Showing 57001 words to 60000 words out of 61652 words

Chapter 20 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4035

yana sona,lokacin da zancen yaje gaban
iyayena,sam babana yace bai san zance ba ,haka zalika yangidanmu suka sani a gaba da
cewa me zanyi da inyamiri kuma arne ,ni kuwa nace na ji na gani haka nakeson abuna ,anyi
fama da ni sosai akan in hakura da patrick amma ina nayi nisa ,shi kanshi patrick din ya hakura
amma ni ban hakura ba,na daura gaba da kowa da kuma abinci,ganin za'a rasa ni yasa babana
ya amince da aurenmu ,bayan patrick ya amshi musulunci,a ranar da ya gama bautar kasa a
ranar aka hadamin jakar kayana ,akace in bi mijina ,tare da cemin duk abinda ya sameni inyi
kuka da kaina ,ni kuwa murna fal cikina na bi mijina garinsu abia state ,ko da muka a isa garin
abia ,naga tashin hankali da masifa a gun mahaifansa domin uwarsa kuka ta dinga yi tana ihu
kamar wacce akace mata gobe zata mutu ,a lokacin da ya shaida musu wacece ni,danginsa
kuwa cewa sukayi basu san zance ba ,kawai su dai ya sakeni ya maidani garinmu faqat ,wai
ina shi ina auren bahaushiya kuma musulma ,patrick shima yayi musu kunnen uwar shegu tare
da yin rantsuwar cewa babu abinda zai rabani dashi sai mutuwa ,a haka ya kaini dakinsa ya ajje
ni ,ya nemo min abinda zanci,tare da kwantar mini da hankali ,ni kuma a lokacin ina mamakin
ganin yadda suke tada jijiyoyin wuya don kawai ya aureni ,idan kuma sun san cewa ya
musulunta fa me zai faru ,domin sarkin yankinsu har gida yazo ya sami patrick game da batuna
,shikuma patrick yace shi fa yana kan bakansa,a haka suka kyaleshi,cikin dare bayan munyi
sallolin mu ,mun kwanta kenan,sai kawai ciwon ciki ya murdeshi ,kafin ace me ,ya fara aman
jini ,ina ji ina gani patrick ya cika da kalmar shahada ,nayi kuka sosai a wannan daren,gashi
kuma ina tsoron in fita in shaida masu ,sai washe gari da safe ,na fito daga dakin idona zuru
zuru ,duk na fige ,a zuciyata ina mai cewa shikenan na rasa patrick a daren dana tare a
matsayin matarsa ,lokacin dana shaida musu cewa patrick ya mutu,naga bala'i,cewa sukayi ni
na kasheshi,duka suka min mai sunan duka ,sannan suka min askin kwal kwal , suka kulle ni a
wani daki mai shegen duhu ,da gani sai daurin kirjin bakin yadi ne a jikina,sai dana shafe kwana
bakwai ina shan ruwan wankar gawar patrick,basa bani abinci ,kullum sai an tambayeni in fadi
gaskiya ni na kashe patrick ,ni kuma sai na dinga rantse musu da cewa bani ba ce ,a rana na

takwas da rasuwarsa,wasu manyan mata guda shida suka zo dakin danake ciki a kulle ,ina ji
ina gani ,suka kwantar dani tare da waremin kafafuna ,suka zambada min dakakken barkonon
su (alligator pepper) a gabana ,ji nayi tamkar an zare min rai a lokacin ,a sume suka fice suka
barni,sai danayi kwana biyu suna zuwa suna zuba min barkonon a gabana su fita su barni a
sume, cikin wani dare bayan na farfado, duk na bi na fita hayyacina ,dani da tababbiya babu
banbanci,wata mata ce tashigo ta sameni jikinta na rawa ,ta bani kaya na saka ,sannan ta bani
abinci naci ,ta bani umarnini in tashi muje ,ko da muka fito ko ina tsit , haka ta rike min hannu ta
kaini wajen mararrabar yankin nasu ,ta bani kudi tace in mike wata hanya har tasha zata kaini in
hau motar garin mu in tafi ,saannan ta juya ta tafi ta barni ,na ci bakar wahala kafin in iso garin
sokoto ,ko da na iso gida babu wanda ya ganeni an dauka mahaukaciya ce,sai daga baya suka
gane nice ,asibiti aka kaini sannan aka hada da bani rubutu inasha ,sannan na dawo daidai ,sai
da kowa ya tausayamin a lokacin dana basu labarin abinda yafaru ,ni kuma tun daga lokacin na
tsani duk wani YARE ,in har ba hausa fulani ba ,......

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Fulani cikin muryar kuka ta dubi mai mai martaba tace"kai kanka ka aureni ba tare da kasan
wannan labarin ba ,kawai dai kasan na taba yin aure mijin ya mutu",sannan ta dora da
cewa"wannan dalilin ne yasa na tsani YARE...!

Written by : ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL=YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~61~
Ko da nawwara ta koma 'daki ,bamidele ko juyowa bai yi ba,hakan yasa ta chanja kayan jikinta
izuwa na bacci ,ita ma ta hau gadon ta kwanta a bayansa ,murya a sanyaye ta fara cewa 'i
know you will be mad at me ,but pls & pls try and understand ,i'm scared of loosing you that's
why i kept quite...',rai a bace bamidele ya dago ya dubeta tare da cewa'you're scared of loosing
me? ,oh i can see ...just hear ur self out,how can u be so cruel and wicked ,i never thought a
day like this will come so soon that i wont be able to trust you anymore,and you know what
?,just pray that all this is a dream,cause if it is'nt.....',kawai sai yayi kwafa ya juya mata baya
,hakan yasa nawwara ita ma tayi kwanciyarta ,a zuciyarta tana mai cewa 'nasan ko ba jima ko
ba dade wannan ranar zatazo ,ranar da mijina zai sa almakashin saki ya datse duk wani igiyar
aure da so a tsakaninmu,ya Allah ka bani juriya da dauriyar karbar ko wanne irin hukunci da
mijina zai yanke min'

Sultan shi ma yana dakinsa yana fama da jinyar zazzabin rashin samun mujiba a matsayin
matar aurensa!

Hisham ya rasa mai yake masa dadi a duniya ,amma ya fawwalawa Allah lamurransa ,hakan
yasa ya fara samun kansa da nisanta zuciyarsa da soyayyar mujiba(bolaji) ,domin yana ji a
jikinsa ya rasa ta har abada ,amma a haka ya bar wa Allah zabi !
* * *

Washe gari misalin karfe 1:00pm ,ummu ta bukaci kowa (wato duk wanda lamarin 'batan bolaji
ya shafa ) ya bayyana kansa a turakar mai martaba ,wanda tun a daren jiya ta shaida masa
cewa akwai wata muhimmiyar boyayyiya a kasa da za' tono!

☆TURAKA☆
mai martaba ,ummu ,fulani,hashim,sultan,bolaji(mujiba),bamidele,nawwara ,badiyya,jakadiya
marakisiya,kurtagu,barde ,dr.ayuba ,da kuma baturen likita mai suna dr.albert!
Dukkansu sun hallara a turaka,masu mamakin wannan haduwa sunayi,wanda kuma cikinsu ya
gama durar ruwa ,suma nasu cikin nayi,sai kuma wanda suka fara kuka tun kafin a fallasa suma
sunayi!
Ummu ce ta fara yin sallama tare da kuma cewa 'ina son kowannenku a nan wajen ya kasance
mai fadin gaskiya a yayin da aka bukaci gaskiyar,domin gara aji kunyar duniya da akan aji
kunyar lahira',sannan kuma ta umarci bolaji ta fadi abinda ya faru gare ta.......'bolaji murya a
sanyaye ta fara bada labarinta tun daga ranar da hashim ya tafi liberia ,har izuwa ranar da
hisham ya kawo ta fada a matsayin kanwarsa' ,mai martaba,sultan,hashim da fulani tare da su
kurtagu mamaki ne ya kamasu kasancewar wai mujiba ce bolaji ,mussaman hashim da shi ya
kura mata idanu yana mai ganin wawancinsa da sokoncinsa na rashin gane matarsa bolaji tun
da take kula dashi ',ummu ta dubi sultan tace 'sultan abinda mujiba ta fada akan ka gaskiya
ne?',sultan idanunsa cike da hawayen nadama yace 'gaskiyane hakan ya faru ,amma har ga
Allah babu hannuna game da abinda ummu da nawwara sukayi mata ,domin ni da kaina a
wannan daren na koma domin dauko bolaji,sai ban tarar da ita ba,amma a kullum addu'a ta
itace Allah ya bayyana mana ita idan tana raye',ummu ta sauke numfashi sannan ta dubi
nawwara tace 'ke kuma me zaki ce game da wannan al'amari',nawwara ta sadda kai tare da
cewa 'gaskiya nasan na aikata babban kuskure ,amma ko ma menene duk makircin umma
fulani ne,domin ta aikata komai bisa kiyayyar da takeyiwa YARE ....amma ni ina neman afuwa
domin ni na riga na saduda kuma Allah ya riga ya nuna min ishara ta hanyar sanya min
soyayyar dan uwan bolaji a zuciyata ,wanda a yanzu haka yake a matsayin mijina",ummu ta
dubi su jakadiya ,kurtagu da barde tare da neman jin ta bakinsu,jikinsu na rawa suka amsa
laifinsu tare da neman sassauci daga gun mai martaba da yarima hashim!
Fulani ji take tamkar kasa ya tsage ta fada viki don tsabagen kunya ,mussaman hashim da
yake mata wani irin kallo ta da ta kasa tantacewa ,ummu ce ta katse mata tunani ta hanyar
cewa 'fulani muna son muji daga gareki ,ki kuma fayyace mana gaskiyar al'amari ga me da
gawar da kika kawo a matsayin gawar bolaji',fulani na zubda hawaye ta labarta musu yadda ta
je gun dr.ayuba ta amshi gawa!',ummu ta dubi Dr.ayuba tare da cewa 'ayuba shin abinda fulani
ta fada gaskiya ne ?",Dr.ayuba jiki na rawa yace 'gaskiyane amma wallahi tallahi da niyyar
taimako na bata gawar", nan ya kwashe yadda sukayi da fulani ya shaida musu ,tare da rokon
dan Allah a rufa masa asiri ',ummu ta juya ta dubi mairmataba tare da cewa 'toh mai martaba
kaji dai duk yanda abubuwa suka faru ,kuma hukunci ya rage gareka',sannan kuma ta umarci
Dr.albert ya miko DNA test result ,bayan an mikawa mai martaba result din ,sai ummu ta labarta
masa rawar data taka ,tun daga ranar da taje ta tadda mujiba(bolaji) kwance akan kirjin hashim
har izuwa daren jiya da likita yazo ya debi jinin bamidele da mujiba (bolaji)!
Maimartaba yayi gyaran murya tare da cewa 'a gaskiya na yi mamakin faruwar wannan al'amari
,duniya kenan ,kana naka Allah na nashi,kun cutar da baiwar Allah ,kun salwantar mata da

rayuwa ,kun mata mafi munin makirci duk sabida ta kasance YARE",sannan ya dubi fulani yace
'fulani bazan taba mamakin ki ba domin kiyayyarki ga YARE a bayyane take ,amma ban taba
zaton zaki je to the extent of doing all this',mai martaba ya bude DNA test result ya karanta
sannan yace 'result dai ya nuna cewa jinin bamidele da mujiba yayi matching,wato kenan
mujiba ce bolaji ,Allahu Akbar ,Allah mabuwayi gagara misali,wallahi ko da ba'ayi test dinnan
ba,babu tantama ko kuma jayayya na kasancewa mujiba ce bolaji ",mai martaba ya dubi fulani
yayi murmushi mai ciwo yace"kin fitar da ita da hannunki domin nisantata da hashim da sultan
,kuma da hannunki kika amsheta a lokacin data dawo,har kike kokarin hada aurenta da
hashim,kuma sultan shima yake kokarin aurenta ,kinga kenan Allah ya nuna miki ishara da
wannan kadai ',fulani kuka take har da majina domin bata taba zaton akwai ranar da dubunta
zai cika ba ,a gaskiya wannan ranar tayi mata zuwan bazata domin batayiwa wannan ranar shiri
ba!
Bolaji kuwa kuka kawai take wanda ta rasa dalilin yinsa ,farin ciki zatayi ko kuma bakin
ciki?,sautin kukanta ne yasa hashim ya mike tsam akan kafafunsa daga kan wheel chair, ya
taho gareta ,ya kamota ya rungume tare da shafa bayanta cikin sigar lallashi !
Fulani jiki a sanyaye tazo gaban hashim da bolaji ta durkusa murya a raunane ta fara cewa 'ku
dubi girman Allah ku yafe min ,nasan na cutar da ku ,na cutar da soyayya da aure,ban cancanci
ku yafe min ba ,amma
dan Allah in ci arzikin kasancewa musulma yar uwarku ku yafe min',idanu jajir hashim ya
dubeta ,jijiyoyin jikinsa duk sun tashi ,kauda kansa yayi ya cigaba da rarrashin matarsa ,hakan
yasa fulani ta cigaba da cewa "nasan zaku so sanin dalilin da yasa bana kaunar YARE a
rayuwata,saboda komai yana faruwa ne bisa dalili da kuma sanadi ,kafin aure na da mai
martaba na taba yin aure....

♡ ♡ ♡ ♡ ♡ ♡
Soyayyata da PATRICK OKWONKWO ya samo asaline a lokacin da aka turoshi makarantar
mu bautan kasa ,lokacin ina ss3,ina sonshi yana sona,lokacin da zancen yaje gaban
iyayena,sam babana yace bai san zance ba ,haka zalika yangidanmu suka sani a gaba da
cewa me zanyi da inyamiri kuma arne ,ni kuwa nace na ji na gani haka nakeson abuna ,anyi
fama da ni sosai akan in hakura da patrick amma ina nayi nisa ,shi kanshi patrick din ya hakura
amma ni ban hakura ba,na daura gaba da kowa da kuma abinci,ganin za'a rasa ni yasa babana
ya amince da aurenmu ,bayan patrick ùa amshi musulunci,a ranar da ya gama bautar kasa a
ranar aka hadamin jakar kayana ,akace in bi mijina ,tare da cemin duk abinda ya sameni inyi
kuka da kaina ,ni kuwa murna fal cikina na bi mijina garinsu abia state ,ko da muka a isa garin
abia ,naga tashin hankali da masifa a gun mahaifansa domin uwarsa kuka ta dinga yi tana ihu
kamar wacce akace mata gobe zata mutu ,a lokacin da ya shaida musu wacece ni,danginsa
kuwa cewa sukayi basu san zance ba ,kawai su dai ya sakeni ya maidani garinmu faqat ,wai
ina shi ina auren bahaushiya kuma musulma ,patrick shima yayi musu kunnen uwar shegu tare
da yin rantsuwar cewa babu abinda zai rabani dashi sai mutuwa ,a haka ya kaini dakinsa ya ajje
ni ,ya nemo min abinda zanci,tare da kwantar mini da hankali ,ni kuma a lokacin ina mamakin
ganin yadda suke tada jijiyoyin wuya don kawai ya aureni ,idan kuma sun san cewa ya
musulunta fa me zai faru ,domin sarkin yankinsu har gida yazo ya sami patrick game da batuna
,shikuma patrick yace shi fa yana kan bakansa,a haka suka kyaleshi,cikin dare bayan munyi

sallolin mu ,mun kwanta kenan,sai kawai ciwon ciki ya murdeshi ,kafin ace me ,ya fara aman
jini ,ina ji ina gani patrick ya cika da kalmar shahada ,nayi kuka sosai a wannan daren,gashi
kuma ina tsoron in fita in shaida masu ,sai washe gari da safe ,na fito daga dakin idona zuru
zuru ,duk na fige ,a zuciyata ina mai cewa shikenan na rasa patrick a daren dana tare a
matsayin matarsa ,lokacin dana shaida musu cewa patrick ya mutu,naga bala'i,cewa sukayi ni
na kasheshi,duka suka min mai sunan duka ,sannan suka min askin kwal kwal , suka kulle ni a
wani daki mai shegen duhu ,da gani sai daurin kirjin bakin yadi ne a jikina,sai dana shafe kwana
bakwai ina shan ruwan wankar gawar patrick,basa bani abinci ,kullum sai an tambayeni in fadi
gaskiya ni na kashe patrick ,ni kuma sai na dinga rantse musu da cewa bani ba ce ,a rana na
takwas da rasuwarsa,wasu manyan mata guda shida suka zo dakin danake ciki a kulle ,ina ji
ina gani ,suka kwantar dani tare da waremin kafafuna ,suka zambada min dakakken barkonon
su (alligator pepper) a gabana ,ji nayi tamkar an zare min rai a lokacin ,a sume suka fice suka
barni,sai danayi kwana biyu suna zuwa suna zuba min barkonon a gabana su fita su barni a
sume, cikin wani dare bayan na farfado, duk na bi na fita hayyacina ,dani da tababbiya babu
banbanci,wata mata ce tashigo ta sameni jikinta na rawa ,ta bani kaya na saka ,sannan ta bani
abinci naci ,ta bani umarnini in tashi muje ,ko da muka fito ko ina tsit , haka ta rike min hannu ta
kaini wajen mararrabar yankin nasu ,ta bani kudi tace in mike wata hanya har tasha zata kaini in
hau motar garin mu in tafi ,saannan ta juya ta tafi ta barni ,na ci bakar wahala kafin in iso garin
sokoto ,ko da na iso gida babu wanda ya ganeni an dauka mahaukaciya ce,sai daga baya suka
gane nice ,asibiti aka kaini sannan aka hada da bani rubutu inasha ,sannan na dawo daidai ,sai
da kowa ya tausayamin a lokacin dana basu labarin abinda yafaru ,ni kuma tun daga lokacin na
tsani duk wani YARE ,in har ba hausa fulani ba ,......

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
Fulani cikin muryar kuka ta dubi mai mai martaba tace"kai kanka ka aureni ba tare da kasan
wannan labarin ba ,kawai dai kasan na taba yin aure mijin ya mutu",sannan ta dora da
cewa"wannan dalilin ne yasa na tsani YARE...!

Written by : ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 1:49 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~62~
Fulani ta cigaba da cewa 'ban baku wannan labarin ba domin kuji tausayi na....",murya a
sanyaye ummu ta katseta ta hanyar cewa " a gaskiya kin cancanci tausayawa domin kafiya da
kuma jayayya da iyaye ne ya jaza miki halin da kika tsinci kanki a ciki a baya ',mai martaba ya
dora da cewa'kuma wannan labari naki bai kamata ya zamo sanadin da zakiyi wa ko wanne irin
YARE wannan mugun kiyayyar ba,ita bolaji me tayi miki da zaki dauki fansar abinda mutanen
tsohon mijinki sukayi miki,bara in gaya miki gaskiya YARE baya taba zama mizanin da zaka
auna halin mutum dashi domin kuwa YARE daban halin mutum daban ,ko da zaki koma baya
cikin labarinki patrick mijinki bai cutar da ke ba ,kuma naga shima inyamiri ne kamar yadda
sauran mutanen garinsu suke,haka zalika matar da ta taimake ki ita ma inyamirar ce ,kin ga

kenan YAREn su daya halayyarsu daban daban ,inaso ki yi nazari da tunani ki gane cewa
YARE kalma ce kawai domin nuni ga harshen da mutum yake ji,kin ga annabinmu muhammad
sallallahu alaihi wa sallam ya kasance balarabe amma hakan ba wai yana nufin duk larabawa
amnabawa bane kamarsa,asalima ba gabadaya larabawa bane suka kasance musulmai
ba,kinga kenan YARE ba zai kasance ma'aunin auna halayyar dan adam ba ',ko da mai
martaba yazo nan a zancensa sai ya dubi hashim da bolaji yana cewa"ina mai baki hakuri bolaji
game da abubuwan da aka aikata a gareki ,ba dan ni ba dan Allah kiyi hakuri ki yafe musu
,domin Allah yana son bayinsa masu yafiya ',bolaji idanunta na fidda hawaye tace 'har ga Allah
na yafe musu',mai martaba yacigaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login