Showing 54001 words to 57000 words out of 61652 words
ko kadan a cikin zuciyata,wallahi da ace
babu auren hashim akaina,da wallahi babu abinda zai zaunar da ni a fada har zuwa wannan
lokacin,domin zuciya da so na gun hisham...',badiyya ce ta mintsineta tare da zabga mata
harara,ummu tace 'kyaleta badiyya ,har ga Allah ban ga laifinta ba,domin zuciya tana son
wanda ya kyautata mata ,kuma hisham ya kyautata mata a rayuwa ,bai cutar da ita ba ,ya bata
sabuwar fuska,sabuwar suna ,sabuwar rayuwa ,ya hadata da zuri'arsa,sun koya mata sabuwar
YARE,su ne suka samar da mujiba ,kinga kenan hisham ya cancanci abinda ya fi haka daga
gun mujiba ,domin mujiba kike a garesu ,mu kuma bolaji kike a gare mu ,ya kamata ki gane
bambancin haka..',sannan kuma ta cigaba da cewa'bolaji ni ba zan tursasa miki ba,rayuwar so
da aure ,rayuwace da kike da ikon zabar wa kanki wanda ya dace kiyi wannan rayuwar
dashi,amma a yanzu abinda ya kamata muyi shine mu san yadda zamu tara hujjoji da shaidu
domin gabatarwa da mai martaba,hashim da kuma dan uwanki',bolaji da badiyya suka sauke
numfashi ,ummu ta cigaba da cewa 'a yanzu haka dan uwanki da matarsa suna hanyar isowa
sokoto,sannan kuma a yanzu zan nemi doctor ayuba a waya ,domin samun shaidar da zamu
gabatar na cewa fulani ta samu gawa ta dalilinsa !',
Misalin karfe 2:00pm Dr.ayuba ya iso fada dalilin neman da ummu take masa ,palace guest
parlour aka saukeshi ,ummu ,badiyya da bolaji suka iskeshi a parlour din,bayan ya gama
gaisawa da ummu ,sai ya dubi bolaji yace 'my patient yau idonki nake gani ,it's been long ',bolaji
tayi murmushi kawai ,ummu ta dubi dr.ayuba tace'na kira ka ne saboda muyi wata muhimmiyar
magana ',dr.ayuba ya russunar da kai tare da cewa a ladabce 'ranki ya dade Allah yasa ba
matsala aka samu game da lafiyar yallabai ba...'',ummu ta katseshi ta hanyar labarta masa
komai dangane da fulani, bolaji,hashim da hisham!
Dr ayuba duk ya bi ya jike da zufa ,jikinsa sai kyarma yake ,idanunsa suka firfito sukayi jajir,ba
shiri ya fara rantse rantse yana cewa 'wallahi tallahi har ga Allah da niyyar taimako na bawa
umma gawa tare da creating fake DNA result ,amma wallahi babu sa hannuna ga duk wani abu
da ya shafi cutar da matar yallabai,ni asali ma ban ma santa ba ,kuma ko da hisham ya kawo
ta asibitin ban san itace ba ,wallahi tallahi.....',,ummu ta dakatar dashi ta hanyar cewa 'kar ka
damu ayuba ,na yarda da kai,abinda nake bukata daga gareka shine ,zan bukaci shaidarka a
duk lokacin da bukatar hakan ya taso,ka tashi ka tafi ,sai na kara nemanka',jikinsa na tsuma ya
amince tare da kuma yin alkawari bada hadin kai dari bisa dari in har asirinsa zai rufu ,da kyar
ya tashi ya tafi yana mai mamakin makirci irin na fulani,amma ko ba komai kwadayi da son abin
duniya ne ya jaza mishi,kuma yasan muddin wannan labarin ya yadu a gari toh babu shakka
bankwana da lasisinsa na zama cikakken likita ya zamar masa tilas!
Misalin 6:00pm bamidele da nawwara suka iso fada ,ummu ce ta tarbesu domin ita fulani
zazzabi yayi mata mugun kamu ,kuma ko da lafiyarta kalau ,bamidele da nawwara bazasu
samu arzikin kallo daga gareta ba balantana kuma tarba,a dakin nawwara da ummu tasa a
gyara aka saukesu,bayan sun kimtsa tare da samun hutu ,misalin karfe 9:00 pm bayan angama
cin dinner kowa ya watse ,domin mai martaba ya wuce turaka ,sai ummu ta bukaci ganin
bamidele da nawwara,a guest parlour suka hadu har da bolaji da badiyya tare da baturen likitan
da ummu ta bukaci matar gwamna ta turo mata shi,bayan kowa ya zauna,ita bolaji sai kallon
bamidele take ,yadda yayi kyau yayi haske yayi fresh kamar bashi ba,tabbas nawwara tana
bashi kulawa wato ta maye mai gurbin iyaye da kuma yar uwarsa ,shi kuwa bamidele tun da
suka zo ya dora idanunsa akan mujiba(bolaji) yaji gabansa na faduwa ,kuma idanuwanta na
masa kama da idanun marigayiyyar yar uwarsa ,ummu ce tayi gyaran murya tare da yin nuni
ga mujiba (bolaji) tare da labartawa bamidele komai dangane da ita cikin harshen
turanci,nawwara idanunta na zubda hawaye ta gasgata zancen ummu ta hanyar labarta musu
abinda duk sukayiwa bolaji tin ranar data shigo fada a matsayin matar hashim,sannan ta dora
da cewa a gaskiya ita tayi nadama domin ta dawo daga rakiyar fulani ne a ranar data kawo
gawa a matsayin gawar bolaji ,kuma sanin kansu ne gaba dayansu basu da tabbacin masaniyar
makomar bolaji a wannan daji',bamidele idanunsa na zubda hawaye ya dubi mujiba(bolaji) tare
da cewa 'bolaji is that really you?',bolaji kasa amsa masa tayi saboda kukan da ya ci karfin ta
,domin ita da kanta tana tausayawa kanta,domin rayuwa ta gara ta tun daga ranar da hashim
ya shigo mata rayuwar ,ummu ce ta yiwa likta umarnin diban jinin bamidele da mujiba(bolaji)
domin gudanar DNA test ,saboda DNA test result dinne zai tabbatar da cewa mujiba itace bolaji
,duk da a yanzu babu shakku ko tantama ita din ce ,a take doctor ya aiwatar da umarnin ummu
ylyare da yi mata alkawarin zai kawo mata result washegari ,bayan likitan ya tafi ,sai ummu ta
tashi ta wuce turaka domin yau kwananta ne , badiyya ta mike tare da riko bolaji suka fice daga
parlour ,nawwara kuwa hankalinta duk ya gama tashi ganin irin kallon da mijinta ke jifanta dashi
,hakan yasa ba shiri ta bi bayan su bolaji dakinsu ,bamidele ya tashi shima kanshi a cunkushe
da tunani ya zarce dakinsu da aka musu masauki a ciki!
Nawwara ta kama hannun bolaji tana cewa 'wallahi tallahi babu kaffara ke ce dai bolaji,daman
jiki na yana bani cewa kina raye kuma zaki dawo",nawwara ta durkusa kan gwiwowinta tana mai
cewa'bolaji ki dubi girman Allah ki yafe min,nasan mun zalunceki ,mun aikata miki mafi munin
cutarwa,pls nd pls find it in ur heart to forgive me',bolaji ta tayar da ita tsaye tare da
cewa'nawwara har ga Allah na yafe miki,domin kin cancanci in yafe muki ko dan kasancewarki
matar brother dina,ki sani kin xama yar uwata ,we r nw family,na yafe miki nawwara,Allah ya
yafe mana gaba daya",cike da farinciki nawwara ta rungume bolaji tana mai zuba
godiya,sannan ta kara dubanta tare da cewa 'Allah mai iko ,bolaji yau ke ce kike jin hausa kuma
kikeyin hausa tamkar dama can bahaushiya ce ke '',badiyya tace 'ke ma dai kya fada,Mujiba
bahaushiya ,bolaji bayarabiya",nawwara tace'tabbas bolaji a yanzu is potraying
2TRIBES(YARE BIYU )!",a haka suka dan taba hira inda nawwara ta ciro wayarta ta nemi
alfarmar bolaji da ta taimaka tayi mata wani abu,sai da badiyya tasa baki sannan bolaji tayiwa
nawwara wannan abun,nawwara murna fal cikinta ta yiwa su bolaji sai da safe tare da wucewa
dakin fulani domin aiwatar da abinda zuciyarta ke bijiro mata!
Fulani ta gama kurbar shayi tare da ahan maganin da jakadiya marakisiya ta kawo mata ,bayan
ta gama sha ,sai ta kwanta tare da bawa jakadiya umarnin kashe mata wutar dakin idan zata
tafi!
kamar a mafarki fulani taji muryar bolaji tana cewa 'mummy folani.....here i come....oduduwa
has given me the will and power to scatter your life.....',suman kwance fulani tayi domin ko
yatsarta ta kasa motsawa,sai zuciyarta dake bugawa pat pat pat ,a zuciyarta cewa 'oh ni sa'a
naga ta kaina ,yanzu 'yar mutan oduduwa fatalwa ......",muryar bolaji ce ta katse mata zancen
zucin da take "mummy folani ,am going to scatter ur face just the way you did the same to my
face ,sango will strike you to death....",wani irin ruwa mai dumi dumi da lami lami fulani taji yana
fita daga kasan mararta bakinta na rawa ta fara jero duk wani addu'ar da yazo bakinta ,ga kuma
dakin babu haske balle ta ga fatalwar bolaji ta kuma bata hakuri, nawwara kuwa gimtse
dariyarta tayi lokacin da kunnawanta suka jiyo mata fulani tana neman gafara cikin muryar kuka
da pidgin english tana cewa 'na una dey see me ,me i no dey see una,abeg bolaji forgive me na
, na devil cos am ,abi u don forget sey me and u na 1 &2 ,abeg no scatter my life .....',nawwara
ta kara danna play din recording din muryar bolaji da sukayi ita da badiyya ,''folani...your end
has come.......',sautin fitar kukan fulani ne yasa nawwara ta sa stop domin fulani ta fara kuka
mai kama da tashin mota,bayan ta yi kokarin gimtse dariyarta tare da boye wayarta cikin skirt
dinta ,sai ta nemi switch ta kunna wutar dakin tana cewa 'umma lafiya na ganki haka hanci duk
majina ?',fulani jiki na rawa tana raba idanu tace'nawwara mun shiga uku ,bolaji ce take min
fatalwa wai she go scatter my life ....',nawwara ta hadiye dariyar daya taho mata tare da cewa
'kin dai shiga uku dai,daman in baki manta ba na gaya miki cewa in har bolaji tana raye zata
dawo ....',fulani ta katseta ta hanyar cewa'haba nawwara wani irin zata dawo ,kar ki sa zuciyata
ta buga mana ,bolaji ta dawo i nagama mutuwa,kidaina ma cewa zata dawo domin ina da
tabbacin cewa bolaji ta riga tayi mushe tunda gashi har fatalwa take yi min ....',nawwara tace
'kika sani ko ita din ce ta dawo a gaske ,sai kuma ta zo miki ta sigar fatalwa .. ',sai kuma
nawwara tace 'daman zuwa nayi mu gaisa dazu da yamma muka iso,ummu ce take ce mana
wai baki jindadi ,kuma ga zahiri na gani ,Allah ya kawo sauki ,sai da safe ',fulani ta kama yi
mata magiya tana cewa'nawwara kar ki tafi ,dan Allah ki kwana a dakin nan....',nawwara tace
'wato shi kuma mijina in barshi shi kadai ko?, wai shin ina hadimanki ne masu tayaki kwanaa?
....',"ni ce na basu umarnin tafiya ...",fulani ta bata amsa,sai nawwara tace 'bara in duba side
dinsu ko marakisiya ce sai na turo miki,sai da safe ',nawwara ta fice ta bar fulani tana kyarma
ta zazzare idanu tamkar berar da tirela ta dannewa bindii,nawwara tana fita ta kwashe da dariya
,sai da tayi mai isarta sannan ta je ta bawa jakadiya da sauran hadimai umarnin zuwa dakin
fulani domin su tayata kwana!
ko da suka iske fulani a daki ,babu kunya tace musu'kuyi min wanka dan Allah ,sannan kuma
kuma ku wanke kayan gadon nan dana fitsare "
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 1:48 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~61~
Ko da nawwara ta koma 'daki ,bamidele ko juyowa bai yi ba,hakan yasa ta chanja kayan jikinta
izuwa na bacci ,ita ma ta hau gadon ta kwanta a bayansa ,murya a sanyaye ta fara cewa 'i
know you will be mad at me ,but pls & pls try and understand ,i'm scared of loosing you that's
why i kept quite...',rai a bace bamidele ya dago ya dubeta tare da cewa'you're scared of loosing
me? ,oh i can see ...just hear ur self out,how can u be so cruel and wicked ,i never thought a
day like this will come so soon that i wont be able to trust you anymore,and you know what
?,just pray that all this is a dream,cause if it is'nt.....',kawai sai yayi kwafa ya juya mata baya
,hakan yasa nawwara ita ma tayi kwanciyarta ,a zuciyarta tana mai cewa 'nasan ko ba jima ko
ba dade wannan ranar zatazo ,ranar da mijina zai sa almakashin saki ya datse duk wani igiyar
aure da so a tsakaninmu,ya Allah ka bani juriya da dauriyar karbar ko wanne irin hukunci da
mijina zai yanke min'
Sultan shi ma yana dakinsa yana fama da jinyar zazzabin rashin samun mujiba a matsayin
matar aurensa!
Hisham ya rasa mai yake masa dadi a duniya ,amma ya fawwalawa Allah lamurransa ,hakan
yasa ya fara samun kansa da nisanta zuciyarsa da soyayyar mujiba(bolaji) ,domin yana ji a
jikinsa ya rasa ta har abada ,amma a haka ya bar wa Allah zabi !
* * *
Washe gari misalin karfe 1:00pm ,ummu ta bukaci kowa (wato duk wanda lamarin 'batan bolaji
ya shafa ) ya bayyana kansa a turakar mai martaba ,wanda tun a daren jiya ta shaida masa
cewa akwai wata muhimmiyar boyayyiya a kasa da za' tono!
☆TURAKA☆
mai martaba ,ummu ,fulani,hashim,sultan,bolaji(mujiba),bamidele,nawwara ,badiyya,jakadiya
marakisiya,kurtagu,barde ,dr.ayuba ,da kuma baturen likita mai suna dr.albert!
Dukkansu sun hallara a turaka,masu mamakin wannan haduwa sunayi,wanda kuma cikinsu ya
gama durar ruwa ,suma nasu cikin nayi,sai kuma wanda suka fara kuka tun kafin a fallasa suma
sunayi!
Ummu ce ta fara yin sallama tare da kuma cewa 'ina son kowannenku a nan wajen ya kasance
mai fadin gaskiya a yayin da aka bukaci gaskiyar,domin gara aji kunyar duniya da akan aji
kunyar lahira',sannan kuma ta umarci bolaji ta fadi abinda ya faru gare ta.......'bolaji murya a
sanyaye ta fara bada labarinta tun daga ranar da hashim ya tafi liberia ,har izuwa ranar da
hisham ya kawo ta fada a matsayin kanwarsa' ,mai martaba,sultan,hashim da fulani tare da su
kurtagu mamaki ne ya kamasu kasancewar wai mujiba ce bolaji ,mussaman hashim da shi ya
kura mata idanu yana mai ganin wawancinsa da sokoncinsa na rashin gane matarsa bolaji tun
da take kula dashi ',ummu ta dubi sultan tace 'sultan abinda mujiba ta fada akan ka gaskiya
ne?',sultan idanunsa cike da hawayen nadama yace 'gaskiyane hakan ya faru ,amma har ga
Allah babu hannuna game da abinda ummu da nawwara sukayi mata ,domin ni da kaina a
wannan daren na koma domin dauko bolaji,sai ban tarar da ita ba,amma a kullum addu'a ta
itace Allah ya bayyana mana ita idan tana raye',ummu ta sauke numfashi sannan ta dubi
nawwara tace 'ke kuma me zaki ce game da wannan al'amari',nawwara ta sadda kai tare da
cewa 'gaskiya nasan na aikata babban kuskure ,amma ko ma menene duk makircin umma
fulani ne,domin ta aikata komai bisa kiyayyar da takeyiwa YARE ....amma ni ina neman afuwa
domin ni na riga na saduda kuma Allah ya riga ya nuna min ishara ta hanyar sanya min
soyayyar dan uwan bolaji a zuciyata ,wanda a yanzu haka yake a matsayin mijina",ummu ta
dubi su jakadiya ,kurtagu da barde tare da neman jin ta bakinsu,jikinsu na rawa suka amsa
laifinsu tare da neman sassauci daga gun mai martaba da yarima hashim!
Fulani ji take tamkar kasa ya tsage ta fada viki don tsabagen kunya ,mussaman hashim da
yake mata wani irin kallo ta da ta kasa tantacewa ,ummu ce ta katse mata tunani ta hanyar
cewa 'fulani muna son muji daga gareki ,ki kuma fayyace mana gaskiyar al'amari ga me da
gawar da kika kawo a matsayin gawar bolaji',fulani na zubda hawaye ta labarta musu yadda ta
je gun dr.ayuba ta amshi gawa!',ummu ta dubi Dr.ayuba tare da cewa 'ayuba shin abinda fulani
ta fada gaskiya ne ?",Dr.ayuba jiki na rawa yace 'gaskiyane amma wallahi tallahi da niyyar
taimako na bata gawar", nan ya kwashe yadda sukayi da fulani ya shaida musu ,tare da rokon
dan Allah a rufa masa asiri ',ummu ta juya ta dubi mairmataba tare da cewa 'toh mai martaba
kaji dai duk yanda abubuwa suka faru ,kuma hukunci ya rage gareka',sannan kuma ta umarci
Dr.albert ya miko DNA test result ,bayan an mikawa mai martaba result din ,sai ummu ta labarta
masa rawar data taka ,tun daga ranar da taje ta tadda mujiba(bolaji) kwance akan kirjin hashim
har izuwa daren jiya da likita yazo ya debi jinin bamidele da mujiba (bolaji)!
Maimartaba yayi gyaran murya tare da cewa 'a gaskiya na yi mamakin faruwar wannan al'amari
,duniya kenan ,kana naka Allah na nashi,kun cutar da baiwar Allah ,kun salwantar mata da
rayuwa ,kun mata mafi munin makirci duk sabida ta kasance YARE",sannan ya dubi fulani yace
'fulani bazan taba mamakin ki ba domin kiyayyarki ga YARE a bayyane take ,amma ban taba
zaton zaki je to the extent of doing all this',mai martaba ya bude DNA test result ya karanta
sannan yace 'result dai ya nuna cewa jinin bamidele da mujiba yayi matching,wato kenan
mujiba ce bolaji ,Allahu Akbar ,Allah mabuwayi gagara misali,wallahi ko da ba'ayi test dinnan
ba,babu tantama ko kuma jayayya na kasancewa mujiba ce bolaji ",mai martaba ya dubi fulani
yayi murmushi mai ciwo yace"kin fitar da ita da hannunki domin nisantata da hashim da sultan
,kuma da hannunki kika amsheta a lokacin data dawo,har kike kokarin hada aurenta da
hashim,kuma sultan shima yake kokarin aurenta ,kinga kenan Allah ya nuna miki ishara da
wannan kadai ',fulani kuka take har da majina domin bata taba zaton akwai ranar da dubunta
zai cika ba ,a gaskiya wannan ranar tayi mata zuwan bazata domin batayiwa wannan ranar shiri
ba!
Bolaji kuwa kuka kawai take wanda ta rasa dalilin yinsa ,farin ciki zatayi ko kuma bakin
ciki?,sautin kukanta ne yasa hashim ya mike tsam akan kafafunsa daga kan wheel chair, ya
taho gareta ,ya kamota ya rungume tare da shafa bayanta cikin sigar lallashi !
Fulani jiki a sanyaye tazo gaban hashim da bolaji ta durkusa murya a raunane ta fara cewa 'ku
dubi girman Allah ku yafe min ,nasan na cutar da ku ,na cutar da soyayya da aure,ban cancanci
ku yafe min ba ,amma
dan Allah in ci arzikin kasancewa musulma yar uwarku ku yafe min',idanu jajir hashim ya
dubeta ,jijiyoyin jikinsa duk sun tashi ,kauda kansa yayi ya cigaba da rarrashin matarsa ,hakan
yasa fulani ta cigaba da cewa "nasan zaku so sanin dalilin da yasa bana kaunar YARE a
rayuwata,saboda komai yana faruwa ne bisa dalili da kuma sanadi ,kafin aure na da mai
martaba na taba yin aure....
♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡
Soyayyata da PATRICK OKWONKWO ya samo asaline a lokacin da aka turoshi makarantar
mu bautan kasa ,lokacin ina ss3,ina sonshi