Showing 48001 words to 51000 words out of 61652 words

Chapter 17 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4046

mai shafa masa kai ,bakinta na
karanto addu'o'i tana tofa masa !
*BAYAN SATI DAYA*

Sultan rayuwa tayi masa dadi mujiba ta amshi tayin soyayyarsa bisa sharadin ya daina nuna
mata so da kulawa,kuam ya daina zuwa gunta abangaren cikin gida,saboda kar mahifiyarsa
(fulani)ta sa musu ido,shi kuwa ya aminci,daman burinsa mujiba ta soshi,amma duk dare sai
yaje gunta bangaren bayi sunyi zance, ita kuwa bolaji tayi hakan ne saboda ta wahalar da
zuciyarsa,domin tasan cewa ko da maza sun kare a duniya bazata auri sultan ba!

A bangaren hisham kuwa ya je wani seminar a abuja,yana trying wayar bolaji a
kashe,hankalinsa duk ya tashi,kuma gashi sai nan da kwana biyar zai dawo!

Kulawa sosai bolaji take bawa hashim ,ta gogeshi,ta chanja masa vest da shortnicker ,ta
wankesu a toilet ta shanya,ta yanke masa farata,bata barin hadimai da kuyangu su shigo dakin
,badiyya kadai ke shigowa ita ma shara da goge goge takeyi ta fita,fulani kuwa ta yaba da
kulawar da mujiba(bolaji) take bawa hashim! Bolaji kuwa a dakin take wuni,tayi sallah ,ta ci abincinta,sai dare take komawa bangaren
bayi,domin in ta gama yi masa duk abinda ya dace ,sai ta sawa kofar dakin key ,ta zo ta kwanta
a gefensa tana masa hira,da surutai,ko kuma ta kwanta a kan kirjinsa ,wani lokacin har bacci ne
yake dauketa!
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/18, 7:21 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~55~

Yau ma kamar kullum bayan ta gama yiwa hashim duk abinda zata yi masa ,sai ta hau kan
gadon ta kwanta gefensa tana mai shafa masa kai ,tana masa hira ahaka bacci ya dauketa,ba
tare da ta sawa kofar dakin key ba!
Ummu ce ta shigo bakinta dauke da sallama,kasancewar bata cika yawo da hadimai ba acikin
gida,ganin bolaji kwance akan kirjin hashim yasa ta fara jero salati,sanadiyar hakan yasa bolaji
ta tashi a firgice,ganin ummu a tsaye da kuma alamun bacin rai akan fuskarta,yasa ta sauko
daga kan gadon tana mai sunkuyar da kanta! Ummu ta dubeta sannan tace'mujiba wacce irin rayuwa ce wannan?,me ya kai ki kwanciya tare
da namijin da ba muharraminki ba?',bolaji shiru tayi ta kasa cewa uffan,hakan yasa ummu ta
cigaba da cewa'ya zama dole ki bar fadar nan a yau,domin zamanki acikinsa babu
amfani....',bolaji ta tari numfashinta ta hanyar cewa 'ranki shi dade meye aibu aciki,don na bawa
yarima kulawan da yake bukata ,meye aibu don na zamo mace me yin aikin lada....','lada ko
zunubi?,muharraminki ne?,wannan ba hakkin ki bane kuma ba aikinki bane ,baki da wata hujja
mujiba ,ki tashi kawai ki fice ,kuma ki shirya komawa gidan iyayenki a yau',bolaji idanunta ya
ciko da kwalla tare da juyawa ta dubi hashim dake kwance tace'OGA HITLER please wake up
and make everything clear,you are my only hope now ,ka tashi ka sake ni ,i want to be free,i
want hisham to be my husband',tana gama fadin haka ta tashi ta fice daga dakin ba tare da ta
dubi ummu ,wacce mamaki ne yayi mata dirar mikiya 'wacece mujiba ?,wacce irin alaka ce
tsakaninta da hashim da hisham?',tabbas mujiba ce kadai zata bata amsoshin tambayoyin da
zuciyarta suke bujiro mata ,jiki a sanyaye ta fuce daga dakin ba tare da ta lura da hashim dake
motsa yatsunshi da kuma bakinsa dake furta 'my better half' a sanyaye!

Bolaji ta labartawa badiyya abinda ya faru ,badiyya ta bata shawaran akan ta shaidawa ummu
gaskiyar wacece ita!

Fulani ce ta iske hashim a zaune ya dafe kansa da hannu biyu ,sauran kadan numfashinta ya
dauke saboda murna,da gudu ta karasa gareshi ta rungumeshi tare da cewa'Alhamdulillah my
souldear has recovered',idanunta na zubar da hawayen farin ciki!
Kafin ace me,fada ya karade da murnar farfadowar yarima hashim,dr.ayuba yazo ya dubashi
tare da tabbatar musu da cewa babu matsala sai dai sanadiyar dadewar da yayi a kwance
yasa ba zai iya tafiya da kafafunsa ba ayanzu, sai nan da dan wasu lokutan kafar zai warware
ya fara tafiya , amma sai dai using wheelchair for now,kafin ya warware gaba daya! Hashim kuwa bai da zance sai na bolaji ,ita kuwa fulani cewa take 'ta mutu ,kawai ka hakura da
ita,zan aura maka mujiba', hashim sai ya dubeta yace'No !,my better half is alive,i felt her
presence!' ,bolaji kuwa da labarin farfadowar hashim ya isketa ,sai da tayi nafila raka'a biyu tana
mai godewa Allah ! Badiyya ce ta shigo ta sameta tare da ce mata 'mujiba ranki shi dade na nemanki '',bolaji ta
tashi ta bi bayanta,a daki suka iske ummu ,bayan badiyya ta basu waje,sai ummu tayi gyaran
murya tare da cewa 'mujiba ki gaya min gaskiya ,wacece ke ,meye alakar ki da hisham ,yayanki
ne wanda kuka fito ciki daya ko kuma me ?',mujiba murya a sanyaye tace 'babu alaka ta jini
tsakanina da hisham ,sai alakar so,wanda nake zaki zamto sila ga cikar burinmu na zama
ma'aurata ta hanyar sanya hashim ya sake ni ',ummu ta dubi bolaji cike da mamaki tace 'ya
sake ki ?,dama akwai wani aure ne a tsakaninku wanda ni ban san da zamansa',bolaji tayi
murmushi mai ciwo tare da cewa 'zan baki labarina tun daga haduwata(oga hitler) da
hashim,har izuwa dalilin da yasa hisham ya kawo ni fada a matsayin kanwarsa',a take bolaji ta
labartawa ummu( naja'atu ) komai da ya shafi rayuwarta ,sannan ta dora da cewa 'nasan bai
zama lallai ki yarda dani ba saboda nazo da wata fuska,suna da kuma YARE daban,amma ina
son ki fara bincike da kanki ,zaki ji labarin haduwarmu da hashim har izuwa aurenmu daga
bakin MD ,sannan kuma ki tuntubi sultan da batun bacewa ta daga fada ,duk da ba zaima lallai
ya fada miki gaskiya ba !',ummu kanta ne ya kulle gaba daya domin dama can ba ta san da
batun daukar fansa da hashim da yaje yi a yankin Erin!
Tirkashi fulani kin gama salwantar min da rayuwar ya'yana !

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 11:46 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~56~
Ummu a take ta nemi number din MD ta kira ,ba tare da bata lokaci ba ya labartawa ummu
komai dangane da haduwar bolaji da hashim har izuwa aurensu ,bayan sun gama magana , sai
ta cigaba da sake saken yadda zata bullowa al'amarin ,amma ta rasa mafita saboda rashin
kwakwarrar hujja domin kuwa idan har mujiba ce bolaji ,toh gawar wacece fulani ta kawo a
matsayin gawar bolaji!
A bangaren bolaji kuwa dakinsu ta wuce tare da janyo wayarta ,tana kunnawa messages din
hisham suka dinga shigowa ,ba ta kai ga dagawa ba ,sai ga kiransa ya shigo,cike da tausayi ta
amsa wayar tare da karawa akan kunnenta tana mai yi masa sallama,ajiyar zuciya ya sauke
tare da cewa '.mujiba meya faru ne kullum wayarki a kashe idan na kiraki ',bolaji tayi murmushi

tare da cewa ''tsabgogi ne sukayi min yawa shiyasa ma wayar nake mantawa da ita ,yasu hajiya
da zuhra ,ina zahra ?,nayi missing dinsu sosai',hisham yace'suna nan lafia ,ni kuma bakiyi
missing dina ba ko?',murmushi kawai tayi mai sauti ,hisham yacigaba da cewa 'ba na gari naje
abuja seminar amma gobe insha Allahu zan dawo ,da zarar na dawo zan zo in ganki ,hope kuma an dace ?',bolaji ta amsa da cewa 'sai dai goben in kazo kawai ",sannan kuma sai
tace masa 'abokinka ya warke fa ,dazu naji labarin wai ya farfado',hisham yayi murna sosai ,a
haka sukayi sallama da junansu akan gobe zai zo ,bolaji ta dubi wayar idanunta na fitar da
wasu zafafan hawaye soyayyar hisham da kuma tausayinsa ne yake nukurkusar zuciyarta! Washe gari fada aka tashi da shiryen shiryen walimar(DINNER) farfadowar hashim,bisa
umarnin fulani,dafe dafe kawai akeyi da gyare gyare ,palace event hall yasha ado da
decorations,duk wani abu da ake buqata tundaga kan mutanen da za a gayyata da kuma
abinda za'a ci asha duk is in order ,abin gwanin sha'awa sai wanda ya gani! Bolaji ita ma ba'a barta a baya duk da yawaitar faduwar gaban da ta ke yi hakan bai hanata
shiga cikinsu badiyya ta tayasu aiki ba,suna cikin yin aikin ne ,sultan ya aiko a kirawo masa ita
,jiki a sanyaye ta je ta same shi a palace parlour ,murmushi yayi mata tare da mi'ka mata wata
katuwar leda ,tare da cewa 'take this ,i want you to wear them for todays event ,i hope you love
it ',bolaji ta amshi ledar tare da cewa' thanks ',sannan ta wuce dakinsu ta ajje ledar ba tare da ta
bude ba, sannan ta dawo kitchen suka cigaba da baking and frying !
Ummu kuwa kanta ne ya dau chaji daga jiya zuwa yau,daga karshe kawai ta yo alwala tare da
yin sallah raka'a biyu tare da rokon Allah ya bayyana duk wani boyayyen al'amari ,ya kuma
bayyana gaskiya a duk inda take ,a haka tasamu zuciyarta tayi sanyi tare da kuma fawallawa
Allah lamarin fulani da sultan! Misalin karfe 7:00pm angama duk wani shirye shirye ,palace event hall ya zama ready,guest
sun fara isowa ,manyan mutane sun fara hallara !
Bolaji ta fito daga wanka ,ta shafa body lotion,badiyya ta tayata taje kanta tare da yi mata
packing,a lokacin ta tuna da ledar da sultan ya bata dazu, daukawa tayi ta bude ,red dinner
gown ne mai adon crystal stones ,hannunsa dogo ne,sai kuma red velvet turban shima anyi
masa ado da stones,da kuma high heel shoe silver mai adon cystal stones da kuma box of
diamond earring and wristwatch, badiyya ta saki baki tana yaba kyawun kayan ,tare da
tambayar bolaji da cewa 'ke kuwa mujiba ina kika samo wadannan kaya haka',bolaji ta dubeta
tare da cewa 'sultan ne ya bani su dazu....',,badiyya ta tabe baki tare da cewa 'ban san meye
hujjarki na kula wannan yaron ba ,ko da kuwa fansa kike san dauka akansa bai dace ki amshi
soyayyarsa tare da kuma kayansa ba',bolaji tayi murmushi tare da cewa 'laifine idan na amshi
kyauta daga gun kanin miji na',badiyya zata bata amsa kenan wata kuyanga tayi sallama
tashigo dakin tare da cewa 'badiyya kizo jakadiya na nemanmu agun taron walima ', daman a
shirye take,kawai sai ta tashi ta fice , bolaji ta shirya cikin gown din ,kayan sun amshe ta
sosai,light and flawless make up kawai tayi powder ta murzawa fuskarta sannan ta shafa gloss
a lebanta ,tayi kyau sosai ',ta saka earring da wrist watch ,sannan ta sanya takalmin,ko da ta
kalli kanta madubi ita ma ta yaba da kyawun fuskar mujiba,murmushi tayiwa kanta sannan ta
fice daga dakin!
A parlour suka hadu da fulani ta ci ado da leshi da gold ,ga kuma alkyabba ,hadimai na biye da
ita ,fulani ta dakata tare da duban mujiba tace 'wow kin yi kyau mujiba '',bolaji tayi murumshi
tare da sunkuyar da kanta ,fulani tace 'kije ku taho tare da souldear ,angama shiryashi ',fulani

nagama fadin haka ta bar wajen ita da hadimai suka wuce wajen walima !
Bolaji ta wuce dakinsu(ita da hashim),a shirye ta iske hashim zaune akan wheel chair ,yayi kyau
sosai har ya gaji da kyau,bolaji ta karasa ta gaishe shi tare da taya shi murnar samun lafiyarsa
,murmushi yayi mata tarea dacewa 'all thanks to you mujiba ,you just acted like my late wife
,nagode sosai da kulawarki gareni ,amma ina son in tambayeki wani abu mana?', bolaji tace 'ina
sauraronka ',hashim yace 'taya kika san cewa matata tana kirana da oga hitler?',bolaji tayi
murmushi tare da cewa 'ummanka ce ta bani labarin ka da matarka ,saboda tanason in maye
gurbinta a wajenka....',hashim ya katseta ta hanyar cewa 'i'm sorry to say mujiba ,a gaskiya no
one can replace my better half,she's irreplaceable in my heart ,ita kadai ce macen da na fara so
a raùuwata ,kuma itace ta karshe ,you can act like her but you can never be her,i will keep on
loving my better till my last breath ,so bazan iya aurenki ba mujiba, saboda na daukar wa kaina
alkwawarin ni da aure èar abada ,tun da na rasa mata ta ,babu wacce zata iya maye mini
gurbinta a zuciyata ',sannan ya goge kwallan daya zubo masa daga ido , sannan yace'bakin
ciki na daya a duniya rashin samun soyayyarta a gareni.....',bolaji ta katseshi ta hanyar cewa
'Allah ya jikanta ya rahamsheta,muje we are running late....',sannan ta turashi akan wheelchair
sukafice daga dakin!
Palace event hall ya cika ùa batse da manyan mutane tun daga kan sarakuna har izuwa
gwamnoni da kuma business tycoons ,a gaban kofar shiga hall din sultan ne a tsaye sanye da
redvelvet suede suit tare da farin shirt da black cover shoe ,yayi kyau sosai,su bolaji na isowa
ya tare su da murmushi sannan ya durkusa ya rungume hashim yana cewa 'bro u look
handsome',hashim ya buga bayansa tare da cewa 'thanks ',sultan ya mike tsaye ya dubi bolaji
cike da shauki ya matsa kusa da ita yana mai mata rada a kunne da cewa 'wow you look
gorgeous,magnificent,beautifull and elegant my love ',matsawa tayi kadan tare da cewa 'all
thanks to you ',hannunsa ya dora akan wheelchair din suka tura hashim ,a daidai lokacin
hisham ya iso gun bisa jagorancin royal guard !
kiran sunan mujiba yayi ,hakan yasa ta juyo ,murmushi yayi mata tare da mikawa sultan hannu
sukayi musabaha ,sannan ya durkusa gaban hashim sukayi musbaha tare da rungume juna
suna masu murnar ganin junansu ,hashim cike da murna yace 'hisham kenan tunda muka
gama NMS muka watsar da junanmu ',sultan ya katsesu ta hanyar cewa 'save all that for some
other time ,the guest are waiting !
A haka su hudu suka dunguma suka shiga hall din!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 11:47 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~57~
Suna shiga hall din kallo ya dawo kansu ,kasancewar spotlight din daya haskaka su, a haka
suka karasa table din da'aka tanadar musu ,kasancewar the hall is decorated with round tables
masu dauke da sixchairs,bayan ko wannensu ya zauna ,hashim shima aka gyara masa
zamansa akan wheelchair,sai governor na wannan lokacin ne ya hau stage ya bude taro da
addu'a tare da taya mai martaba da iyalansa murnar farfadowar yarima hashim,mai martaba
shi ma ya fita yayi nasa jawabin tare da yin godiya ga Allah ,haka zalika ummu da fulani su ma

sun hau stage sunyi nasu jawabin,daga nan sai hadimai suka fara serving ,bayan angama
refreshment,firstlady din garin sokoto ta fito ta bada tarihin masarautar modibbo ,daga nan
sultan ya fita shima ya bada tarihin hashim ,sai kuma hisham ya tura hashim zuwa stage
din,sultan ya bashi mic ,da farko yayi godiya sosai ga Allah,iyayensa da kuma guests din suka
hallarci wannan taro ,sannan kuma ya bukaci ayiwa marigayiya bolaji addua tare da kuma yi wa
kowa fatan komawa gida lafia!, hisham ne ya tura shi suka koma mazauninsu ,masu daukan
hoto sunayi masu video taping suma sunayi ,yayan manya kuwa sai selfie suke ana dorawa a
instagaram ,sultan ya amshi mic tare da cewa " i want to make an important announcement but
please i want mujiba to come forward to the stage',bolaji gabanta ne ya fadi ,gashi an kuma
haskota da spotlight ,hisham ne yayi mata murmushi tare da yi mata alamun cewa tashi kije
,domin ko kadan bai kawo komai a ransa ba ,hakan yasa bolaji ta tashi ta tafi stage ,kowa ya
yaba da class and charisma dinta,domin kayanta sunyi mata kyau matu'ka ,sultan ne ya dubeta
yayi murmushi sannan ya dawo da kallonsa ga jama'a yana cewa 'this is mujiba ,the love of my
life,the half that completes me ,my wife to be insha Allah .......',hisham hankalinsa ya
tashi,idanunsa sukayi jajawur saboda wani irin zazzafan kishi dake nukurkusarsa,ranshi a bace
ya tashi ya fita daga hall din ba tare da yayi wa hashim sallama ba ,akan stage kuwa sultan
yayiwa wata hadima alamu da hannunsa ,hadima ta karaso rike da wani farantin gwal a
hannunta mai dauke da ring box,sultan ya bude box din ya ciro diamond ring din,sannan ya
durkusa a gaban bolaji ,tuni hall aka fara tafi ,yan mata da samari suka fara daukansu hoto
,fulani idan ranta yayi dubu yaa baci,,sultan ya kamo hannun bolaji yana cewa 'mujiba i want
you to be my mrs,i want you to be the mother of my children,i want you to complete me and
spend the rest of ur life with me ,mujiba will you marry me ?",bolaji ta fisge hannunta ,tare da
cewa 'No ,i will not and will never marry you',sannan ta juya ta sauka daga kan stage din,tare da
ficewa daga hall din gaba daya,sultan kuwa mutuwar tsugunne yayi !
Bolaji tana fita daga hall ,hisham ya tareta sannan ya damki hannunta ya jata zuwa inda yayi
parking motarsa ,idanu jajir ya dubeta tare da kama kafadarta yana cewa 'mujiba menene
tsakaninki da sultan?',bolaji jikinta na rawa saboda ta tsorata da yanayinsa tace 'wallahi tallahi
babu wani abu tsakanina dashi ....',hisham yace 'toh shikenan,shiga mota mu koma
gida,zamanki a palace dinnan ya kare,domin bazan zuba ido wani kato ya kwacemin ke ba
....',bolaji ta katseshi ta hanyar cewa 'hisham kayi hakuri bazan iya bin ka ba',hisham ransa a
bace yace 'saboda ki zauna da masoyinki ko ?,saboda kin samu wanda ya fini ko ?.... ',bolaji
idanunta suka fara tsiyayar hawaye saboda kalaman hisham sun soki zuciyarta ,murya a
raunane tace 'hisham try and understand my memory is back ,ni matar aure ce ,hashim ne
mijina ',hisham mutuwar tsaye yayi ,baki bude ya tsaya kallon bolaji ,sannan kawai ya kwashe
da dariya wanda yazo da zubar hawaye yace 'mujiba kenan ,ta nan kika bullo ,daman
tsintacciyar mage bata mage ,kwadayi da son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login