Showing 39001 words to 42000 words out of 61652 words

Chapter 14 - YARE BIYU COMPLETED BOOK HAUSA NOVELS .pdf

Nil   

01 Jul 2025

4057

ISMA'IL
[10/17, 5:59 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~45~
Hisham ya tari numfashin bolaji ta hanyar cewa 'alright amma duk da haka ya kamata mu jira
ko nan da shekara d'aya ne kiyi regaining memory dinki,kar azo a aikata aikin dana sani!
Bolaji tayi amanna da batun ,amma a zuciyarta ta kud'iri aniyar cewa ko da tayi regaining
memory dinta,hisham will always be hers!
* * *
Tsaftacciyar Soyayya ce tayi karfi tsakanin bolaji(mujiba) da hisham wanda su kansu suna
masu mamakin junansu ta yadda ko wannensu baya son yaga koda kud'a ya taba waninsu!
zuhra da zahra sunji dadin faruwar wannan al'amari,haka zalika hajiya da daddy!
A kullum addu'arsu shine 'Allah yasa mujiba(bolaji) tayi regaining memory dinta '!
* * *
A bangaren nawwara da mijinta bamidele,suna gudanar zallar soyayya a gidan aurensu ,wanda
nawwara a kullum take mamakin wai itace da auren YARE ,Allah kenan! Tsakaninta da

funmilayo kuwa ,aminci yana nan daram ,kuma a kullum sai bolaji ta fado mata a rai ,
ji take kamar ta shaidawa mijinta komai ,ta gaya masa gaskiya,amma zuciyarta tana kwa6arta
da cewa kar ta kuskura ta yi wannan gangancin in har ba so take aurenta da bamidele ya zamo
mushe ba !

*BAYAN WATANNI BAKWAI*

A firgice bolaji ta farka daga bacci bakinta d'auke da salati ,jikinta sai kyarma yake, hannu ta
dora akan goshinta saboda azabar radadi da kanta keyi mata ,a cikin wannan yanayi zuhra ta
shigo ta sameta ,da hanzari ta karasa ga bolaji tana mai cewa 'menene mujiba? what's wrong?'
, da kyar bolaji ta bud'e baki tace'kaina ne ke ciwo' ,zuhra tace'ayya bara na gayawa hajiya ,sai
a kira doctor' ,tana gama fad'in haka ta tashi ta fita daga dakin !
Bayan shudewar minti biyar sai ga zuhra ta dawo dakin tare dasu hisham da hajiya ,hajiya ta
rungumo bolaji tana mai cewa 'sannu mujiba' ,sannan ta dubi hisham tace ' bugawa doctor
ayuba waya mana,yazo ya dubata',hisham murya a sanyaye yace 'na kira wayarsa amma not
reachable', bolaji tace'dont mind ,ya ma daina ciwon,daman tun lastweek ne idan na kwanta
bacci,sai nayi mafarkin da zaiyi sanadiyar farkawata da kuma ciwon kai!' ,gaba dayansu suka
hada baki tare da cewa 'MAFARKI?' ,'wani irin mafarki ?' Hisham ya jefa mata tambayar,bolaji ta
amsa masa da cewa 'wani katon gidane mai kyau da kayan alatu, sai kuma wani mutum a
kwance a wani daki, rufe yake ruf da farin kyalle, macizai sunyi masa dabaibayi ,kalmar MY
BETTER HALF yana fita daga bakinsa,da zarar nasa hannu zan yaye farin kyallen da ya rufe
masa fuska ,sai na farka',sannan ta cigaba da cewa 'amma fa kar ku damu fa its just a dream!
Hajiya tace'ya kamata dai kiga doctor domin........',bolaji ta katse hajiya ta hanyar cewa 'am
fine wallahi,kar ku damu' ,hajiya tace'shikenan toh,sai ki tashi kishirya ,ki fito ki yi breakfast kafin
malaminku ya iso " ,hajiya ta tashi ta fice ,zuhra da zahra suka bi bayanta !
Hisham ya dubi bolaji yace 'are you sure ba abin da ke damunki,ko dai still in kira doctor?', bolaji
ta mi'ke tsaye tare da cewa ' i'm fine and ok ,dont mind my love',sannan ta fada'a toilet!
Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:19 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~46~
Cike da hanzari bolaji ta watsa ruwa ta fito ta shirya ,ta fita tayi breakfast a gurguje ,domin
malam har ya iso!
Misalin karfe 5:00pm hisham ya dawo daga wajen aiki , bolaji ta gabatar masa da abinci da abin
sha ,bayan ya ci ya sha yayi hani'an sai ya wuce daki ya cire kayansa tare da watsa ruwa,batun
mafarkin bolaji ne ya tsaya masa a rai ,domin anashi hasashen yana ganin tamkar mafarkin
yana da ala'ka da asalin mujiba(bolaji),amma ko ma menene yana ganin ya zama tilas ya 'kara
tarar ta da batun ,saboda sanin wacece ita da kuma asalinta ne kad'ai zai zamto sila ga cikar
burinsu naganin sun zama ma'auratan juna!
* * *
A bangaren sultan kuwa tun daga ranar da suka hadu da mujiba(bolaji) a mall ya rasa sukuni
,gashi kuma watanni sun ja ,ya rasa ta inda zai fara nemanta,hakan yasa ya zama kamar wani

zautacce ,duk inda yaga mace fuskarta dauke da niqab ,sai yasa hannu ya yaye niqab din ,akan
haka har mari yasha ,da kuma duka daga gun mazajen wasu matan,amma duk da haka bai
daddara ba ,domin har ila yau bai fidda tsammanin sake haduwa da ita ba!
Capt. Yarima hashim ! Allah sarki! Har yanzu dai yana nan dai kwance tamkar matacce ,sai dai
yayi haske ya 'kara kyau ,har yar 'kiba yayi!
Fulani kuwa ta d'aura aure da kuka,takaici da kuma ba'kin ciki,a kullum ta dubi hashim sai ta
zubda hawayen bakin ciki da tausayi,mai martaba da ummu a kullum nasiha suke mata da bada
baki akan cewa 'cuta da waraka duk na Allah ne!

* * *
Misalin 8:50pm na dare Bayan Dad da hisham sun dawo daga masallaci ,a kitchen hisham ya
iske bolaji ita dasu hajiya suna hada hadar had"a abincin dare ,dubanta yayi tare da cewa ' ina
son muyi wata magana after we finish eating dinner' ,bolaji ta amsa da 'alright!'! Hajiya ta
dubeshi tare da cewa 'd'an nema a gabana kake cewa d'iyata tazo zance gunka ko?', hisham
yana sosa keùa a kunyace ya amsa da cewa 'hajiya ba fa zance nace tazo guna muyi
ba,magana zamuyi ,wato zamu dan tattauna ne....', yana gama fadin haka ya fice ,su zuhra da
zahra suka kwashe da dariya ,zahra dake yanka kankana a bowl tace ' yaya sham kenan,ashe
rana irin ta yau zata zo da zai kara yin soyayya da wata bayan marigayiya',zuhra ta cafke da
cewa'ita ma wannan din dai mujibar ce dai,ko kinga bambamci ne?', zahra tace'babu wani
bambamci ,kawai dai waccan ta rasu ,wannan kuma tana raye ',bolaji ta hararesu tare da cewa
'enough ,ya isa haka,ku ba kwa ganin abu ,ku ja bakinku kuyi shiru ko?,toh dai hisham is meant
for mujiba, wether she or me..' ,hajiya ta amshe da cewa 'tell them my daughter,hisham naki ne'
tare da yin murmushi,a take bolaji ta ryfe fuskarta domin taji kunya sosai,su zuhra kuwa sai
tsokanarta suke,a haka dai suka kamalla hada dinner !

A balcony bolaji taje ta samu hisham yana jiranta,sallama tayi tare da mi'ka masa glass cup
mai d'auke da ruwan dabino mai sanyi,amsa sallamar yayi tare da karban glass cup din yana
cewa 'sai yanzu ?','i'm sorry dear,kayan da aka gama cin abinci dasu muka wanke',bolaji ta
bashi amsa a sanyaye,hisham yace 'its ok,daman game da mafarkin nan nakeso in
tambayeki',bolaji tace 'i'm all ears', hisham ya kurbi ruwan dabino sannan yace ' gidan da ki
kace kin gani a mafarkin,ke a ganinki zaki iya tunawa ko kin san gidan ,as in a gaske?, 'no'
bolaji ta amsa tare da cewa'but i don't know if gidan is related with my identity',hisham yace'may
be ,amma a yanzu ina son ki min kwatancen yadda gidan yake ,as in the building and
everything',bolaji tayi jim tana tunani sannan ta yatsine fuska tare da cewa 'toh dai the house is
huge ,something like a mansion or a castle..' sai kuma tayi caraf tace 'why not in zana maka
gidan kawai ,i can draw it!',hisham ya yi dariya tare da cewa 'are you sure that u can draw it'
,'yes my love ,i can ,or are u trying to under estimate me?' ,hisham ya gimtse dariyarsa tare da
cewa 'no my dear,lets go to the study room!
suna shiga studyroom hisham ya dauko farar cardboard paper da biro bic ,ya mika mata biro din
tare da spreading cardboard paper din akan table,sannan yace 'oya mujiba start drawing',bolaji
kuwa ta takarkare ta fara zane ,sai da ta shafe minti 20 ta rasa me zata zana ,hisham kuwa
yana gefe yana gumtse dariyarsa,wutar nepar da aka d'auke ne yasa bolaji ta gimtse idanunta
,a take gidan da take mafarki ya bayyana a bangon kwakwaluwarta(brain) ,hakan yasa a take

yatsun hannunta suka fara sarrafa biro , zanen gidan ta fara tiryan tiryan,hisham kuwa ganin an
dauke nepa yasa ya ciro waya daga aljihunsa ya kunna musu haske,ganin bolaji ta dage tana
zane idanunta a rufe yasa yayi mutuwar tsaye yana duban fuskarta ta hasken da wayarsa ke
fitarwa ,bolaji na gama zana gidan,ta bud'e idanunta,a take nepa suka dawo da wuta,dubanta
takai ga hisham tare da cewa 'yes ! Ga gidan na zana',idanunsa hisham ya kai ga zanen yana
mai 'karewa hoton zanen gidan kallo,idanuwansa ya ware don tsabagen mamaki,bakinsa na
rawa ya furta kalmar 'MO..DIBBO..'S PA...LACE!'

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~47~
Fuskarta dauke da alamun tambaya ta dubi hisham tana mai tambayarsa cewa 'shin daman
akwai wannan gidan a gaske?', yatsanta na nuni ga zanen da tayi,hisham ya amsa da
cewa'tabbas akwai wannan gida gaske ,kuma wannan gida babban masarauta ce dake cikin
yankin yabo,to cut the story short ,few days back naje palace din dubo abokina wanda kusan
lokaci daya aka kwantar dashi da ke a asibiti ,yanzu haka he is still in coma ,dalilin
mutuwar matarsa!',sai kuma hisham yaja numfashi tare da cigaba da cewa 'duk ba wannan ba
,wai shin meye had'inki da masarautar modibbo da har zaki ga masarautar a mafarkin ki?',bolaji
ta amsa da cewa 'nima amsar tambayar da zuciyata take muradin samu kenan',sai kuma ta
cigaba da cewa 'baka ganin wannan masarautar tana da ala'ka da asalina ,zan iya kasancewa
d'iya ko kuma .....',hisham ya katseta ta hanyar cewa 'sai dai ki kasance baiwa ko kuma
kuyanga ,domin babu d'iya a wannan masarauta,asali ma yaya maza guda biyu ...(nan ya
kwashe takaitaccen labarin asalin masarautar modibbo da ya sani ,ya labartawa bolaji)!
Bolaji ta numfasa sannan tace'shikenan kawai,mafarki ba gaskiya bane....',hisham ya tari
numfashinta ta hanyar cewa'tabbas mafarki ba gaskiya bane ,amma ni a hasashena ina ganin
cewa akwai wani boyayyen al'amari game da mafarkinki,ya zama dole ni da ke mu kai ziyara ga
masauratar ,'kila ziyartar masarautar ya zama sanadin dawowar memory dinki',bolaji ta yarfa
hannayenta tare da cewa 'alright,sai kasa mana rana muje ', hisham ya dubi agogon wayarsa
sannan yace'shikenan yanzu dare yayi muje mu kwanta,ranar lahadi insha Allah sai muje,amma
fa ina son wannan maganar ya zama sirri a tsakaninmu,saboda ina son mu bi komai a
sannu',bolaji ta amsa da 'toh my dear',hisham ya dauki cardboard paper din ya nad'e,sannan
suka fice daga study room din!
*RANAR LAHADI*

Misalin karfe 10 na safe bolaji sanye take cikin doguwar baby pink abaya tare da hijab rose
pink,sai kuma niqab ,hisham a shirye yashigo falo tare da duban bolaji yana cewa'are you
set?',bolaji ta amsa da 'yes',hajiya ta dubesu tace 'wai shin ku biyu zakuje asibitin,idan ni
bazakuje dani ba ,ko zahra ce sai ta raka ku....',hisham ya katse hajiya ta hanyar cewa 'hajiya
wai shin baki yarda dani bane ?',hajiya ta girgiza kanta tana cewa 'ba wani abu nake nufi
ba,kuje kawai ,Allah ya tsare',bolaji da hisham suka amsa da 'amin',zahra da zuhra suka musu
rakiya izuwa harabar gidan ,hisham ya fito da mota ,bolaji ta shiga ta zauna ,bala direba ya

bude gate,hisham ya harba mota waje ,sai masarautar modibbo!

Hisham ya dubi bolaji da tayi shiru tunda suka hau kan titi,sai yayi gyaran murya tare da jifanta
da tambayar 'are you nervous?',murya a sanyaye bolaji ta amsa da cewa 'no i'm just
scared','scared' hisham ya maimaita,bolaji ta amsa da 'yes i'm scared ,coz bansan me zamuje
mu tarar ba,ina tsoron rasaka hisham,ina tsoron inyi regaining memory dina ,inzo in kasance ni
baiwace mai munin asali',gefen hanya hisham ya samu yayi parking ,sannan ya dubi bolaji tare
da sa hannu ya daga niqab din dake kan fuskarta,ganin hawaye acikin idanunta yasa
yace'mujiba me kike tsoro ,idan kin kasance baiwa ,toh meye zai faru?,bolaji ta amsa da cewa
'shin hajiya da dad zasu kyaleka ka auri baiwa',hisham yayi murmushi mai ciwo sannan yace
'mujiba kenan,baki san yadda nake jinki a zuciyata bane,shiyasa kike fadan haka,amma ina son
ki sani cewa ni hisham naki ne har abada,haka zalika ke tawa ce,mutuwa ce kad'ai zata iya
rabamu mujiba ',sannan yace 'ki share hawayenki ,you have to be strong,saboda regaining
memory dinki kadai me zai sa mu mallaki junanmu a matsayin ma'aurata,kuma a shirye nake in
fuskanci ko wanne irin hukunci a kanki,in har hukuncin bai zo da kaddarar rabuwar mu ba
,mujiba ina tare da ke,kuma zan cigaba da kasancewa tare da ke a ko da yaushe',bolaji tayi
murmushi tare da goge hawayen idanunta tace 'nagode my life,you mean alot to me,i will
forever be grateful to you!', hisham yayi murmushi sannan ya tada mota suka cigaba tafiya,suna
masu bayyanawa juna SO !

Written by: ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~48~
Ko da suka iso gaban fada sai bolaji taji kanta yana juyawa ,jiri na d'ibar ta ,hakan ya janyo
sanadiyar fitar 'innalillahi wa inna ilaihi raji'un' daga bakinta ,hisham ya dubeta yana cewa 'lafia
mujiba?',da kyar ta iya budan baki tace 'kaina yake min wani iri',da sauri hisham ya samu waje
nesa da fada yayi parking tare da juyowaya fuskanci mujiba ,wacca tuni ta sume ,ganin alamu
bata motsi yasa ya yaye mata niqab dinta ,tare da dauko ruwa a back seat ,ya shafa mata a
fuska,ajiyar zuciya ta sauke tare da bude idanunta ,hisham cike da tausayawa yace 'sannu!'
bolaji ta amsa da 'yawwa','do u remember anything?' Hisham ya tambaya ,bolaji ta amsa da
'no,but its like am gettin a little flashback,shiyasa kaina ya dinga min wani iri da naga palace
din',hisham yace 'toh yanzu ya zaayi mu shiga ciki ko kuma mu koma gida nr ?,coz ina tsoron
kar brain dinki ya takura',bolaji tace 'kar ka damu my love ,tabbas gidannan yana da alaka da
my past and identity,amma ba zan iya tabbatar da haka ba sai nayi rayuwa acikin gidan, wanda
a hankali zan gano wacece ni?',hisham yayi jim yana tunani ,sai kuma ya sauke ajiyar zuciya
sannan yace'eh toh hakane kam,da ace asalin fuskarki gareki da ko hoto sai nayi miki in shiga
in nuna musu ko shin zasu san wacece ke ,amma yanzu matsalar shine ta yaya zaki yi rayuwa
a gidan ?,gaba dayansu suka yi shiru suna masu tunanin mafita ,bayan minti 30,sai kawai
hisham ya tada mota tare da cewa' muje ciki i will come up with a plan'!,mujiba tasa hannu ta
cire niqab din ,ta ajje a gefe,a yayin da hisham ya iso gate palace yana horn,royal guards suka
fito ,ganim cewa shine sai aka bude masa gate ya shiga da motarsa ,bayan yayi parking,suka

fito daga motar,guest parlour aka yi musu izinin shiga ,bayan sun zauna sai hisham ya nemi
izinin a yi musu iso gun fulani,ita kuwa bolaji ware idanu ta yi tana kallon duniya,sai da suka
shafe minti 40 suna zaman jira ,sannan kuyanga badiyya tazo tayi musu jagora zuwa royal
parlour ,suna shiga fulani da ummu suka tadda a zaune ,ganin hisham ya russuna yana mika
gaisuwa ,hakan yasa bolaji itama ta russuna tana mika tata gaisuwar,fulani ta amsa cike da
fara'a tana cewa 'tashi ku zauna mana ,ashe kaine kazo ' hisham kuwa a kasan ya zauna ,haka
yasa ita ma bolaji ta zauna tana mai zare idanu,tufafin dake jikin fulani da ummu ne suka bata
shaawa,ummu ta dubesu tana cewa 'sannu hisham,kana kokari zuwa duba abokinka,Allah ya
bada lada',cike da ladabi hisham ya amsa da 'amin',fulani kuwa tace 'duk cikin abokan souldear
wannan kad'ai ke zuwa dubashi lokaci zuwa lokaci,daman baka sanin masoyanka zai musiba ta
sameka ",sannan ta kai dubanta ga bolaji tana mai tambayar hisham 'wannan kanwarka ce?',
hisham ya amsa da 'eh kanwata ce',fulani tayi murmushi tare da yafito bolaji tana cewa 'yan
mata zo nan kusa dani ki zauna', a kunyace bolaji ta zo ta zauna tana mai jin nauyi ,ummu tace
'yanmata ya sunanki?', 'mujiba' bolaji ta amsa ,fulani tace 'lallai kin amsa sunanki',ummu tayi
murmushi ,hisham yayi gyaran murya,yana mai kara russunawa ,ya dubi fulani tare da cewa
'ranki ya dade daman wata y'ar alfarma nazo nema ',fulani tace 'alfarma ?wacce iri?',hisham ya
kara russunuwa cikin tsara kalamai daki daki yace 'daman wannan 'kanwar tawa ce za'ayi wa
aure,shi wanda za'a aura mata d'ane ga yayan mahifinmu ,ita kuma bata sonshi sabida dan giya
ne,amma iyayenmu sun rantse sai anyi auren,ita kuma rannan sai naji hirarsu ita da kawayenta
tana cewa zata gudu ta bar gida in yaso ta shiga duniya, ni kuma naga da akan hakan ya faru
gwara na nema mata mafita ,shine a yau na yanke shawara muzo in nema mata aiki a nan,in
yaso sai tayi zamanta a fada tana muku hidima ,nasan cewa idan ba a ganta ba zaa hakura da
zancen auren,idan komai ya lafa sai nazo in dauketa in maidata gida',ummu cike da tausayawa
tace 'Allah sarki ,dan uwa mai dadi',fulani tayi caraf tace 'yanzu wannan zukekiyar yarinyar za'a
yiwa auren dole a wannan zamanin ,lallai wasu iyayen akwai karfin hali', sannan ta dafa bolaji
tana cewa 'kayi tunani mai kyau da ka kawota nan,amma fa baza'a amshe ta a matsayin
hadima ba',hisham ya zare idanu cike da fargabar wargajewar plan dinsa ,zai bude baki yayi
magana fulani ta katseshi ta hanyar cewa 'kar ka samu damuwa ka bar min ita ,zan ri'keta
tamkar d'iyar dana haifa!'

Written by :ABDULAZIZ ILILEE ISMA'IL
[10/17, 8:20 PM] ‪+234 806 079 4214‬: =YARE BIYU=
[ 2tribes ]
na ILILEE
~49~


Hisham me zaiyi in ba ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login