Showing 6001 words to 9000 words out of 61652 words

Chapter 3 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4054

ta bar fadar nan a yau
d'innan,domin zamanta a fadar ya 'kare a
yau,tunda har ta kai ka fara hai'ke mata ,toh dole
inyiwa tufkar hanci!'
Ta juya ta fita daga d'akin tare da nufar gun
hadiman data dakatar a waje!
Dubansu tayi
a kausashe tace 'kuna iya tafiya,ke kuma badiyya
ki tsaya' ,sum sum sum suka watse,sai wacce ake

kira da badiyya ce kawai ta tsaya,kanta a sunkuye
tace 'ranki shi dad'e,ALLAH ùa ja zamaninki'
Fulani ta katseta da cewa 'ki hanzarta yanzu kije ki
kirawomin mara'kisiya[jakadiya]' ,'an gama ranki
shi dad'e' badiyya ta fad'i tare da barin wajen,cikin
mintuna da basu wuce d'aya ba,sai ga kuyanga
badiyya tare da jakadiya mara'kisiya!
a gaban fulani ta rusuna tana zabga gaisuwa!
Fulani da dubi ba'kin fuskarta tace 'su mai
martaba basu dawo daga rangadi ba ko' ,'eh ranki
shi dad'e ,sai zuwa yamma' mara'kisiya ta amsa.
Fulani tace 'toh tashi kije ki kira min barde da
kurtagu yanzunnan' sannan ta dubi badiyya tace'ke
kuma biyo ni',da hanzari mara'kisiya ta tashi ta
fice domin cika umarnin uwargijiyarta,ita kuma
badiyya ta bi bayan fulani suka shiga d'akin bolaji!
Sultan yana nan inda fulani ta barshi a tsaye
,hankalinsa a tashe ganin bolaji bata farfad'o ba!
Fulani ta umarci kuyanga badiyya da ta d'auko
doguwar riga ta sanyawa Fulani ta umarci kuyanga
badiyya da ta d'auko doguwar riga ta sanyawa
bolaji!
Cikin minti biyu badiyya ta aikata hakan!
Fulani tace mata 'zaki iya tafiya' ,a bakin 'kofa
badiyya tayi kici6us da jakadiya mara'kisiya tare
da barde da kurtagu,cike da azama badiyya ta
koma gun fulani ta rusuna tana cewa 'ranki shi
dad'e ,ga jakadiya ta iso da su barden' ,'ki ce masu
su shigo',badiyya ta tashi taje ta fad'a masu
sannan tayi tafiyarta ,jakadiya da su barden suka
shigo da'kin suna masu mi'ka gaisuwa ga sultan
da fulani !
A 'kasaice fulani ta dubi barde da kurtagu,tayi
murmushi mai sanyi sannan tace 'wani aikin sirri
nake so in yi daku,saboda ku ukun nan na aminta
daku' ,gaba d'ayansu suka had'a baki wajen cewa
'godiya muke ranki shi dad'e ,kuma an gama ranki
shi dad'e,umarninki kawai muke bid'a'
fulani ta dubi kurtagu wanda ya kasance
gamsasshen 'kato ne maji 'karfi ,tace 'ka je ka
cewa direba ya fito da highlander mai duhun
gilashi ya zagaya ta baya ya jira mu
anan' ,'angama ranki shi dad'e' kurtagu ya bada

amsa tare da ficewa cike da zafin nama ,sannan ta
dubi barde mai 'kira kamar ta samudawan farko
tace 'kai kuma buhu zakaje ka samo mai fad'i da
girma yanzunnan' ,'an gama ranki ya dad'e' barde
ya fad'a cikin katuwar muryarsa,sannan ya fice.
Fulani ta dubi jakadiya dake dur'kushe a gun tace
'mara'kisiya nemo tsumma ,ki tamke min bakin
bayarabiyar nan' ,da hanzari jakadiya ta kunce
d'amarar da tayi da dankwali ,ta 'karasa ga bolaji
dake kwance a sume ,ta d'aga kanta ta d'ora akan
cinyarta sannan ta tamke bakinta da dankwali
tamau!
Bayan mintuna talatin sai ga barde ya shigo d'akin
hannunsa ri'ke da 'katon buhu ,kurtagu shima ya
shigo ya rusuna yanacewa' angama ranki shi
dad'e' ,fulani ta murmusa tace 'madalla,yanzu ku
had'u ku d'au wannan ku sata acikin buhun' tana
mai nuna musu bolaji dake kwance a sume bakinta
tamke da d'ankwali....
Written by :AB
[10/15, 8:22 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE


~10~

Tana gama cin abinci,ta ajje littafin,ta nufi kitchen ta kwamfaci ruwa ta sha ,sannan ta had'a kan
kwanuka ta fito ta wankesu tas ,sannan ta dawo ta zauna tana cigaba da duba littafinta ,maami
tana mata sannu ta hanyar cewa 'ekhuse' ,bolaji ta amsa da 'eshe'!
Babalaji ya shigo da sallama,gaba d'aya suka amsa ,bolaji taje ta amshi ledar hannunsa tana ce
masa 'ekabo' ,babalaji ya amsa 'my daughter eshe',maami ta tashi da 'kyar tana gyara d'aurin
zanin nata,tabarma ta shimfid'a masa,tana mai cewa babalaji 'ekabo' ,bayan ya zauna yana
sauke ajiyar zuciya yace 'iya bolaji[maman bolaji] eshe oh,how body' ,'we thank God oh,my
husband,how's your day,hope it went well' ,bolaji ta iso da ruwa a cikin kofin silva,ta russuna ta
mi'kawa babanta,ya amsa ya shanye tas,bayan ya shanye ya dubi bolaji yana cewa 'thank you
my daughter,may the almighty oluwa bless you' 'amin oh' bolaji da maami suka amsa!
Babalaji ya dawo da dubansa ga maami yana mai cewa 'hmm,i'm tired oh,we the labourers
have been standing at the company's entrance for the past 4hours waiting for our 7month salary
to be paid to us,before we get back to work and call of the strike,but the payment did'nt take
place,instead the manager told us to excersise patient,and we should come back on tuesday
cause the owner of the company will come and tackle the problems!' ,maami ta dubi mijinta cike
da tausayi tace 'this is wickedness,i don't know what this country is becoming,but no

wahala,oluwa dey ,he dey watch and he's in control' ,babalaji ya amsa mata da 'na so oh,let's
wait for the tuesday,we shall see' ,maami ta tashi ta d'auko masa abinci ta kawo masa,yana ci
,tana masa firfita tare da jan sa da hira!
¤¤¤¤
Ranar litinin misalin 7:30am hashim ya gama shiryawa,yayi sallama da iyayensa,direba ya
saukeshi a airport,inda palace pilot ke jiransa,ya shiga private jet d'insu,suka d'aga kaduna!
Misalin 'karfe 10 na dare ,mai martaba na zaune kishingid'e a d'akin fulani,kasancewar ranar
girkinta ne!
Fulani ta dubi mai martaba tare da cewa 'gobe ne tafiyar taku ko?' ,'insha Allah' mai martaba ya
bata amsa,fulani ta gyara zama tana cewa 'abban hashim baka ganin cewa daraja da arzikin
wannan masarauta ya wuce ace ka bud'e kamfani[companies/factories] a garuruwa,ni a ganina
sarauta da mulkin ka sun girmi hakan, ,musamman kamfanin pure water da aka bud'e a kano
,da kuma na manja da aka bud'e a garinsu oduduwa,bai kamaci wannan masarautar ba,da
kuma kai kanka da ka kasance tsohon gwamna' ,mai martaba yayi murmushi wanda ya 'karawa
fuskarsa kwarjini ,yace 'fulani kenan,ni ba kowa bane face d'an adam kamar kowa,wad'annan
kamfanonin ba'a bud'e su domin samun kud'i ba ,an bud'esu ne saboda talakawa mazauna
yankin da aka bud'e kamfanonin, su samu hanyar da zasu nemi halas da guminsu ta hanyar
samun aiki a kamfanonin,kuma kinga a yanayin da 'kasar tamu take ciki,aiki yana yi wa matasa
wuyar samu duk da kwalin degree d'insu,,kinga kenan samun aikin matasa a kamfanonina zai
sa a rage samun matasa masu zaman banza da kashe wando[jobless youths],kuma da kike
cewa masarautar nan ta girmi hakan,ta ina masarautar nan ta girmi haka,me kike d'au sarauta a
duniyar nan ne?,mu da mutanen gari,musamman talakawa ,duk d'aya muke a gun Allah!
sarauta da mulki sai sarautar ALLAH s.w.t 'malikul mulk',mabuwayi,gagara misali,wanda
dukkan mu gaba d'ayan mu a 'karkashin ikonsa da mulkinsa muke! kuma kamfani yanzu na fara
'bud'ewa ,in akwai abinda yafi purewater 'kas'kanci idan har na samu dama sai na bud'e
kamfaninsa,in har hakan zai zamo alkhairi ga al'ummar annabi muhammad [s.a.w],musamman
talakawa!
masarauta bata girmi yin ko wacce irin halastaciyyar sana'a ba,ko da kuwa wannan masarautar
tana da daraja da arziki' ,jiki a sanyaye fulaîi tace 'ALLAH ya bada lada,ya kuma 'kara arziki,na
fahimci manufarka,kuma ina fatan sauran sarakuna irinka zasu koyi da kai' ,mai martaba yace
'amin fulani,addu'arku kawai nake bu'kata a kullum,' ,haka suka cigaba hira na farantawa juna
rai ,har izuwa lokacin da bacci ya riskesu!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/15, 8:54 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~11~


Washegari da misalin 'karfe 11:00am mai martaba yayi sallama da matansa! Ya kuma d'amka
komai da ya shafi fada ga waziri!

SULTAN BELLO AIRPORT
mai martaba da sultan suka nufa bisa rakiyar fadawa da royal chambers[hakimai,galadima,su
shamaki da dai sauransu]!
Misalin 'karfe 12:00 na rana modibbo palace private jet ya nausa da mai martaba da sultan
sararin samaniya izuwa birnin ikko [lagos] Misalin 'karfe 12:00 na rana modibbo palace private
jet ya nausa da mai martaba da sultan sararin samaniya izuwa birnin ikko [lagos]!
Da isar su airport d'in jihar lagos ,suke iske an turo masu motoci daga masarautar osun
state,da yake 'oba'[sarkin masarautar osun] ya san da zuwan mai martaba!
Tafiyar awanni 'kalilan ne tsakanin lagos zuwa osun!
Bayan sun d'an huta a masauratar osun,sun gabatar da sallar zuhr,sai suka wuce yankin 'erin'
dake jihar osun, bisa rakiyar royal guards na osun's palace!
¤ ¤ ¤ ¤
Gaban gate d'in kamfanin manja na modibbo [MODIBBO RED OIL COMPANY ! Erin] cike
yake ma'kil da 'kananan ma'aikatan da ba'a biya su albashinsu ba na tsawon wata bakwai tare
da matayensu da 'ya'yayensu,suna masu zanga-zanga,hannayensu ri'ke da cardboard papers
mai d'auke da rubutun 'WE N O GO GREE' ,'PAY US OUR SALARY' 'baro 'baro! Cikin wad'annan ma'aikata masu zanga zanga harda babalaji da iyalansa,da yake yau bolaji
batada paper hakan yasa ta biyo mahaifinta,haka zalika maami duk da cikin dake jikinta hakan
bai hanata biyo bayan mijinta ba domin nema masa ha'kkinsa ,bamidele shi ma yana nan tsaye
cikin matasa irinsa,hannunsu ri'ke ganyen darbejiya sai ihu suke suna cewa 'we no go
gree,pay our parents their 7months salary!'
a gefe guda yan jarida ne suke d'aukan rahoton wannan zanga zangar[demonstrati a gefe guda
yan jarida ne suke d'aukan rahoton wannan zanga zangar[demonstration]!
A cikin wannan yanayin su mai martaba suka iso kamfani,bai zaci abin ya kai haka ba,domin
da 'kyar aka samu ma'aikatan suka matsa daga gaban gate d'n shiga kamfanin!
motocinsu suka samu daman wucewa izuwa cikin harabar kamfanin!
Mai martaba bai jira an bud'e masa kofar mota ba yafito,sultan na biye dashi,MD dasauran
manyan ma'aikata suka zo suna mi'ka gaisuwa!
Mai martaba ya umarcesu da yana bu'katan ganawa da manyan shugabannin da aka wakilta a
kamfanin domin gano silar wannan matsalar na rashin biyan 'kananun ma'aikata albashi,kuma
yana son a kuma shawo kan matsalar!
Zaune suke a conference room mai martaba yana tattaunawa dasu !
Bayan tattaunawar ne ,aka gano cewa ashe bursar[ma'aji] ne ya ke danne kud'in albashin
'kananun ma'aikata idan ance ya raba masu baya basu da kuma had'in bakin accountant!
A take mai martaba yasa aka rubuta masu takardar kora daga kamfani!
Sannan kuma yace wa MD Yaje yasa a bud'ewa ma'aikata gate su shigo domin ya kwantar
masu da hankali !
Bayan securities sun bud'e masu gate sun shigo harabar kamfanin sun tsaya suna ifice
ificensu!
MD ne ri'ke da bututun magana yana mai umartarsu dasuyi shiru su saurari mai
martaba,saboda yanzu komai yazo 'karshe ,domin mai martaba [founder of the company] da
kansa zai gana dasu !

Bayan sun yi tsit ,Mai martaba ya amshi bututun[mic] ya fara masu magana cikin harshen
turanci,yana mai 'kara basu ha'kuri,yan jarida suna gefe suna d'aukan hoto da rahoto!
Maami ita ko in banda hararar mai martaba ba abinda takeyi,domin duk jawabin nan nasa ba
fahimta take ba,gani take kamar harda sa hannunsa wajen rashin biyan 'kananun ma'aikata
albashinsu har na tsawon wata 7!
Dur'kusawa tayi da 'kyar tasa yatsu tana laluben dutse,can yatsunta suka dam'ko mata katon
dutse a 'kasa ,mi'kewa tayi tsaye tayi jifa da dutsen,batare da kowa ya lura ba sai 'iya
folake'[maman folake] dbke tsaye kusa da ita, sauran kuma gaba d'aya hankalinsu na ga mai
martaba dake kwararo masu bayani dalla dalla! Mai martaba baiyi aune ba yaji saukar dutse a goshinsa,wanda hakan yayi sanadiyar fitar jini
daga goshinsa,jinin kuwa ya 6ata masa farin tufafin dake jikinsa!

Hannu yasa ya dafe goshin nasa sanadiyar zogin azaba da rad'ad'i da yaji!

Tuni hankula suka tashi,sultan hankalinsa a tashe yayi kan mahaifinsa ,ya ri'ke shi,yana mai
cewa MD ya kira ambulance!

Security da royal guards[osun palace] suka raraki ma'aikatan da duka,tuni suka tarwatse kowa
ya arce,bolaji,babalaji da bamidele suna ri'ke da maami,wacca take jan 'kafa da 'kyar a haka
suka fice daga harabar kamfanin,maami ko zuciyarta wasai ,ita a ganinta tayi maganin
azzalumi!
Ni kuma ililee nace' hmm 'tsuliyar dodo ki ta6o!'

written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/15, 8:55 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~12~

Motar ambulance ce ta shigo harabar kamfanin,a take male nurses suka fito daga motar,suka
nufi wajen mai martaba domin shigar da shi cikin motar,bayan sun kwantar dashi ,likitan da aka
zo dashi yayi masa treating d'in ciwo tare da yi masa dressing d'in ciwon!
Bayan likitan ya gama yi masa treatment d'in!
Ambulance d'in suka tarkata suka tafi ! ,mai martaba ya umarci royal guards dasu wuce dashi
airport ,bayan ya jaddadawa MD cewa ya tabbatar ya biya ma'aikatannan albashinsu,kuma kar
ya kuskura yaji anyi masu wani abu!

Ta waya mai martaba yayi sallama da 'oba' domin basu biya ta fada [osun's palace] ba, airport
d'in lagos,suka wuce,mai martaba da sultan suka haye modibbo's palace private jet, pilot ya
d'aga dasu izuwa jihar sokoto!

Suma royal guards suka juya suka koma jihar osun!
¤ ¤ ¤
Fulani ce ta taresu cike da fargaba ganin mai martaba goshinsa d'aure da plaster ,duba ta kai
ga sultan tana mai tambayarsa 'lafiya? Meya sami goshin abbanku',mai martaba ya nemi gu ya
zauna,sultan kuma ya labartawa fulani abinda ya faru,daman me neman kuka ne aka jefe shi da
kashin awaki,nan fulani ta fara zuba bala'i kamar zata ari baki tana cewa 'kaga irin ta ko,tsiyar
YARE kenan,in mutum yayi magana kuce an cika nuna kabilanci,a gaskiya idan akace mutum
ba bahaushe bane ,toh yayi asara babba' ,ummu ce ta shigo rest room d'in ,domin yiwa mai
martaba sannu da dawowa ,maganganun fulani ne yasa tayi turus tana tambayar lafiya ,fulani ta
amshe da cewa 'ina lafiya kuwa,dubi goshinsa ki gani,mutanen oduduwa masu kashi a leda ,su
ne sukaso su halaka mana shi,toh ta Allah ba tasu ba ,tubabbu kawai',mai martaba ne ya
katseta ta hanyar cewa 'ya isa haka ,bana son in 'kara jin kin tada zancennan,tsautsayi ne
,kuma baya wuce ranarsa',ranta bai so ba,amma ba yadda ta iya,dole tayi shiru ,ummu kuwa
tayiwa mai martaba sannu da zuwa ,takuma jajanta masa,sannan ta ja hannun sultan suka fice
,fulani kuwa ficewa tayi taje tasa hadimai su jera abinci akan dinning ,wato suyi setting table
.saboda mai martaba zai zo yaci!

¤¤¤

Cikin dare fulani na zaune ita kad'ai a d'akinta,abin duniya ya isheta,'kiyayyar YARE na 'kara
ruruwa a zuciyarta!
kasancewar mai martaba yau a d'akin ummu yake!
Hadimanta kuma suna zauna a gaban d'akin nata!
Wayarta ta janyo domin bugawa hashim !
Ringing biyu Hashim ya d'auka , tun kafin yayi magana ,fulani ta fara cewa 'ina son ka d'ibi
sojoji,gobe kuje yankin erin dake jihar osun,ku ci uban duk wani 'karamin ma'aikacin kamfanin
abbanku' ,a tausashe hashim yace 'umma meye faru' ,nan fulani ta kwashe labari kamar yadda
sultan ya labarta mata ta gaya masa,har da 'karin gishiri! Hashim wanda ransa ya gama 6aci da jin haka,allurar tasa ta motsa ,cikin 6acin rai yace 'ina
abban yake,ya jikin nasa?' ,fulani ta amsa da 'da sauki,gashi can a kwance,kanshi ya suntume! '
sannan tace'my soul dear ya zama dole ka d'au mataki fa,ya kamata ka d'au fansa ga jinin
abbanku da suka zubar' ,hashim ranshi a 6ace yace 'angama ,insha Allahu gobe da safe zamu
tashi izuwa garin,zasu gane kurensu ,sai sun gane cewa ba'a ja da masauratar modibbo a
zauna lafia' ,fulani tace 'thats my souldear ,the soldier of the nation,ALLAH ya kai ku lafiya' ,a
haka sukayi sallama fulani tana mai 'kara zugasHashim wanda ransa ya gama 6aci da jin
haka,allurar tasa ta motsa ,cikin 6acin rai yace 'ina abban yake,ya jikin nasa?' ,fulani ta amsa da
'da sauki,gashi can a kwance,kanshi ya suntume! ' sannan tace'my soul dear ya zama dole ka
d'au mataki fa,ya kamata ka d'au fansa ga jinin abbanku da suka zubar',hashim ranshi a 6ace
yace'angama insha Allahu,gobe da safe zamu tashi iúuwa garin,zasu gane kurensu,sai sun
gane cewa ba'a ja da masarautar modibbo a zauna lafiya',fulani tace'that's my souldear,the
soldier of the nation ,ALLAH ya kai ku lafiya!'
a haka sukayi sallama,tana mai 'kara zugashi!

Bayan sun gama wayar ,ta ajje ,ta bi lafiyar gadonta,tayi kwanciyarta zuciyarta fari Tas!

Written by:ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/15, 8:56 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE


~13~



Tunda garin Allah ya waye maami take fama da ciwon na'kuda ,amma ahaka ta daure ta cije
tana tsoran kar bolaji ta gane halin da take ciki,saboda gane hakan ,na iya sawa bolaji ta fasa
zuwa makaranta!
Bolaji ta fito daga d'akinta sanye da farin shirt long sleeve,sai guntun blue skirt daya wuce
'kaurinta,sai kuma blue baret[hula]data kifa akanta,kafarta sanye da farin safa da brown
sandal,hannunta ri'ke da biro da pencil!

Fuskarta d'auke da murmushi tayiwa
Maami da babalaji sallama,sannan ta fice daga gidan!
Murna kawai take , saboda yau zasu zana jarabawar 'karshe wato yoruba language!

¤¤¤
Misalin 'karfe 1:00 na rana convoy d'in gwanayen motocin Nigerian army guda goma,suka
d'inga shigowa yankin 'erin'!

Mutanen yankin sai bin motocin suke da kallo suna masu tambayar junansu 'lafiya!'

MODIBBO RED OIL COMPANY motocin suka nufa,da isar su kamfanin, Gateman ya wangale
masu gate jikinsa na rawa!

Bayan sunyi parking motocin a harabar kamfanin!

Sojoji ne d'auke da bindigu suka d'inga durowa daga motocin,fuskarsu babu alamun wasa!

Capt.hashim ne jagoransu,domin shine a gaba,fuskarsa babu annuri ko kad'an ,jikinsa a murd'e

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login