Showing 51001 words to 54000 words out of 61652 words

Chapter 18 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4045

zuciya sunyi miki jagora wajen alakanta kanki da
hashim a matsayin matarsa ta aure ,mujiba kin bani mamaki ,wato kwadayin dukiya da daular
sarauta sun sa zaki gujeni.... ',mamaki ne ya kama bolaji ,cike da firgici ta bude bakinta tana
cewa'hisham...',dakatar da ita yayi ta hanyar cewa 'baki da abin da zaki ce min mujiba
,everything is crystal cleared to me ,nagode mujiba ,rayuwa ce',bai jira jin ta bakinta ba ,ya fada
cikin mota ,ya tayar yayi reverse ,guards suka bude mai gate ,ya fice a guje! .
Bolaji kuka ne ya kwace mata sosai,kalaman hisham suna dada yi mata kuwwa a kwanyarta!,jiki
a sanyaye ta koma cikin gida !

A parlour tayi kicibis da fulani ,fulani ta rungumota tare da cewa 'mujiba kinyi min daidai da
kikayi denying proposal din sultan ,da yardar Allah baki da mijin da ya wuce souldear ',bolaji ba
tace uffan ba ta wuce kitchen tana matsar kwalla ,badiyya ce tashigo kitchen din ,ganin bolaji
tana kuka yasa takarasa gareta tare da dafata tana cewa 'lallai sultan yayi rashin hankali ,amma
koma menene laifinki ne da kika amshi soyayyarsa.....',wasu hadimai da kuyangu ne suka shigo
kitchen din da kayan wanke wanke niki niki ,hakan yasa badiyya tayi shiru ,su kuwa cewa suke '
a gaskiya mujiba kin yi ganganci ,kowa ganin rashin kyautawarki yake yi,sultan guda ya nemi
aurenki amma ki watsa masa kasa a ido ....,ko kallo basu isheta ba balle ta tanka musu,sultan
ne yashigo kitchen din a birkice ,sannan ya umarci kowa ya fice daga kitchen din ,he wants to
be left alone with mujiba ,bayan kowa ya fice ,sai sultan ya dubi bolaji idanunsa na zubda
hawaye yace 'why mujiba ? Please why ?',uffan batace ba ta yi hanyar ficewa daga kitchen
din,hannunta ya damko yana cewa 'babu inda zaki sai kin gaya min dalilin da yasa kikayi
denying proposal dina ',idanu jajir ta dubeshi tare da cewa 'saboda bana sonka ,na tsaneka ,na
tsaneka sultan',sultan baki bude ya tsaya kallonta ,cike da takaici bolaji tace 'ka cika min hannu
na ',sultan ya tattaro duk wani jarumta da ya rage , tare da cewa 'bazan cika ki ba ,har sai kinyi
accepting proposal dina,ko kuma mu dawwama a haka ni dake ',ganin da gaske yake bazai
cikata ba ,hakan yasa idanunta suka fara nema mataa mafita,hango wuka tayi a kusa dasu ,
daya hannunta tasa ta dau wukar sannan ta dora wukar akan hannunta da ya rike tana
cewa'wallahi tallahi mujiba can cut her hand and give it to you,but you can never have her "
,sannan ta fara dadirawa hannunta wukar ,ganin jini ya fara fita yasa sultan ya cikata ,yana mai
mamakin mujiba ,ita kuwa ta yar da wukar tare da ficewa daga kitchen bayan taja wani dogon
tsaki....

Written by: ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 11:47 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~58~
Da Taimakon Allah hisham ya isa gida ,yana shiga ciki, ya zarce dakinsa ,ya rasa me yake
masa dadi a duniya ,wai shi mujiba zatayiwa haka ,amma babu damuwa daman he saw it
coming tunda ta kashe wayarta baùa samunta yasan da walakin,yayi kuka sosai ,sannan ya
tashi yayo alwala ya gabatar da sallah hakan yasa yaji sanyi a zuciyarshi,daga karshe sai ya
kashe wayarsa gaba daya ,yayi kwanciyarsa ba tare da ya nemi kowa ba !

A bangaren bolaji kuwa ,daki ta shiga ,ta dauko wayarta ta fara neman wayar hisham ba tare da
tabi ta kan ciwon dake hannunta ba ,'the number u r trying to call is currently switch off",amsar
da matar network ke bata kenan,ta buga yafi sau ashirin ,amma amsa daya take maimaita
mata,jiki a sanyaye ta watsar da wayar,tare da fashewa da kuka mai ciwo, cikin wannan yanayi
badiyya ta shigo ta sameta ,"ke kuwa mujiba lafia kike kuka kamar wacce aka ce mata anjima
zata mutu ta shiga jahannama","badiyya ina zan sa kaina ,hisham ya juya min baya.....(nan ta
kwashe labarin yadda suka kwashe dashi dazu,ta fadawa badiyya),badiyya ta tabe baki tare da
cewa 'sai me?,ba shi ya jiyo ba,idan tayi wari shi ma zai jiyo ,ya kuma èakura ya bar wa yarima
matarsa ',bolaji ta kara sautin kukanta ,badiyya taja wata doguwar hamma tare da yin mika

,sannan tace 'idan kin gama kukan tarawa kai zunubi,sai ki tashi kije mijinki na kira ',bolaji a
fusace tace 'me kuma zanyi masa ?',badiyya tace 'ko ma me zakiyi masa ,ki tashi kije ,domin
amsa kiransa yafi wannan kukan da kikeyi lada ",bolaji tayi mursisi tace babu inda zata ,ganin
badiyya bazata kyaleta ba ,yasa ta tashi ta fice ba dan ranta yaso ba ! A bangaren sultan kuwa goma da ashirin ne suka hadar mai ,domin bayan bolaji ta fita ta
kyaleshi a kitchen,jiki a sanyaye ya fice shima ,a hanyarsa na zuwa dakinsa , fulani ta tareshi
tayi masa wankin babban bargo ,harda ce masa 'kaji kunya wallahi ,ni dana hada walima domin
murnar samun lafiyar d'ana ,saika maida min walimar wajen aikata abinda ka koyo daga gun
yahudu wa nasara ,ina d'an bahaushe kuma musulmi da proposing ,abinda ba al'adarmu bane
balle kuma addininmu ',sultan murmushin takaici kawai yayi tare da wucewa dakinsa yana
cewa a ransa 'daman umma ta san da Allah ,ta aikata abinda ta aikata ga bolaji'!
☆☆☆
Da sallama tashiga dakin ,a kwance ta iskeshi akan gado ,yana sanye da kayan bacci ,akan
stool ta zauna tare da cewa 'gani !',hashim ya tashi ya zauna sannan ya dubeta tare da cewa
'sai yanzu ?',ganin bazata tanka masa ba yasa ya cigaba da maganarsa kamar haka'abinda
kika aikata dazu a gun walima baki kyauta ba mujiba ,meyasa zaki yi denying proposal din dan
uwana? Why?',"saboda bana sonsa kuma bazan taba son sa ba',bolaji ta bashi amsa ,hashim
murya a kausashe yace 'ya zama tilas ki so shi domin,ni dinnan da kike burin mallaka ,bazaki
sameni ba domin zuciyata da gangar jiki na duk mallakin matata ne,kamar yadda na fada miki
dazu cewa ni da aure...',bolaji ta katseshi ta hanyar cewa 'ka daina yaudarar kanka hashim ,kai
ma bana sonka kamar yadda bana son dan uwanka ,kuma kai da kake ikirarin cewa zuciyarka
da gangar jikinka mallakin matacciyar matarka ce ,haka zalika nima tawa zuciyar da gangar
jikina mallakin.....',sai kuma ta kasa karasawa,idanunta suka ciko da kwalla ,hashim yayi dariya
sosai tare da cewa 'mujiba kenan dani dake wanene yake yaudarar kansa ,in har ba kya sona
meyasa kika bani kulawa da duk wani kula da mata take bawa mijinta?',sannan yayi dariya ya
kuma cewa'idan da babu so ko kauna ,hakan ba zai taba faruwa ba',murmushi bolaji tayi mai
ciwo tare da cewa "hashim kar ka dauka nayi duk wannan ne saboda so ,nayi ne kawai saboda
ina son in cimma wani buri ne a rayuwata",'wani buri kenan?',hashim ya tambayeta ,bolaji tace
'wannan kuma bai shafe ka ba ,yanzu kawai bukatarka shine in auri sultan ko?',hashim yayi
murmushi yace'zan fi kowa farin ciki da faruwar hakan',bolaji tayi murmushi irin na gatse
,sannan tace 'toh zan auri sultan bisa sharadi guda daya tak','wanne sharadi kenan?',hashim ya
tambayeta ,bolaji ta amsa da cewa 'sharadin shine ina son ka rubutawa tsohuwar matacciyar
matarka takardar saki',a hargitse murya a kausashe hashim ya katseta ta hanyar cewa 'how
dare you ?',bolaji tace 'dakata malam in gama magana,saki uku zaka rubuta ,ni kuma na maka
alkawari idan har ka cika wannan sharadi zan auri dan uwanka ( a zuciyarta tace 'hisham
kenan') ,hashim ransa a bace yace 'mujiba da ace ina iya tafiya da wallahi babu abinda zai
hanani tasowa in zo sharara maki mari,kin haukace ne ,matar tawa kike son in saka ,never
over my dead body wallahi',bolaji ta tafa hannunta tace 'aww ho ,matacciya kenan,ka kasa
sakar matacciyyar matarka ,ta ya kake son ni kuma in rabu da rayayyen masoyina ,ka ga kenan
ba zata sabu ba ',hashim ya dubeta idanu jajir tare da cewa'wai shin mujiba ,me cece alakarki
da matata da kike alakanta ta a cikin sharadinki',bolaji ta tashi tsaye tare da cewa 'wannan
kuma baza kaji daga bakina ba ,sai da safe ',tana gama fadin haka ta fice ,ta bar hashim da
bacin rai ,ji yake tamkar ya tashi ya sha'kota ya sha'ka mata kamshin lahira!

* * *
Written by : ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 11:47 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~59~
Washegari da safe bayan an gama yin karin kumallo,mai martaba yayi wa sultan fada sosai
game ga dabi'ar yahudu wa nasara dayayi a gun walima a daren jiya,sannan kuma ya ja masa
kunne akan cewa kar ya kuskura yace zai takurawa yar mutane wajen tilasta mata ta aureshi
,ita ma fulani tazo da bukatar ta na son a hada auren mujiba da hashim,mai martaba ita ma
yace mata baya son fa a tilastawa wani ko wata in dai maganar aurene idan har suna son
junansu ,su zo su fada masa ba wai itace zata yanke hukunci ba ,don haka magana ta mutu kar
a kara tada ita!

A bangaren ummu kuwa tunda asuba ta bugawa MD waya tare da bashi umarnin ya je ya
shaidawa bamidele da nawwara su zo sokoto a yau dinnan domin warware wani boyayyen
al'amari game da bolaji!
Ko da MD yaje gidansu bamidele ya shaida masa sakon ummu,babu bata lokaci ,yace nawwara
ta shirya zasu wuce sokoto!

Misalin karfe 11:00am ummu ta nufi dakin fulani ba tare da rakiyar ko wacce hadima ba ,ko da
ta shiga dakin,fulani ta tarbe ta da fara'a tare da tambayarta dafatan lafiya ,ummu tace 'wata
muhimmiyar magana nakeson muyi ,amma ina son ki sallami hadimanki',cikin 20secs gaba
daya hadiman suka fice daga dakin, Bayan sun fice , sai ummu ta murzawa kofar dakin key ,tare da karasawa gun fulani ,fulani
kuwa tuni tasha jinin jikinta ,amma bata gama shan jinin jikinta ba sai da ummu tace 'fulani ki
dubi girman Allah da manzonsa sallallahu alaihi wa salam,ki fada min gaskiya ,meye faru a
ranar da muka fita rangadi da mai martaba ?",fulani bakinta na rawa tace 'naja'atu wacce irin
tambaya ce wannan,ni ban gane abinda kike nufi ba ,meye faru kuwa ',ummu ta ja numfashi
,murya a tausashe tace 'abinda nake nufi shine ina son sanin gaskiyar abinda ya faru game ga
al'amarin batan bolaji ?',fulani duk sanyin a.c da ya gauraye dakin,sai da zufa ya fara keto mata
,a fusace ta fara cewa'haba naja'atu wacce gaskiyar kike nema bayan guduwar da yarinyar
nan,dalilin haka ta riski mutuwarta na kuma tsinto gawarta a asibiti',ganin yanayin fulani yasa
ummu ta fara yarda da cewa zancen mujiba akwai alamun kamshin gaskiya ,sanin cewa fulani
ba kanwar lasa bace yasa tace 'zan kara tambayarki a karo na karshe ,ki gayamin
gaskiya....',cike da masifar wanda hausawa suke cewa tabarmar kunya.....,fulani ta juyawa
ummu baùa tana cewa 'wai shin me kike nufi ne naja'atu ,wani irin titsiye ne wannan,kina nufin
nice nake da sa hannu game da bacewarta daga fada?',ummu ta amsa mata da cewa 'ba wai
ina nufi bane ,ni ina da tabbacin cewa kece ki kulla duk wani kulle kullenki game ga bacewarta
daga fada ',a zafafe fulani ta juyo tana cewa 'amma naja.....', ji kake TAS! wani wawan marin
bazata ummu ta zabgawa fulani ,wanda hakan yasa fulani ta katse maganar da zatayi tare ta
dafe kumatunta tana kallon ummu cike da mamaki,'ni kika mara ?' Fulani ta jefeta da
tambayar,ummu tace 'eh na mareki ,kuma zan cigaba da marinki idan har bazaki fada min

gaskiya ba,domin babu mutuncinki da kuma darajarki na kasancewarki uwargida da ya saura a
cikin idanuna',fulani ta daga hannunta zata rama marin da ummu tayi mata,amma ina.... ta
makaro ,domin ummu hannunta na hagu tasa tayiwa hannun fulani dam'kar karfi,tare da kuma
zabga mata wani lafiyayyen mari da hannunta na dama ,fulani hawaye fal idanunta tace 'akan
me zaki mare n....',ummu ta kara zabga mata wani marin tare da cewa 'zaki fadamin gaskiya ko
kuwa ba zaki fada ba',fulani kuka ne ya kwace mata gashi kuma ta kasa kwatar hannunta
,murya a cunkushe tace 'wai wani gaskiya .....',kafin ta karasa furucin,ummu ta zabgeta da wani
hadadden marin ,fulani fuska tayi jajawur kamar tattasai ,amma bakinta fadi yake 'ni fa wallahi
babu sa hannuna ga batan gwolaji daga fada ',wasu maruka ummu ta kara zabga mata hagu
da dama tare da cewa 'tunda bazaki fada min gaskiya ba ,.ni kuma bazan gaji da marinki
ba',Tas ! TASS!! TASS! TASS! ,ummu ta cigaba da zabge kumatun fulani da lafiyayyun maruka
,wanda a kirge sunfi goma,fulani ganin ba sarki sai Allah,in ba tayi da gaske ba ,zawo da fitsari
zasu iya kufce mata don azabar zafin mari,ba shiri ta fara labartawa ummu duk wani makirci da
ta kulla game da batan bolaji !
Ummu kanta ne yayi mugun kullewa ,mamaki ne ya cikata domin ba ta taba zaton kiyayyar da
fulani take yiwa YARE ya kai wannan matsayin ba!
Cike da bakin ciki da takaici ummu ta cika mata hannu tare da nuna ta da yatsa tana cewa'tir da
halinki fulani ,kin zama shaidaniya fulani,saboda mai imani ba zai taba aikata abinda kika aikata
ba,fulani wallahi nayi dana sanin baki dana kyauta ,domin kin salwantar da rayuwarsa ta
fuskoki da dama,kin sashi yayi sanadiyar mutuwar iyayen yarinya,ta Allah ta kasance yarinyar
ta zama matarsa duk da haka baki kyaleta ba sai da kikayi sanadinta ,wanda hakan ya jawo ya
shiga wani hali,haba fulani ,kar fa ki dauka bana kaunar d'ana ,kara da kawaici kawai nake
domin ke ma ki na kaunarsa ,amma kaunar da kike masa makaho ne ,tunda ba kya sara kina
duba bakin gatari ,kuma abin takaici shine yadda ki ka hada baki da nawwara da sultan wajen
aikata wannan mugun aiki,mecece fa'idar ki na aikata hakan,shima sultan din da kika haifa da
cikinki ba ki bashi tarbiya ba ,ashe ni ina gyara kina warwarewa ,fulani wallahi baki cancanci a
kira ki da sunan uwa ba ko kadan,sannan kuma ko ba komai nawwara tata tayi kyau ,tunda har
dan uwan bolaji ya zama mijinta i shikenan,wannan kadai ya isheta ishara ',fulani kuka take
tana cewa'naja'atu bazaki ta ba ganewa ba....',ummu ta katseta ta hanyar cewa 'daman ba zan
taba ganewa ba mana,amma ki kwana da sanin cewa ,za'ayi walkiya ,kuma xa'a ganki ,ke ma
kuma zakiga bolaji',ummu na gama fadin haka ta nufi kofa ta murza key tare da ficewa daga
dakin ,ta bar fulani tana rawar dari ,domin har wani zazzafan zazzabi ne ya dirar mata ,cewa
kawai take 'na shiga uku ,oh ni 'yasu ,kar dai gwolaji tana raye ?',ba shiri ta haye kan gado ta
kwanta tare da lullube kanta da bargo dalilin sanyi sanyin zazzabi da ya addabeta ,ga kuma
fuskarta da ke yi mata zogi da radadin zafin marukan da bata taba shansu a rayuwarta ba!"

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/19, 11:48 AM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~60~
Ko da hadimai suka shigo ,tsawa ta daka musu da cewa su fice su bar ta ita kadai!
Ummu tana fitowa daga dakin fulani ,sai ta umarci hadimanta da suje dakin nawwara su kwaso

duk wani kayan bolaji da fulani tasa akai wa mujiba dakin,su dawo dashi dakin hashim,ko da
hashim ya ga ana shigowa da kaya ,sai ya nemi yaji dalili,ummu ta amsa masa da cewa'kayan
matarka ne ,ummanka ta kyautar dasu ga mujiba,shine na ce a dawowa da matarka kayanta
,tunda mujiba ba ta cikin jerin mutanen da zasu ci gadonta",bata jira jin ta bakinsa ta fice daga
dakin,bayan hadimai sun gama kwashe kayan daga dakin nawwara sai kuma ummu ta
umarcesu da cewa ,su gyara dakin!
A bangaren bolaji kuwa badiyya ce tasa ta a gaba da cewa 'ki bani adireshin gidansu hisham in
je ni in warware masa zare da abawa,tunda naga kin damu kanki da batunsa'",bolaji ta bude
bakinta da niyyar bawa badiyya amsa , shigowar wata hadima dakin ne ya katse mata
zancenta,hadimar ta dubi bolaji tare da cewa wai taje ummu na nemanta,bolaji ta dubi badiyya
,sannan ta dubi hadimar tare da cewa 'gani nan zuwa',bayan hadimar ta fice sai bolaji tace
'badiyya don Allah tashi muje ki rakani','ke fa aka ce tana kira .....',bolaji ta katseta ta hanyar
cewa 'da Allah na hadaki fa',badiyya babu yadda zatayi ba dan taso ba ta tashi suka fice !

Ummu ta dubesu tare da cewa 'mujiba magana nakeson muyi ni da ke game da maganarki da
mukayi a baya",ummu ta gama fadin haka tana mai kallon badiyya ,bolaji ta ce 'kar ki samu
damuwa ummu, badiyya ita ma ta san komai',ummu tace 'shikenan!' Sannan ta dubi badiyya
tare da cewa ' badiyya tashi ki rufe kofar da mukulli',bayan badiyya ta aiwatar da haka ,cike da
nutsuwa ummu ta fara labarta musu yadda ta kasance tsakaninta da fulani ,sannan kuma ta
dora da cewa'a gaskiya bolaji zuwan d'ana cikin rayuwarki ne ya jawo miki duk wani tsanani
da kika tsinci kanki a ciki,amma ki sani duk hakan ya faru ne dalilin fulani,kuma bawa a kullum
ba ya gujewa kaddararsa,ina son ki dauki komai ki daura akan mizanin kaddara,wanda nake
fatan hakan ya rinjayi kiyayyar da kike wa hashim ,ki hakura ki cigiba da zama dashi a matsayin
mijinki ,domin a gaskiya baki da masoyi da ya wuce shi',bolaji idanunta cike da hawaye tace
'ummu kar ki ga laifina ,kuma bana son ki dubi maganar da zanyi miki a yanzu a matsayin
rashin kunya ,a gaskiya bana miki kallon suruka face kallon uwar da ta haifeni,ummu zuciyata
bata taba son hashim ba,ni kaina tsoron kaina nake ,har ga Allah na yafewa hashim abunda
yayi min a rayuwa ,amma har yau bana jin soyayyarsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login