Showing 12001 words to 15000 words out of 61652 words

Chapter 5 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4051

isha ,kowannesu ya shige [tent] ya kwanta ,hashim zuciyarsa
tafarfasa take ga abinda bolaji ta aiketa a gareshi ,domin tunda uwarsa ta haifeshi ,mace bata
ta6a d'aga masa murya ba,balle kuma ace tasa hannu ta mareshi,ya zama dole ya koyawa
bolaji hankali,saboda ba'a ta6a CAPT.YARIMA HASHIM ATTAHIRU MODIBBO! a kuma zauna
lafiya ,ya zama dole ya d'au fansa ga marin da bolaji tayi masa!
Yana mai shafa kumatunsa!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL=YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~15~

Furucin bamidele ne yasa bolaji dake kwance akan gawar maami tana risgar kuka d'agowa
tare da kai dubanta ga gawar babalaji da ke kwance a jikin bamidele!
A fusace bolaji ta mi'ke tsaye cikin zafin nama ta tunkari hashim da ke tsaye 'kikam ko gezau
bai motsa ba ,sojoji na bayansa ,fuskarsu a mutur'ke,hannunsu ri'ke da bindigu!
Bolaji ta dage iya 'karfinta ta d'aga hannu tare da ware yatsunta guda biyar,ta zabgawa
kumatun hashim mari gudu uku kyawawa,d'aya bayan d'aya,kuma hagu da dama!
Ji kake GAU! GAU! GAU!
Hashim yana tsaye 'kikam ko 'kadan marin bai sa ya motsa ba,yana tsaye daram saikace dutse!
Da sauri sojoji su ka yo mata caaa da bindigarsu !
Hashim ya dakatar dasu ta hanyar d'aga musu hannunsa guda d'aya!

Bolaji tasa hannu ta cakumi kwalar khakinsa,jajayen idanunta akan nasa,muryarta a kausashe
ta fara ce masa
''who the hell are you?,
what gave you the right to slap my mother?,
what sort of crime did my mother commit,that you can't wait for her to give birth!
if you don't have respect for womanhood ,you ought to have respect for motherhood?
why is own your case different?'' Bolaji ta tambaya cikin karaji ,hannunta ri'ke da kwalar
khakinsa ta maimata kalmar 'WHY?'
Hashim ya rintse idanunsa gam,duk tsigar jikinsa ya tashi,gashin jikinsa duk suka
mimmi'ke,jijiyoyin jikinsa duk suka kumbura!
Bolaji ta cika masa kwalar khakinsa,ta fara dukan 'kirjinsa da hannunta duka biyun ,tana kuka

tana cewa'
You are heartless! Ruthless! You are so evil and mean!
You are an imbecile,a monster!,you have no heart at all!
Hashim bud'e idanunsa yayi da sukayi jajir ya d'amki hannayen bolaji da take dukan 'kirjansa
dasu!
Cike da zafin nama yayi watsi da ita,wanda hakan yayi sanadiyar fad'uwarta 'kasa,ta kuma buge
goshinta da jikin gadon da gawar maami ke kwance!
Tashi tayi zaune da 'kyar ,ta dafe goshinta tana mai cigaba da risgar kuka ,ta d'aga kanta ta dubi
hashim da rinannun idanunta tace 'you are the cause of my parents death!
may you live long so as to live your life in sadness and sorrow! you will never know happiness
in your life,you will live your life in misery and pain..!'
Hashim a fusace ya d'aga hannunsa a dun'kule da niyyar naushinta! Sai kuma ya fasa,yayi
'kwafa yace 'we shall see!' ,sannan ya juya ya dubi sojojin yace dasu 'lets go !',
Bayan ficewarsu hashim daga d'akin ,su iya folake suka fashe da kuka suna masu tsinewa
wad'annan sojojin,domin basu ta6a zaton haka daga garesu ba,sun zata cewa ganin iya bolaji
a halin na'kuda zai sa su fasa aikata 'kudirinsu !
Jiki a sanyaye suka nufi bolaji suna lallashinta,suna kuma tsinewa wannan akurkin asibitin dake
fama da rashin wadatattun ma'aikJiki a sanyaye suka nufi bolaji suna lallashinta,suna kuma
tsinewa wannan akurkin asibitin dake fama da rashin wadatattun ma'aikata!
Iya ayomide ce ta fita taje ta sanarwa da mutanen yankin ,mutuwar babalaji da maami!
Cikin 'kan'kanin lokaci mutanen yankin suka zo asibitin da makara guda biyu , suka d'auki
gawar maami da babalaji,suka kai gida,aka musu wanka ,aka yi musu suttura,aka sallacesu
sannan aka sadasu da gidansu na gaskiya!
Bolaji da bamidele sun sha kuka sosai,domin kowa ya tausayawa musu !
¤¤¤¤
Wayar hashim ce tayi ringing ,sai da wayar ta kusan tsinkewa sannan hashim d'in ya amsa,yana
amsawa kuwa,a d'aya bangaren fulani ce ta washe baki tana cewa 'my souldear,dafatan ka
d'auki fansa ga jinin da mutanen oduduwa suka fitar daga goshin mahaifinka ko?', da 'eh'
hashim ya bata amsa ,fulani tayi 'kasa da murya tana cewa 'yawwa my souldear,the soldier of
the nation,yanzu abinda nake so da kai ,shine ina son kajawa MD da sauran ma'aikatan
kamfanin kunnen da kada su kuskura mahaifinku yaji labarin zuwanka erin' ,hashim yace
'angama umma' ,fulani tace 'kasan halinsa na 'kaunar YARE da talakawa,yanzu yana samun
labarin zuwanka ,zai tadawa mutane hankali a banza,kaima idan kunyi waya ,kada ma ka nuna
masa cewa kasan da zancen mutanen oduduwa sun jefeshi da dutse',a haka sukayi
sallamWayar hashim ce tayi ringing ,sai da wayar ta kusan tsinkewa sannan hashim d'in ya
amsa,yana amsawa kuwa,a d'aya bangaren fulani ce ta washe baki tana cewa 'my
souldear,dafatan ka d'auki fansa ga jinin da mutanen oduduwa suka fitar daga goshin
mahaifinka ko?', da 'eh' hashim ya bata amsa ,fulani tayi 'kasa da murya tana cewa 'yawwa my
souldear,the soldier of the nation,yanzu abinda nake so da kai ,shine ina son kajawa MD da
sauran ma'aikatan kamfanin kunnen da kada su kuskura mahaifinku yaji labarin zuwanka erin'
,hashim yace 'angama umma' ,fulani tace 'kasan halinsa na 'kaunar YARE da talakawa,yanzu
yana samun labarin zuwanka ,zai tadawa mutane hankali a banza,kaima idan kunyi waya ,kada
ma ka nuna masa cewa kasan da zancen mutanen oduduwa sun jefeshi da dutse',a haka

sukayi sallama!
Hashim kuwa, ya cika umarnin fulani ,ta hanyar jawa MD da sauran ma'aikata kunne da kada su
kuskura ya ji labarin cewa sun shaidawa mai martaba zuwansa da sojoji yankin erin,in ba haka
ba zasu yabawa aya za'kinta' ,MD da sauran ma'aikata jiki na rawa suka amsa da 'toh!'
Cikin dare hashim da sauran sojoji ,suka samu daji acikin yankin erin suka yada zango ,domin
hashim ya buga waya can kaduna ya nemi izini akan cewa sai nan da kwana hud'u zasu
dawo,domin basu gama da abinda ya kawosu yankin erin ba!
A dajin suka kafa {tent},kuma duk abinda xasu bu'kata ,hashim ya amshi kud'i gu MD,sun je
kasuwa sun siyo!
Bayan sun gabatar da sallar isha ,kowannesu ya shige [tent] ya kwanta ,hashim zuciyarsa
tafarfasa take ga abinda bolaji ta aiketa a gareshi ,domin tunda uwarsa ta haifeshi ,mace bata
ta6a d'aga masa murya ba,balle kuma ace tasa hannu ta mareshi,ya zama dole ya koyawa
bolaji hankali,saboda ba'a ta6a CAPT.YARIMA HASHIM ATTAHIRU MODIBBO! a kuma zauna
lafiya ,ya zama dole ya d'au fansa ga marin da bolaji tayi masa!
Yana mai shafa kumatunsa!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 10:51 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE


~16~

Bolaji in banda kuka da ajiyar zuciya da yin addu'o'i babu abinda takeyi,kowa ya ganta sai ya
tausaya mata duk ta 'kara yin duhu ta rame,haka zalika bamidele ya shiga wani hali sanadiyar
rasuwar iyayensa,a haka suka cigaba da amsar gaisuwa har akayi sadakar Uku!

Cikin dare bolaji da bamidele suna Zaune a tsakar gida tare da wasu dangin iyayensu wanda
basu wuce guda goma ba!

Kawai sai ganin sojoji sukayi sun fad'o gidan batare da sallama ba,wanda hakan yasa gaba
d'ayansu suka tsure in an d'auke bolaji !
Tsoro ya bayyana 'karara akan fuskar bamidele wanda a yanzu in akwai abinda yake tsoro a
duniya toh bai wuce soja ba!

Gadan gadan sojojin sukayi kan bolaji dake zaune akan darduma sanye da hijab,ko kad'an bata
tsorata ba!
Cicci6arta sukayi,tare da ficewa da ita waje, batare da kowa yayi yun'kurin hanasu ba,ita kanta
bolaji kallonsu kawai take taga iya gudun ruwansu,hakan yasa tayi lamo a hannunsu!
Dajin da suka yada zango suka wuce da ita! Yan yankin erin suka fito daga gidanjensu, suna
kallon yadda sojojin suka wuce da bolaji daji ,suna masu tausayawa mata,da kuma tsinewa
capt.hashim a zukatansu,suna son taimakawa bolaji ,amma babu hali domin suna tsoron a

harbesu!
Capt.hashim yana zaune akan wani kututturen icce dake tsakiyar dajin,sanye yake da ba'kar
body hug ,da kuma wandon khaki,fuskarsa babu annuri ko kad'an!
Ko da sojojin suka iso gareshi,sai suka watsar da bolaji a gaban kafafunsa!
Hashim ya d'aga kai ya dubesu yace 'leave us alone!',sannan ya dawo da dubansa ga bolaji
wacce ta tashi zaune tana kakka6e hijabinta!
Tsawa ya daka mata yana cewa 'hey! behave your self!' ,she'ke'ke ta tsaya kallonsa ,sannan ta
kai dubanta ga dajin idanu,wanda hasken wata ne ya haska Tsawa ya daka mata yana cewa
'hey! behave your self!' ,she'ke'ke ta tsaya kallonsa ,sannan ta kai dubanta ga dajin
idanu,wanda hasken wata ne ya haskake!
Sannan tayi 'kwafa ta cigaba da kakka6e hijabinta ba tare da tasan me take kakka6ewa!
Murya a kausashe hashim yace 'hey....' ,bolaji tayi saurin katseshi ta hanyar cewa 'abeg oh,free
me jorh,na wetin,ahh the wickedness wey do me ,never do you?
oya kill me too,make i go join my parent for heaven.....'' ,hashim ne ya katseta ta hanyar cewa
'keep your mouth shut! don't you have manners,i'm talking you are talking ,who is the master
here! 'GOD!' ,bolaji ta bashi amsa tana mai tashi tsaye sannan ta she'ke da dariya wanda ya
taho da zubar hawaye daga idanunta,tana tafa hannayenta tace'see who's talking about
manners oh,manners my feet!' ,hashim a zafafe ya mi'ke ,idanunsa jajir ya nunata da yatsa
yana cewa 'don't try to mess with me ,cause you don't know what i'm capable of doing to you!'
,bolaji ta chafke ta hanyar cewa 'you are capable of killing,so i'm not scared of you .cause you
have done enough damage to my life,so what else are going to do ,to me? Kill me?' bolaji ta
tambayeshi tana mai tsurawa idanunsa ido!

Hashim zuciyarsa na tafasa yasa hannu d'aya ya fisgota ta fad'o kirjinsa,ya ri'keta gam!

Bolaji tasa Hannu tana dukan 'kirjinsa tana cewa 'get your filthy hands off me,you imbecile!
Animal! Monster! I said get your...!'

A zafafe Hashim ya katseta ta hanyar manna mata pinklips d'insa akan nata...,hakan yasa
numfashin bolaji ya tsaya cak!
Sai da hashim yayi minti talatin yana kissing d'inta,sannan ya cikata ta fad'i 'kasa wanwar a
sume ,ya wuce ya barta anan a kwance!

Ya umarci sauran sojojin dasu fito da motoci ,saboda cikin daren nan yake son su koma
kadunYa umarci sauran sojojin dasu fito da motoci ,saboda cikin daren nan yake son su koma
kaduna!
Da hanzari suka had'a komatsansu,suka watsa a motocinsu,sannan suka bar dajin suka d'au
hanyar komawa kaduna !
Batare kowannensu ya bi takan
Bolaji dake kwance a sume a tsakiyar dajin!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL

[10/16, 11:01 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE


~17~

Ganin ficewar motocin sojoji daga dajin yasa mutanen yankin ,suka yanke shawarar shiga
dajin domin nemo bolaji!
Haka suka d'unguma hannunsu ri'ke da torchlight suka shiga dajin!
A tsakiyar daji suka tadda bolaji yashe a kwance ,cikin hanzari suka sungumeta suka kaita
gida,a d'akinta suka kwantar da ita!
Iya folake ce ta yayyafawa bolaji ruwan tulu,ajiyar zuciya bolaji ta sauke ,tare da bud'e
idanunta,ganin mutane sun tsaya cirko cirko suna ce mata 'kpele oh',yasa ta yi 'karfin halin tashi
zaune tana murmushi,iya folake ce tayi caraf tace 'bolaji,wetin happen,wetin the devil did to you
again?, murmushi bolaji tayi ta amsa da 'nothing,i just fainted due to stress',nan dai kowa yayi
mata sannu ya fice!
Bamidele ya matso yana cewa 'hope you are ok?, 'yes i'm ok' ,bolaji ta amsa masa,sannan yayi
mata sannu ya fice bayan ya rufeta da bargo!
Ficewarsa ke da wuya ,bolaji ta tashi zaune ta fara goge le6enta da hannunta ,tana mai tsinewa
capt.hashim albarka,wanda a zuciyarta ta la'kaba masa suna 'OGA HITLER',domin ya cancanta
da a kirashi da wannan suna,saboda rashin imaninsa,a haka ta kwanta idanunta na zubar da
hawaye tana mai yiwa iyayenta addu'a a zuci! A haka gwanin sata ya saceta!
Washegari taji labarin cewa capt.hashim da tawagarsa sun bar yankin a daren jiya!

¤¤¤

Ranar sadakar bakwai MD yazo gidansu bolaji yayi masu gaisuwa tare da basu albashin
babalaji kamar yadda ya biya sauran 'kananun ma'aikata albashinsu!

Sannan kuma ya jajanta musu ga abinda hashim ya aikata a garesu ,inda kuma ya fahimtar
dasu cewa babu sa hannun mai martaba sam, da abinda hashim ya aikata a garesu,ya kuma
sanar da bolaji wanene mai martaba? Wanene hashim!
Anan take taji ta kamu da 'kaunar mai martaba da halayensa,yayin da 'kiyayyar hashim da
halayensa suka 'kara ninkuwa a zuciyarta

¤¤¤

A yau sultan zai wuce enugu bautar 'kasa,fulani ce ta zaunar dashi a d'akinta tana mai yi masa
magana kamar haka 'sultan ina son ka bud'e kunnuwanka kaji abinda zan fad'a maka da
kyau,nasan cewa zuwanka malaysia karatu ne yasa ka zama gawurtaccen manemin
mata',sultan a razane ya bud'e baki zaiyi magana ,fulani ta dakatar dashi ta hanyar cewa 'ka

bari in dire tukun,kana mamakin yadda akayi nasani ko,ba abin mamaki bane idan nace maka
inada mutanen dana wakilta su d'inga bibiyarka,domin naga kai kanada rawar kai ,ba kamar
yayanka ba ,namiji managarci,wanda mace bata dameshi ba ko kad'an ,kuma gashi bashi da
matsala,na yarda dashi d'ari bisa d'ari ' fulani ta cigaba da cewa 'duk ba wannan ba,yanzu
abinda nakeso da kai shine ,kar ka kuskura ka nemi matan enugu,inyamurai masu 'karnin
janaba,kai in ta'kaice maka kawai bana son ko da wasa ka kuskura ka nemi macen da ta
kasance ba YAREN hausa/fulani ba,domin sa6awa hakan na nufin tabbatar tsinuwata
akanka,tashi ka tafi ,ALLAH ya tsare ,ya kuma kareka daga musibar inyamurai masu mugun
hali',jiki a sanyaye sultan ya mi'ke ya fice yana mamakin kiyayyar da mahaifiyarsa tayi wa
YARE!
A haka ya fito,royal chaffeur ya wuce dashi airport,ya hau jirgi ya wuce enugu, Bayan yayi
sallama da ummu da mai martaba!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/16, 11:02 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

~18~

Kwanaki,satuttuka da watanni sun shud'e!

Cikin ikon Allah Sultan ya fara gudanar da bautar 'kasarsa a jihar enugu,kuma da alamu
kashedin da fulani tayi masa yayi tasiri a kansa!

Bolaji da bamidele suna tafiyar da rayuwarsu cikin kwanciyar hankali,da kuma taimakon Allah
,maraicinsu baisa sun ha'kura da cigaba da gudanar da rayuwarsu ba!

kasancewar 'kudin albashin mahaifinsu da MD ya basu da d'an kauri,da kudin bolaji ta fara
'kananun sana'o'i a cikin gida,tana gasa doya,agada[plantain] da masara,kuma alhamdulillah
tana ciniki Allah ya sawa sana'ar tata albarka ,yayin da bamidele ya cigaba da sana'arshi na
siyar da bunburutu,basu nemi wani abu ba sun rasa!
Yan yankin erin,sun yanke shawara sun had'a kai sun bawa bolaji da bamidele kyautar wani
wawakaken gona bisa dalilin ganin cewa kamar ta sanadiyarsu ne mahaifansu suka rasa
rayuwankansu!
Sunyi farin ciki da wannan halaccin da yan yankin suka musu,kuma sunyi godiya!
¤¤¤
Hashim kuwa ko da suka isa kaduna, bai 'waiwayi ,masauratar modibbo,tsakaninsa da su
waya,a kullum suka tambayeshi rashin zuwansa ,sai yace masu aiki ne yayi masa yawa!
Hashim gaba d'aya ya susuce,ya zama tamkar mara lafiya,zuciyarsa kullum a kuntacce
take,bai 'kara sanin wani abu wai shi farinciki ba tundaga ranar da ya mari maami,tunanin bolaji
yaùi masa katutu a zuciya,fuskarta kawai yake tunowa ,zuciyarsa tayi sanyi,a kullum yana

'karyata zuciyarsa ga abinda take bijiro masa akan bolaji!
yayi takaici,yayi bakinciki ga kamuwar zuciyarsa da wannan cuta,ya kai kukansa ga Allah akan
ya yaye masa wannan mugun ciwon,duk sujjadar da zaiyi a sallah,sai ya kai kukansa ga Allah
,amma duk a banza!
Domin a yanzu ya gama amincewa Allah ne ya jarabceshi da wannan cuta a zuciya ,wanda
maganin wannan ciwo ita ce BOLAJI!

¤¤¤
A yau hashim ya yanke shawarar zuwa garin sokoto!
Cikin ikon Allah ya iso masarautar modibbo!
Bayan ya gama gaisawa da mahaifansa,anyi hirar yaushe rabo,sannan fulani ta ja shi d'akinta
ta sanar dashi cewa tayi masa mata ,d'iyar yayarta da suke uwa d'aya uba d'aya ,hashim ya
tambaya ' umma wacece ita?' ,fulani ta amsa masa da 'NAWWARA ce,d'iyar anty mannira,last
two weeks ta dawo daga U.s.a ,ta kamalla degree d'inta,my souldear na gaji da ganinka haka
ba tare da kayi aure ba!
Hashim ya numfasa yace'umma ina mai neman alfarmar da ki bani lokaci ,in yi tunani
akai',fulani da fara'arta tace masa 'no problem my soul dear,take your time,kawai dai ina son
kasan da zancen auranka da nawwara ne' !

Cikin dare hashim ya je ya samu mai martaba a falonsa shi kad'ai yana shirin zuwa d'akin
ummu,bayan sun d'anyi barkwanci,sai hashim yayi gyaran murya ya fara cewa ' abba na zo ne
akan yarinyar da nake son aure,ina neman alfarmar aje yankin erin ,a nema mini auranta!
Mai martaba yayi mamakin jin kalaman hashim sosai sai ya dubi hashim d'in tare da jifansa da
tambayar cewa 'ta yaya kuka had'u da ita?',hashim yan sosa 'keya yace 'mun had'u ne a lokacin
da mukaje yankin kwantar da wata tarzoma,kuma munyi amanna da junanmu,itace ma tace in
turo',mai martaba yace 'toh shikenan ,zamu je mu nemo maka auranta,ALLAH ya sanya alkhairi'
,'ameen,kuma ina neman alfarmar dan Allah kar ka sanar da ummata,saboda....' ,mai martaba
ya katseshi ta hanyar cewa 'kar ka damu,in dai fulani ce,nasan ta yadda zan 6ullo mata,kar kaji
komai'

hashim yayi godiya suka yi sallama!

¤¤¤
A yau mai martaba ya had'a manyan mutanen da zasu masa rakiya zuwa garin osun,yankin
erin,domin nemawa CAP.T YARIMA HASHIM auran BOLAJI!

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL=YARE BIYU=
{ 2tribes }
na ILILEE

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login