Showing 45001 words to 48000 words out of 61652 words
ya amsa ,fes fes dashi ,sai taji kawai ya bata tausayi,ta kuma kare godewa Allah da ya barta da
lafiyarta har take iya sarrafa gangar jikinta,a cikin wannan yanayi kuyanga badiyya ta shigo
dakin ta sameta ,murya a sanyaye ta dubi bolaji tare da cewa 'ranki shi dade,yarima sultan ne
yake bukatar ganinki a lambu','me zanyi masa ?',bolaji ta tambayeta ,'ban sani ba,yace dai in
taho da ke','bazataje ba',fulani ta bada amsa ,sannan ta bawa badiyya umarnin fita daga dakin!
Fulani ta dubi bolaji tare da cewa 'menene tsakaninki da sultan?,'babu!' Bolaji ta bata amsa
,fulani ta cigaba da cewa'toh ina son hakan ya cigaba da kasancewa tsakaninku,domin bana
bukatar soyayya tayi tasiri a tsakaninku ,kamar yadda na gaya miki dazu hashim zan nemawa
aurenki da zarar yayanki ya maida ki gida',bolaji kasa tankawa tayi hakan yasa ta fice ,tana isa
dakinta ,wayar da hisham ya bata ya fara ringing ,jikinta na rawa ta dauki wayar ta amsa tare da
yi masa sallama,bayan ya amsa sai ya jefeta da tambayar'yanaji muryarki haka',ta budi baki da
niyyar labarta masa abinda ya faru ,sai wata zuciyarta ta kwa'beta da cewa'kar ki dagawa
bawan Allah hankali,tunda ke kanki kinsan cewa ta shi ce ke,da zarar yazo ya daukeki kun
koma gida shikenan',sai kawai tace 'daga bacci na tashi,yasu hajiya da zuhra"',hisham ya amsa
da 'duk suna lafia ,sai dai fa duk sunyi fushi dani,gani suke tamkar na rabaki dasu',bolaji
tace'ayya nima nan i'm already missing them,but soon zan dawo garesu',sannan suka cigaba
da hirar so, daga karshe sukayi sallama !
Sultan ne yayi sallama ya shigo dakin,bolaji ta amsa tare da janyo hijab ta sa,idanu ya watsa
mata yana mai jifanta da wani irin shu'umin murmushi,sannan yayi gyaran murya tare da cewa
'mujiba kenan,meyesa kike son wahalar da zuciyata ne ,ni mai kaunarki ne,ki bani dama',bolaji
ko kallonsa batayi ba bare yasa ran zata amsa masa! Fulani ce ta shigo dakin dalilin tasa jakadiya tazo ta sanar da ita a duk lokacin da taga
shigowar sultan dakin mujiba(bolaji)!
Murya a kausashe fulani ta kira sunansa tare da cewa 'kai sultan ka fita idanuna in rufe
,ummunka bata fada maka sakona ba ,toh hashim zan aurawa mujiba,domin kai baka dace da
ita ba,kuma in kace zaka yi jayayya ga hukuncin dana yanke ,wallahi zan tsine maka albarka ka
bi duniya',bolaji ce ta mike a razane tare da cewa'hasbunallahu wa ni'imal wakil, ya zama dole
in bar muku gida,haka kawai daga jiya zuwa yanzu zuwana ya fara haifar da fitina',fulani ta
dubeta tace 'ki kwantar da hankalinki mujiba,babu in da zakije ,kiyi zamanki har izuwa ranar da
yayanki zai zo ya tafi dake ',sannan ta maida dubanta ga sultan tace 'kai kuma dafatan zaka
daina takura mata,ka fita daga harkarta ,ita ma ba sonka take ba',a fusace sultan ya bar dakin
ba tare da yace uffan ba,hakan ya bawa fulani daman rarrashin bolaji,amma fafur bolaji taki
amincewa da zaman fadan,daga karshe sai tace zata koma bangarensu kuyangu da
zama,fulani ta amince!
A kwana a tashi yau satin bolaji daya a fada ,ita da kuyanga badiyya sun zama kawayen juna
,tare suke zama suyi hira kasancewar dakinsu daya,fulani bata daina jan bolaji a jiki ba ,domin a
kullum sai ta aika an kira mata ita,haka zalika ummu ita ma tana jan bolaji a jiki tana yi mata
nasiha a ko dayaushe akan ta guji son zuciya ,kuma ta dinga sanya Allah a lamarinta tare da
neman zabinsa a ko dayaushe,hisham kuwa suna waya akai akai ,kuma a kullum sai ya
tambayeta ko an dace ,ita kuma sai tace masa har yanzu shiru no response!
Sultan kuwa takanas yaje ya samu fulani a daki ya shaida mata cewa 'wallahi tallahi idan har
kika cigaba da shiga tsakanina da soyayyar mujiba wallahi nima zan shiga tsakaninki da mai
martaba da hashim wajen tona asirin abunda kika aikata ga bolaji',fulani bata san lokacin da ta
dauke fuskar sultan da mari ba,shi kuwa yayi murmushi tare da cewa 'ni dai nagama magana,ki
fitar da kanki daga sha'ani na da mujiba',dalilin da yasa fulani tayi sanyi tare da fitar da kanta
daga tsabgar sultan,tana ji tana gani sultan ya fara neman soyayyar mujiba(bolaji),duk da ita ma
bolaji bata bashi fuska ba,dawowar memory dinta ne ya dameta!
Written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/18, 7:19 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~52~
Kamar kullum cikin dare bolaji da badiyya suna kwance suna hira kafin bacci ya riskesu ,sai
bolaji ta tashi ta shiga toilet din dake cikin dakin, baùan shigarta da second 40,sai taji kamar
motsi irin na fitar numfashin wahala,da hanzari ta gama abinda take ta fito ,me zata gani kuwa
,badiyya ta gani kwance ,barde ya rufe mata baki da hannunsa yana kokarin keta mata haddi
,tuni kan bolaji yafara juyawa wadansu al'amura da suka taba shudewa a rayuwarta a baya
suka dinga dawo mata (wato arangamarta da sultan a ranar da zai mata fyade) amma hakan
bai hanata yunkurin dauko wani katon wood flower vase dake gefen wardrobe din dakin, tare da
sakarwa barde shi akai ,ji kake tum! ,hakan ya biyo da daukewar numfashinsa ba tare da ya kai
ga cimma burinsa ba akan badiyya ,bolaji kuwa juwa ce ta dauketa ,hakan yasa ita ma ta fadi a
wajen a sume!
Badiyya kuwa rudewa kam ta gama yi ,domin rasa yadda zatayi dasu tayi,da kyar ta samu ta
tattaro nutsuwarta ta shiga toilet da debo ruwa tazo ta shafawa bolaji a fuska,bolaji ta sauke
ajiyar zuciya tare da mikewa zaune tana dafe da kanta ta dubi badiyya tare da cewa 'ina
BOLAJI? MATAR HASHIM?,badiyya ta bude baki cike da mamaki tare da cewa 'mujiba wacce
irin tambaya ce wannan ,meye had'inki da ita?',bolaji ta dubeta tare da cewa 'wannan bai
shafeki ba ki gaya min gaskiya',sai badiyya tace 'toh matar yarima dai guduwa tayi a hanyarta
na guduwa hatsari ya riskesu, hakan yayi sanadiyar mutuwarta',bolaji tayi murmushi mai kama
da yake sannan tacee'shikenan yanzu ki je bangaren royal guards ki kirawo su ,su zo su fice da
wannan',jiki na rawa badiyya ta fice taje ta kira su kurtagu da sauransu ,sukazo suka fice da
barde wanda har yanzu bai farfado ba!
Bayan an fice dashi sai bolaji ta dubi badiyya bayan ko wannensu ya zauna akan
gadonsa,murya a sanyaye bolaji ta fara cewa'badiyya a yadda na daukeki a kwanakin nan,ban
taba zatan zaki yi min karya ba ,amma bara na fayyace miki wani boyayyen al'amari a game
dani',badiyya jiki a mace ta rafka tagumi tare da zubawa bakin bolaji na mujiya',bolaji ta cigaba
da cewa 'faruwar al'amarin da ya wakana tsakaninki da barde a d'azu yasa hakan ya zama
sanadiyar dawowar memory dina ,wanda na rasashi na tsawon lokaci ta dalilin jefar dani dasu
barde da kurtagu sukayi a daji mai tattare da tarin duwatsu.....',badiyya cike da mamaki ta katse
bolaji ta hanyar cewa 'ke kuwa mujiba meye hadaki da barde da kurtagu,naga baki dade da
zuwa fadar nan ba..',bolaji tayi murmushi wanda ya taho da zubar hawaye sannan tace 'badiyya
ki nutsu kiji labarin da zan baki domin BOLAJI ce a gabanki mai dauke da fuskar MUJIBA'(nan
ta kwashe labarin yadda suka kwashe da sultan a ranar da yazo yi mata fyad'e,da kuma lokacin
data farfado ta ganta a hannunsu barde ,har izuwa lokacin da fulani ta fara yanka mata fuska da
aska wanda hakan yayi sanadiyar sumarta ,kuma bata kara sanin in da kanta yake ba sai ranar
data farfad'o a matsayin wacce tayi loosing memory dinta,zamanta a asibitin,tafiyarta kasar
waje tare da hisham domin gyara mata fuska,canjin fuskarta,rayuwarta a gidansu hisham da
kuma zuwanta fada domin sanin ko wacece ita,soyayyar da sultan yake ikirarin yake mata da
kuma auren hashim da fulani take so tayi ),badiyya mamaki ne ya cikata ,domin tabbas zancen
mujiba(bolaji) akwai kamshin gaskiya ,amma duk da haka sai tayi ajiyar zuciya tare da cewa 'toh
a gaskiya mujiba ranar da matar yarima aka ce ta bata a fada ,bazan manta ba a ranar mu
kazo wucewa tare da fulani ta gaban dakinsu,sai kawai mukaji karar bugu,sai fulani ta bamu
umarnin tsayawa sai ita ta shiga ciki,bayan wasu mintuna sai tafito ta sallami kowa tace ni in
tsaya ,sannan ta bani umarnin in kirawo jakadiya,a gaban idonaa ta umarci jakadiya akan taje ta
kirawo mata barde da kurtagu,ni kuma tace in biyota cikin dakin,da muka shiga na hango matar
yarima a kwance daure da towel cikin rashin hayyacci,sai kuma sultan a tsaye a gefe cikin
yanayi na tashin hankali,ni dai umarni fulani ta bani wai in sanyawa matar yarima doguwar
riga,ina gama saka mata tace min na tafi. toh nidai daga lokacin sai zancen bacewarta ne ya
ne ya karade fada(ta labarta dawowar hashim,kawo gawar da fulani da tayi a matsayin gawar
bolaji da kuma shiga coman da hashim yayi sanadiyar ganin gawar)',badiyya ta tsurawa bolaji
idanu kamar tana son karanto wani abu a tattare da ita ,sannan tace 'toh yanzu dai abin nufi
kenan a nan shine fulani,nawwara ,jakadiya,barde da kurtagu suna da sa hannu wajen kawar
da matar yarima daga fadar nan?', ',sai kuma tayi ajiyar zuciya tare da dafe kuncinta sannan ta
cigaba da cewa ' idan har kece matar yarima ,toh gawar waye fulani ta kawo a matsayin gawar
Bolaji?' Bolaji tabata amsa da cewa 'amsar da nima nake neman amsarta kenan,amma a yanzu
ya zama dole ki yarda dani ,wallahi tallahi nice bolaji matar hashim',a take ta bawa badiyya
labarin asalinta ,jifan da maami tayiwa maimartaba,fansar hashim...........har izuwa aurensu !
Badiyya tayi jim tare da yin wasu tunane tunane sannan tace 'toh ranki shi dade idan ni na
amince cewa kece matar yarima ,taya zaki gamsar da sauran mutane har su yarda cewa ke din
ce',bolaji tashi tayi daga kan gadonta tazo kusa da badiyya ta zauna ,sai ta dafata tare da cewa
'ni duk wannan bai dameni ba ,abin da ya dameni shine auren hashim dake kaine ..'
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/18, 7:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~53~
Badiyya ta katseta ta hanyar cewa 'auren dake kanki ba matsala bane ,domin mijinki kawai zaki
komawa,dadin abun ma ,bakiyi aure kan aure ba',bolaji ta share hawayen daya zubo mata tare
da cewa 'ya zanyi da hisham,me zance masa ,ta ina zan fara shaida masa cewa ni matar aure
ce ',sannan ta dubi badiyya cikin ido tare da cewa 'wallahi badiyya da babu auren hashim
akaina ,babu abinda zai hanani auren hisham,domin hisham ya cancanci in aureshi,kinga ni
wallahi da hashim zai sawwake min dana huta ,domin hisham .....',badiyya ta tare numfashinta
tare da cewa 'dakata ranki shi dade kar ki ma soma wannan zancen ,ki fa tuna ke matar aure ce
,kuma ko ba komai ya kamata ki bawa aure darajar sa,kuma yarima yana sonki ,ni a ganina duk
wani masoyinki ya biyo bayan yarima ,kuma ko ba komai yakamata yarima ya samu tausayawa
daga gareki', bolaji ta yi jim sannan tace 'har ga Allah na tausayawa hashim musamman ayanzu
da yake kwance tamkar matacce',badiyya tace 'addu'a zaki cigaba dayi masa ,Allah ya tashi
kafadarshi....' , bolaji ta amsa da 'amin',tare da kuma tambayar badiyya da cewa 'ina nawwara
kuwa?,zan so in ganta.. ',badiyya tayi kwafa tare da cewa'nawwara ta zama sirikar ki domin
yayanki take aure ,tana can garinku',bolaji ta ware idanu tare da cewa 'kina nufin nawwara ta
zama matar bamidele?",nan badiyya ta kwashe labarin soyayyar nawwara da bamidele da
kuma tawayen da nawwara tayi wa fulani da sauransu ta labartawa bolaji!
Bolaji ta jinjina lamarin tare da cewa 'amma ya kamata ace nawwara ta shaidawa mijinta
gaskiyar al'amari game da bacewata daga fada',badiyya tace 'tabbas da ace ta fada mai
gaskiya,ina ga da har yanzu ana kan bincike domin nasan bazai dau abin da wasa ba,amma
inaga ita ma shirun tayi kamar yadda sauran sukayi shiru',bolaji ta amshe da cewa'amma kuwa
da nawwara taci amanar so...',badiyya ta katseta ta hanyar cewa'kar kiga laifinta,domin zai iya
yiwuwa tayi shiru ne bisa rashin sanin kina raye ko a mace ,kuma sanin kanmu ne aurenta da
yayanki zai iya zama matacce da zarar ta gaya masa gaskiya,kinga kenan soyayya ce zata sa
ta gimtse bakinta domin masoyi yana iya yin komai don ganin bai rasa masoyinsa ba',bolaji tace
'kuma hakane',sannan to dora da cewa 'toh ni dai yanzu na rasa yadda zanyi ,ta ina zanfara
fuskantar gyara rayuwata da fulani ta rugurguza mini da makircinta? ',badiyya ta dubeta tare da
cewa'ranki shi dade....!',bolaji ta dakatar da ita ta hanyar cewa 'kicigiba da kirana mujiba
kawai',badiyya tace 'toh ',sannan ta cigaba da cewa 'da farko ya kamata mijinki ya ci darajar
aure ya samu kulawarki,domin kulawarki gareshi zai iya zamowa silar tashinsa ',bolaji tace 'toh
zan jarraba,hisham kuma fa ya zanyi dashi',badiyya tace kawai ki gaya masa
gaskiya,saboda....',bolaji ta tari numfashinta ta hanyar cewa'bazan iya ba ,bazan iya jurar ganin
hisham cikin tashin hankali da bakin ciki ba,ya rasa mujiba a karo na farko,da wani idon zan
dubeshi kuma da wani bakin zan shaida masa cewa ya rasa mujiba a karo na biyu',sannan ta
fashe da kuka mai tsuma zuciya domin har ga Allah zuciyarta na kaunar hisham,cike da
tausayawa badiyya tace 'toh Allah ya kawo miki mafita a cikin wannan al'amarin,tabbas hisham
ya cancanci a tausaya masa',sannan tace 'game da sultan kuwa kawai ki watsar da lamarinsa
.....',bolaji ta amshe da cewa 'kyaleni dashi zanyi maganinsa ,wallahi sai na wahalar dashi,sai na
dandana masa bakinciki,sai rayuwarsa ta salwanta kamar yadda ya zama sila ga salwantar
tawa rayuwar',badiyya ta jinjina al'amarin sannan tace 'toh mu barwa gobe komai ,domin dare
yayi sosai ,ya kamata mu kwanta haka ',bolaji ta tashi ta koma kan gadonta ta kwanta ,zuciyarta
na tufka da warwara,badiyya ta kashe wuta sannan ta kwanta ita ma ,bayan minti daya sai
badiyya tace 'kinyi bacci?', da "a'a",bolaji ta amsa ,sai badiyya tace'kinsan me yake bani
mamaki?',bolaji tace'sai kin fada',badiyya tace 'kin bar fada a matsayin BAYARABIYA ,gashi
kuma kin dawo a matsayin BAHAUSHIYA!',bolaji tace'ikon ALLAH kenan',badiyya tace'tabbas
zancenki dutse,babu ta yadda Allah baya tsarawa bawansa lamarinsa,ke d'aya kin zama mai
suna biyu',bolaji tace 'da kuma YARE BIYU!
a haka gwanin sata ya sace su!
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/18, 7:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~54~
Washegari da safe bayan an gama yin breakfast ,bolaji taje daki ta samu fulani,ko da tashiga
fulani ta dubeta tare da yin murmushi tace'mujiba yaya dai?',bolaji ta gimtse bakin cikinta tare
da shimfida wani irin malalacin murmushi akan fuskarta tace' magana nake son muyi in bazaki
damu ba',fulani ta sallami ko wacce kuyanga dake cikin dakin ,sannan ta dubi bolaji tace'ke
nake sauraro',bayan sun zauna akan couch,bolaji tayi gyaran murya tare da cewa'game da
batun hashim ne,na amince zan aure shi.....',fulani murna fal cikinta ta rungumo bolaji tana
cewa ' wallahi mujiba kin gama yimin komai....... ',bolaji ta katseta ta hanyar cewa'ina son
kulawarsa ya dawo hannuna,kuma zan koma dakinsa da kwana',fulani tayi jim kamar tana
tunani ,bolaji ta katse mata tunani ta hanyar cewa'me kike tunani?,ko kina tsoro ne?',fulani tayi
zuru ba tare da tanka mata ba,bolaji tayi murmushin yake tare da kada kanta sannan tace.'ki
kwantar da hankali ,babu abinda zai faru tsakanina da hashim,ki yarda dani,ki cire zargi daga
zuciyarki,bazan cutar dashi ba', fulani tace'nifa ba zargin komai nake ba,na yarda da hashim ko
dayake da lafia mace bata dameshi ba ,balle kuma yanzu da baida lafia,kawai abin da nake
tsoro shine kar mai martaba yaji kina kwana a dakin,muzo mu shiga uku',bolaji ta dubeta tare da
cewa
a zuci 'zaki shiga miliyan uku ne a ranar da asirinki ya tonu',amma a zahiri sai tace 'shikenan
zan dinga kula dashi kawai ,domin ina son in shaku da mijin da zan aura ',fulani tace'shikenan
mujiba,kinga kenan da zarar kin koma gida sai ayi zancen aurenku',nan suka cigaba da hira
fulani tana mai bawa mujiba(bolaji) labarin (karya da gaskiya)bolaji! Ganin hirar bazata kare ba yasa tayiwa fulani sallama,hakan yasa fulani tace 'muje in rakaki
dakin hashim',suna shiga dakin suka tadda hadimai maza guda uku da suke kula dashi ,suna
goge masa jiki da towel da ruwan dumi,daga vest sai short knicker ne a jikinsa,duk sunyi kalar
datti ,kwalla ya cikowa bolaji a ido,a wayance ta goge ,sannan ta dubi fulani tace 'kice musu su
tafi',fulani cike da mamaki ta umarci hadiman da su fice,sannan bolaji tace mata ''ke ma ki fita!'
,fulani cike da takaici tace'in fita inje ina?',sai bolaji ta juya da niyyar fita ,fulani ta tsaidata tare
da cewa 'haba mujiba,kar muyi haka da ke,ina zaki je','fita zanyi daga dakin tunda har yanzu
baki aminta dani ba,ina son kasancewa da mijina,domin babu wanda ya dace ya bashi kulawa
face ni matarsa',fulani ta maimaita kalmar 'mijinki? matarshi?',bolaji ta amsa da cewa'matarsa
mana,tunda shine mijin da zan aura ,ya kamata tun yanzu in fara koyan yadda zan kula da shi
tun kafin muyi aure,idan kuma baki aminta dani ba shikenan,sai na bar miki danki kawai,naga
macen da zata aureshi a haka',fulani ba tace uffan ba ,da hanzari ta fice daga dakin!
Tana fita bolaji ta sawa kofar dakin key ,sannan ta wuce toilet din dake cikin dakin, ta hado
ruwan dumi a bowl tare da zuba antibacterial da bathing perfume ,sannan ta zo ta ajje a gefen
gadon da hashim ke kwance ,cike da tausayawa tasa karfinta ta cire masa singlet din da short
nicker,sannan tasa towel a ruwan tana goge masa jikinsa ,hawaye na zuba daga idanunta,yau
oga hitler ne a kwance tamkar matacce ,inda ranka...
A haka tagama gogeshi,sannan ta dauko masa singlet da vest masu kyau ta feshesu da turare
ta saka masa,ta shafa masa lotion,ta taje masa kai,ta gyara masa kwanciyarsa ,ta maida bowl
da towel din toilet,sannan ta dawo ta kwanta a gefensa tana