu ita ma tana jan bolaji a jiki tana yi mata
nasiha a ko dayaushe akan ta guji son zuciya ,kuma ta dinga sanya Allah a lamarinta tare da
neman zabinsa a ko dayaushe,hisham kuwa suna waya akai akai ,kuma a kullum sai ya
tambayeta ko an dace ,ita kuma sai tace masa har yanzu shiru no response!
Sultan kuwa takanas yaje ya samu fulani a daki ya shaida mata cewa 'wallahi tallahi idan har
kika cigaba da shiga tsakanina da soyayyar mujiba wallahi nima zan shiga tsakaninki da mai
martaba da hashim wajen tona asirin abunda kika aikata ga bolaji',fulani bata san lokacin da ta
dauke fuskar sultan da mari ba,shi kuwa yayi murmushi tare da cewa 'ni dai nagama magana,ki
fitar da kanki daga sha'ani na da mujiba',dalilin da yasa fulani tayi sanyi tare da fitar da kanta
daga tsabgar sultan,tana ji tana gani sultan ya fara neman soyayyar mujiba(bolaji),duk da ita ma
bolaji bata bashi fuska ba,dawowar memory dinta ne ya dameta!

Written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL=YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~51~

Fulani na gama fadin haka ta mike tsaye ta fice daga dakin!
Jiki a sanyaye Bolaji ta dubi hashim dake kwance idanunsa a bude tamkar kayi masa magana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login